BA NI DA MADOGARA

Chapter 20

by @narrnarhhbukar00

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*











*Ba ni da Madogara*
  (Sai Allah...)




 
    
020

Gaban kowa sai faɗuwa yake yi suna tunanin meke faruwa ne haka da za a tara manyan mutane da kuma ƴan gari, wani tashin hankali daya matuƙar gigita ƙwaƙwalansu shi ne *Gawawwaki* ne har biyu a kwance an rufesu da zani da alamu gawawwakin na yara ne. Kafin su ƙarasa sai yarinyar Zaliha ta rugo da gudu ta faɗa  jikin mahaifiyarta tana matsanancin kuka duk da ƙaracin shekarunta, jijjigata Zaliha ta fara yi  hankali a matuƙar tashe tana faɗin

"Baraka! Baraka lafiya waya rasu? meke faruwa ne?" 

Cikin kuka Baraka ta ce

"Mamaaa idanun Ɗahiru aaaaka ciree, gashi can yyayyanaa bacci..."

Bata ƙarasa abin da ta yi niyyar faɗa ba ta sake fashewa da matsanancin kuka. Lokaci ɗaya ƙwaƙwalwar Zaliha ta tafi wucin gadi na ɗan wasu sakanni,komai ya tsaya mata cak! Ji take duniyar na  mata juyin waina. Wata razananniyar ƙara ta saki tare da ɗora hannayanta sama tana faɗin

"Wayyoooooo Dahiru naaaaaa!!! Na shiga uku na lalace"

Kafin Murja ta gane meke faruwa sai kawai ta tsinci Zaliha ta falla a guje zuwa wurin gawawwakin, kafin ta yi wani motsi sai ta ji wani sabon ihu na tashi daga bayanta kamar haɗin baki, matar mai unguwa ce amaryarsa ita da wasu mata a bayanta tana gudu zuwa wurin da aka ajiye gawawwakin. Kafin Zaliha ta iso wurin mutane suka hanata zuwa sai haƙuri suke bata, ita kuma ta tirje sai ta je wurin gawawwakin. Suna a haka amaryar mai unguwa ta iso wurin da gunjin kukanta, wasu yara ne suka sanar mata abin da ke faruwa, sai bata yi ƙasa a gwiwa ba ta nufa wurin tare da maƙotan da suke mutunci. Isarta wurin ita da maƙarrabanta keda wurin Zaliha ta yaye zanin da aka lulluɓe gawawwakin. Tashin hankali wada ba a saka masa rana, tuni ta zube warwas a ƙasa sumamma, ita amaryar mai unguwa yaronta ta rumgumo tana sake fashewa da matsanancin kuka mai rasa jini da ɓargon duk wani mai sauraronta. Duka gawawwakin yaran an ƙwaƙule musu idanu, da alamu ba idanun kaɗai aka ƙwaƙule ba har da wasu sassan jikinsu, sosai amaryar mai unguwa take rungume da ɗanta tana kuka. Zaliha kuwa mata ne suka taimaka aka cicciɓeta zuwa cikin gidansu sai Murja ya yayyafa mata ruwa a jiki amma shiru babu motsi. Nan da nan ta kira wayar innar Zaliha da Kawu ta sanar musu abin da ke faruwa. Cike da ɗimautuwa suka ce gasu nan zuwa, babu wanda a garin hankalinsa bai tashi ba,domin duk rashin imaninka idan ka yi arba da gawawwakin yaran nan dole hankalinka ya yi ƙololuwan tashi. 

A can daidai wata gindin bishiyar mangwaro na hangi mai unguwa da Alhaji Zakari suna tattaunawa, kowanne ka duba fuskarsa shimfiɗe take da damuwa haɗi ta tashin hankali. Cike da tsantsan tashin hankali mai unguwa ya dubi Alhaji Zakari ya ce

"Zakari mun shiga uku kar dai a ce da saka hannun mai gidanka Alhaji Sambo dala a wannan aikin?" 

Alhaji Zakari daya lula duniyar tunani ya yi saurin juyowa ya zube masa jajayan idanunsa ba tare da ya ce komai ba, sake tambayarsa mai unguwa ya yi,kamar ba zai tanka masa ba sai kuma can ya fara magana cikin raunin murya mai nuni da damuwa haɗi da ɓacin rai. 

"Nima karan kaina abin da nake tunani ke nan mai unguwa, bana zargin kowa sai shi saboda a kwanankin baya ya kirani akan Hujayrah ta gudo gida, wasu suka ce masa ni da kaina da ɗauketa na ɓoye, alhalin bansan komai a kai ba" 

"Ikon Allah shi banda abinsa ma taya za ka ga Hujayrah ba tare da ka kira ka sanar masa ba, ni tsorona kar wata rana ya sake cewa zai farmaki ahalinmu fa" 

Cije lips da ƙarfi Alhaji Zakari ya yi kafin ya ce wani abu ya ji wayarsa na ringing. Ba tare da ya kawo komai a ransa  ya ciro wayan. Sunan wanda ya gani a screen ɗin wayar ne ya saka hantar cikinsa kaɗawa. Mai unguwa ne ya dubesa ya ce

"Zakari ɗauki kiran mana ko so kake ya yanke" 

"Alhaji Sambo Dala ne ke kiran" 

Wato idanunsa mai unguwa ya yi waje yana faɗin

"Toooh Allah yasa ba wani sabon mugunta yake da shirin haɗa mana ba" 

Kafin kiran ya yanke Alhaji Zakari ya ɗauki kiran tare da yin sallama, a can Alhaji Sambo Dala ya bushe da dariya yana cewa

"Zakari to ya kake ganin wasan da daɗi ko? " 

Gumi ne ke kwaranyo wa Alhaji Zakari yana gogewa don ya tabbata da matuƙar wuya Alhaji Sambo Dala bai sake kai wa iyalansu wani sabon farmakin ba. Ya rasa ina zai saka rayuwarsa ya ji daɗi. 

"Yallabai wallahi tallahi summa billahil azim Idan na san inda Hujayrah take Ubangiji ya ɗauki raina a yanzun nan. Yallabai bazan taɓa maka ƙarya ba ko ni karan kaina za ka hallakar sai dai ka hallakar don bansan inda Hujayrah take ba, Duk wanda ya faɗa maka ya ganni na ɗauki Hujayrah na gudu na ita to sharri yake bi na da shi, Yallabai ka yarda dani" cewar Alhaji Zakari yana matsar ƙwalla. 

Shiru Alhaji Sambo Dala ya yi yana tunani, anya Alhaji Zakari yasan inda Hujayrah take kuwa domin idan yasan inda take to lallai da ya yi gaggawar ɗaukota a yau ganin kisan wulaƙancin da ya saka su Nasir suka yi ma yaransu. Akwai wata ƙasa Alhaji Zakari bai san komai ba to amma ya ake yi Nasir ya ce wasu sun ce masa sunga lokacin da ya gudu da Hujayrah,this just sound so confusing. Can Kuma ya ce

"Shikenan na ji batunka zan sake bincike idan baka da hannu a ɓatanta fine I will set you free amma idan aka sake tabbatar min da akwai hannunka a ciki, believe me Zakari sai na yi maka illa mai munin gaske kai da mai unguwar garinku don nasan akwai nasa haɗin bakin, that's why from initial na ce su haɗa da yaronsa. Zan sake bincike "

Kit! ya yanke kiran, wani sanyi Alhaji Zakari ya ji a ransa ko babu komai da alamu ya ɗan yarda da maganarsa. Juyowa ya yi yana duban mai unguwa ya ce

" Mai unguwa da alama Alhaji Sambo Dala zai duba mana "

Taɓe baki mai unguwa ya yi sannan ya ce

" Zai dai duba maka ba ni ba, ai laifinka ne ya shafe ni har ya taɓa ɗana ban ji ba gani ba, kai da ba ma yaronka ya taɓa ba har kake da bakin magana" 

Sakin baki Alhaji Zakari ya yi yana duban mai unguwa wai yau shi yake gaggasawa maganganu. Girgiza kai kawai ya yi sannan ya ce

"Bari ka ji mai unguwa koda ba yarona aka kashe ba amma ka sani wannan yafi duka yarana ƙima da daraja, don ina matuƙar ƙaunarsa fiye da yarana kai in taƙaice maka ni da yarona aka kashe wallahi bazan wani damu..." 

"Baka da hankali ne Zakari!!" cewar mai unguwa yana katse masa magana. Shima Alhaji Zakari hayayyaƙo masa ya yi yana cewa

"Da hankalina sarai mai unguwa! ba ƙarya na yi ba nafi son Ɗahiru fiye da yarana su dukkaninsu" 

Sauri riƙe bakinsa mai unguwa ya yi yana cewa 

"A'uzubillahi anya uwarsa bata tsubbuceka ba kuwa Zakari?" 

Wani wawan tsaki Alhaji Zakari ya ja sannan ya ce

"Kaga mai unguwa yanzu ba lokacin wannan zance ba ne, taso muje ayi wa yara wanka mu kaisu gidansu na gaskiya" yana  maganar yana tafiya, biyosa mai unguwa ya yi a baya yana mamakin canjawar amininsa, duk da ba yanzu yake ganin canjawar tasa ba, tun lokacin da ya saki Hannatu saki ɗaya yasan da walakin goro a biya, ba haka nan amaryarsa ta barsa ba. Yana wannan zancen zucin har suka iso inda mutane suke.Nan da nan aka yi wa yara wanka sai aka sallacesu daya bisani aka kaisu gidansu na gaskiya. Bayan an dawo sai kowa ya zauna a wajen gidansa don amsar gaisuwa. 

A can cikin gidansu Alhaji Zakari suman Zaliha uku ana yayyafa mata ruwa tana farfaɗowa, don da ta farfaɗo bata minti biyar take sake sumewa, duk ta yi wujiga-wujiga da ita, har da wata ƴar rama ta yi saboda tashin hankali. Su mammin Hujayrah da Fatsima suna sashenta har da Kakulle ta shigo,ba a maganar Murja wacce kuka take yi sosai tana taya ƴar uwarta alhini. Yaran gidan mata waɗanda suke aure sunzo don labarin ya kai garesu, kan ka ce me gidan ya cika da ƴan uwa da abokan arziƙi, duk da ba kowa yasan Zaliha ba sai dai jin Alhaji Zakari take aure sannan ƴar uwar Murja ce yasa matan garin zuwa gidan. Kawu Isa da matansa har da wasu daga cikin yaransa sun iso, ba a daɗe ba Innar Zaliha da sauran yaranta suka zo. Gidan kam babu masaka tsinke, masu kuka na yi masu jajantawa na yi, har da masu gulma da tsaigumi duk suna yi.

Haka aka kwana uku ana amsar gaisuwa daga bisani mutane suka rage zuwa gidan. Zaliha ta zamo kamar wata kurma babu umm babu um-um sai dai kallo, ko abinci bata ci sai Murja ta tursasata. Alhaji Zakari kuwa tun lokacin da ta ganshi a ranar da aka yi rasuwan bata sake tozali da shi ba har kusan kwana uku da rasuwan, da yake a ɗakin Hannatu yake kwana tun lokacin baya so ya takura mata. A daren yau Zaliha ta shirya tunkarar Zakari a yi ta ta ƙare, zunbulelan hijabi ta saka kamar wata matar liman ta shiga ɗakin babu ko sallama. A zaune yake ya yi tagumi tare da ƙurama wuri guda ido yana karanta wasiƙar jaki ya ji tsayuwan mutum a kansa. A hankali ya ɗago da jajayan idanunsa ya kallonta ba tare da ya ce komai ba. Taɓe baki ta yi sannan ta riƙe ƙugu tana masa kallon ƙiyayya ta fara magana cike da rashin kunya

"Zakari na zo a yau ba sai gobe ba ka bani takardar sakina, auran na fasa don bazan sake rayuwata da na ƴan marayun yarana ba cikin wahala da tashin hankali" 

Sheƙeƙe ya tsaya yana kallonta babu ko ƙifta idanu, sosai ya shiga mamakinta don yadda yake mutuwar so da ƙaunarta yana tunani ko Kakulle ta umurcesa akan ya saketa, ba zai saketa ba sai dai idan tsine masa za ta yi. 

"Ni da ke mutu ka raba takalmin kaza, Zaliha idan kinga na rabu da ke to ki tabbata a ranar nabar duniya, ke ɗin wata jigo ce a rayuwata wacca nake kallo na yi farin ciki, ko uwata bata kai ki daraja a idanuna ba" Alhaji Zakari ya ce yana sakar mata wani sassayan murmushi mai narkar da zuciyar wanda ake bege. 

Madadin Zaliha ta yi farin ciki haɗi da murna jin Alhaji Zakari ita ce kaɗai a cikin zuciyarsa, Ina ai wani malololan baƙin ciki ne ya taso mata tun daga ƙahon zuciyarta bai tsaya ko'ina ba sai a daidai maƙogoranta. Kuka ta saki babu shiri tuno da kisan wulaƙancin da aka yi wa ɗanta duk saboda tana auran Alhaji Zakari, sai yanzu ta tuna da shawarar da Boka mai zamani ya bata akan auran Alhaji Zakari,shikenan son abin duniyarta ya ja mata rasuwan babban ɗanta. Sosai take kuka har da cire hijabi tana ajiyewa gefe, miƙewa Alhaji Zakari ya yi yana ƙarasowa wurinta yana faɗin

"Haba masoyiyar Alhaji Zakari, wa ya taɓa min ke a duk garin nan ya fuskanci tsattsauran hukunci, zo Zalihatuwataaa a yau ba sai gobe ba zamu sake samun Ɗahiru ƙarami kinn ji babyta ". Yana maganar yana kamo hannunta, da sauri ta fizge hannunta ta watsa masa mugun kallo har da urguɗa masa baki. 

" Wallahi bazan zauna da kai ba gobe zan bar maka gidanka na fasa auran, ka maido da uwar gidanka don ni bazan bari silar zamana da kai yarana su mutu ba, na tsaneka Zakari! Wallahi na tsanekaaaa!" 

"Ni kuma ina sonki Zaliha! Ina mutuwar so da ƙaunarki wanda zan iya rasa raina idan kika gujeni, tunda kina son Hannatu ta dawo shi ke nan zan maido da ita amma saboda kin buƙaci hakan ne, amma sakin da kike buƙata na yi miki wannan kuma ba za ki taɓa samu ba, don kamar yadda na faɗa miki aurena da ke sai mutu kaɗai ce za ta rabamu "Alhaji Zakari ya ce yana sake kamo hannunta. Kamar an jona ma Zaliha wutar lantarki ta ji a lokacin da ya riƙe hannunta. Babu shiri ta sake fizge hannunta ta janyo hijabinta ta saka tare da goge hawayen sa suke rige-rigen sauka daga idanunta. 

" Wallahi tallahi bazan zauna da kai ba koda kuwa mutuwa za ka yi sai dai ka yi wannan bata shefeni ba, ana kammala sadakar bakwai zan bar maka gida koda baka sakeni ba" cewar Zaliha tana barin ɗakin. Komawa saman kujerar da ya taso ya yi, a hankali ya zauna kamar mai jin tsoran kujerar kar ta karye, hannu biyu ya tallabo haɓarsa ya tsurama ma wuri guda ido. Sosai ya shiga tashin hankali jin sahibarsa Zaliha na shirin guduwa da barsa, babu abin  da ya kai wannan tashin hankali a wurinsa, bai ƙi ya rabu da kowa ba har da uwarsa indai Zaliha za ta haƙura ta zauna dashi. Ya rasa wani irin makahon so yake yi wa Zaliha wanda lokaci guda ya ɗarsu a cikin zuciyarsa. Haka ya ci gaba da saƙa da warwara daga bisani ya wuce uwar ɗaka ya yi kwanciyarsa bayan ya kashe wutar ɗakin. 

A ɓangaren Zaliha bayan ta koma ɗakinta wani sabon kukan ta saki, ta yi kuka sosai kamar ranta zai fita. Da yake sauran yaran nata sun yi bacci sai ya zamana babu wanda yasan ta yi kukan a cikinsu. Ta daɗe tana kuka daga bisani ta kwanta a kusa da ƙaramar yarinyarta tana tuno Ɗahirunta wanda a duk lokacin da ya ganta cikin damuwa sosai hankalinsa ke tashi, wani lokacin har ya yi kuka idan ya tambayeta ta ƙi bashi amsa. Ta ɗau alƙawarin ba za ta faɗawa kowa abin da take shiryawa ba koda mahaifiyarta ce balle Murja. Da zarar an yi sadakar bakwai za ta tattara yaranta su koma Ƙwarin ɗan dodo, duk abin da za a mata ba za ta dawo wannan gidan ba sai dai ya mutu. Haka nan ba za ta saka kanta da yaranta cikin bala'i ba, sai yanzu take da na sanin rashin bin shawarar Innarta, boka mai zamani, Kawu Isa da Murja, musamman boka mai zamani da ya ce mata akwai wasu bala'i kala-kala da suke shirin tunkarar Alhaji Zakari sannan ita abin zai shafa ba uwar gidansa ba, tun ba a je ko'ina ba ta rasa Ɗahiru daga auranta ko wata ɗaya ba a yi ba. Sosai ta yi zurfi a cikin kogin tunaninta, ƙarar agogo ta ji alamun dare ya tsala, wayarta ya kunna tare da duba lokaci, waro ido ta yi waje ganin 12:01am na dare, mamaki ne ya cikata ganin har lokaci ya ja, kashe wayar ta yi sannan ta gyara kwanciyarta, daga bisani bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita babu zato babu tsammani... ✍️

          🌎🌎🌎🌎🌎🌎

Kai kawo yake yi a bedroom ɗinsa, ya rasa meke masa daɗi a rai, ɗan guntun lissafin da ya rage masa ya ɓace, hannunsa a goye yana safa da marwa. Can kuma ya tsaya cak! Ya ce

"Kina inaaaaa!" 

Babu mai bashi amsa kasancewar shi kaɗai ne a ɗakin, tun bayan wayar da ya yi da Alhaji Zakari hankalinsa ya dugunzuma ya yi ƙololuwan tashi, ke nan Hujayrah bata ƙauyen, to ina ta tafi ne? A ina zai ganta tun kafin hukuncin DODO ƘURNUSSA ya sauka akan shi, gashi lokacin da aka ɗibar masa akan ya kawota ƙungiya ya kusa, bai fi ƴan kwanaki ba. Wuri ya samu a saman sofa ya zauna tare da share zufar da ta tsattsago masa a saman goshinsa. Ciro wayarsa da ke gaban aljihunsa ya yi. Kai tsaye ya shiga contact ya fara scrolling, numban da yake buƙata ya yi dialing, ringing biyu wayar ta yi aka ɗauka. 

"Nasirrrr!" Alhaji Sambo Dala ya kira sunan a ɗan zafafe. 

Nasir da hantar cikinsa ta fara kaɗawa tun lokacin da yaga kiransa ya amsa masa cike da girmamawa 

"Nnaa'amm Boss" 

Wata nauyayyar ajiyar zuciya Alhaji Sambo dala ya sauke sannan ya fara magana 

"Tell me the truth Nasir shin kun ga sanda Zakari ya gudu da yarinyar? kasan Bana son ƙarya ko" 

Daram! Dam! Dadammm! Sosai zuciyarsa ta buga, tsoro da firgici suka ɗarsu a cikin zuciyar, babu abin da yake tunani illa ahalinsa, kar ya faɗi gaskiya Boss ɗinsa ya illata su don kaɗan daga cikin aikinsa ne wannan. 

"Yallaɓai mu ma wasu a garin ne suka faɗa mana, ba da kanmu muka ga lokacin da ya gudu da ita ba"  Nasir ya faɗa yana goge zufa a goshinsa . 

Shiru Alhaji Sambo Dala ya yi kamar ba zai ce komai ba sai kuma can ya ci gaba da cewa

"You guys a not even sure ya gudu da ita ma, Mts! I'm so disappointed in you Nasir. Yanzu dole a canja salon nemanta, Ina tunanin da wuya bata cikin garin Bauchi,Habib da Black scorpion squad za su ci gaba da nemanta a nan, what I want you to do now is Ku ci gaba da neman yara tare da tafiya da su Maiduguri don a kai su ƙungiya, bana son a samu matsala koda sau ɗaya ne, Understood? "

" Yes Sir! " Nasir ya ce fuskarsa a washe, ko babu komai alamu sun nuna ba zai masa komai ba. Daga haka ya yanke kiran... ✍️

            🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Ƙungiyar Black Pythons Society*
*ƙarfe 1:35am na dare*

Kamar yadda al'adar ƙungiyar take, bayan members sun hallara daga baya Demon King da DODO ƘURNUSSA a suffarsa na maciji suka bayyana, kai tsaye suka nufi  kujerarsu ta mulki. Shiru wajen ya yi baka cin motsin komai sai sautin kukan mujiya wanda babu daɗin ji balle sauraro.

"Linkakuuuuuu!!!!" Demon king ya kira cikin amon muryarsa mai firgitarwa. 

Alhaji Sambo Dala da ke cikin layi zuciyarsa na lugudan bugu tun bayan zuwan Demon king da DODO ƘURNUSSA sai ya sake kiɗimewa, don yasan yau kam zai kwashi kashinsa a hannun tun da ya gaza kawo Hujayrah ƙungiya. Jiki na rawa ya fito daga layin yana ranƙwafar da kansa alamun gaisuwa. Yatsarsa  manuniya Demon king ya nuna Alhaji Sambo dala tare da lanƙwasa yatsan yana kallon sama. Kamar almara wuyan Alhaji Sambo dala ya ji kamar an shaƙesa sannan ƙafarsa  ta bar ƙasa. Hannu bibbiyu Alhaji Sambo Dala yake riƙe wuyansa yana kakarin amai, amma kamar ƙara matse wuyansa ake yi, idanunsa sun fiffito, jijiyoyin kansa sun yi raɗo-raɗo, ba a maganar fuskarsa don kamar jan gauta haka ta koma kasancewarsa fari. Ya daɗe a wannan mawuyacin halin daga bisani Demon king ya sake yatsansa, ji kake sharafff! Ya faɗi ƙasa kamar kayan wanki, haki yake yana sauke numfashi akai-akai kamar wanda ya yi tseran gudu. Kamar saukar aradu ya ji Demon king na magana wanda cak! Ƙwaƙwalwarsa ta tsaya da aiki na ɗan wasu sakanni, babu shiri ya ɗago jajayan idanunsa daga duƙyen da yake ya zubesu a fuskar Demon king. 

"Linkakuuuu! Dole ka fuskanci hukunci mai tsanani!!!  Hukuncin zai faɗa kan ƴarka wacca tafi soyuwa a gareka nan da kwana biyu!!! Babu ban haƙuri balle sassauci!!!  Kana cike ranar da muka ɗiban maka akan kawo yarinyar ƙungiya to a ranar hukuncin ƙarshe zai sauka a gareka, DODO ƘURNUSSA zai duba idon da halin ƙara maka kwanaki" cewar demon king yana miƙewa tsaye. 

Sauran members ɗin russunar da kawunansu suka yi cike da tsoro haɗi da fargaba, sun san hukuncin ƙungiya babu daɗi, idan ta kama har kisa mutum zai iya fuskanta ko kuma ahalinsa. 

Tashin hankali wanda ba a sa masa rana, haƙiƙa Alhaji Sambo dala bai taɓa shiga tashin hankali wanda yake kallon mutuwarsa a nan kusa  irin wannan. Yasan hukuncin ƙungiya babu sauƙi, gashi  ƴarsa Sabrin wacce yake mutuwar so da ƙauna hukuncin zai sauka akanta, bata ji bata gani ba, ba isasshen lafiya ta cika ba kasancewar tana da sickler. Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro masa a bisa kuncinsa, miyau ya haɗiye mai ɗacin gaske ji kake muƙut! Har Adam apple ɗinsa na ƙasa da sama. A sanyaye ya miƙe daga duƙyen da yake ya shiga layi kamar sauran members. 

Rukunun mutanan da suke kawo musu jini da pepper soup ɗin sassan jikin mutane sun kawo kamar kodayaushe, sun ci sannan sun sha daga bisani kowa ya ɓa ce zuwa gidansa sai gidan ya nutse cikin ruwa...✍️

             🌎🌎🌎🌎🌎🌎

Alhaji Sambo dala bai bayyana a ko'ina ba sai a saman katafaren gadonsa. Kamar a ƙaya ya sauka, wani irin juyi ya yi tare da wuntsilowa ƙasan carpet,jikinsa na rawa ya miƙe cikin sassarfa ya isa wardrobe ɗin gadonsa, wayarsa ya ɗauko ya shiga contact ya yi scrolling sunaye, a letter H ya tsaya daidai sunan Habib, dialing numban ya yi, ringing ɗaya-biyu a na ukun aka ɗauki kiran. Cike da tashin hankali ya fara magana

"Habib duk inda kuke a faɗin Nijeriya, Inaso zuwa gobe na ganku a secret house, Sannan ka sanar da Nasir ya zo da mutanansa na Kaduna complete, sai Chukwuze da gangs ɗinsa, I want them all tomorrow, in fact duk yarana da kasani waɗanda suke a different states I want to see them tomorrow "

" OK Sir" cewar Habib gabansa na faɗuwa don bai taɓa jin muryar uban gidansa a haka ba. Yana gama basa umarni ya katse kiran, cilli da wayar ya yi, lokaci ɗaya ya fara parade a tsakiyar ɗakinsa, kamar wani zautacce sai faman yamutsa suman kansa yake yana bubbuga kansa. Ya ɗauki mintuna kusan uku yana kai kawo a ɗakin daga bisani ya shiga haɗadɗan bayinsa ya watsa ruwa, yana fitowa yabi lafiyar gado da yake matarsa Hajiya Mariya ba a ɗaki ɗaya suke kwana ba, sai idan yana da buƙatuwa da ita yake zuwa bedroom ɗinta ko ita ta zo nashi. 

Washe gari da yamma Alhaji Sambo dala ya tafi secret house ɗinsa inda ya taɓa kawo Hujayrah ta gudu. Ya samu yaransa kowa ya zo har da waɗanda suke nesa. Bayan ya kowa ya matso kusa dashi sai ya fara musu bayani cike da gargaɗi tare da barazana. 

"Wannan aikin da za ku yi mai hatsari ne because idan baku yi wining ba to I assure you guys a painful life or your families will be affected, akwai yarinyar da na kawota gidan nan ta gudu, I don't really know her name but the gurl is unique, tana da idanu daban wanda babu mai irinsa a duk faɗin Nijeriya. Her eyes are green and she is dark in complexion, Ina so ku nemomi yarinyar nan a garin Bauchi da kuma hanyar Kaduna, that's the only place nake tunanin tana wurin, har cikin dazuzzuka da villages nake so ku shiga. Duk wanda ya yi nasara nemota ko kuma rukunin da suka nemota, I promise them a huge amount of money as a gift. Sannan idan kuka kasa nemota Hmmmm abin da zai zo daga baya You guys won't like it. Ku maida hankali daga yau zuwa jibi i want her hereeee!!! "

Cike da girmamawa suka amsa masa a tare har da sara masa kamar wani soldier. Daga haka Kowa ya kama hanyarsa yana addu'a zamantowa shi ne zai kawo Hujayrah don ya samu kyautar da Alhaji Sambo dala ya yi alƙwarin zai bada... ✍️

         🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Gidan Professor Abdulrahman Saminu Kwankiyal*

A ɓangaren Hajiya Nafisa tun bayan Hujayrah ta cire waɗannan abubuwan da aka birne a gidan wata shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninta da mijinta Prof, sosai suke shan soyayya kamar wasu sabbin amare. Bayan kwana shida da faruwar haka, Hajiya Nafisa ta fara rashin lafiya wanda ya tada hankalin prof sosai, yaso su je asibiti amma taƙi haka nan ya haƙura. Da rana za ka kanta lafiya lau tana harkokinta kamar ba ita ba, amma yamma na yi masassara za ta yo mata sallama, duk abin da ta ci a nan take amansa. Su Mas'ud da Nazima hankalinsu ya tashi sosai ganin yadda mahaifiyarsu take shan wahala amma sun yi da ita su je asibiti taƙi. 

Abin da basu sani ba shi ne, hankalin Hajiya Nafisa a tashe yake domin tsoro take ji, aje asibiti a dubata likita ya ce ciki gareta don shi take tunanin take da shi duba da har yanzu bata ga al'adar ta ba. Shi yasa take kawai basarwa tana shan maganin saukar da zazzaɓi. Yau dai duk yadda ta so dojewa akan zuwa asibiti hakan ya faskara don Prof tasata a gaba ya yi suka fito, a hankali suke tafiya har suka isa parking space, a daidai lokacin Hajiya Zinatu ta danno kan motarta cikin gidan kasancewar gate ɗin gidan a buɗe yake. Tana haɗa ido dasu gabanta ya faɗi, kai tsaye ta wuce parking space ta ajiye motarta. Suna tsaye har ta yi parking ta fito, cike da tsantsan bariki ta saki murmushi tana ƙarasowa inda suke tana faɗin

"My Prof Sai Ina Haka?" 

Ba tare da ya kawo komai a ransa ba ya ce

"She's sick so za mu je yanzu mu ga likata" 

"OK I see, Allah ya ƙara afuwa" tana maganar tana wucesu. 

Shiga motar suka yi ya taga sannan suka bar gidan, private hospital ɗin da ake dubasu ya kaita, bayan gwaje-gwajenm da ƴan wasu tambayoyi da likitan ya yi wa Hajiya Nafisa, sai ya ɗibi jininta ya aika dashi lab. Kasancewar suna mutunci sosai da likitan sai kawai ya ce su zauna a office ɗin su jira sakamako. Babu musu saku zauna jiran medical lab scientist. Bayan kusan rabin awa sai lab scientist ta shigo da result ɗin. Amsar result ɗin ya yi ya duba, lokaci guda ya saki murmushi yana ɗagowa ya miƙa wa Prof hannu, shima miƙa masa hannu ya yi duk da bai san meke faruwa ba. 

"Congratulations Prof matarka na ɗauki da ciki na tsawan sati daya da wasu awanni, we are very lucky da muka gano a cikin ƙanƙanin  kwanaki" cewar likita yana sake sakar wa Prof murmushi. 

Waro idanu Prof ya yi waje don mamaki, lokaci guda kuma ya saki murmushi yana sake shaking hands da likita. 

"Allahu Akhbar!! Alhamdulillahillazi bi ni'imatihi tatimmul salihat, Maa shaa Allah. Tabarakallah, wooooooh ya Rahman!!! Likata har na man rasa abin faɗa because ina cikin farin ciki sosai wanda na gaza misaltawa, yau My Nafy keda ciki Alhamdulillah!" ya yi maganar yana rungume Hajiya Nafisa. Ita kuwa duk kunya ta lulluɓeta don har ta fara harsashe kowa ya ganta da ciki tsofai-tsofai da ita. Sassanyar murmushi ta sakar masa, shima ya mayar mata da martanin murmushin, likita dai ya zama ɗan kallo, sai faman aikawa junansu kallo soyyaya suke har sun manta a idan suke. Gyaran murya likata ya yi yana dubansu, sai a sannan ne suka tuna a inda suke.

"Ga result na test ɗin sannan za ku je pharmacy siyan magani, bayan haka dole Hajiya ki kula da kanki sosai, banda aiki mai yawa If possible ki daina aiki har sai cikin jikinki ya yi ƙwari" 

Jinjina masa kai ta yi sai Prof ya amsa takardar suka bar Office ɗin baya ya yi wa likita sha-tara ta arziƙi. Kai tsaye suka nufi pharmacy suka biya kuɗin magani, daga nan suka zarce accountant office suka biya kuɗin asibiti wanda daga nan suka taho gida zuciyoyinsu cike da farin ciki. Suna isa main falo suka tarar da Hajiya Zinatu a zaune tana kallon Tv, ganin kowannansu da murmushi a fuskarta yasa ta gaza haƙuri ta tambayi Prof da cewa

"My Prof naga kowannanku fuskarsa ɗauke da murmushi, nima a faɗa min what's going on da ya saka ku farin ciki sai mu yi tare" 

Gyara babbar rigarsa ya yi yana sake sakin wani ƙasaitaccen murmushi ya ce

"Laila na gab da samun ƙani" 

Bata fahimci mai yake nufi ba sai ta sake cewa

"Ƙani kamar ya ban gane ba" 

Bai kawo komai a ransa ba ya ce

"Ina nufin Nafisa na da juna biyu so kinga ke nan Laila na gab da samun ƙani" ya ƙarashe maganar yana sakar wa Hajiya Nafisa murmushi har da kashe mata ido,turo baki waje Hajiya Nafisa ta yi don a haƙiƙanin gaskiya bata so Prof ya sanar wa Hajiya Zinatu ba, tafi so kawai sai dai ta ganta da cikinta. (Ohhh nii Narrnarhh Bukar 🤭yau naga abin da yafi ƙarfina, Ashe haka kake Proff🤭🤭🤭). 

Kamar wacce aka soka wa mashi mai matuƙar kaifi da tsini a ƙahon zuciya haka ta yi sauri dafe daidai saitin zuciyarta, lokaci guda gabanta ya yanke ya faɗi.cike da ƙarfin hali ta dubi Prof ta ce

"Allah ya inganta" tana gama maganar ta ɗauki wayarta ta wuce part ɗinta fuuuu! Kamar tashin iska. Da kallo suka bita daga bisani suka ƙarasa part ɗin Hajiya Nafisa. 

Da gudu-gudu da isa sashenta, kukan da take riƙewa ta saki tun kan ta shiga falon. Tana shiga falonta ta shire ɗan kwalin kanta tana susar kai tana kuka, zaman ƴar bori ta yi tana sambatu iri-iri kamar mai tashin jinnu. Sai faman rantsuwa take tana girgiza kai tana cewa

"Saina ɓarar da cikin nan!!! Baki isa ki haihu na Prof ba, Prof nawa ne ni kaɗai! Ƙarya kike wallahi!!! Na rantse da Izo hamsin-hamdin sai na ɓarar na cikin nan koda kuwa zan koma ina yawo tsirara ne!!! Yeeeeee!!! Na shiga uku ba lalace ni Zinatuuuu!!! Wuuuuuuu!!! Dole na koma wurin bokaaaa dole ne!!! "

Tana a zauna ta ɗauki wayarta, hannunta na rawa ta kira Hajiyan sama, ta daɗe wayar  tana ringing har sai da ta kusa yankewa Hajiyan Sama ta yi picking, da yake bata kusa da wayan kasancewar gobe da rana Khalil zai dawo Nijeriya, tana can tana shirye-shiryan dawowansa. Kamar jira Hajiya Zinatu take yi Hajiyan sama ta ɗauki kiran. Kuka ta sake fashewa tana cewa

"Aminiya na shiga uku ba lalace, shikenan lokacin mutuwata ta zo" 

Cike tashin hankali Hajiyan sama ta waro idanu kamar tana ganinta ta ce

"Meke faruwa ne Aminiya, yau mun shiga uku mun lalace" 

Hajiya Zinatu bata tsaya komai ba ta labarta mata duk abin da ke faruwa tun daga haukan ta Rayyan yake yi da kuma tunanin  wani ya haƙo asiran da ta birne har zuwa yau da Prof yake ce mata Hajiya Nafisa na da ciki. Sosai Hajiyan Sama ta shiga tashin hankali don ba kawai ƙawa ta ɗauki Hajiya Zinatu ba, jinta take a jininta kamar ƴar uwarta, komai ya shafeta dole ita ma ya shafeta. Fara kwantar mata da hankali Hajiyan Sama ta yi tana cewa

"Aminiya ki kwantar da hankalinki Nafisa bata isa da haihu da Prof ba domin Prof naki ne ke kaɗai, bai kamata a ce kin ɓoye min tun farko ba, ai da tuni munyi wa tufkar hanci. Yanzu ma dai ba latti muka yi ba zuwa jibi sai mu shirya tafiya wurin boka Turnuss, gobe Khalil zai dawo kinga kuwa babu halin fita sai jibi, Ni ma goben da daddare zan bijiro wa Alhaji batun auran Fauziyya da Arqam sai Khalil da Nazima, Ina fatan ya amince da auran nasu duk da bani da haufi a kai"

Sai yanzu hankalinta ya ɗan kwanta tuno da aikin bokan nasu na daban ne, ko a cikin bokaye da matuƙar wuya a samu irin nasu don ya daɗe yana musu aiki ba tare da an samu matsala ba. Sun daɗe suna waya daga bisani suka yi sallama... ✍️

         🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Gida dubi, Gubi housing Estate, Bauchi state. Nijeriya*
*Ƙarfe 2:24pm na rana*

A daidai wannan lokacin Arqam, Mas'ud da Mahmoud suna zaune a secret zone ɗin Arqam suna tattaunawa a kan batun Hujayrah. Mas'ud ne ke bayani hannunsa riƙe da biro yana zane a takardar da ke saman centre table, su Arqam da Mahmoud sun maida hankalinsu kacokar suna kallon abin da yake zanawa yana musu bayani. Jinjina kai kawai suke suna kallon rubutun da yake yi. Bayan ya kammala rubutun da bayanin sai kowa ya sauke ajiyar zuciya. Miƙa Mas'ud ya yi yana salati tare da lanƙwasa yatsun hannayansa lokaci guda suka bada sautin Ƙas! Ƙas! Ƙaƙass! Dubansu ya yi sannan ya ce

"Kunsan yanzu haka yaron Uncle Ayyub (Alhaji Sambo dala) is My friend?" 

"How did you make him be your friend Mas'ud?" a sanyaye Arqam ya yi maganar kamar an yi masa dole. 

Murmushi mai ƙayatarwa Mas'ud ya yi sannan ya ce

"Bro wai ka manta How I use to be ne?, kasan na faɗa muku akwai wanda na samu ɗan uwansa yaron Uncle Ayyub ne, so bayan na sakar masa kuɗi ya bani labarin abin da ɗan uwan nasa yake yi wa Uncle Ayyub daga baya ya haɗani dashi, amma ban nuna masa ni DSS officer ba ne, sai dai na ce masa ina so na shiga harkarasu idan zai iya taimaka min. What's surprise me is that, wai  akwai sharaɗi  babba  idan mutum yana son zama yaron Uncle Ayyub, shawara ya bani kar na shiga, shima yana so Allah ya cireshi daga wannan halakar da yake ciki. Friends guest what! "

Cike da zaƙuwa Mahmoud ya ce

" All ears Mas'ud, wallahi ka cika jan labari da tsayo har kasa mutum zaƙuwa"

Dariya Mas'ud ya yi sannan ya ce

"Kai kuma ga ka da shegen son labari kamar mace, Ok Let's keep that aside. Yanxu haka mun zama abokai da yaron sunansa Habib, kuma yana ɗaya daga cikin manyan yaran Uncle Ayyub wanda yake ji dasu, kaga kuwa abubuwa za su zo mana da sauƙi" 

"Good job bro Allah ya dafa mana, hmmm amma fa akwai matsala" cewar Arqam yana tamke fuska. 

"matsala kuma? Wace kala?" cewar Mas'ud yana duban Arqam da kyau. 

"Jiya Abba yake sanar min da an saka ranar aurena  da  Tahseen nan da sati biyu" 

Waro idanu waje Mas'ud da Mahmoud suka yi, kamar haɗi baki a tare suka furta

"Sati biyyyyuuuuu!!!" 

Jinjina musu kai ya yi fuskarsa shimfiɗe da damuwa. 

"Amma gaskiya I'm not happy at all, Tahseen fa! Haba don Allah, yarinyar da take cikin ƙungiyar ƴan lesbian ita da Sakhiyya, me yasa su Ammie suka zaɓeta" cewar Mas'ud rai ɓace. 

"Ashe kaima ka sani ke nan" faɗin Arqam yana miƙar da ƙafafunsa. 

"Wani abu ne ban sani ba akan Tahseen, Sakhiyya har da ma Fauziyyan Hajiyan Sama, ita ma Fauziyya da kake ganinta ƴar ƙwaya ce sai dai ta ɓoye halinta, Nima wani abokina Musa yake faɗa min saboda shi aikin NDLEA yake yi, so a wani patron da suka je wani night club ya ga Fauziyya a cikin matan da suke shaye-shaye, da yake yasanta a saboda ni kawai ya ƙyaleta ba tare da ya saka an kamata ba. But ya yi mata concrete warning wanda ta yi matuƙar tsorata" cewar Mas'ud tana miƙar da wuyansa. 

"Allah ya kyauta, amma sun ɓata rawarsu da tsalle wallahi, Mts!" cewar Mahmoud. 

Sun yi hira sosai daga bisani suka miƙe zuwa masallaci kasancewar har an kira sallar Asr. 

        🌎🌎🌎🌎🌎🌎

A ɓangarensu Hujayrah fitowansu ke nan daga garden za su shiga cikin gidan ita da Razina. Kamar wasu yara haka suke wasa suna tsalle. Sanye suke da atamfa kalar fara da ratsin blue da ɓaƙi-ɓaki, ɗinkin riga da skirt ne a jikinsu, sun yi kyau sosai kamar ka sace su ka gudu saboda kyauwun da suka yi. Hujayrah har wani sheƙi da santsi jikinta yake yi, ta murje ta yi ɓul-ɓul da ita, idanunta sun ƙara fari tar dasu, ƙwayar idonta ya ƙara kore kamar ganye. Ta yi ɗaurin nan wanda ake kira da ture kaga tsiya, duk da ta ɗaure gashin kanta da ribbom amma sai da jelar gashin ya sauko har gadon bayan, baƙi siɗik! Sai sheƙi yake. Razina da tsokanar tsiya ta fizge flawar da Hujayrah ta tsinko a garden Mai launin orange da ruwan madara ta kwasa a guje, sai ita ma Hujayrah kamar wata ƙaramar yarinya ta kwasa a guje tana kiran Razina tana faɗin ta bata flawarta. Razina sai dariya take yi tana gudu har da yi mata gwalo. Tsere suka shiga yi a gidan, Razina taƙi bari Hujayrah ta kamata. Suna wannan guje-gujen sai wata zazzafar mota da danno kai cikin gidan bayan mai gadin Second gate ya buɗe musu. Khalil ne da Akmal wato yaron Alhaji Sambo Dala,da yake Akmal ne ya je airport ɗaukosa kasancewar bai da abokin da ya wuce Khalil. Garin guje-gujen su Hujayrah wanda basu lura da motar su Akmal ba, sai Hujayrah ta biyo Razina ta gaban motar, ƙiris ya rage motar da bige Hujayrah, don wani sauti motar ta bada, ji kake ƙiiiiiiii! Ta tsaya cak!. Hujayrah ma tsayawa ta yi saboda ta yi matuƙar tsorata, a daidai wannan lokacin su Arqam, Mahmoud da Mas'ud suka dawo daga masallaci wanda yake a cikin gidan. Tsayawa suka yi suna ganin Ikon Allah, da yake suna kallon lokacin da motar da kusa bige Hujayrah. 

Da sauri Akmal ya fito daga motar shi da Khalil, kallonsu na yi da kyau ganin suma kyawawa ne ajin farko, masu ji da ƙudi da tsantsan Habiba musamman Akmal, kyakkyawa ne na ƙin ƙarawa kuma ingarman namiji. Sai dai duk wannan kyawu nasa bai kai Arqam ba, don shi Arqam sha kundum ne indai  wajen kyau ne da kwarjini. Bayan sun fito sai Akmal ya isa inda Hujayrah take a daskare idanunta a ƙasa, lokaci guda gabansa ya yi mugun bugawa, bai taɓa ganin halittar da ta tafi da imaninsa irin surar Hujayrah da kyawunta. Kamar wani wawa haka ya tsaya yana zubawa Hujayrah idanu baya ko ƙyaftawa. Har Khalil ya ƙaraso inda suka Akmal bai san ya zo ba. Sai da Khalil ya fada kafaɗunsa sannan ya sauke ajiyar zuciya. Sai a sannan Hujayrah ta ɗago kanta tana kallonsu. Turo baki ta yi waje tana cewa

"Kawai-kawai kun wani zo za ku bige mutum, Allah ko Hmmmm da kun bigeni hahahaaaa! " a shagwaɓe ta yi maganar wanda ya ƙara ƙawata kyawun fuskarta. 

"Man wallahi naga matar aure, AL Qur'an naga wife material a nan, the queen of beauty ke nan" cewar Akmal yana sakin murmushi wanda ya ƙara fiddo da tsantsan kyawunsa. A daidai lokacin Arqam ya ƙaraso wurin a fusace kuma ya ji mai Akmal ya ce. Sake tamke fuska ya yi sannan ya dubi Akmal ido cikin ido ya ce

"She will never be yours Akmal Saboda wannan da kake ganinta a gabanka she is ... ✍️







*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***