GARWASHI

Chapter 16

by @gidaniko422

*Idan Ubangiji yayiwa bawa mafita, kofar da take kulle ma sai ta bude mishi ko bai saka makulli ba, da ace bawa ya San abinda yake gaibun Ubangiji to da ya kwanta ya hutawa rayuwar sa bai yi kokarin kwatar kayi ta yaki halal yaki haram ba, Allah ka budewa musulmin  bayin kofar da take rufe, ka sadar da mu ga rabon duniya da lahira a cikin Aljannah*



_Masu sharing littafin nan na jinjina muku Allah ya kara daga daraja_


*Complete na littafin 1k ne if you want it DM ****


..........Duk murmushin da yarima Gibson ke jifata dashi na Jin Dadin ganina hakan Bai sa naji nayi farin cikin ganin shi a wanna lokacin ba sai ma wani turirin baking ciki  da naji zuciya ta nayi, don Ina ganin zai kawo min cikas akan zuwan Umar

Ina tsaye Ina kallon yadda motocin gidan sarautar suka jeru ana ta faman faman tattare mishi tsadaddiyar Rigar sa ta wani kyakkyawan leshi mai tsada, aka shimfida mishi dogon kafet din mai ruwan hold da zai taka shi har cikin falon saukar bakin ma'azi Nkem, yarima Gibson kuma Yana ta jifa na da murmushin da dai boye yadda take jina a zuciyar sa ba.
Ya karaso Yana me Rungume ni da tattausan hannuwan sa kafin ya sumbaci goshi na Yana fada min wasu kalamai Wanda Rashin sa ar da ya tako Bai taba burgeni ba bare naji son a zuciya ta, bare Kuma kalaman nashi suyi min Dadi. Ya saka tafin hannun shi cikin nawa hannun ya Runtse Yana ci gaba da rada min kalaman kauna a kanne na Yana Kara Rungume Ni tsam a jikin shi yayin da tsanar shi ke Kara zagaye jikina da zuciya ta, na Soma zare hannu na daga nashi hannun Ina Shirin zare jikina naji Amaka tana isowa tanawa Gibson barka da zuwa tamkar zata sunkuya mishi ko ta  mayar da shi cikin ta ta sake haifar shi, inda Kuma naji waya ta ta dauki tsuwwa bans kuma ko tantamar umar ne, na duba na kuma ga Umar faruk ne, nayi saurij sulalewa daga wurin  na daga da sauri inda Yake fada min ya karaso
Gaba na yayi masifar faduwa don lamarin ya zo min da zak'i da madaci, da ace Amaka Bata karaso ba to da na sulale na fice zuwa wurin Umar faruk, yadda kumw na kula tana ta bare baren miki tamkar zata sumkuya da murnar zuwan Gibson idan nace zan fita komai zai iya faruwa, Idan nace komai to ina nufin komai, Kuma banajin zan iya barin Umar a waje na shanya shi don zuwan wani Gibson da bana kallon shi a wata tsiya sai wanda ya nemi yi mishi shigar Sauri da katse min kwanciyar hankali  a rana tsaka da kuma shiga Rayuwa ta ta karfi da yaji ba don na gayyace shi ba

Na daga wayar Umar Ina mishi sannu da Zuwa na Kuma tambaye shi ya karaso? Yace min gashi a kusa da gidan mu nace gani Nan Zuwa

Amaka ta kwada min harara wai bata ga Ina murna da zuwan yarima Gibson ba   ban sauki Gibson din yadda ya kamata ba na barshi a tsaye . Na SHIGA laluben yadda za ayi na sulale na fita wurin Umar ba tare da Amaka ta nemi kunya Tani a gaban Gibson ba. sai Kuma na Gane in ba tarairayar Gibson nayi ba to kuwa ba Zan samu na fita cikin sauki ba don Haka sai nayi nufin karrama shi. Na ruko hannun sa INA mishi wani kyakkyawan murmushi Wanda yasa amaka ta gamsu

Na sauke shi a falon saukar Bakin Maazi Nkem na Kuma shiga kawo mishi abin tarba na gararib dangin Ruwa da lemukada  nau'ikan namo mi da abinci irin na girma da kasaitacce irin barasake  yarima Gibson

Amaka kuwa  sai barin jiki take tana fito min da Kaya na garari Wai inyi kwalliya don har da murjanai ta fito min dasu Wai nayiwa yarima Gibson kwalliya

Nayi hikimar cewa Amaka Zan karbo abu wurin grace wata yarinya ce Nan makociyar mu inda Amaka tace nayi maza na dawo nayi wanka Kar ya tsaya jirana
Aguje na fita na hango Umar a bangon gidan su grace Yana tsaye cikin fararen Kaya Wanda suka Kara fito da kwarjinin shi naji kamar na Rungume shi don tsabar kyan da yayi min a ido

Bakine kalar fatar jikin shi ba Kuma Baki sosai ba irin kalar Nan da ake cewa cokulat kala shi ba Baki ba shi Kuma ba fari ba wankan tarwada. Dogo ne sosai Kuma Mai murdadden jiki Yana da fadi a kirji da Kuma dogon wuya sai idanun shi matsakaita da tattausar suna irin ta labarawan Maiduguri wato shuwa sai sajen fuskar shi da hancin shi mikakke dodar a Kan dakalin fuskar shi sai Kuma wani annuri a goshin sa Mai Kama da an diga mishi bakin Abu a tsakiyar goshi 

Na karasa gareshi Ina murmushi nayi mishi barka da zuwa shima yayi min murmushi Yana kallon tsakiyar idanu na kunya ta kamani na sunnar da kaina kasa. 

"Shikenan Kuma sai na Rabu da jinki Justina? Na tsinto maganar tashi Akan kaina

"Kayi hakuri ban San zaka nemi Ni bane 
Na fada inajin kallon Nan nashi har jinin jikina.

"Gani to na neme ki Kuma Zan gaida mama da Baba.....
Rudewar da nayi har shi ya fahimci hakan don Haka sai nace mu SHIGA gidan su grace zanyi wanka yanzu Kuma na kawo mishi Ruwa
Muka SHIGA gidan su grace na sauke shi a parking space na karbo fararen kujeru wurin maman Grace na Kuma fada Mata na sauki bako na a parking space tace ok

Na fito na aje Mana kujerun na Kuma ce mishi ya bani minti goma Zan dawo 
Na fice zuwa gida na fada wanka na fito na saka kayan da Amaka ta fito min dasu ita da kanta ta SHIGA tsara min kwalliya kasancewar ta kwararriya a fannin make up don har kanti ta bude inda ake tsantsara kwalliyar kanti. Ta daura min murjanai ta Kuma fesheni da turare kala kala na nufi inda Gibson Yake Amma Kuma zuciya ta tana wurin Umar Wanda nayi fatan ace wurin shi na wuce Kai tsaye Amma Kuma ban Isa ba koda kuwa na Sha giyar wake

Fadawan dake gadi a kofar inda Gibson Yake suka sunkuyar da kawunan su Wai don kar su kalleni na wuce su Ina Jan tsaki Araina

Na shigo na same shi Yana kishingide irin kwanciyar jinin sarauta Amma Yana ganin na shigo ya taso ya tarbeni Yana bani hot kiss abinda ya ke bakan ta min Rai shi Kuma Yana ganin ta Haka NE zai nuna min yadda yake jina a zuciyar shi
Muka tsurawa juna ido muna kallon juna a tsakiyar ido kafin ya zaunar Dani dab dashi na Kuma kula da bai taba komai ba don Haka na Soma service din shi da nau ikan abin da aka Tara mishi Kuma ya dan taba kadan daga cikin abinda na zuba mishi Yana ci kuwa yana kallo na

"Ina fatan dai ke kikayi girkin Nan? Ya fada Yana Ruko tsintsiyar hannu na na kada mishi Kai Alamar bani nayi ba sai ya mayar da Naman da yakai Baki Yana gutsura kamar Dan yaro
Ya yagi tissue paper Yana goge hannun shi da Bakin shi ya Dan kurbi lemun Dana zuba mishi a tanbulan sai kawai Naga ya kwanta Akan cinyoyi na Yana Riko hannun na Yana matsawa Yana Kuma kallon idona Yana fada min nayi mishi girki kafin ya tafi don yaji irin dandanon hannuna Wai ta dandanon girkin mace ake ita din wacece a cikin Mata
Maganar tashi ta bani haushi ba kadan don Haka na tambaye shi yaushe ne zai tafi? Yace 4:00 na yamma na dubi agogo Kuma 2:51 ne don Haka nace to ya jirani na SHIGA kichen yanzu nayi mishi girki don har coice din shi na tambaya don nasan na Gama samun damar da nake ta neman samu ta zuwa wurin Umar

Na fito nacewa Amaka yace girki na Yake so nayi mishi Amaka tace to na SHIGA kichen Mana nayi mishi me shegen dadin da zai manta da kunnen shi

Na SHIGA kichen Ina hada slinder na kuma Dora tukunya da sauri Kuma na fice zuwa wurin Umar Wanda nayi dabarar fito mishi da Ruwa da lemu har da nama

Muna ta fira Yana fada min shi Yana so ne yayi min silar da Zan Rabu da ciwona na bugun aljanu don abin Yana Ranshi idan ya tuno da yadda abin ke samu na. Ban boye mishi ba na sanar dashi yadda nake son karatun Alkur ani da Kuma mafarkan da nake yawan yi Wai Ina salla har na Fara tunanin yadda Za ayi na taka tsanin da Zan zamo Ina yin sallar Nan shi Kuma Yana Kara fada min girman iyaye da hakkin su na ayi musu biyayya hakan ya Kara jefa Ni cikin Rudani don na Rasa ta Ina Zan Fara?

Mun Dade muna fira har bamu San lokaci yaja ba sai da Rutu Mai aikin gidan mu tazo take fada min wai sanwar da na Dora ta kone har ta so haifar da gobara don Haka na biyo Rutu muka taho inda na iske Amaka ta cika ta batse kadan ya Rage ta fashe muna shigowa ta wurgo min wata matsiyaciyar harara tamkar idanun ta zasu zubo kasa.................



Kar ku bari ayi tafiyar nan babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran


Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI🥰


_Masu Neman labarin garwashi daga farko su duba cikin channel din mu zasu samu labarin daga farko_