Chapter 33
by @umsar
WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
@umsarArewapen
Wattpad: Umma Mustapha
PAGE 33
ƙarfe takwas da rabi na dare Irfan ya Bude idonsa. Ɗakin asibitin ya yi shiru, ba ka jin komai sai ƙarar na'urar sanyaya ɗakin.
Ya ɗan motsa jikinsa a hankali, sannan ya kalli gefen gadon kamar mai neman wani abu.
Yana cikin wannan yanayin ne wata ma'aikaciyar jinya ta shigo. Ta ƙaraso wajensa tana masa sannu, sannan ta juya domin kiran Dr. Anwar.
Ba daɗewa ta dawo tare da Dr. Anwar din. Likitan ya duba Irfan sosai, sannan ya tabbatar masa cewa babu wata matsala.
Ya kalli ma'aikaciyar jinyar.
"Za ki iya tafiya. Idan ina buƙatar wani abu, zan kiraki."
"Okay, Doctor."
Bayan ta fita, Irfan ya kalli Dr. Anwar.
"Ina Jabir?"
Kafin likitan ya samu damar amsa masa, sai ga sallamar Jabir.
Jabir ya shigo, ya nemi kujera ya zauna, tare da ajiye abubuwan da ke hannunsa a gefe.
Dr. Anwar ya kalli Jabir.
"Ina ganin za ku iya tafiya da shi. Idan wani abu ya taso, sai ka kira ni."
Jabir ya ɗan yi shiru, sannan ya tambaya:
"Amma Doctor, ka tabbatar babu wata matsala? Kar mu je cikin dare ciwon ya sake tashi."
"Insha Allah, babu matsala. An yi masa allurai da duk abin da ya kamata. Idan Allah Ya kai mu gobe, zan zo in ƙarasa masa sauran allurar."
Irfan yana jin duk bayanin da Dr. Anwar yake yi, amma bai ce komai ba.
Jabir ya miƙe, ya kwashe kayan da ya kawo ya kai su mota, sannan ya dawo ya taimaka wa Irfan suka fice daga asibitin.
Suna shiga gida, Irfan wanka ya shiga. Bayan ya fito, ya rama sallolin da ake binsa. Jabir ya kawo masa abinci tare da magungunansa.
Bayan Irfan ya gama cin abincin, ya kalli Jabir.
"Ina wayata?"
Jabir ya kalleshi da mamaki.
"Daga fara samun sauƙi har ka fara neman waya? Ni wallahi ma ban san inda take ba."
"To, sai ka tashi ka nemota min."
Jabir ya miƙe ya fita. Bai ɗauki lokaci mai tsawo ba sai ga shi ya dawo da wayar a hannunsa. Ya ajiye ta a kan cinyar Irfan, sannan ya koma falo, tunda ba ya jin bacci saboda ya ɗan yi barci da suka dawo.
Irfan ya ɗauki wayar. Abu na farko da ya fara cin karo da shi shi ne missed call ɗin Nihla, sannan ya ga saƙon da ta tura masa.
Murmushi ya ɗan bayyana a fuskarsa.
"Wannan ma alamar nasara ce."
Ya so ya kira ta, amma ya tuna cewa zuwa wannan lokacin wataƙila ta riga ta yi bacci. Sai dai ya kasa barin abin haka. Ya rubuta mata ɗan gajeren saƙo.
"Yan mata na." ❤️
Yana turawa, ya ajiye wayar a gefe, ya kwanta yana jin wani irin daɗi a zuciyarsa.
Nihla ba ta tashi da wuri ba sai ƙarfe shida na safe, sakamakon nauyin baccin da ya ɗauke ta.
A gaggauce ta tashi, ta yi alwala ta gabatar da sallar Asuba. Bayan ta idar, ta gudanar da addu'o'inta, ta karanta azkar.
Har wajen ƙarfe bakwai da kwata tana cikin ibada. Da ta gama, ta cire hijabinta. Wayarta ta ciro daga caji, ta zauna ta fara daddannawa. Saƙon Irfan ne ya bayyana a kan screen ɗin wayar.
Duk da kalmar da ya turo mata ba wata kalma ce mai tsayi ba, amma ta ji daɗi.
Ta sauke ajiyar zuciya tare da ɗan murmushi.
Ta kalli agogo. Har yanzu akwai sauran lokaci. Karfe takwas Irfan yake kiranta, amma za ta bari takwas ya yi, idan bai kira ta ba, ita za ta kira shi.
Ta ajiye wayar a gefe, ta juya ta kwanta, da niyyar ta ci gaba da baccinta. Sai dai da ta rufe ido, kalaman Irfan ne suke dawo mata.
"I love you with all my heart."
Kalmar ta tsaya mata a rai.
Bacci ya gagara ɗaukar Nihla ko kaɗan. Duk wani motsi da za ta yi, sai ta ɗauki wayarta ta duba agogo. Idan ta ga takwas ba ta Yi ba, sai ta ajiye wayar.
Tana nan tana faman juyi a kan gadon har ƙarfe takwas ɗin ya cika.
Ta ɗauki wayarta da niyyar kiran Irfan, amma sai ta tsaya tana ɗan tunani.
"Me ya sa nake rawar jiki a kansa haka? Me ya sa na kasa samun sukuni a zuciyata? Me ya sa da na ga saƙonsa jiya na ji daɗi haka?"
Ta yi shiru na ɗan lokaci.
"Ko dai da gaske na faɗa cikin komar so, kamar yadda Fatima ta ce?"
"Ah-ah! Kawai shakuwace da kuma sabawar da na yi da shi. Amma ba soyayya ba ce."
Wani sashe na zuciyarta ya faɗa mata haka.
Ba ta ƙara tunanin komai ba. Ta fara kiran layinsa.
Kiran ya kusa yankewa kafin aka ɗaga.
"Hello."
Muryarsa ta sauka a kunnenta.
Nan take Nihla ta daidaita kanta, sannan ta amsa masa tare da gaida shi.
"Sorry, na tashe ka daga bacci?"
"Ah-ah, idona biyu."
"Amma na ji muryarka kamar mai bacci."
Irfan ya ɗan yi shiru kafin ya ce:
"Ba ni da lafiya ne."
"Subhanallah!"
Nihla ta furta hakan cikin damuwa.
"Me ya same ka?"
"Zazzabi da ciwon kai," ya amsa, yana ɓoye mata ainihin abin da ya faru da shi.
"Ayyah, sannu. Ko shi ya sa jiya na yi ta kiran ka ban same ka ba. Na yi tunanin ko fushi kake yi da ni."
"Me ya sa zan yi fushi da ke?"
"To ai ban sani ba. Ko na ɓata maka rai ne daren da muka rabu?"
"Ba ki yi min komai ba."
"Amma me ya sa yanayinka ya sauya a lokacin?"
Irfan ya yi ajiyar zuciya.
"Ba komai. Kawai ina cikin fargabar ko za ki karɓi soyayyata, ko kuma za ki yi rejecting ɗina."
Shiru ya biyo baya.
Nihla ta rasa abin da za ta ce. Tambayar ta yi mata nauyi, musamman da yake har yanzu ita kanta ba ta san ainihin abin da zuciyarta take so ba.
"Allah Ya ba ka lafiya," ta faɗa, tana ƙoƙarin kashe wayar.
"Kar ki kashe min waya. Ba mu gama magana ba."
"To ai ni ban san me zan ce ba," ta faɗa cikin shagwaɓa, kamar za ta saki kuka.
Irfan ya ɗan murmusa. Yana son irin wannan shagwaɓar tata.
"Shi ya sa na ba ki lokaci. Na ce ki yi tunani."
Kafin Nihla ta samu damar amsa masa, sai Jabir ya leƙo cikin ɗakin.
"Dr. Anwar ya zo. Zai duba ka."
Irfan ya kalli Jabir, sannan ya koma kan wayar.
"Dr. ya zo zai dubani. An jima zan sake kiranki."
"To."
Suka yi sallama, Nihla ta ajiye wayar a hankali.
Ta daɗe tana kallon screen ɗin wayar, zuciyarta cike da tunani.
Tambayar Fatima ta sake dawo mata a rai.
"Kina son Irfan ko ba kya sonsa?"
A wannan karon, Nihla ta kasa ba zuciyarta amsar da ta dace.
Umsar ✍️