Chapter 21
by @reza12
Chapter 21
Bayan sun gama wayar ta ja tsaki tana faɗin "Wallahi ba zan karanta ba, karshe dai ace ya sake ta ba shikenan ba". Sai dai kuma gaba ɗaya lamarin ya kasa barin tunanin ta. Tana fasalta halin Yasir da na Hafiz. A fili tace "Duk ɗaya suke babu gara, Allah ya saka mana". Kiching ta shiga ta ɗaura girki daidai cikinta, wanda zata ci yanzu da kuma safe. Tana gamawa kuwa ta gyra gurin dan ma karya gane anyi girki. Daidai ana kiran sallar magariba ya shigo gidan da sallama. A lokacin tana palon ta cika tayi fam domin bai saba kaiwa har haka ba. Duk da suna faɗa amma hakan ya mata zafi. Bata amsa ba sai bin hannunsa da tayi da kallo. Shima bai bi ta kanta ba ya ajiye abincin da ya shigo da shi ya shige ciki. Yana shiga ta tashi da sauri ta fara buɗe wa domin ganin abun da yake ciki. Tana cikin haka sai gashi ya fito ya tsaya a bayanta. Tsayuwar tasa ce ta tabbatar mata da yana gurin. Hakan yasa ta tsaya chak daga abun da take yi, kunya da tsoro na kamtaa. Ganin bai ce komai ba sai ta fara borin kunya tana faɗin "Saboda zubar da mutunci kana magidanci kana shigo da abinci gida a leda ko kunya baka ji, to wallahi ba zan juri haka ba, ai gara ka tsaya a cen kaci idan kuma ba ni kake son al'ummar gari su dinga zagi ba" Hafiz yay mata wani kallon baki da hankali sannan ya ɗauki abincin ya shige ciki ya barta. Ta bishi da kallo tana cigaba da maganganun ta. Bayan yayi sallar isha ya shiga kiching ya ɗauko plet ya juye abincin yana ci. Ta fito ta zauna. Ganin bai ce komai ba sai ta fara haibaici da shaguɓe. "Duk macen da ta ɗauki na miji uba zata mutu marainiya. Na mijin alkakin dalma. Namiji gubar ajali. Yarda da namiji tamkar yarda da fitar ƙahon jaki ne". Yana zaune yana jinta bai tankaba. Ta sake faɗin "Ya Allah ka biwa duk macen da aka zalunta hakkinta". Ya juyo suka haɗa ido sai ta kawar da kai tana cigaba da maganar. Ya sha ruwa kafin ya ce "Bari na faɗa miki gaskiya, Hafiza wannan abun da kike yi halin jahilan mata ne da basuyi karatu ba, ba wai irinki da kike Hafiza mai hadda ba. Kin bani mamaki, nasan dole a cikin biyu za'ayi ɗaya. Ko dai ƙawaye ne suka zuga ki, ko kuma wannan shegiyar wayar da ta zama abokiyar rayuwarki ta kwana biyu, ina sake faɗa miki wannan turbar da kika ɗauka ba inda zata kaiki wallahi sai da na sani. Abu na gaba kuma ina mai sanar dake cewar na fara aikina yau. Ba zan taɓa iya mantawa da irin gudunmawar da kika bani ba, Allah ya miki albarka, kuma har gobe kina cikin raina, ina fatan Allah ya dawo miki da hankalinki da ya bar jikinki". Daga haka bai tsaya jin mai zata ce ba ya ƙara gaba. Ta zauna a gurin tana mamakin kenan ita yake kira da jahila. Gaba ɗaya wannan kalmar tai mata zafi wanda har ta kasa barci. Da safe kuwa bayan tayi Sallah ta ɗaga hannu tana addu'ar idan har ba alkairi a tare da zaman ta da shi Allah ya shiga tsakaninsu kafin akai ga ya sayar mata da ƙoda". Ta ɗauki Alkur'ani tana karatu. Izu uku tayi kafin ta fito tana jin ranta wasai ko haushin nasa ma ya gudu. Har zai fita ta ce
"Ina son zanje gida?"
Ya juyo ya ce "Gida yin me?"
"Gidan namu ne ake tambaya yin me zan je?"
"Eh gidan naku, mai zaki je yi?"
"Zan je yawo ne". Ta bashi amsa a gatsale. Domin idan ba ma rainin wayo ba, gida fa tace zata je, yaushe rabon ma taje gidan.
"To ba zaki je ba".
Yana faɗa yayi gaba. Sai ta biyo shi tana faɗin "Saboda me? Ko dan ma kayi sa'a na tambaye ka" Ya sake tsayawa ya juyo a fusace ya ce "Nace ba zaki je, idan kuma ban isa bane ga hanyar nan". Ya faɗa yana nuna mata hanya. Yanayin yadda yayi maganar ta tsorata. Dama ƙarar sa zata kai gida, hakan yasa ta ce "Wallahi ba wanda ya isa ya hana ni zuwa gidan mu". Tana faɗa ta koma ciki da gudu. Shima ya shiga Mota ya tafi abunsa.
Tana shiga ta dauki waya ta nemo number Hajiya. Har ta lasat kira kuma ta kashe. Tana tunanin to me zata ce. Tana cikin haka sai ga kiran hajiyar kuwa saboda kiran da tayi ya shiga. Ta ɗaga suka gaisa. Har hajiyar na mata barka da samun aikin nasu. Ta amsa tana son yin magana kuma taji yadda Hajiyar ke ta sa mata albarka da yabonta. Hakan yasa ta kasa cewa komai. Amma da ta tuno yadda yake jin maganar ta, kuma tasan idan tai masa magana zai ji. Sai kuwa dake ta kawar da kunya ta ce "Amm Hajiya wai ko ya miki maganar zai ƙara aure?" Ta faɗa harda sinne kai. Hajiya ta ce "Aure kuma? Hafiz ɗin ne ya faɗa miki haka? Daga samun aiki? Bashi da hankali ne? To ban san da maganar ba, kuma ba ma abun da zai yiwu bane, ki kwantar da hankali yau ɗin nan idan ya dawo zanji daga gare shi". Ta ce "Wallahi fa Hajiya, ai ranar haka ya kalli cikin idona ya faɗa min wai aure zai ƙara. Har ina faɗa masa cewar daga samun aiki ya bari mana ya fara aikin". Hajiya ta ce "Bama zai saɓu ba, yana da Mace kamar ke mai kuma zai nema a mace, ko ni ban lamunce". Suna gama wayar ta rangaɗa guɗa tana faɗin "Alhamdu lillah, Allah ka shiga tsakanin da wannan yar iskar.
Gaba ɗaya ta jita a cikin farinciki domin dai ta san batun aure babu shi ya bi ruwa. Ta ɗauko abincinta ta ɗumama ta fara ci. Tana ci tana murmushi ita ɗaya. Bayan ta gama ta ɗauki waya ta kunna data. Ganin Hadiza a online ne yasa suka dinga hira. Tayi-tayi ta bata labarin abun da ya faru a littafin amma tace wallahi ba zata bata ba, sai dai ta karanta da kanta. Hakan yasa ranta ya ɓaci ta sauƙa daga online ɗin domin taje ta karanta. Ta kashe datar ta shiga cikin littafin daidai gurin da ta tsaya sannan ta ɗora.
***
Wayarta ta ɗauko ta kunna, nan ta shiga goge gaba ɗaya hoton da suka ɗauka tare. Ta goge number sa, sannan ta cire layin daga wayar gaba ɗaya. Idan ta tuna tana ɗauke da hiv abun na ƙara mata raɗaɗi a rai. Ji take ina ma Allah ya kawo dalilin da zata mutu kar ta zamarwa na tare da ita aiki, domin tasan dole ba zasu sake da ita ba. Haka aka ware mata iya kwanon da zata dinga amfani da shi. Da kuma kofin da zata dinga amfani da shi. Haka zalika kowa na gidan baya-baya yake da ita. Hatta Mama sai ta uni bata shiga gurinta ba idan ba abinci zata miƙa mata ba. Sai dai ta ɗaga labule tai mata magana daga waje. Nana kuwa gidan ma ta daina kwana saboda ɗakin sune yanzu Amal ɗin ke ciki, kuma tana tsoron su kwana a daki ɗaya. Sai dai zata dai zo su gaisa daga waje saboda ko ɗakin bata shiga dakin. Kwana goma kenan da dawowarsu daga asibiti, amma gaba ɗaya zaman baya mata dad'i, gashi ba abokin hira, ko Hafsa ɗin ma tun da tazo sau ɗaya bata ƙara zuwa ba. Ganin haka yasa Mama ta ce mata ko zata koma gidan nata ne ta zauna tunda har yanzu da aure a tsakaninsu, kuma ko ba komai cen ɗin gidan ta ne, zata fi sakewa, sannan akwai komai a cen ba kamar nan ba". Ranar da Mama tai mata wannan maganar ranta ya ɓaci da sai da ta faɗawa Mama maganar da tayi nadama daga baya. Tace idan ta gaji ne kawai tace ta bar mata gida, ba sai ta mata kora da hali ba. Hakan yasa yanzu take ta tunin barin gidan ta tafi wata duniyar ta rayu ita ɗaya. Kuka kawai take yi idan ta tuna yadda rayuwa ta maida ta a lokaci ƙadan. Ga ciwon ƙoda, ga hiv, sannan mahaifarta ta samu matsala. Take ta ɗaga kai tana kallon sama, tana ta tunanin to ina zata je. Take wata zuciya ta aiyano mata wani abu. Hakan yasa ta tsaya shiru tana nazari. Tashi tayi ta ɗauki wata karamar jaka ta ɗauki abun da zata dauka. Ta kwashi maganinta tayi waje. Lokacin ba kowa a gidan hakan yasa ta nufi waje da sauri ba tare da tasan inda zata je ba. Tana fita ƙofar gidan taga Mama da Yaya a tsaye suna magana. Kallo ɗaya Yaya yayi mata hankalin ya tashi. Wannan ƙurajen sunyi baƙi sun sa fuskar tata ta yi baƙi. Ga ramar jikinta ta sake baiyan sosai. Ta tsaya tana kallonsu suna kallonta. Mama ta ce "Amal ina zaki je harda jaka?" Ta kasa bata amsa sai kallon yaya da take yi tana hango Yasir a cikin jikinsa. Ta ƙura masa ido kamar mai kallonsa har hanji. Hakan ya basu tsoron irin kallon. Kafin su ankara kuwa ta jofo masa jakar hannunta. Kuma ta fashe da kuka ta yo kansa tana faɗin ya bar musu gida ko ta kashe shi. Sosai take ihu da zagi tana kai masa yaƙushi wanda har sai da ta ture Mama gefe ta isa gare shi. Kawai Yasir take gani ba Yaya ba. Da ƙyar ya shiga motarsa ya bar gurin domin har an taro a gurin. Wanda basu ga yadda ta koma ba ma sai yanzu suka ganta. Mama ta kama hannunta tana kuka ta jata ciki ta tura ta daki ta fara mata faɗa. Ai kuwa itama ta hayayyaƙo mata kamar zata kai mata duka. Haka Amal taci gaba da zaman kaɗaici a gidan. Sai a lokacin ma ta samu labarin ashe wai Nana gidan Yasir wato gidan ta ta koma da zama. Bata ce komai ba, hasali ma bata nuna mata ta sani ba. Tun tana kokarin haukata kanta har yanzu da ta yarda da gaddara. Ta rungumi hakan a matsayin abun da Allah ya tsaɓar mata. Watan farko yaya ne ya amso mata magani. Wata na biyu kuma da kanta taje ta bi layi ta amsa. Yanzu bata jin koami sai yawan bushewar maƙogaro da kuma ƙaiƙayin da fuskarta ta keyi, wanda likitan ya ce mata na warkewa ne. Yau tana zaune taji sallama a cikin ɗakin nata, tayi mamaki jin muryoyi da yawa. Ta amsa tana kokarin rufe fuskarta. Amma har an shigo. Ƙawayenta ne na makaranta wanda Hafsa tai musu jagora sun kai goma sha. A tsatsaye suka gaisa suna mata fatan samun lafiya da sauransu. Ita sam bata ji daɗin hakan ba, tasan gulma ya kawo su. Hakan yasa suna fita ta hau Hafsa da faɗa akan mai yasa bata faɗa mata ba, ita bata ji dad'i ba. Ta ce a group ne suke ta damunta shi yasa ta kawo su. Kuma tace ta kira number ta bata shiga shi yasa. Ita dai har ga Allah bata ji dad'in hakan ba.
Washegari tana daki lokacin ta ɗauki wayarta tana kokarin saka layin domin ta duba account ɗin ta, saboda tana buƙatar wasu abubuwan na rayuwa, domin tasan tana da kuɗi a account dinta na opay. Wayar na kawowa sai ga hoton ta ita da shi a farkon wayar. Hakan yayi daidai da shigowar Mama ɗakin da sallama. Bata amsa ba, sai ma swapin ɗin wayar da take ƙoƙarin yi yadda komai zai fita ta dawo sabuwa. Mama ta ce "Amal magana nazo muyi dake a matsayin mahaifiyar ki". Sai da ta tabbatar ta goge komai kafin ta kalli Mama ta ce ,"Yau kece har cikin dakin mai cutar ƙanjamau?" Mama ta ce "Eh ya zama dole ne, kuma ke ɗin dolen muce idan wasu sun guje ki to mu ba zamu iya ba". "To ina jinki Mama, na tashi na bar miki gida ko ko kuma yaya?" Mama ta ce "An samu likitan da zai miki aiki wanda zaki iya rabuwa da wannan ciwon. Yaya ya ɗauki nauyin komai da za'ayi shine nace bari na tambaye ki, dan Allah ki bada haɗin kai, Kinga dai wannan bawan Allan da gaske yake son taimaka mana". Amal tayi wata dariya wacce sam bata da haɗi da nishadi sai ma abun kallo da dariyar ta zama saboda karon farko kenan da tayi. Daidai lokacin app ɗin opay ya gama sauƙa a wayarta tana kokarin yin logging ta ce "Mama ke mahaifiyata ce, bana son na faɗa miki maganar da bata dace ba, dan haka ki daina min maganar wannan mutanen. Ni na yarda da gaddarar da Allah ya ɗora min, kuma idan zai cire min shi zai ga dama a lokacin da yake so. Kaman yadda ban san lokacin da na samu cutar ba, haka ban san lokacin da zai cire min ba, kuma wannan cutar ba'a cire ta a jikin mutum. Sannan ba zan sake yarda da wani mutum ya sake taɓa jikina da nufin yin magani ba, dan haka karki ɓata lokaci da bakinki dan Allah". Ta faɗa tana kokarin ɗaukar hoto kaman yadda opay ɗin suka buƙata domin tabbatar da cewar account ɗin nata ne. Daidai lokacin kuwa account ɗin ya buɗe bayan ta saka otp ɗin da suka turo mata.
Mama ta ce "Amal ba wasa nake miki ba, wallahi da gaske ne, har ni ya kaini munyi magana da likitan da zai miki aikin. Dan Allah Amal ki amince da wannan abun alkairin. Kika sani ko Allah ne ya toro Shi ɗin kamar yadda kika ce? Shi baki so wancen ɗan iskan ya samu labarin kin warke? Baki so baƙin cikin hakan ya dame shi?". Amal ta ƙurawa account ɗin ta ido ganin kuɗaɗe a ciki. Adadin kuɗin da yake bata a duk lokacin da akai masa salary sune har lokacin bai daina sawa ba. Ga na karshe ma da ya shigo yau kwana shida. Take ta shiga gurin da ake mayar da Taransifa idan an maka. Ai kuwa ta mayar masa da kayansa. Ta bi ɗaya bayan ɗaya wanda ya turo mata tun daga lokacin da abun ya faru ta mayar. Sannan ta tashi da ɗauki liƙab ta saka tasa hijjabi. Mama dai tana ta kallonta. Ganin zata fita tace "Amal magana fa nake yi?" Sai ta ce "Ai na gama magana da ke Mama". Tana faɗa ta fita. Bata tsaya a ko ina ba sai wani shagon ƙasan layinsu. Ta sa ya kwashe mata sauran kuɗin ta. Sannan ta tambaye shi ko ya iya rufe account. Yace bai iya ba. Ta amshi kuɗin ta sake zuwa wani shagon ta tambaye shi. Ya ce sai dai ayi delete ɗin sa, amma hakan ba zai hana idan kinga dama kiyi logging ba". Ta ce kawai ya barshi. Tana so a rufe ne yadda ba za'a iya tura kuɗi ba. Ta sayi abun da zata saya ta dawo gida. Tana shiga gidan ta tarar da Yaya tare da Anty Maryam zaune suna jiranta. Tayi kamar bata gansu ba ta cire nikab ɗin tayi dakinta. Anty Maryam ta biyota tana Mata magana...📝
Mijin Amal