KIRAN KADDARA

THE SECRETS OF RAHMAN AND BASHIR

by @nihaalmaalik


BALARABE MANSION, ABUJA

Tun da Maryam ta buɗe idanunta da safiyar yau, hankalinta yake kan akwatin da suka samo daga dakin nan, ynzu haka ta tasa shi gaba tana kallo, tana jiran zayd ya qare shiryawa su wuche part din mammi

Ta ɗauki wayarta ta sake kallon hoton rubutun da ke jiki

“Rouhi…”

Zaid, wanda yake gyara agogonsa a gaban madubi, ya juyo.

“Yes, Haya?”

“mutumin da zai buɗe mana wannan akwatin yaushe yache zezo?”

Zaid ya ƙarasa ya zauna kusa da ita.

“Ya ce zai zo da ƙarfe goma. Yanada experience na bude old locks”

Maryam ta numfasa.

“Allah ya sa mu sami abin da muke nema. Na gaji da rayuwa cikin tambayoyi. Tun rasuwar Baba bamusan abin da ya faru ba amma mun tabbata sharri akayima baban mu, se ga yayata ta bache”

Zaid ya riƙe hannunta.

“In shaa Allah zamusan komai”

Maryam ta jingina da shi.

Seda suka qare shiryawa misalin ƙarfe tara, suka wuche part din mammi, suka tarar da Mammi da Hajiya Raliya a parlour.

Mammi ta kalli akwatin da Zaid yake riƙe da shi

Suka gaida su a natse, suka amsa suna tambayar maryam jiki se sunkuyar da kai takeyi ta kasa amsawa

Maryam ta zauna kusa da ita.

“An samu me bude akawatin?”

“Eh, Mammi. Lock Smith zai zo ya buɗe shi”

Hajiya Raliya ta gyara zamanta.

“Jiya inata tunanin abin da babanku yayi, Idan da gaske ya ɓoye yarjejeniyar nan a cikin wannan akwatin, to dole ne yasa yayi hakan, kenan ya san akwai wanda zai iya neman lalata ta.”

Haj Raliya ta gyada kai

“Haka ne, kuma Idan har yarjejeniyar tana nan a ciki, za mu samu hujjar da za ta nuna muna abin da ya faru tsakanin Alh Rahman, Alh Bashir, da kamfanin Northern Crest Holdings.”

Mammi ta sauke numfashi.

“Allah yasa gaskiya ta bayyana.”

Maryam ta rungume ta.

“In shaa Allah, Mammi.”

A lokacin ne sukaji qarar horn, bayan dan lokaci daya daga cikin securites din yazo yache musu wai ga me bude makulli, sun bashi izinin ya shigo dashi sannan ya juya, su kuma suka fita zuwa qaramin parlor da ke farko kafin a shigo babban parlorn na mammi

Nan ya shigo ya samesu, ya gaisa da Zaid, sannan ya gaida Maryam, Mammi da Hajiya Raliya.

ya duba akwatin a hankali. Ya juya shi, ya binciki wurin makullin, sannan ya kalli Zaid.

“This is an old custom lock. Whoever made it wanted it to stay closed”

Zaid ya gyada kai.

“Can you open it without damaging the contents?”

“I’ll do my best.”

Alok ya zauna a gaban akwatin ya fara aiki. Maryam ta tsaya kusa da Zaid, tana matse hannunsa saboda tsananin fargabar abnda zasu samu a ciki

Ya dade yana abu daya, har mammi ta kira masu aiki aka kawo mishi snacks da drinks, Bayan dogon lokaci, sai aka ji wani sauti.

Click.

ya ɗaga kai ya kalli Zayd 

“There we go.”

Maryam ta numfasa sosai.

“Ya Allah…”

Zaid yayi mishi godiya ya sallameshi, sannan ya buɗe akwatin a hankali.

A ciki akwai wasu envelopes, tsofaffin bayanan kasuwanci, wani littafin rubutu, da kuma wani file mai kauri wadda aka ɗaure da igiya.

A kan file ɗin, an rubuta da tsohon rubutun hannu:

R-Ω-XVII — FILE 17

Maryam ta rufe bakinta da hannunta.

“FILE 17…”

Mammi ta fara jero hamdala 

“Alhamdulillah! mun same shi!”

Hajiya Raliya ta zauna a kan ƙaramar kujera da ke kusa da su, tana kallon file ɗin kamar ba ta yarda da abin da idonta yake gani ba.

Zaid ya ɗauki file ɗin ya ajiye a kan table, ya fara buɗe file ɗin a hankali.

FILE 17 — AINIHI DA HUJJOJI

Takardar farko ta bayyana cewa Rahman da Bashir sun kafa haɗin gwiwar kasuwanci a Northern Crest Holdings, tare da rabon hannun jari daidai: kashi hamsin cikin ɗari ga kowane ɗayansu.

Maryam ta kalli sunan mahaifinta dakyau, shin babanta nada kaso har rabi a kampanin northern crest?

Batasan lokacin da bakinta ya furta

“Baba bai taɓa satar kuɗin kamfani ba kenan?”

Zaid ya duba takardar.

“A cewar wannan yarjejeniya, mahaifinki halastaccen abokin mallakar kamfanin ne. Amma har yanzu muna buƙatar haɗa wannan takarda da bayanan kuɗi da kuma zarge-zargen da aka yi masa.”

Ya juya shafi na gaba.

Akwai copy din wannan yarjejeniyar da sa hannun Rahman da Bashir. An haɗa da shaidar rajistar kamfani, bayanan rabon hannun jari, da wasu takardun kuɗi da aka adana a cikin file ɗin.

Hajiya Raliya ta ɗauki ɗaya daga cikin takardun.

“Wannan shi ne abin da Malam Nuhu ya yi magana a kai, dubi yadda aka nuna rabon hannun jarin, tabbas Bashir bai kasance ma’aikaci kawai ba, abokin hulɗa ne da ya mallaki rabin kamfanin.”

Mammi ta girgiza kai cikin mamaki.

“To, me ya sa aka ce yana satar kuɗin kamfanin? Wanda keda kuddi a kampani ai baze sachi kuddin kampani ba”

Zaid ya fara duba bayanan kuɗin da ya gani 

Akwai takardun da ke nuna cewa wasu kuɗaɗe sun fita daga asusun kamfanin zuwa wasu asusu da ba su cikin tsarin kasuwancin NCH. Akwai kwanan wata, lambobin ciniki, sunayen kamfanonin da aka tura kuɗin, da kuma sa hannun izini.

Wasu daga cikin waɗannan cinikayyar sun faru ne a lokacin da Fahad yake kula da harkokin kuɗin kamfanin

Maryam ta ɗauki wata takarda, tana karanta ta a hankali.

“Rouhi, dubi wannan. A nan an nuna cewa an tura kuɗi zuwa wani kamfani da ba ya cikin jerin masu samar da kayayyaki na Northern Crest.”

Zaid ya karɓi takardar.

“To, duba wannan ma, An rubuta wannan ciniki sau biyu a cikin bayanan, amma kuɗin sun shiga wani asusun daban.”

Hajiya Raliya ta matso kusa.

“Wannan tabbas itache takardar binciken da Bashir yayi, lokacin da yaga chewa kudadan kampani suna bachewa”

Zaid ya ci gaba da duba sauran takardun. Akwai reports na binciken kuɗi da Bashir ya fara kafin rasuwar shi. An jera wasu ma’amaloli da ya yi alama a kansu, tare da rubutun hannunsa yana nuna cewa ya lura da rashin daidaito tsakanin kuɗin da aka samu da kuɗin da aka cire.

Maryam ta fara kuka.

“Baba ya gano abin da yake faruwa, shiyasa aka yi masa wannan sharrin…”

Zaid ya rungume ta.

“Haya, shhhh ya isa, we’re going to prove it properly.”

Ya juya zuwa shafi na gaba.

Akwai wani rahoto da ya nuna cewa bayan Bashir ya fara tambayar yadda aka sarrafa kuɗin, an gabatar da wasu bayanan da suka nuna kamar shi ne ya amince da cire kuɗin. Amma sa hannun da ke kan takardun bai yi daidai da sa hannunshi da ke kan ainihin yarjejeniyar ba.

Akwai kuma bayanin wani tsohon ma’aikaci da ya ce an matsa masa ya amince da rahoton da ya ɗora laifi kan Bashir ko kuma a kashe shi, kuma ya amince duk da cewa bai ga Bashir ya bayar da izinin waɗannan ma’amaloli ba.

Mammi ta share hawayenta.

“Allah ya san gaskiya, an zalunci mutumin da bai ji ba be gani ba.”

Zaid ya kalli takardun.

“Idan muka haɗa duk bayanan kuɗin nan wuri guda, za mu ga yadda abubuwan suka faru akwai kuɗaɗen da aka tura ta hanyoyin da ake zargi, an sauya wasu takardun amincewa, sannan aka yi amfani da wani rahoto wajen ɗora laifi kan Alh Bashir”

Maryam ta gyada kai.

Daga gefe A cikin akwatin, akwai wani envelope mai rubutun:

RECORD OF ORIGINAL AGREEMENTS

Zaid ya buɗe shi, A ciki akwai wata takarda da Rahman ya rubuta kafin rasuwarsa, wannan rubutun baba ne, zayd ya fadi a raunane, mammi ta duba, tabbas handwriting din mijinta ne

Ya karanta ta a bayyane:

“An yi ainihin copies uku na yarjejeniyar haɗin gwiwar Northern Crest Holdings. An ba Bashir Misalati copy na farko, ni kuma na riƙe na biyu. An ba lauyanmu copy na uku domin adanawa a matsayin hujja mai zaman kanta. Babu wani daga cikinmu da zai canza ko lalata waɗannan copies din”

Maryam ta kalli Zaid.

“Copies uku…”

Zaid ya ci gaba da karantawa.

“Bayan rasuwar lauyanmu, an mayar da wasu takardu daga ofishinsa. Na karɓi copy din da yake hannunsa tare da sauran bayanan da suka shafi yarjejeniyar. Na ajiye shi a cikin wannan file domin kada a rasa shi.”

Hajiya Raliya ta yi mamaki.

“To, copy lauyan ne wannan kenan, Toh Ina na rahman?

Zaid ya nuna mata takardar.

“Haka akache a nan, kuma tabbas rubutun baba ne”

“Wato akwai copies uku na asali tun farko, sannan copy din lauyan ya dawo hannun shi bayan rasuwar lauyan?”

“Exactly,” Zaid ya amsa. “Copy din da ke hannun lauyan ba wani sabo ba ne da aka ƙirƙira daga baya ba, Asali na uku ne, wanda aka mayar wa baba bayan rasuwar lauyan.”

A ƙarƙashin bayanin, akwai jerin takardun da aka karɓa daga ofishin lauyan, da kwanan wata, da sa hannun mutumin da ya tabbatar da karɓar su.

Akwai kuma takardar da yaran lauyan suka sanya wa hannu bayan rasuwar mahaifinsu, tana tabbatar da cewa an mika ragowar files din dake hannun mahaifinsu ga Rahman bisa buƙatar da ya gabatar.

Maryam ta kalli sunayen.

Mammi ta sauke numfashi

“Alhamdulillah! Gaskiya tanata bayyana.”

Zaid ya juya zuwa ƙarshen file ɗin. A can akwai wani envelope da aka rubuta:

PRIVATE — TO BE OPENED ONLY IF THE AGREEMENT IS CHALLENGED

Ya buɗe shi a hankali.

A ciki akwai takardar da Rahman ya rubuta, tare da wasu copies na bayanan banki, rahoton binciken kuɗi, da jerin sunayen mutanen da suka sa hannu a wasu ma’amaloli.

A ƙasan takardar, akwai rubutu mai kauri kamar an tura shi dakyau saboda anaso a ganshi 

“Bashir ya gano cewa ana karkatar da kuɗin kamfani, ina kwache a gida Banida lfya, Ya zo wurina da hujjoji, kuma ya tabbatar min da wanda ke satar kuddin, ya kuma ce yana son a dauki mataki amma yanajin nauyi sabida ni. Na ba shi shawarar ya tattara duk abin da yake da shi na hujja ya kawo min su a nan gida kafin ya fuskanci mutumin da yake zargi, Idan wani abu ya same shi kafin a kammala binciken, a duba waɗannan bayanan da kuma sa hannun da ke kan izinin cire kuɗi. Kwanakin baya na gayama Fahad asalin alaqar shi damu, yanayin da na gani a fuskar shi lokacin da nache mishi Alh bashir nada rabin kaso a northern crest ya nuna tsananin tashin hnkali fiyeda yadda yaji lokacin da yasan bamu muka haife shi ba, saboda haka nache mishi kada ya bari abun Duniya ya rufe mishi ido ko ya kaishi ga aikata wani abu, amma ynzu reports din da Alh bashir ya kawo min sun tabbatar min da Fahad be dauki shawarata ba, bayan haka, shekaranjiya ya shigo dakina da dare, yana tunanin ko nayi baccee, ya bude safe dita ya dauko copy din agreement dina ya fita dashi besan ina kallon shi ba, don haka in shaa Allah za’a dauki matakin da ya dache. Wannan copy din agreement din da ke cikin file dinnan shine wanda ke hannun lawyer dinmu da ya rasu, don haka za’a iya amfani dashi, akwai signature dina da ta Bashir a ciki, hadda shedu guda biyu sannan da sa hannun lauyan mu”

Maryam ta fara kuka sosai.

Zaid ya rungumeta

“I’m sorry, Haya.”

Ta riƙe rigarsa.

“Ya rasu yana ƙoƙarin kare gaskiya, kuma an bar mutane suna tunanin cewa shi ne mai laifi.”

Mammi ma ta share hawayenta.

“Allah Ya jiƙansa. Allah ya saka masa da aljanna.”

Zaid ya duba sauran takardun. Akwai copy din wata wasiƙa da Bashir ya aika wa Rahman, yana neman a yi binciken kuɗin kamfanin kafin a ɗauki matakin shari’a.

A ƙarshen file ɗin, akwai wata takarda da aka rubuta:


PERSON OF INTEREST: FAHAD RAHMAN BALARABE

A ciki, an jera ma’amalolin da ya amince da su, bayanan kuɗin da suka ɓace, da kuma takardun da aka canza bayan Bashir ya fara bincike.

Maryam ta kalli sunan Fahad.

“Fahad…”

Zaid ya yi shiru na ɗan lokaci yana tunanin dan uwan shi 

Hajiya Raliya ta sauke numfashi

“Dole ne a kai waɗannan takardu ga hukumomi”

Zaid ya fara shirya takardun a hankali, ya ware ainihin copy da agreement tsakanin Alh Bashir da Alh Rahman, ya ɗauki hotunan kowane shafi, sannan ya rubuta jerin abubuwan da za a buƙaci ƙwararru su tantance

Maryam ta share hawayenta.

“Yanzu mun samu hujjoji masu ma’ana da za su kai mu ga gaskiya, yarjejeniyar asali, bayanan kuɗi, takardun amincewa da aka sauya, da kuma shaidar mutanen da suka riƙe waɗannan takardu a hannunsu.”

A lokacin ne wayar Zaid ta yi ƙara.

Saƙo ne daga unknown number.

“Yanzu kun ga abin da margayi Rahman ya ɓoye, akwai wani mutum da ya san yadda aka shirya zargin Bashir, kuma shima zezo ya fadi abnda ya sani”

Zaid ya nuna wa Maryam saƙon.

Ta kalle shi cikin mamaki.

“Wane mutum kuma?”

Zaid ya ajiye wayar.

“Someone who was involved, or someone who knows who was involved.”

A lokacin ne suka ji ƙarar ƙwanƙwasa ƙofa

Duk suka juya, zaid ya tambayi waye 

Ali ne a tsaye a ƙofar, ya bude ya shigo da sallama

Suka amsa duk suna kallon shi, ita dai mammi zaune kawai take amma ta kasa magana tundazu da komi yayi nuni zuwa ga Fahad gabadaya bata cikin natsuwarta, ta rasa me takeji a ranta

“Sir, inaso inyi magana daku idan ba matsala”

Zaid ya kalle shi cikin shakku, yana ganin shi tareda Fahad, har gida yana ganin shi yana zuwa wani lokaci wurin Fahad 

“Lfya?”

Ali ya kalli Maryam, sannan ya sunkuyar da kai.

“Maganar Oga Fahad, da maganar Aisha.”

Maryam ta miƙe tsaye.

“Aisha? Me ka sani game da yayata?”

Zaid ya tashi ya riqe hannunta yana zaunar da ita a hnkali 

Ali ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya dago kai

“Nazo ne inyi bayanin komai”

“Bismillah zauna” chewar zayd

Hajiya Raliya kam tasan Ali, amma bata taba tunanin zezo nan ba, balle a wannan lokacin 

Ali ya zauna a gabansu, ya kasa ɗaga kai ya kalli Maryam da ta kafe shi da idanu kamar zasu fito

Zaid ya fara magana.

“Muna jinka, bismillah”

Ali ya numfasa sosai.

“Na daɗe ina ɓoye wannan magana bnsan yadda zata fito ba, amma nasan dole ta bayyana saboda na yi wa mahaifina alkawari, koda na gaya muku a loakcin da mahaifina ya gayamin ba lallai ku yadda dani ba, amma yanzu da kuka riga kuka ga FILE 17, lokaci ya yi da gaskiya za ta fito.”

Mammi da zaid mamakinsu ya fito qarara ta yadda yasan file 17 yayin da maryam ta qosa taji gameda Aisha 

Maryam ta riƙe hannun Zaid.

“Ka san inda Aisha take?”

Ali ya ɗaga kai.

“Eh.”

Maryam ta miƙe tsaye da sauri.

“Ina take? Ina yayata take?”

Ali ya ɗaga hannunsa kaɗan.

“ki yi haƙuri. Zan bayyana miki komai, amma ki ba ni damar in fara daga inda abin ya samo asali.”

Zayd ya sake zaunar da ita a hankali yana riqe hannyenta cikin nashi, zuciyarta tana bugawa.

Ali ya fara magana.

“Na yi aiki tare da Fahad tsawon shekaru. Ya amince da ni saboda yana ganin ina yi masa biyayya. Ya ɗauke ni a matsayin mutumin da zai iya taimaka masa wajen gano duk wanda yake binciken abubuwan da suka faru a Northern Crest, sannan kuma yana sani ina yimishi ayyuka daban daban”

Zaid ya kalle shi.

“Amma kai ne kake aiko muna saƙonnin kana ɓoye sunanka.”

Ali ya ɗaga kai cikin mamaki.

“Eh nine, ya akayi kuka gane?”

Zaid ya gyada kai.

“Saƙonninka sun ƙunshi bayanai da yawa fiye da kima, ka san abubuwa kan gidan nan, kuma ka san abin da Fahad yake nema.”

Ali ya sauke numfashi.

“Eh, nine nake aiko muku saƙonnin, Ni ne na samo mabudin da ze iya bude wannan qofar na ɓoye mabuɗin a qasan kujerun garden. Na san cewa idan kuka samu damar shiga ɗakin, za ku iya gano abin da margayi Rahman ya ɓoye.”

Maryam ta kalle shi.

“Amma me ya sa ka taimaka mana, alhali kana aiki da Fahad?”

Ali ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya amsa.

“Saboda mahaifina yana da hannu a wasu abubuwan da suka faru a Northern Crest. Ya taimaka wa Fahad wajen canza wasu bayanai da sukasa aka zargi Bashir da laifin da bai aikata ba. Mahaifina ya yi shiru na tsawon lokaci, amma daga baya laifin ya fara damunsa sosai, har Ya bar aiki kamfanin, kuma kafin ya rasu ya gaya mini duk abin da yayi”

Mammi ta kalli Ali cikin mamaki.

“Wato mahaifinka ya san abin da ya faru?”

Ali ya sunkuyar da kai.

“Ya san wasu daga cikin abubuwan da suka faru, ya san cewa an yi wa Bashir zalunci, Ya kuma san cewa Fahad yana ƙoƙarin ɓoye wasu hujjoji.”

Zaid ya tambaya

“Did your father give you any documents?”

“Aa ya dai bar mini wasu bayanai da sunayen mutanen da suka san abin da ya faru. Amma bai bar mini documents ba. Shi ya gayamin komai gameda file 17, yache a lokacin da abun ke faruwa yazo ya gayama Alh Rahman gaskiyar duk abnda ya faru, kuma Alh Rahman yache mishi kada ya damu ya Riga yayi recording komai ya ajiye cikin file 17, ze kira Bashir ya bashi, amma se gashi ya rasu kafin yaba alh Bashir, kuma ana tsakiyar binciken alh Bashir shima ya rasu, mahaifina ya shiga tsananin tashin hnkali lokacin”

Ali ya kalli Maryam.

“Ya kuma gaya mini cewa Alh Bashir yana da ’ya’ya mata biyu, Kuma Ya ji labarin cewa babbar ’yarsa ta fara aiki a Northern Crest don haka inje in taimake ta, wannan Itache wasiyyar qarshe da ya barmin, yache in gayama Aisha ta nemi file 17, lokacin ne naje na nemi aikin security a northern crest, kuma nasan yadda nayi har Fahad ya lura dani ya fara sani ina mishi aiki, a hnkali a hnkali har ya yadda dani sosai, Lokacin da Fahad ya kirani yache yana son a kamo mishi Aisha, na fara fahimtar cewa rayuwar ’yan gidan margayi Bashir tana cikin haɗari gabadaya”

Maryam ta fara kuka.

“Ka san yayata kenan?”

Ali ya gyada kai.

“Eh. Kuma ba wai ina jin labarinta kawai ba ne,  Na taimaka mata.”

Maryam ta rufe bakinta da hannunta tana chigaba da kuka

Hajiya Raliya ta ɗago kai, 

“Ali ka bayyana komai kawai har inda zan shigo cikin labarin”

da wani irin mamaki suka kalleta duka hadda mammi da take zaune tundazu kamar robot tana bin kowa da ido

Ali ya numfasa sosai.

“A shekaru uku da suka wuche, nine Oga Fahad yasa in sato mishi Aisha, kuma na aiwatar da abnda ya umurceni ba don in cutar da Aisha ba, se don inga abnda Fahad yake qoqarin yi kuma in tabbatar da zargin da mahaifina yache min yanayi gameda chewa Fahad shine wanda ya qirqiri hatsarin da yayi sanadiyyar margayi Bashir”

Dam! Damm!! Dammm!! 

Haka qirjin Zayd, Mammi, da maryam ke bugawa da tsananin qarfin gaske, bnda hajiya raliya da ta riga tasan komai

“Seda na tabbatar da dalilin da yasa na sato Aisha saboda tana binciken abubuwan da suka shafi mutuwar mahaifinta da kuma wasu bayanan abubuwan Northern Crest, a lokacin na tabbatar da komai, hatta da chewa shi ya hada accident din da yayi sanadiyayr rayuwar alh bashir, saboda sanda yazo a chan kangon gidan da muka ajiye Aisha a chan qauyen dange shuni, kiri kiri ya gayamata chewa ze kawar da ita kamar yadda ya kawar da mahaifinta, na san cewa idan na bayyana komai kai tsaye, Fahd ze iya batar dani nima, kuma idan nazo na gaya muku a lokacin bazaku yadda ba saboda ku ahalin shi ne, don haka na yi amfani da damar da nake da ita wajen taimaka mata ta tsere, nache tayita gudu har se ta tsira kuma ta boye, an dauki dan lokaci kafin sauran mutanen da muke tare dasu su ankara chewa ta gudu, daga nan na bisu tare muka bazama nemanta, nasan hanyar da tabi don haka nache musu zanje ta nan su kuma subi sauran hanyoyin, ina binta a baya ina ganinta sanda take gudu har ta hau titi mota ta bugeta, matar da ke cikin motar ta fito tareda driver suna duba ta, a lokacin na iso kan titin nache don Allah su taimaka su tafi da ita a kaita asibiti sabida rayuwarta na cikin hadari, na karbi number wayarta nache gobe zan kira ta, daga nan na dawo na hadu da sauran nache musu ban ganta ba sukace suma basu ganta ba,na kira Fahd na gaya mishi ta gudu, ya shiga tashin hankali sosai, nache mishi kada ya damu zamu nemo ta”

Maryam ta katse shi 

“An kaita asibiti? Ta rayu?”

“Washegari na kira lambar matar nan ta gayamin asibitin da ta takai maryam tache amma tazo wani aiki ne a sokoto don haka bata asibitin a lokacin amma ta kusa komawa, naje asibitin na shiga dakin da ta gayamin na tarar da maryam tana baccee, ina nan har matar tazo ta sameni, tache min inyi hakuri tazo supervising aiki ne a northern crest, gabana ya fadi kuma naji tsoro sosai, daga nan tache in gaya mata abnda ke faruwa, nache mata ai qanwata che yan fashi suka biyomu amma ynzu komi lfya, tayimin kallon tuhuma, tache idan ban gaya mata gaskiya ba zata hadani da yan sanda saboda jiya da suka kawo Aisha asibiti tanata surutu cikin fitar hayyaci tana chewa Fahad rahman shi ya kashe babanta Bashir maisalati, a raina nache shikenan mun kawo kan mu inda zaa halaka mu, ina cikin tunanin yadda zanyi mu tsira da rayuwar mu se baiwar Allahn ta dafa kafada ta tache sunanta hajiya raliya, kuma ita yayar margayi Rahman Balarabe che, tanaso in gaya mata komai, kuma tayi alqawarin taimaka muna, nan na fayyace mata komai, ita tache min in tafi in chigaba da aiki da Fahad ina lura dashi, kuma zatayi jinyar Aisha, zata dauketa taje da ita Abj ta boyeta a chan, saboda sanadiyyar buguwar da Aisha tayi jiya ta kamu da post traumatic amnesia, wato ta manta da abunda ya faru, amma in shaa Allah ana saka ran cikin wani dan lokaci zata tuna, ita ta tafi da Aisha Abuja bayan an sallameta, kuma tayita kula da ita tsawon Shekaru biyu kafin ta kirani tache Aisha taji sauki kuma ta tuna rayuwarta ta baya, amma bazata bari ta dawo gida ba don kada a chutar da ita da ahalinta, na goyi bayan haka, muna nan muna shawarar yadda zaayi se hajiya raliya tazo muna da labarin maryam zata auri Zayd, hnkalin Aisha ya tashi sosae tache inyi qoqari in hana auren shiyasa lokacin na aiko miki ta takardar nan nache kada ki auri zayd Balarabe kuma har bayan auren inata dan gargadin ki, amma daga baya da hajiya raliya taji abnda mukeyi tache mu dena, idan har taimako zamuyi toh sedai idan zan lurar daku abnda na sani ba tareda ba bayyana kaina ba tunda bamuda sheda, tache idan har kikasan wani abu toh zaki yima zayd magana kuma zaku iya fara bincike har Allah yasa ku gane gaskiya”

Maryam ta share hawayenta, tana girgiza kai.

“Kun san irin wahalar da muka sha? Mama tana kuka kullum na tsawon watanni, Ni kuma na yi tunanin na rasa yayata har abada.”

Ali ya sunkuyar da kai.

Hajiya Raliya ta karbi zanchen 

“Na san cewa kun sha wahala, kuma na yi nadamar rashin bayyana muku gaskiya da wuri, Amma na yi imanin cewa idan Fahad ya gano cewa Aisha tana raye, zai iya sake neman cutar da ita daku gabadaya”

Maryam ta kama hannun Zaid, tana kuka.

“Rouhi, yayata tana raye…”

Zaid ya rungume ta.

“Na ji, Haya. She’s alive alhamdulillah”

Maryam ta juya ta kalli Ali ta kalli hajiya raliya 

“Don Allah, ka kai ni wurinta. Ina so in gan ta yanzu. Ina so in rungume ta. Ina so in tabbatar da cewa ba mafarki nake yi ba.”

Ali ya kalleta da tausayawa.

“Maryam, ki yi haƙuri. Ba sai kin je nemanta ba.”

Ta kalle shi a rude

“Me kake nufi?”

Ali ya yi murmushi kaɗan.

“Aisha tana kan hanyarta ta zuwa nan ynzu haka, Hajiya Raliya ta aika driver yazo da ita”

Maryam ta tsaya cak.

“Me?”

Hajiya Raliya ta kalleta cikin tausayi 

Ai tunda file 17 ya bayyana munada hujja kuma kowa ya yadda da abnda Fahad ya aikata don haka ynzu dukanmu zamu iya kare Aisha”

Maryam ta fashe da kuka, ta rufe fuskarta da hannayenta.

“Ya Allah…”

Mammi ta miqe zata tashi tsaye amma ta tafi qasa luuu, zayd ne yayi saurin riqota amma ta suma, maryam tayi saurin dauko bottled water din da ke ajiye gefen table tana shafa mata a fuska se kuka takeyi “Mammi, mammi, don Allah mammi ki tashi” Mammi taja numfashi ta bude ido tana kallonsu, ynzu kam ta tabbata ba mafarki takeyi ba, lokacin ne wani irin kuka me raunana zuciyar me saurare ya kucce mata, se chewa takeyi “Fahad..Fahad..Fahad dina, dana, yarona..” ta rungume maryam wadda itama kukan taketa yi, se hajiya raliya da zayd da keta lallashin su, gabadaya hnkalin zayd a tashe yake, beson kukan nan yasa hawan jinin mammi ya tashi, a gefe daya yana tsoron kar kukan maryam ya janyo mata wani complication, sannan kuma ga tunanin abnda dan uwan shi ya aikata

Hajiya Raliya se famar share hawaye takeyi

Ali kuma zaune yake shuru yanajin kamar ya sauke nauyin da mahaifinshi ya daura mishi

Zaid ya riƙe Maryam a hannunsa.

“Your sister is coming home, Haya, kukan ya isa haka pleaseee”

Maryam ta ɗaga kai tana kuka.

“Rouhi, ban san abin da zan ce ba. Nayi tunanin cewa wataƙila ba zan sake ganinta ba.”

“You don’t have to say anything. Just get ready to see her.”

Ali ya miƙe tsaye.

“Zan dan fita waje, ni Fahad yasa in kula da duk abnda ke faruwa a gidan nan, Amma akwai abu ɗaya da nake son ku sani, Fahad bai san cewa Aisha tana raye ba. Kuma yanzu da ya fara zargin cewa wani yana taimaka muku, dole ne mu yi taka tsantsan.”

Zaid ya gyada kai.

“Zamu kiyaye”

Ali ya amsa:

“Hakan shi ne yafi.”

Maryam ta share hawayenta tana qara rungume mammi da ke zaune amma hawayenta sun kasa daina fitowa 

Ta shafe shekaru tana tunanin cewa ƙaddararta ita ce rayuwa cikin rashin tabbas, tana kewar mahaifinta da ’yar’uwarta.

Amma a yau, bayan sun gano FILE 17, bayan sun ga hujjojin da za su iya wanke sunan mahaifinta, yanzu kuma ta san cewa Aisha tana raye kuma zata dawo gida.

Bayan wasu mintuna, Maryam ta ji ƙarar mota a harabar gidan.

Ta miƙe tsaye da sauri, zuciyarta tana bugawa.

Zaid ya kama hannunta.

“Easy, Haya.”

Ta girgiza kai, hawaye suna gangarowa a fuskarta.

“Ba zan iya ba, Rouhi. Ina son in gan ta.”

Tare suka fita

A nesa, Maryam ta hango wata mata tana takowa a hankali. Fuskarta ta dan canza, amma be hana maryam ta ganeta ba

Aisha.

Maryam ta rufe bakinta da hannunta.

“Aisha…”

Aisha ta tsaya tana kallon wadda ke tsaye a bakin ƙofar, idanunta suka cika da hawaye.

“Maryam…”

Maryam ta sheqa zuwa gare ta, suka rungume juna da ƙarfi.

“Na yi tunanin na rasa ki har abada!”

Aisha ta rungume ta tana kuka.

“Ki yi haƙuri, Maryam. Ki yi haƙuri…”

Mammi se share hawayenta takeyi 

“Alhamdulillah!” Kawai ta iya furtawa saboda zuciyar da ke wani irin nauyi

Zaid ya tsaya yana kallonsu, zuciyarsa cike da godiya ga Allah, Hajiya Raliya ta share hawayenta, yayin da Ali ya tsaya a gefe, yana jin sauƙi a ranshi, a ƙarshe ya cika alkawarin da ya yi wa mahaifinsa.

Amma farin cikin dawowar Aisha ba yana nufin cewa komai ya ƙare ba.

Fahad har yanzu yana waje, bai san cewa mutanen da yake ƙoƙarin ɓoyewa gaskiyarsu sun haɗu ba.

Yanzu suna da FILE 17, hujjojin, yarjejeniyar Rahman da Bashir, da kuma Aisha wadda za ta iya ba da shaidar abin da ta sani.


 Tabbas gaskiya na iya jinkiri… amma ba lallai ta ɓace ba. ❤️‍🔥


Join our WhatsApp group:

***

79C9C35F-C506-4CF1-AE01-804821F10288.png