KADDARAR ZUCIYA

THE PROMISE OF HALAL

by @jiddaahbarkum

KADDARAR ZUCIYA

CHAPTER FORTY-TWO: 42

THE PROMISE OF HALAL

JIDDAAH BARKUM

——-

Bayan Nana ta sauko ƙasa, ta nufi wajen dining table ɗin da ta ajiye abinci, inda Umar yake zaune, ta fara zuba masa abinci, amma tun kafin ta gama, Umar ya lura cewa sam ba ta da walwala, fuskarta ba ta nuna farin ciki ba, kuma motsinta ya rasa kuzarin da ya saba gani a tare da ita, lokacin da ta ɗauki warmer ɗin pepper soup domin ta zuba masa, sai ya miƙa hannu ya riƙe hannunta a hankali, yana kallon fuskarta, Nana ta ɗago kai, suka haɗa ido, Umar ya ɗaga gira ɗaya, sannan ya tambaya cikin natsuwa, “What’s wrong, Madam?” Nana ta ƙaƙalo wani ɗan gajeren murmushi, irin na wanda yake ƙoƙarin ɓoye damuwarsa, “Nothing, babe… kawai ina ɗan jin ciwon kai ne, I need to get some rest,” Umar ya gyada kansa cikin fahimta, “Bani, na ƙarasa zubawa, ki ɗan ci abinci kaɗan, sai ki sha magani ki kwanta,” ya karɓi warmer ɗin daga hannunta, ya zuba abincin, sannan ya fara ba ta a baki da kansa, duk da cewa Nana ba ta da sha’awar cin abincin, ta ci kaɗan-kaɗan saboda ba ta son ta ƙi abin da yake yi mata, Umar bai matsa mata ba, ya ci gaba da ba ta abincin cikin kulawa har sai da ta ce ta ƙoshi, bayan sun gama, ya kama hannunta ya raka ta har ɗakinsu, ya taimaka mata ta kwanta, sannan ya rufa mata bargo, ya sunkuya ya yi mata peck a goshinta, “Rest well, darling,” Nana ta kalle shi da ɗan murmushi, amma zuciyarta har yanzu cike take da damuwar da ta kasa bayyana masa, Umar ya juyo ya fita, ya nufi study room ɗinsa domin samun sararin yin tunani.

A ɗayan ɓangaren kuma, Aliyu ya fito daga wanka, ya nufi inda ya ajiye wayarsa, yana ɗaukar wayar, sai ya ga alamar cewa Inteesar ta kira shi, kuma an amsa kiran, ya ɗan tsaya cak, yana kallon wayar cikin mamaki, daga nan ya juya ya dubi matarsa, Safiyya, wadda ke zaune tana danna wayarta, “An kirani… me ya sa kika ɗaga wayata?” Aliyu ya tambaya cikin murya mai ɗauke da zargi da ɓacin rai, Safiyya ta ɗago ta kalle shi sama da ƙasa, kafin ta amsa cikin halin ko-in-kula, “Na ga ba ka kusa ne, and ba wani abu mai zafi na faɗa ba, kawai na ce ka shiga wankan Sunnah ne… Is that an offence?” Ta faɗa tana kafe shi da idanunta, kamar ba ta ga wani laifi a abin da ta yi ba, Aliyu ya kalle ta cikin tsantsar mamaki da firgici, “Safiyya, is that what you told her?” Ya faɗa cikin ɓacin rai, domin ya san cewa wannan ba ƙaramin abu ba ne a wajen Inteesar, ya san Inteesar tana ƙoƙarin sabawa da kasancewarsa mai mata biyu, kuma ba ya son wani abu ya faru da zai sa ta fara shakkar dangantakarsu, ganin cewa Safiyya za ta iya jawo musu babbar matsala, Aliyu bai tsaya saurarenta ba, ya juya da sauri ya fita daga ɗakin, yana danna kiran Inteesar, a wannan lokacin, jikinsa har rawa yake yi saboda fargaba, yana tafiya cikin gidan yana jiran ta ɗaga, amma shiru, ya fita waje gaba ɗaya, wayarsa tana ta ringing, amma babu amsa, Aliyu bai karaya ba, ya sake danna kira na biyu, sannan na uku, ya ci gaba da ƙoƙari, yana fatan Inteesar za ta ɗaga wayar ko da kuwa tana cikin wani yanayi ne, amma a ƙarshe, sai ya ji muryar na’ura tana sanar da shi cewa wayar a kashe take, ya tsaya a wurin na ɗan lokaci, yana kallon wayarsa, “Ya Allah…” ya furta a hankali.

A ɗayan ɓangaren kuma, Inteesar tana kwance rubda-ciki a kan pillow, tana kuka yayin da take kallon yadda wayarta ke ta haskakawa da kiran Aliyu, tana ji tana gani, amma ta ƙi ɗagawa, kowane sabon kira yana ƙara hura mata wutar kishin da ke ƙirjinta, ba ta son jin muryarsa a wannan lokacin, domin tana tsoron idan ta ji shi, za ta kasa ɓoye masa raɗaɗin da take ji, ganin kiran yana neman ya dame ta, ta miƙa hannu da ƙyar ta ɗauki wayar, ba tare da ta duba ko ta yi wani tunani ba, ta danna maɓallin kashe wayar gaba ɗaya, ta jefa wayar a gefe guda, sannan ta sake rushewa da sabon kuka, a wannan lokacin, ba ta son jin komai, ba ta son tunanin matar da ta ɗauki wayar, ba ta son tunanin yadda Aliyu yake rayuwa a gidansa, abin da take so kawai shi ne ta samu damar yin kuka ba tare da wani ya ji ta ba.

Aliyu ya sake komawa ɗakin Safiyya, fuskarsa cike da ɓacin rai, a karon farko cikin shekaru da dama, ya ji wani irin rashin jin daɗin halinta, ba wai don ya ɗauki abin da ta yi a matsayin ƙaramin abu ba, sai don ya san yadda hakan zai iya shafar dangantakarsa da Inteesar, ya tsaya gabanta, sannan ya kira sunanta, “Safiyya,” ta ɗago kai, “Na’am?” Muryar Aliyu ta yi sanyi, amma tana ɗauke da gargaɗi mai nauyi, “A da ni ne na ba ki damar ɗaukar wayata a duk lokacin da kike so, amma daga yanzu, na hana wannan, kada na sake ajiye waya ki ɗauka, ko da an kirani ki ɗaga,” ya faɗa cikin tsauraran kalamai, yana nuna cewa wannan karon ba wasa yake yi ba, Safiyya ta ɗan daure fuska, “Ni fa ban yi komai ba,” Aliyu ya girgiza kai, “Kin yi, saboda kin san abin da kalamanki za su iya haifarwa, sannan kasancewata a gida ba yana nufin babu wanda zai kirani ba ne, ki sake ki kiyaye hakan,” kalaman nasa sun fi dukan tsawa zafi, domin Aliyu mutum ne mai sanyin hali, idan har ya kai ga yin magana da wannan yanayin, to lallai abin ya ɓata masa rai, ya juya ya fita, ya bar Safiyya tana bin sa da kallo, tana taɓe baki.

Tun daga wannan lokacin, Aliyu ya kasa samun nutsuwa, ya dafe kansa, sannan ya fita ya faɗa kan kujera, yana ƙoƙarin tsara tunaninsa, yana tunanin yadda abubuwa suka rikice cikin ƙanƙanin lokaci, ya san cewa Inteesar ta riga ta san yana da mata biyu, amma ya kuma san cewa sanin abu da fuskantar sa a zahiri abubuwa ne biyu daban, ya san ta ji zafi, abin da bai sani ba shi ne girman zafin da take ji a wannan lokacin, ganin yadda abubuwa ke neman lalacewa, sai Aliyu ya yanke wani hukunci a ransa, ya ƙudura cewa ba zai ƙara ɓata lokaci ba, zai tura magabatansa zuwa gidan Alhaji Kabeeru domin su nemi masa auren Inteesar a hukumance, ya gaji da ɓoye soyayyarsa, ya gaji da jira, ya gaji da kasancewa nesa da matar da zuciyarsa ta zaɓa, alhali yana son ya gina rayuwa da ita cikin halal, a gefe guda kuma, hankalinsa ya kasa kwanciya saboda sanin cewa wayarta tana a kashe, ya ɗauki wayarsa, ya fara aika mata saƙonnin neman afuwa ta WhatsApp da text message, yana bayyana mata gaskiyar abin da ya faru tare da fatan za ta kunna wayarta ta ga saƙonnin, ya rubuta mata, babygirl, please ki yi haƙuri, wallahi ban san za ta ɗaga wayar ba, kada ki yi min hukunci da laifin da ba nawa ba, ya tsaya na ɗan lokaci, yana kallon saƙonnin, kafin ya sake rubuta wani, please, babygirl, kada ki yi fushi da ni saboda abin da ban shirya ba, I miss you, please, babygirl… I love you, ya aika saƙonnin, sannan ya jingina bayansa da kujera, yana sauke numfashi mai nauyi, “Ya Salam…” ya sake faɗa a hankali, zuciyarsa tana son ta ji muryar Inteesar, ko da kuwa za ta yi masa faɗa ne, abin da yake so kawai shi ne ya tabbatar da cewa ba ta yanke shawarar nisanta kanta da shi ba saboda abin da ya faru.

Da daddare, Inteesar ta kunna wayarta, nan take saƙonni suka fara shigowa jere-jere, har wayar ta yi ta jijjiga a hannunta, ta turo baki, sannan ta buɗe saƙonnin Aliyu, ta karanta su ɗaya bayan ɗaya, tana ƙoƙarin hana zuciyarta tausaya masa, babygirl, please ki yi haƙuri, wallahi ban san za ta ɗaga wayar ba, kada ki yi min hukunci da laifin da ba nawa ba, please, babygirl, kada ki yi fushi da ni saboda abin da ban shirya ba, I miss you, please, babygirl… I love you, Inteesar ta yi shiru, ta karanta saƙonnin sau biyu, amma duk da haka, kalaman matar sun kasa fita daga cikin kanta, tana cikin wannan tunanin, sai wayarta ta sake ringing, ta kalli screen ɗin, Mi Amor ❤️ Sunansa ya bayyana a kan wayar, ta yi shiru, tana kallon sunan na ɗan lokaci, kafin ta kyale kiran ya yanke, bai ɗauki lokaci ba, ya sake kira, ta share kiran, ya sake kira na uku, Inteesar ta cije leɓenta, tana ƙoƙarin hana kanta ɗagawa, amma da ya sake kira a karo na huɗu, sai ta ɗaga wayar a hankali, ba ta ce komai ba, a ɗayan ɓangaren kuwa, da Aliyu ya ji an ɗaga wayar, sai ya sauke numfashi mai nauyi, “Alhamdulillah… Babygirl…” Shiru, ya ɗan jira, amma ba ta amsa ba, “Please, ki yi magana,” har yanzu shiru, Inteesar ta turo baki, tana kallon bango kamar Aliyu yana iya ganinta, Aliyu ya yi murmushi a ɗayan ɓangaren, “Okay, ko ba kya son magana, ki bar ni in yi, wai kina so ki kashe ni ne? Tun safe na rasa nutsuwata,” a hankali, Inteesar ta buɗe baki ta ce, “Ka gama?” Nan take Aliyu ya yi murmushi mai faɗi, “Finally! Kin yi magana,” ta amsa sama-sama, “Uhmm,” “Yanzu ka samu abin da kake so,” ta faɗa cikin ɗan fushi, “A’a, abin da nake so shi ne murmushinki,” ta ƙara turo baki, “To ai kana da waɗanda za su yi murmushin, ka ji daɗi,” Aliyu ya yi shiru na daƙiƙa kaɗan, kafin ya fahimci inda maganarta ta dosa, sai ya yi murmushi, “Babygirl… are you jealous?” “Ba ruwanka,” nan take ya saki wata dariya mai daɗi, “Allah! Kin san yadda kishinki yake da daɗi?” “Mi Amor, har yanzu ina fushi,” “Good,” Inteesar ta zaro ido, duk da cewa ba ya iya ganinta, “Good?” “Eh, saboda hakan yana nufin kina sona,” ta yi ƙoƙarin riƙe fushinta, amma ta kasa hana kanta dariya, Aliyu ya ji dariyarta, kuma a take zuciyarsa ta yi wani irin laushi, kamar an cire masa wani nauyi daga ƙirji, “That’s my girl,” ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan muryarsa ta sauya zuwa wata mai cike da taushin zuciya, “Babygirl… thank you,” ta ɗan yi mamaki, “Saboda me?” “Saboda duk da shekaruna, duk da cewa ina da mata biyu, har yanzu kika zaɓe ni,” Inteesar ta yi murmushi, amma ba ta ce komai ba, Aliyu ya lumshe idanunsa, yana murmushi shi kaɗai, “Ya Allah… kin san kina sa ni jin kamar matashi?” Ta yi dariya, “Ni ma ai ina kallonka kamar ɗan shekara ashirin,” Aliyu ya dafe ƙirjinsa kamar ta harbe shi da kalamanta, “One day, you’ll kill me with love,” dukansu suka yi dariya, sai dai bayan dariyar ta lafa, Aliyu ya yi shiru na ɗan lokaci, a wannan karon, akwai wani abu mai muhimmanci da yake son ya tambaye ta, “Babygirl…” “Uhmm?” “Zan iya tura magabatana wajen Daddy?” Nan take zuciyar Inteesar ta fara bugawa da sauri, ta miƙe zaune a kan gadon, tana riƙe da wayar sosai a kunnenta, Aliyu ya ci gaba cikin natsuwa, muryarsa cike da gaskiya, “Na gaji da sonki a ɓoye, ina son ki zama halal dina, ki ba ni izini, su zo su nema min aurenki,” shiru ya mamaye wayar, Inteesar ta sunkuyar da kanta, tana jin kunya da farin ciki sun haɗu a zuciyarta, wannan shi ne abin da ta daɗe tana jira, amma jin sa daga bakin Aliyu ya sa maganar ta zama kamar mafarki, a hankali ta yi murmushi, “Mi Amor…” “Uhmm?” “Na amince,” Aliyu ya lumshe idanunsa, “Alhamdulillah…” Ya sauke numfashi mai nauyi, kamar an cire masa wani babban kaya daga zuciya, “Thank you, Babygirl, wallahi, ba za ki taɓa nadamar amincewa da ni ba,” sai ya ƙara da wata murya mai cike da tsantsar soyayya, yana son ya tabbatar mata cewa ba kalaman baki kawai yake yi ba, “And I promise you…” Ya ɗan dakata, “From now on, I will spend the rest of my life proving that you made the right choice,” Inteesar ta lumshe idanunta, wani murmushi mai cike da nutsuwa yana shimfiɗe a fuskarta, a wannan lokacin, zuciyarta ta yi mata wani irin daɗi da ba ta iya bayyanawa, domin a karon farko, ba wai kawai tana jin Aliyu yana sonta ba ne, tana jin yana son ya ɗauki alhakin soyayyarsu, yana son ya fito fili da ita, yana son ya nemi yardar iyayenta, ya bi hanyar da ta dace, ya mayar da ita halal ɗinsa, a karon farko… Kalmar halal ta sa zuciyarta bugawa fiye da kalmar I love you.