LOKACI

LOKACI CHAPTER 26

by @fulani32

***


  ⏳🕛 LOKACI 🕛⏳

RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI 

YOTA

Under Team Yota's Amazing Pen's.

FULANI ❣️ 
***

  PAGE 2️⃣ 6️⃣

A hankali ya tura ƙofar ofishinsa ya shiga, yana jin har lokacin yanda muryarta take amsa kuwwa a cikin kunnuwansa.

"Akan wani kike cewa na rabu da ke?"

Kai tsaye ta kalli idonsa ta ce masa "Eh!" 

Cak ya tsaya a tsakiyar office ɗin, sai kuma ya yi dariyar takaici, kalaman ta sunƙi barin kunnuwansa su huta, agogon hannunsa ya cire ya ɗora akan tebur, kujera ya ja ya zauna, sai dai gaba ɗaya ya rasa nutsuwar da yake samu a duk lokacin da yake cikin office ɗin, jingina bayansa ya yi da kujerar, lumshe idonsa ya yi, yana tuna yanda ta tsaya a gabansa tana rawar jiki, da yanda take kuka duk a ƙoƙarinta na son shawo kansa ya ƙyaleta.

Ya yi dansanin baro Abuja, da ya san abin da zai tarar kenan da babu tsautsayin da zai saka shi ya dawo, gwara ya ƙyaleta, ya yi niyyar bata lokaci, saboda ya fahimci abubuwa da yawa sun faru a rayuwarsu, kuma akwai abubuwan da ya kamata su tattauna kafin su iya komawa yadda suke, shi ya sa ya rarrashi kansa, tun ranar, kwana ɗaya ya iya ƙarawa a Kano ya tafi Abuja, amman yanzu da ta tsaya a gabansa tana faɗa masa maganar banza, dole zai ɗauki mataki, shi ba lusarin namiji bane, idonsa ya buɗe da sukayi jajir, wayarsa ya ɗauka ya kira number.

"Assalamu alaikum ya Zay'd" Muryar Salmah ta karaɗe office ɗin.

Bai iya amsa mata ba sai tambayar da ya jefa mata "yaushe ne bikin yayarki?" 

Da mamaki Salmah ta ce "wata yayar tawa?" 

Bai bata amsa ba dan yasan tasan ai akan wa yake magana.

"Ba bikinta za'ayi ba, ba ta da saurayi" ta basa amsa, katse wayar ya yi, yana jin abin da ya tsaya masa ya faɗa masa.

Miƙewa ya yi ya nufi wajen tagar office ɗin, daga nan yana iya ganin wani ɓangare na ajiye motoci, inda ma'aikata suke zirga-zirga, tuna lokacin da ya fara ganin Zahra a Dara ya yi, baisan ita bace, amman yaji kamar wani abu yana fusgarsa zuwa gare ta, haka ranar da ya yi mata gani na biyu, baiga fuskarta sosai ba, amman ranar sosai ya tsorota da bugun da zuciyarsa take masa, wanda a take ya yanke hukuncin ya tsani yarinyar, dan sai da ya ganta sannan ya shiga cikin yanayin da ya kusa zautasa, ranar da ya ganta kuma ya tabbar itace, a take ya ji, kamar wani ɓangare na rayuwarsa da kullum yake jinsa empty ya cike.

Wani makirin murmushi ya yi "kin yi kuskure Besty, da alama dai kin manta ni ne dai Muhammad ɗin da kika sani" ya yi maganar yana barin wajen, wata drawer ya saka key ya buɗe, wata ƙaramar akwati ya zaro, buɗewa ya yi, zobe ne a ciki na zallar azurfa da tagulla, iri ɗaya ne da ta hannun Zahra banbancin kaɗan ne, ido ya zuba mata ya na dubawa, a ƙaramin yatsansa ya saka, akwatin ya mayar inda ya ke.

Tsayin shekaru ya na riƙe da alƙawarin da ya yi mata, shiyasa bayan kwana biyu da maganar su, ya bata zoben nan ranar jiniour candynsu, wanda shi a wajensa alƙawari ne, amman yasan ita batayi wannan tunanin ba, a lokacin da ya yi mata maganar aure, ta yi dariya saboda ta ɗauki maganarsa wasa, ta ce ba za ta taɓa auren age mate ɗinta ba, balle classmate ɗinta, ya san tayi maganar ne saboda yadda take kallon batun aure a lokaci.

Amman shi, ba wasa ya yi mata ba, dagaske ya ke, ya faɗa mata abin da yake ransa, wanda har yau bai canza ra'ayinsa ba. Rufe akwatin ya yi ya mayar da shi inda ya ke, sannan ya ƙara ɗaukar wayarsa ya yi kira.

"Hello dude" Sameer ya ce bayan amsa kiran.

"Ina buƙatarka a Kano dude"

Da mamaki Sameer ya ce "yaushe kuma, kasan fa akwai aiki" 

"Aure zanyi Sameer!" Muryarsa ta fita a hankali.

Dariya Sameer ya saka dan shi dai yasan wasa yake, mutumin da bai da budurwa ne yake maganar zai yi aure "da ƴar tsana zaka yi auren?"

Tsaki ya ja "ina maka magana kana shirme zan kashe wayata"

"Toh ai naji maganar taka wata iri ce, naga duk yanda ƴan mata suke binka kake wulaƙantasu, ka ce kai babu aure a tsarin ka, ko maganar muke baka saka baki, kuma kwatsam yanzu kace min zakayi aure, yaushe kayi budurwar ma?" Jin ya yi masa banza ne ya sa ya koma seriose.

"Na same ta dude" 

"Dagaske Zay'd? A ina?" Ya jera masa tambayar.

"Labarin dogo ne, ba zan iya jira ba, idan na ci gaba da jiranta komai zai iya faruwa, ka zo ka raka ni wajen Abhie, ko kuma na aike ka"

A ɓangaren Sameer sosai farin cikin da ya shiga ya kasa ɓoyuwa, dan ya san yanda yake sonta, dan haka a take ya ce masa zai samu ya shigo in sha Allah.


★★★

Washe gari da asubah kamar yanda ya saba idan yana gari, kitchen suke bin Ammie shi da Khaleel yau ma hakan ce ta kasance, sanye yake da jallabiya fara sosai tayi masa kyau, wata iriyar nutsuwa ce ta bayyana a tare da shi, bayan sun gaisa da Ammie bayanta yaje ya tsaya, magana yake son mata amman ya rasa ta ina zai fara, kamar ƙaramin yaro ya kwanta a bayanta.

Dakatawa da abin da take ta yi, Khaleel da Princess suna ganin haka suka kalli juna, hannayenta ta ɗauraye ta juyo tana kallonsa, ganin yanda ya marairaice mata ne ya sa tayi murmushi.

"Me ya faru me babban suna?" Ta tambayesa tana kallonsa.

Shiru ya yi mata sai bin ta da kallo da yake.

"Shi kenan jirani a parlow" fita ya yi ya zauna, wayarsa ya zaro yana dannawa, bata jima ba suka fito su dukansu. 

"Gani Zay'd"

Ɗago kansa ya yi daga kan wayar, ya mayar da kallonsa kanta, shiru ya yai mata, sunfi 30minutes yaƙi magana, ita kuma ta kasa tafiya, shi kuma Khaleel gulma ce ta hanasa ta shi, itama Princess tana zaune, duk sun gaji da zaman saboda ba magana suke ba, ko wani abu.

"Me ya ke faruwa ne Zay'd, hankalina ya fara tashi, ko baka da lafiya?"

Ajiye wayarsa ya yi, ɗan shiru ya yi, ya tattaro kalaman bakinsa.

"Ammie aure na ke son aje nemo min" maganarsa ta ratsa kunnuwansu.

Ido gaba ɗaya suka zuba masa.

"Aure Muhammad?"

Kansa ya gyaɗa mata.

"Wace yarinyar?"

"Sunanta Fatima Zahra"

Wannan karon kallon mamaki take bin sa da shi.

"Please Ammie ki yi wa Abhie magana, yau nake son aje"

"Yau kuma?" Ta tambayesa mamakinta na ƙaruwa, tsawon wane lokaci tana masa maganar auren, sai kuma yau kwatsam ya zo da maganar kai tsaye haka. Bai iya ce mata komai ba.

Ta shi ta yi ta hau sama, ta ɗan jima ta sakko, "zo nan" ta shi ya yi ya bi bayanta saman suka nufa tare, Abhie ya na zaune da jarida a hannunsa.

"Barka da safiya" ya ce cike da girmamawa.

Ajiye jaridar hannunsa ya yi "naji saƙonka, wacece yarinyar?" A taƙaice ya yi masa bayani, address ɗin gidan ya tambaya ya basa, sai kuma ya tura masa number Baffa da ya saka Salmah ta tura masa, sallamarsa ya yi, sakkowa ya yi yana jin kamar ya sauke nauyi a kansa.

★★★

Baffa ya na zaune ya amsa kiran waya, ya jima yana wayar, ya na gamawa ya kira yayansa suka yi magana, kiran ya bi sukayi magana sannan ya katse, Mahmah da take jin duk abin da ake cewa jikinta ne ya fara rawa, idonta taf hawaye take kallon Baffa.

Murmushi ya yi mata "me ya faru?" Kanta ta girgiza masa ba tare da ta iya ce masa komai ba. "Ki shirya zamu yi baƙi nan da 12, a shirya duk abin da ake buƙata" kamar kurma ta gyaɗa masa kai.

Waje ta fito da nufin kiran Salmah, kawai ta sameta tana gyara parlown baƙi na waje, da ɗan mamaki ta ce "ke kuma aikin me kike da farar safiya haka?" 

Juyowa ta yi ta kalleta "lah Mahmah kawai yau sha'awar aiki nake" ta bata amsa tana ci gaba da aikinta, nan kuwa ita kaɗai tasan dalili aikin.

"Zahra!!" Mahmah ta ƙwalla mata kira.

"Na'am" ta amsa daga ciki tana fitowa.

"Kayan snacks nake so yanzu baƙi za muyi, masu ɗan yawa, ki shiga ki duba abin da ake buƙata, sai kuma girki" 

Duk da tana da zuwa wajen aiki, haka ta shiga kitchen ɗin, dan tana jin tsoron ta yi magana tayi laifi, kusan duk suna da abin da take buƙata, saboda bata rabo da siya ta ajiye, kayan cefane kawai take buƙata, fitowa ta yi ta faɗa mata abin da take buƙata ita kuma ta koma cikin kitchen ɗin, aikin ta fara cikin sauri cike da ƙwarewa, Salmah ce ta shigo ta kama mata wasu aikin, dake suna da duk kayan aiki, nan da nan suka kusa gamawa, Baffa ne ya kawo cefane har da kaji, ga kuma lemuka da ruwa katan_katan, tana gani ana shiga dasu ɗakin baƙi, amman duk ba ta kawo komai a ranta ba, lafiyayyen abinci ta haɗa bayan kayan snacks ɗin, a manyan flate su kayi rapping na kayan.

Suna gama wa ta shige ɗaki ta yi wanka, sha ɗaya ta kusa lokacin da ta gama shiryawa, fitowa ta yi da shirin tafiya aiki.

"Yau ki haƙura da zuwa aikin nan Mamana" Baffa ya ce bayan ta fito. Da mamaki take kallonsa, amman ba ta iya ce masa komai ba, sai toh.

"Autah" ya ƙwallawa Salmah kira. Fitowa ta yi daga ɗaki. "Gani Baffa" "kuje gidan Inna ke da yayarki" kuɗin mota ya basu.

Fita suka yi, suka samu napep ya kai su, lokacin da suka je suka samu Inna na rabon abincin sadaka, har da ruwa da lemo.

"Inna amman dai naga yau ba juma'a ba ko?" Salmah da bakinta baya shiru ga tambayeta, ba tare da sun gaisa ba. Banza tayi mata, sai Zahra data kalla tayi wani irin yalwataccen murmushi.

"Sannu Fatsima" 

"Halan kinga ina cuta ne?" 

"Duk kuci kanku farin cikin da nake ciki, ba zai barni na kula ku ba yawwa" daga haka tama bar musu ɗakin.

Haka kawai ta ke jin fargabar da ta rasa ta mece, amman tana ta addu'a a zuciyarta, duk yanda tayi ƙoƙarin tayi bacci ta kasa, gatanan dai kawai a kwance idonta a lumshe, Salmah ce ta shigo da wani irin gudu tana ihu, a tsorace ta ɗago ta kalleta "ke lafiyarki?" 

Kasa zama waje ɗaya tayi, ƙarshe kawai ta janyo hannunta, tana miƙewa Salmah tayi mata wata wawiyar runguma "Alhamdullah! alhamdullah!! Alhamdullah" shine abin da kawai Salmah take maimaita wa.

Haka kawai taji jikinta ya yi sanyi, janye jikinta ta yi daga na Salmah "me ya faru Autah? wannan murnar duk ta meye?"

Hannunta Salmah ta riƙe "Baƙin da Baffa zai yi sun zo har sun tafi" Salmah ta bata amsa tana ta bin ta da kallo, har sai da ta tsargu. 

"Su waye baƙin?" 

"Ban san su ba Big Sister" 

Ɗan ƙaramin tsaki ta yi "shine kuma kike wannan abin"

"Ba za ki gane ba big sister" jin wayarta na ringing ne yasa ta duba me kiran, rashin gaskiya ne ƙarara ya bayyana a fuskarta, da sauri ta fita ta ɗaga wayar, ba ta jima ba ta dawo, sai kuma ta fita wajen Inna, magana suka yi, a take Inna ta washe bakinta, ɗan gyare-gyare suka fara, duk da gidan baiyi wani datti ba.

★

"Fatsima zo ki je ki siyo min goro a gidan maƙociyata"

"Ki aiki Salmah ko Maryam, amman babu inda zani, kawai na tafi siyo miki goro Allah ya kiyaye"

"Ba shakka nuna min bani na haifeki ba, to bara na kira Habibu na aikesa" tsaki ta yi ta karɓi kuɗin ta fita tana gunguni, ta ɗan jima a gidan sannan ta juyo, sosai ta yi mamakin ganin mota fake a ƙofar gidan bata kawo komai a ranta ba ta shiga da sallama, jin wani irin ƙamshi ne ya sa ta tsaya cak, amman sai tayi tunanin, tunanin me turaren ne ya sa take jin ƙamshin, me zai kawo sa nan, da haka ta ɗaga ƙafarta ta shiga ɗakin Inna.

Ƙamewa ta yi a inda take tsaye, sosai ta saki baki da hanci tana kallonsa, ya na zaune cikin manyan kaya da hula, sosai yayi wani irin fitinanne kyau a cikin kayan, juyawa ta yi zata fita.

"Kina fita zan yi miki abin da baki yi tunani ba"

Ledar hannunta ce ta kusa faɗuwa, amman ta yi saurin riƙe ta, runtse idonta ta yi, sannan ta juya a hankali tana kallonsa. Har ya miƙe tsaye, babu alamar wasa a fuskarsa, ya zuba mata ido, saurin kawar da kanta ta yi, a zuciyarta tana mamakin yanda yake cika mata ido.

"Me ka zo yi anan kuma?" Ta tambayesa cikin sanyin murya ba tare da ta kallesa ba.

"Lefi ne dan ango ya zo ganin amaryarsa?" Ya mayar mata da tambayarta.

Murmushin da ba tayi niyya bane ya ƙwace mata, dan bata ɗauki maganar ta sa ta mai hankali ba.

Shima murmushin ya yi, dan ko bata faɗa ba yasan tunanin me take a ranta. "An je nema min aurenki yau Alhamdullah kuma an bani, nan da sati 4 zaki zama matar Muhammad in sha Allah"

A take murmushin fuskarta ya ɗauke, ido ta zuba masa ba tare da ta motsa ba, ko ta ce masa wani abu, saboda yanda taji numfashinta ya ɗauke na wucin gadi, sannan ta fuzgosa da ƙarfi, kallon rashin fahimta take masa, kanta ta girgiza tana tunanin ba ta ji abin da ya ce dai-dai ba, wataƙila shima bai san abin da ya ce ba.

"Me.. me.. ka ce.. Muhan?"

Ba tare da ya ɗauke idonsa a kanta ba ya ce "na ce an nema min aurenki"

Jiri ne ya ɗebeta ta yi baya, zata faɗi, Allah ya taimake ta tana kusa da bango. 

"A'uzubillahi!" Ta furta ba tare da ta sani ba, tana girgiza kanta.

"Ni ne sheɗan?"

"Anya lafiya kake Muhan? Ka shigo har nan ka tsaya a gabana kana gaya min maganar banza, sa'ar ka ce ni da za ka ce an nema maka aure na? Wannan wane irin wasan banza ne" a karon farko da ta yi masa magana cikin ɗaga murya, har ta na haki.

"Ba wasa nake miki ba" ya bata amsa cikin kwantar da murya ba tare da ya biye wa faɗan ta ba.

"Ka dena bana so Muhan"

"Ba zan daina na"

Buɗe bakinta tayi, sai ta kasa ce masa komai ma, saboda mamaki. Zama ya yi ya nuna mata kusa da shi "zo ki zauna" a hasale ta ce "ba zan zauna ba"

"Ba matsala ki tsaya a tsayen" ido ta zuba masa, cike da mamaki, ganin ruwa ma ya ɗauka zai sha, ita hankalinta a tashe, amman shi wata iriyar nutsuwa ma take gani a tare da shi, alamun ko a jikinsa.

"Muhan wallahi ko maza sun ƙare bazan aure ka ba, duka nawa kake da zaka ce zaka aureni tsabar tsaurin ido, toh ma da izinin wa ka aika gidanmu, kai ni ba yanzu zanyi aure ba ma"

"Sai yaushe kenan?" 

Shiru tayi masa ganin duk haƙilon da take, shi hankalinsa a kwance ya ke.

"Ko auren ne ba zaki ba gaba ɗaya"

Cize leɓenta ta yi, hannunta ta saka ta share zufar da ta fara tsatstsafo mata a goshi "ka nemi wata ka aura, duk ga mata nan a gari, mata suna da yawa, me ya sa sai ni"

"Saboda ke na ke so" ya bata amsa kai tsaye.

Juyar da fuskarta gefe ta yi.

"Ni kuma ba na son ka!"

Miƙewa ya yi daga zaunen da yake, gabanta ya matso ya tsaya. 

"Fatima"

Da fargaba ta juyo ta kallesa, dan zata iya cewa bata taɓa jin ya kira ta da Fatima ba.

"Na gaji da zama babu aure, alhalin ina da buƙatarsa, tuntuni nake buƙata amman na haƙura saboda ke, yanzu kuma na same ki, ba zan iya ci gaba da zama a haka ba, ina buƙatar mace a tare da ni"

Da sauri ta toshe kunnenta. "Ba zan taɓa aurenka ba, haba kawai sai ace na auri yaro, Allah ya kiyaye, wallahi bazan aure ka ba" 

Taɓe bakinsa ya yi, sai kuma yayi murmushi.

Haka kawai murmushin nasa ya ƙara ɗaga mata hankali "me kake wa murmushi?"

"Wani abu ne yake bani mamaki, amman idan kika kuma cemin yaro, ke ce zaki mamaki bani ba"

Tsit ta yi.

Ƙara matsowa kusa da ita ya yi "tun da har nayi alƙawari, kinsan sai na cika sa, duk ki ajiye rigimarki, ki tara idan kinzo gidana sai kiyi, anan ne zan rarrasheki"

Kuka ta sakar masa.

"Allah ba zan aure ka ba, kuma nasan ma ƙarya kake ta ya ma za ma ce wai ka aika a nema maka aurena, babu ta yanda za'ayi Baffa ya baka aurena ba tare da ya ji ta bakina ba, ni kuma magana ɗaya ce ba zan iya auren yaro ba, wallahi ko da maza sun ƙare"

"Zamu gani ai ki kulamin da kanki Besty" bai jira cewarta ba ya sa kai ya fice....

FULANI
***