006
by @swrites22
_ NI DA YAYA NABEEL _
_YOUNG WRITER✍️
* 006 *
Ko kallon ta Asum batayi ba ballantana ta nuna ta san da wanzuwarta. A hasale ta sake fadin, "Wai ba dake nake Magana ba?". Kallon 9/3 ta mata kafin ta ja tsaki ta ɗauke kai. A fusace ta taso ta isa gaban Asum ɗin kamar zata Kai Mata duka tace, "Ke har kin isa nayi magana kimin tsaki? To tashi mun a falo tunda ba falon ubanki bane".
Miqewa Asum tayi kamar zata tada aljanu ta danqi wuyan Jumaymah, ƙoƙarin kwacewa ta shiga yi idanunta duk sun firfito waje. "Whl, Whl, kinji na rantse kika Kara kuskuren zagin ubana saikin jiyo kamshin lahira. Shegiya kodaddiyar banza me zubin fararen aljanu".
Cikin dakakkiyar murya Nabeel yace, "Sake ta". Juyowa tayi ta kalleshi sai kuma ta saketa haɗi da hankadata ta fada Kan kujerar. Karasowa yayi ya dagota, cikin fushi ta bige hannun sa kafin tace, "Babe haka mukayi da kai? Ina cewa haka kace yarinyar nan aiki zata dinga mun amma a gabanka take kokarin kasheni ka kasa ɗaukan mataki".
A dakile Asum tace, "Tho kuwa bakiji daidai ba, dan matsayina da naki duk daya, ko ma nace na fiki tunda nice uwar gidan, dan haka dole kiyi biyayya yarinya". Tana gama fadin haka ta juya ta bar musu falon tana jin yadda suka balle da hayaniya tace kanku akeji ta wucewarta ɗaki.
"Ni whl bazan yadda ba babe, kawai ka san yadda zakayi tun wuri". Ta faɗa cikin ɗaga murya. "Wai tsaya Jumaymah, ni kikeso in dinga tare Miki fada ko me? To in ma wanna Tunanin kike tun wuri ki daina. Akan me kin tsaya sakarci yarinya kanwar² bayanki tana miki abinda taga dama saboda kin bada kanki kin zubar da girman ki a wurinta kuma kizo kina min wani zancen banza. To ni ba yaro bane ba kuma abinda ya dameni da fadan ku, duk kuma lokacin da kika tsokano ta, in kin iya ki kwaci kanki in baki iyaba ta naɗa miki shegen duka ba abinda ya dameni ko sannu ba zance miki ba. Ba dai sabgarta kike son shiga ba, to ke zakiji a jikin ki, gwara ma ki kama kanki tun kafin ya gudu ya barki".
Da mugun mamaki take kallonsa har ya gama ya gyara zamansa, yayi relaxing akan kujerar yana ɗaukan remote dan canza channel. "B..babe ni kake gayawa magana haka, tun ba'a je ko ina ba har ka fara nuna min ni bare ce? Babe yau ni ce sakaryar?". Ta Ƙarashe kuka na kwace mata. Tsaki yaja ya tashi ya bar mata falon.
**************
Rayuwa ta miqa Asum har an fara university anan Russia bisa umarnin Baffah, sosai ta ƙara gogewa ta Kara kyau abinta shar² da ita ga kawaye wayayyu yan gayu data sake yi dan Asum akwai san kurewa gayu gudu. A bangaren zaman gidan Genar kuwa tuni zaman lpy ya qaurace masa kullum cikin tashin hankali ake, rikicin yanzu daban na anjima daban kuma duk Jumayma ce me tsokano Asum ɗin amma sai ta janye tace Asum ce, dan ta yarda da cewa ta hakan ne kawai in abun ya ishi Nabeel din zai dau mataki, ita kuma tasan rashin hakurinta ba zai barta tayi shuru ba ta san dole zata faɗawa Baffah, shi kuma daga nan zai iya cewa tunda abun haka ne Nabil ya saki Asum ɗin. Ita kuwa Asum a bangarenta sam auren Nabil ɗin baya gabanta dan har lokacin tana Kan bakarta na cewa zata kaso auran, a aurawa Naseem shi shiyasa itama take biyewa Jumaymah. Kai kuruci dangin hauka.
Kamar yanzu da take zaune a falon shigowar ta kenan daga makaranta ta ɗan zauna ta huta sakamakon gajiyar data kwaso. Wayarta ce tayi Ƙara ganin Naseem ya sata ɗagawa tana murmushi. Naseem ɗin ce tace, "Yar uwa rabin jiki kwana biyu, ina kika shige ko dai Amarcin ne har yanzu ba'a gama ba".
"Ke bari kawai Naseem whl scul ce ta sakoni gaba. Ykk? ya su umma".
"Lpy kalau Alhamdulillah guess what?". Naseem ɗin ta fada.
"Shaqa min mana, ai bama haka". Ta fada cikin zumudi tana gyara zama. Dariya tayi tare da faɗin, "Anya zan fada Miki kuwa?".
"Haba twinny ni ɗin? Dan Allah mana".
"Su hamma Muneeb ne suka zo". Wani ihun farin ciki Asum ɗin tayi kafin tace, "Wayyo Allah da gaske? ina ma ina nan". Ta Ƙarashe kamar zata yi kuka.
"Tho sai abu na biyu kuma, wato dalilin zuwan nasu".
"Inaji²". Ta sake faɗa tana jin kamar zata fita ta cikin wayar. "An saka ranar aure na da Hamma Awwab, sai Hamdah da Hamma Abid".
"Whatttt, dan maimaita inji Naseem, banji sosai ba". Asum ta fada a rikice tana miqewa. Cikin tashin hankali tace, "Kin manta da maganar mu ne Naseem, Meysa zaki amincewa Hamma Awwab bayan kinsan wanda zuciyarki take so?". Shuru Naseem ɗin tayi kafin tace, "Asum kar dai kice min har yanzu baki rungumi auren ki kin zauna lpy ba? Innalillahi wa inna ilaihir Rajuun. Wai Assuma ina cewa mun gama maganar nan ko, na riga na fada miki na ƙara, whl kunyar maimaita zancen nan nake ma, amma tuni Ya Nabil ya fice min a zuciyata Asum, ina kallon sa ne kamar su Hamma safwan. Yanzu fa zancen da nake Miki ma wata biyar aka tsaida ranar auren mu, ina me baki shawara da ki Kula da naki auran, ki riqe Mijinki, karki bar wanna fringilliyar matar ta karasa mallake shi".
Shuru Asum tayi ta rasa ta cewa har Naseem ɗin ta gama faɗin abinda zata faɗa tayi mata sallama ta kashe wayar. Tana zaune cikin rashin sanin maqamar yadda zata bullowa wannan katobarar data tabka wani Kiran ya sake shigowa, saidai har ya katse ta kasa tattaro kuzarin da zata iya kai hannu ta dauki wayar, wani kiran ne ya sake shigowa, dakyar ta iya kai hannu ta dauka, ganin Umma ce yasa ta tattaro nutsuwarta kafin ta ɗaga da sallama.
Daga ɗaya bangaren Umma na amsa sallamar ta rufeta da faɗa kan Maganar da taji sunyi yanzu da Naseem. Sosai take faɗa kamar ta ari baki saida taji Asum ɗin ta fashe da kuka kafin ta sassauta ta koma lallashi, "Haba assumi tah ya ina yabonki sallah zaki kasa alwala, wani irin wauta ce wannan? Da nasan har yanzu baki yi hankali da nutsuwar da zaki iya tafiyar da kanki ko bakya gaban mu ba da ban yarda kin tafi a yanzu ba. Ai bansan cewa har yanzu yarinta na dawainiya dake ba, ni dan Allah dan annabi a ina kika dauko wanna taurin kan ne Asum? Gabadaya kin kasa nutsuwa ki san abinda duniya take ciki? Ko min kankantar shekarun mace akace an Mata aure ai ta fita sahun yara, amma ke kamar dusa ma aka zuba miki a cikin kan naki". Haka Umma ta karaci maganganunta ta kashe Asum ɗin bata iya ko tari ba sai kuka da take marar sauti. Sai da tayi me isarta kafin ta tashi ta shige ɗaki.
Wanka tayi ta fito. Doguwar riga kawai ta zura kafin ta ɗaura hijab akai ta tada sallar magrib, tana idarwa kuma ta zauna karatun Alkur'ani mai girma har lokacin sallar isha yayi ta tashi ta gabatar. Tashi tayi ta cire kayan jikin nata sannan ta sake shiryawa cikin wasu arnan english wear, sky blue Jeans da yayi matuqar kama jikinta sai brown t-shirt body hug, ta gyara gashin ta tayi parking a gefen kunne stylishly, kafin ta zauna ta tsara simple make up, tabi jikinta da turaruka masu kamshin daɗi da saukar da nutsuwa. Tsayawa tayi kallon kanta a cikin mirror, har lokacin kuma bata daina sauke ajiyar zuciyar kukan da tasha ba, murmushi me cike da tarin ma'anoni tayi kafin ta wuce ta ɗauki high heel ta sanya sannan ta fita.
A falo ta hange su zaune, yana sanye da kayan sojojin ƙasar, da alama bai dade da shigowa gidan ba Jumaymah na zaune a jikinsa duk tabi ta kanainaye shi sai wani magana take masa kasa² a kunne, shi kuma yana mata ɗan murmushin nan nasa mai tsada. Wani abu Asum taji ya tsaya mata a maqoshi wanda bata taɓa ji ba, cox da ko a jikinta saboda bata masa kallon miji, amma yanzu data shirya amsar sa matsayin miji hakan ya taba zuciyarta matuqa. Daurewa tayi ta wuce, a yayin da duk taku ɗaya sai ƙarar takalmin ta ya sauka a kunnuwansu. Wanda hakan ya jawo hankalinsu su dukan, zuba mata Ido sukayi a lokaci guda kamshin turaren ta ya musu sallama. Dan lumshe Ido Nabeel yayi dan ba ƙaramin daɗi kamshin ya masa ba kasancewar sa ma'abocin shiri da kamshi. Yayin da Jumaymah kuma ta haɗiye wani abu muqut.
Ita dai Asum bata san sunayi ba ta wuce kitchen ta zubo kunun ayar da tayi da safe kafin ta fita school ta dawo falon, direct kujerar da suke Kai ta nufa kasancewar two seater ce, ita kuma Jumaymah tana kan cinyar sa ne. Gefen su ta zauna tare da ɗaukan remote ta shiga canja channel tana kurbar kununta cikin wani salo. Ɗan satar kallonsu tayi jin yadda sukayi tsit kamar basa wurin sai kuwa idon su ya shige cikin na juna, irin kallon da taga yana mata yasa ta kusa kwarewa, ta ɗan yi gyaran murya kafin tace, "Sannu da dawowa, ya aiki ?".
"Aikin ubanki, tashi daga kusa da mijina". Jumaymah ta faɗa a Hasale. Runtse ido Nabeel yayi, shi ya rasa dalilin da yasa basa zama wuri guda ba tare da sunyi fada ba sai kace wuta da ruwa.
Asum na shirin magana ya kai hannu ya zare tumbler ɗin dake hannunta dan ɗauke hankalinta daga bawa Jumaymah amsa, saboda kansa ciwo yake baya san hayaniya. Kasa² yace, "Sai ki zubo ke kaɗai, ina namu?".
Ɗan langwabe kai tayi cikin shagwabar da bata san ta iya ba tace, "Ai bansan kuna so ba...". Kiff Jumaymah ta bige tumbler ɗin sai kuwa kunun ayar yayi fuskar asum, tumbler ɗin kuma ya daki goshin Nabeel. A ɗan zafafe yace, "Sauka daga jikina kafin nayi gutsi² dake a wurin tunda ke baki da hankali".
Kukan takaici ta fashe dashi tare miqewa idonta ya sauka kan bindigar da ya shigo da ita ya aje Kan center table, da gudu ta dauka tana fadin, "Ni zaku haɗewa kai to whl yau ko ni ko Ku, munafiki, makaryaci, maciyi amana. Kuma zalintata da kayi Allah ya isa ban yafe ba, dama Kana son ta ai shiyasa kaki sakinta, nace Ka kama mata hayar gida daban kuma kaki saboda kana so Ka dinga ganin ta, toh whl yau sai na kasheta na kashe kaina".
Tashi Asum tayi a fusace, da sauri shi ma ya miqe tare kamo hannun ta ya jata zuwa bayan sa, a dake yace, "Ajje bindigar nan Jumaymah".
"Whl bazan ajje ba, yau in kaga na ajje to nayi abinda nace ne".
"Ki ajje nace". Ya fada a tsawace. Ita ma a tsawacen tace, "Ka daina min tsawa Nabil, kai ma zan iya haɗawa da kai kowa ya rasa, mugu kawai makaryaci, kace nice zabinka, kace ita matsayin yar aiki Ka ajje min, kace bata isa Ka haɗa jiki da ita ba, kace ba ajinka bace, ashe duk karya ce da daɗin baki kakemin". Dafe kansa yayi cikin takaici, lalle ya zama soko da har ya saki baki yayi irin wadannan maganganun da Jumaymah, shi kuma ya fada ne a lokacin da yaje daukota tace ta gama auran sa saidai yaje ya zauna da zabin mahaifin nasa duk da ba hakan ya faɗa mata ba amma ji yadda ta juya maganar. Shi dai kawai ya san yace itace zabin sa kuma ba wata da yake kallo matsayin mace in ba ita ba, dan haka ta kwantar da hankalinta kar ta ɗau Asum matsayin kishiya. Sai gashi yanzu tana neman kwanto masa kura a daji dan yasan yanzu sai Asum ta iya fadawa su Baffah in baiyi Sa'a ba.
"Oh ni ya zanyi da raina ne wai". Ya faɗa a zuciyarsa. A fili kuma cikin lallashi yace, "Duk naji amma ki ajje bindigar nan muyi magana, ko me kike so za'ayi". Bai rufe bakin sa ba Asum tayi tsalle ta dire, unexpected ta kai wa hannun Jumayman wani mugun bugu sai ga bindigar ta dawo hannunta, idanunta sunyi ja saboda ɓacin rai har wani haki take kamar wadda tayi tseren gudu. Zaro Ido yayi yana binsu da kallon tsoro kafin yace, "Wai me hakan kukeyi ne?".
Kokarin rumbatar Asum Jumayma ta shiga yi, ai kuwa cikin wata irin tsawa da bata san ta iya ba tace, "Billahillazi kika matso in da nake a yanzu saina aika ki in da kike son zuwa, in taqamar ki hauka ni zan sauke miki duk wata tsutsar iskanci dake cizon ƙwaƙwalwar kanki. Ba mutuwa kike so ba to kin tara kin samu taho Kinji". A tsorace Jumaymah ta shiga yin baya baya dan taga da gsk Asum ɗin take .
Nabeel ne ya nufeta gadan gadan. Rufe Idanunta tayi tare da fadin, " Ka tsaya Inda kake, karkayi kuskuren matsowa kusa dani, ka tsaya nace".
"Ke wai miye hakan? Ki nutsu mana, ni bana san iskanci fa". Ɗaga bindigar tayi sama ta harba sannan ta maida kanta kasa ta harba. A razane Jumayma tayi tsalle ta kankame Nabeel da yayi suman tsaye. Sojojin dake gadin gidan ne suka shigo da gudu, hannu Nabeel ya ɗaga musu alamar baya bukatar su, zasuyi magana ya daka musu tsawa da sauri suka ƙame haɗi da Sara masa kafin su juya su fice.
Maida kallon sa yayi kanta, zuwa lokacin kuka take sosai kamar ana yankar naman jikinta, cire Jumaymah yayi daga jikinsa ya fara takawa zuwa wurinta, cillar da bindigar tayi ta zagaya ta ɗaya side ɗin, wani irin duka ta kaiwa center table ɗin take glass ɗin ya tarwatse, ɗaukan yankakken glass din tayi ta wurga masa tana faɗin, "Na tsaneka, Na tsaneka munafikin mata whl yau ba sai gobe ba sai ka maidani Inda ka daukoni". Da sauri yayi kasa saboda wani gutsararren glass ɗin da ta wurgo masa.
Shahada yayi ya ƙarasa wurinta, hannayen ta ya riqo tare da rungume ta qam² a jikinsa. Bori take sosai amma ta kasa kwacewa, wani kukan ta sake fashewa dashi tare da kwantar da kanta a kirjinsa ta cigaba da yi. Ajiyar zuciya ya sauke yana bubbuga bayanta a hankali alamar rarrashi, a kunnen ta ya raɗa mata, "Am so sorry, don't hurt yourself please. Karki biye wa Jumaymah". Ganin bata ma san yana yi ba ya sashi rankwafawa ya ɗauketa gabaɗayanta ya nufi ɗakin sa da ita.
A bakin gado ya zaunar da ita kafin yaje ya dauko first aid box ya dawo, hannayen ta ya riqo ya fara mata dressing in da ta yayyanke, har lokacin kuka take, wato wannan shi ne zafi kan zafi kunama ta harbi gyambo. Saida ya gama mata dressing ɗin sannan ya tashi ya zauna a gefenta tare da ɗago kafarsa, runtse Idanunsa yayi ya sanya hannu ya ciro glass ɗin da ya shige masa ciki, sannan yayi dressing wurin, ya naɗe da bandage. Muryarsa a matuqar sanyaye yace, "Plz kukan ya isa haka". Cox dauriya yake kawai amma ji yake kamar ya rufe ta da duka ita ɗin ma, yaje waje ya sha aiki ya dawo gida ma sun sake tara masa wata gajiyar to ina zai sa kansa shi kuwa?.
Ko kulashi batayi ba, zuba mata ido yayi kafin can kuma ya kai hannu zai riqota, miqewa tayi da sauri tare da faɗin, "Karka kuskura Ka sake taba ni whl".
"It's ohk naji bazan Kara ba, amma ki daina kukan nan to, yana damu na ne whl, na gaji da yawa ina so in huta". Tashi tayi zata bar masa ɗakin amma sai yayi saurin shan gabanta. A fusace tace, "Ka bani hanya in wuce".
"Zan baki hanya amma ki tsaya muyi magana ta fahimta Assumah". Duk tsawon zaman su bata tabajin ya kira sunan ta ba sai yau, ashe dama yasan sunan. "Bani da wata sauran magana da kai, saidai tsakanin ka da su Baffah, dan zamana da kai ya zo ƙarshe, ba dai duk saboda na yarda da auren ka bane Shiyasa kake tozarta ni wurin wancan munafukar matar taka, to ka san ranka a Inuwa, auren mu yazo ƙarshe".
"Ohk calm down, duk naji abinda kika ce, amma zan rokeki wata alfarma, ban taba neman alfarma wajen wani dan adam ba sai ke. Please kar ki fadawa su Baffah wanna maganar dan Allah, ki bari mu sulhunta a tsakanin mu". A tsiwace tace, "Akan me bazan fada ba, wato a barka ka cigaba da zalintata kana zuwa kuna cin nama na da matar ka ko? Kana mantawa da ni yar uwar ka ce ko, ai ko ba aure a tsakanin mu zaka kare min mutunci na a wurinta, amma wai tana matsayin kishiyata kaje kana faɗa mata irin wadannan maganganun a kai na. Amma ba komai, akwai Allah dan ban yafe ba, kuma sai ya saka min".
Dafe kansa yayi lokaci guda idanunsa suka rikide zuwa ja, duk yadda yake kokarin controlling kansa yarinyar nan so take ta kureshi dan haka a tsawace yace, "Ke ba saki kike so bane, kuma a gaban ki kinji alwashin Baffah akan sakin ki. Bana so ki faɗa musu ne saboda mu samu mu nutsu mu samo hanyar da zan baki takardar ki ba tare da na samu matsala da su ba. Amma ina bin ki kina wani botsarewa". Girgiza kai tayi kawai ta kebe ta wuce shi ta bar ɗakin. Ya jima tsaye kafin ya sauke nannauyan numfashi ya fara rage kayan jikin sa ya wuce bathroom.