Chapter 5
Free book
Page 5
TA'AYE RASTORENT
Sabon waje ne da aka buɗe a unguwar Dosa, wajen yana da kyau da ƙyale -ƙyale kamar a ƙasar waje, kuma wajen ya na daga gefen yamma ne yana kallon gabas, gaba da( Zonel JAMB OFFICE Na KADUNA) , Tunda sukaja birki wajan jikin Namsiyya ya fara rawar jin daɗi da annashuwa, saboda yadda taga irin mutanen dake wajan, domin kuwa duk wanda yakeji yakai to a wannan waje yake burin yayi kalacin safe saboda yadda suke da nau'ikan abinci kala-kala masu HANGEN DALA
daɗi da kyau, sai dai fa akwai tsada.
Sholy nayin parking ɗin motar ta ta fito da kayan kwalliyarta dake cikin ƴar ƙaramar jikkar da take yawo da ita , ta fito da madubi ta kalli fuskar ta ta ƙara shafeta tsaf da poder kafin suka fito suka nufi wajan da aka tanaza dan zaman customer suna zama kallo ya dawo kansu saboda irin yadda sukai kyau na kece raini ga su kyawawa don kuwa bazaka iya fitar da wacce tafi kyau tsakanin Sholy da Namsiyya ba, ɗan ƙaramin book ɗin da aka ajiye akan kowane Table mai ɗauke da jerin sunayen nau'ikan abincin da suke dasu Sholy ta ɗauka ta zaɓi abinda take so kafin tai magana sai ga wani matashi ya iso wajen mai sanye da kayan aikin wajan jajaye masu ɗauke da photos na tanbarin TA'AYE RASTORENT.
“ me ake so hajiya?. "
yayi tanbayar yana kallon ta don tai masa ƙarin bayani
Da hannu ta nuna basa abinda take so batare da tace uffan ba.
Cikin mintina biyu ya haɗo masu duk abinda suka buƙata acikin wani kwando ya kawo ya jere a gabansu.
Fara cin abincin nasu keda wuya wajan ya kacame da hayaniya da ihun murna da karaɗi....
KATSINA
Filin folo gaba da gidan biredi kadan, Abbas ne tsaye a ƙofar gidan sa yana nazari da tunanin irin kalaman da zai furta ma Ahanah ta bama mahaifiyar ta haƙuri tajanye wannan baƙin burin nata na son raba aure, da sallama ya shiga gidan ya nufi Ɗakin matar tasa.
Dam! Dam!! Gaban Ahanah ya faɗi jin sallamar Abbas don tun da ya maƙareta ɗazu har taga barzahu take wani irin mugun tsoron sa musamman ma da ta kasance ira ɗaya a gida , don haka yana shigowa ɗakin tai tsalle ɗaya ta shige kusurwar ɗakin tana mazurai, amma ga mamakinta sai taji yana faɗin
“ Babu abinda zan maki Ahanah magana nazo muyi don haka kikwantar da hankalinki. ”
Jin abinda yace yasa Ahanah fitowa daga kusurwar da ta shige tai tsaye tana kallon sa tana mai zare ido cike da tsoron abinda zai biyo baya.
Ganin haka yasa Abbas ya sassauta fushin fuskarsa zuwa fara'a ya na murmushi yace" zonan " yakai ƙarshen maganar yana nuna mata inda yake zaune.
" A a nidai kayi maganar ka daga nan haka ina jinka ”. Tai maganar cikin shagwaɓa da tsoro don ita tuni ta gama yin saranda da Abbas zai iya ƙasheta inhar ransa ya ɓaci.
“ Ni nace kizo wallahi babu abinda zan maki ”. Cewar Abbas ɗin saboda lura da yanayinta
Jin yayi rantsuwa yasa ta zo cikin sanyin jiki ta zauna inda yace.
Tana zama yai saurin kama hannayenta biyu yana mai marairaice fuska kafin yace “ Tanbayarki zanyi Ahanah me nai maki kike burin rabuwa da ni, ko na rageki da wani abu acikin zaman aurenmu na ci ko na sha ko na mu'amullar zamanrakewar yau da kullum?. ”
“ ko ɗaya kana mani komai wallahi gwalgwadon ikon ka. ”
“To me yasa kike burin kiga bamu tare ko wani laifi akace nayi wanda bazaki iya gayamanba sai dai ki yanke hukunci da kanki. ”
Sai da ta gyara zaman ta zauna sosai kafin tace “ Babu laifin da kai. ”
Sai da ya marairaice murya tai sanyi kafin yace “ To meyasa kike son rabuwarmu bayan kina sane da irin son da nake maki, bama wannan ba kinje makaranta kinsan irin hukuncin da Allah ya tanazar ga mata masu cewa da mijinsu ya sakesu, manzon Allah (S. A. W ) ya ce wasu matane nagani fuskokinsu a ƙone halshensu ya zazzago ana masu azaba acikin jahannama, ko da manzon Allah ya tanbayi su waye sai mala'ika Jibrilu yace sune mata masu cewa mazajensu susakesu batare da wani daliliba,
Alokacin da yai mi'iraji to meyasa kike son shiga cikin sahun wa'inan matan.
“ Yauwa kaima da kanka kace batare da daliliba toni ina da dalilina ”.
“ To meye dalilin naki”?, ya tanbaya cike da son jin abinda zata faɗa.
“ Talaucin ka shine dalilina Abbas nagaji da zaman uƙuba, agidan ka bayan ina da yadda zaniyi, rabona da nama a gidan nan ankai wata tara, don haka nasamar makaina masalaha tunda nima mutunce ƴar adama mai son rayuwar jin daɗi da hutu don haka ina haɗaka da Allah ka rabudani kaban takardata nagaji. ” ta kai ƙarshen maganar tana mai ɗaga murya.
“ Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un Subhanalla wannan rayuwa Allah kasa mu dace akan na kasance Talakka kike son rabuwa dani to ina mai sanar da ke cewa HANGEN DALA dai ba shiga birni bane, shiga cikin ɗaula bayana nufin hutu da jin daɗi ba , suma masu kuɗin da akwai ƙalubalin da ya ke tare da su don kowanne ɗan Adam cikin jarabawa yake har ya mutu, kiyi aure gidan da zakizo baki Azumin nafila, ki koya agidan,
kiyi aure gidan da baki san sallah ba ki koya agidan ko akaiki inda zaki koya,
kiyi aure gidan da baki sallar dare ki koya agidan,
Kiyi aure gidan da baki da haddar izif ɗaya ki haddace al'ƙur'ani agidan,
Kiyi aure gidan da baki san Allah ba,
ki koyi Aƙida da tauheedi agidan,
shine kikai sa'ar ɗakin miji don shine gidan da zaki alfahari da shi don an ɗauraki hanyar Aljanna kiyi biyayya ga Allah da manzon sa, kibi umarnin mijinki kigani yadda ƙarshenki zai kasance, don kinyi koyi da matan Aljanna, kuma sakamakon ki zai kasance Aljanna, ki natsu kiji tsoron Allah abin duniya ya daina birgeki don ba mai dawwama bane, idon kinga ƙawarki tasa zani mai tsada mijinki baida ikon sai maki kiyi haƙuri zakisa na Aljanna, domin kuwa adon matan aljanna kaya kala saba'in suke sakawa kuma kayan ( Taransferent) ne har yadda jini yake gudana ajikinsu ana gani tsabar kyalli , miji zai kalli fuskar matarsa yayi kwalliya kamar madubi tsabar ƙyalli, idon wani ya saima matarsa gold ya burgeki kuma mijinki baida ikon saye kiyi haƙuri zaki saka na Aljanna, zinaren Aljanna saboda ƙyalli sau saba'in yake canza kala acikin awa ɗaya, don haka ina mai neman alfarma kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki mu zauna lafiya. ”
“ Idon akabi miji ake samun Aljanna ko Abbas, to zan samu don zanma wanda zan aura biyayya nasa gold a duniya kuma nasaka na Aljanna ”.
Zaiyi magana wayarsa ta hau ruri, ya fiddo ya ɗauka kafin ya kara a kunnensa yana faɗin “Hajiya ganin nan.......
Kukan da aka fashe da shi shine ya katse masa maganar da yake shirin yi, cikin kuka da shaƙewar murya Hajiya Larai tace Abbas Akwai matsala kai sauri ka iso gida.
“ To Hajiya gani nan yanzu yanzu zan iso, ” yana gama faɗar haka ya katse wayar ya maida ita aljihu ya fice a ɗari ukku da sittin yana fitowa daga gidan sa ya fara waigen inda zai samu mashin amma babu, kawai sai ya fara tafiya a ƙafafunsa yana sauri , har yayi nisa da gidan amma babu mashin ganin yana ɓata lokacin sa yasa ya fara fofoci yana yi yana waigen baya da gefe ko zai hangi ɗan acaɓa, sai da ta iso dai dai ƙofar farko ta shiga unguwar kafin ya samu mashin cikin sauri ya hawo ya sanar sashi cewa Gobarau zai kaishi bayan hasumiya batare da sunyi ciniki ba, suna isa dai dai firamare inda masu saida icce faskare suke, mai mashin ɗin ya tsaya saboda lungun yayi wani irin yanayi mashin bazai iya wucewaba .