HANGEN DALA

Chapter 6

by @abdulhakimumar122

Page 6

Free book 

Ɗari biyu Abbas ya ciro acikin aljihunsa tsohuwa duk ta cukurkuɗe yabama ɗan acaɓar, sai da mai acaɓar ya kallesa sama da ƙasa kafin yace “ malam ɗari ukku ne kuɗin ka”. 
“ Don Allah mai gida kai haƙuri wallahi matsalace ta taso shiyasa na ruɗe ban tsaya jin kuɗinba kuma ita kaɗai ke gareni kai haƙuri kayafeman sauran da inada shi ko nawa ne zan biya wallahi nasan ban kyauta ba amma kayi haƙuri Allah ya haɗaka da mai baka fiye da abinda ka buƙata Allah ya tsare asauka lafiya. ”

Amsar ɗari biyun mai mashin ɗin yai yana cewa 
“ amma mai gida idon baka da kuɗi ka dinga sanar da mutum kafin ka hau don ba kowa ne yake da haƙuri ba, ” 

yana maganar yana tada mashin ɗin sa ya tafi. 

  Abbas tundaga nesa yake kallon cacurindon jama'ar da ke ƙofar gidan su maza da mata, sai asanan ya ga motar ƴan sandar dake bakin lungun, don haka ya isa da sauri domin yaga abinda ke faruwa.
 
Mahaifiyar sa ce ya gani tsaye a ƙofar gidan su ƴan sanda hudu mata biyu maza biyu suna ƙoƙarin tafiya da ita jama'ar unguwar sun hana anata hayaniya, gefe ɗaya kuma ga mahaifiyar Ahanah tsaye ta zuba masu ido ta rasa abin yi. 

“ inna lillahi wa innah ilaihir raju'un mme yake faruwane anan, " 

faɗin Abbas cike da son ƙarin bayani
Kafin kowa yayi magana maman Ahanah tace 

“ Yawwa kai kawai nake jira don ƴan sanda na ɗauko su kama man mahaifiyar ka su kulle idon taji duka da ukubar prision tasa ka sakar mani ƴata ”. 

Kuka Hajiya Larai mahaifiyar Abbas ta sake fashewa da shi tana faɗin

 “ kaga abinda kaja mani Abbas tun da uwata ta haifeni ko ziyara banyaɓa zuwa prision ba amma yau gashi za a kamani dalilin aurenka, don haka indai na isa gareka to ka gaggauta sakin Ahanah yanzu yanzu nan..... "

“ ba haka za'ayiba Hajiya tunda nazo yanzu komai zai dai dai ta don sakin aure abune mai girma...... 
Da sauri Hajiyar ta ƙatsesa da faɗin 

“ lallai Abbas duk abinda yake faruwa bai isheka iznah ba sasanci ma kakeso ko to bari kaji Ahanah ko itace autar mata yau sai ka saketa don haka maza ka furta tun kafin in ɗaga maka nono natsine maka albarka kabi duniya...... 
“ Zan aikata Hajiya abin bai kai hakaba " 
sai ya kalli maman Ahanah yace

 “ ni Abbas Dauda na saki matata Ahanah saki ɗaya. ”

“Alhamdulillah yanzu kacika ɗan Halak Abbas kayi abinda ya dace. "

Nan take mama ta bama ƴan sanda dubu goma tai umarnin su rabu da Hajiya komai ta zo ƙarshe, nan rake ƴan sandan suka shiga motar su sukabar wajen, Abbas da Hajiya ma gida suka koma ransu duk a jagule, ita ko mahaifiyar Ahanah kamar an mata bushara da Aljanna haka takeji tsabar zumuɗi da murna, kanta tsaye filin polo ta nufa gidan ƴartata, 

Abbas yana shiga cikin gidan nasu ya zauna akan turmi ya dafe gefen kansa dake masa wani irin fitinanne ciwo kunci da baƙin ciki sukai masa cah acikin rayuwa yane mi walwala da annashuwa ya rasa komai ya fice masa arai bai san sadda wani irin hawaye mai zafi ya fara bin fuskar saba, ruwan sanyi Hajiya Larai ta mmiƙo masa tana cewa

 “ Amshi sha ruwan sanyi ranka ya rage kuna kai haƙuri komai mai huce wane Allah zai baka madadinta koma wacce ta fita tunda na kirki basa karewa aduniya, kar ka kalleni da zarafin rabaka da auren ka abinda nai shine dai dai, don Allah Subhanahu wata Ala yace da manzon Allah idon har duniya ce gaban maranka to ka rabu da su don ba abokan zama bane don haka kayi koyi tunda Allah yace ( laƙaddkana lakum fi rasulillah uswatan hasana liman kana yarjullaha wal yaumin ahir.) 
Don haka bazaka taɓeba aduniya ba tunda ka bi umarnina kuma kayi abinda Allah yace don haka sakamakon ka mai girma ne. ”

Bai iya cewa komai ba saboda yadda zuciyarsa tai masa nauyi kawai sai ya amsa ruwan ya soma sha, kurɓa biyu yayi ya sarke da tari ya fara tari ƙuhul-ƙuhul kamar zai shiɗe. 
Take Hajiya ta ruɗe tana faɗin sannu kafin tai kicin ta ɗebo toka ta na shafamasa ga ƙirji tana ta jera masa sannu,
Abu kamar wasa tari yaƙi tsayawa tun yanayi zaune har ya duƙa akan guyagunsa yana yi kafin kuma ya fara aman majina, sai da ya amaye komai da yaci aranar kafin ya faɗi kwashaf akan tabarma jiki babu ƙarfi sai nishi yake kamar wanda yaci uban gudu kafin kace me zazzafan zazzaɓi ya rufesa ya faɗi a tabarma babu lafiya. 
      **** . ****
Assalama alaikum mama ta faɗi tana kutsa kai cikin gidan kafin taci gaba da faɗin

 “ ƴar albarka fito fito mu tafi yau dai burina yana daf da cika don Abbas ya sakeki", 

Dam! Taji gabanta ya faɗi don saboda girma kalmar sai ta farajin awani abu yana mata yawo a cikin zuciyarta mai kama da nadama da dana sani sai dai batai zurfi acikin wannan yanayi ba kamanninta suka sauya zuwa jin daɗi saboda jin abinda mahaifiyar ta ke faɗa

“ Shikenan Ahanah yanzu zaki iya auren Samir babu wani shamaki yanzu zaki zama miloniya cikin ƴan shekaru zaki kere sa'a don samir ya shedaman Ana ɗaura auren ku zaku wuce saudi arebiya da ƙasashen turai cin Amarki ni ko hon mi ake cema abin oho dai shi ya sani, yanzu haɗo kayanki kizo mu huce gida ”. 

Babu musu ta shiga haɗa abinda zata buƙata ta cika jikka dam kafin suka fito suka kulle gidan suka hau kekenapep sai unguwar masanawa inda gidan su yake. 
                   CHARANCHI LOCAL GOVERNMENT
Ƙauyen fulani, 

 ƙauye ne da yake acikin garin charanchi, kuma ƙauyene mai yalwar arziƙi da tarin ni'imomin rayuwa, mafi yawan mutanan garin fulani ne kuma makiyaya. 
Malam Giɗaɗo yana ɗaya daga cikin mazauna garin kuma haifaffen garin ne iyaye da kakanni, bayan sana'ar kiyon da yake yana sana'ar saida kayan kaba wanda da kansa yake zaunawa ya haɗa abinda ya danganci Hular kaba, Tabarmar kaba, Faifai , igiya, da sauransu. 
Malam Giɗaɗo mutum ne da bai son zama waje daya hakan yasa kullum cikin tashe tashe yake, yana da mata guda ɗaya mai suna Basira sai yaransa biyu duka mata Azima da Muheebaht, malam Giɗaɗo farine dogo kyakkyawan bahillace haka matarsa da ƴaƴan nasa abin birgewa gasu da farin jinin Al'umma, domin malam Giɗaɗo mutum ne na gari mai halin kirki, zumunci, kyauta, da alkhairi, da son jama'a bai da son abin daniya ko kaɗan hakan yasa mutane ke mutuntashi da bashi girma, yana son yaga yara da ilimin addini da na zamani hakan yasa ya tsayama yaransa tsayin daka ganin sun sami nagartaccen ilimi na bokon da na addinin domin kuwa duk ƙauyen yaransa ne kawai suka shiga sakandare, mafi yawan Al'ummar dake rayuwa a garin basu wani damu da ilimi ba sai kiwo da noma da shiga kasuwannin ƙauye don neman kuɗi , hakan yasa basusan komai ba sai zafin nema