HANGEN DALA

Chapter 7

by @abdulhakimumar122

Page 7
*** 


Ayanzu haka malam Giɗaɗo ya koma ƙauyen Jikamshi babu daɗewa shida iyalinsa, innda ya tashi daga unguwar kashe nera, anan unguwar yaransa sukai karatun firamare ɗinsu har suka gama ayanzu haka basu daɗe da fara zuwa makarantar sakandarba dake nan cikin charanchi a sabon layi, kullum yake kawosu da kansa kuma idon antashi yazo ya ɗaukesu akan mashin ɗinsa jencan ƙarfe wanda ya tsufa har ya kwararraɓe, Azima itace babba shekarunta sha shidda tana aji biyu a babbar sakandare wato (ss2) ita kuma Muheebaht shekarunta sha huɗu tana aji ukku a ƙaramar sakansare wato (Jss3). 
           

                       JIKAMSHI

 
Ranar talata goma ga watan Yuni shekarar dubu biyu da ashirin da biyar da misalin ƙarfe bakwai na safe. 
Malam Giɗaɗo ne zuƙunne a tsakar gidan sa yana gyaran kacar mashin ɗinsa da wani waje ya fara tsatsa, yana ƙarasa gyaran ya fara kiran “Azima kufito muje karku makara "
“ To Baba ” Azima ta furta tana fitowa daga cikin ɗaki riƙe da kofin kwakko da ƙosain da take kalaci da shi, A tsaitsaye ta shanye kafin ta isa inda Baban yake jiranta don tuni Muheebbah ta gama shirin nata ita ɗaya suke jira, tana isowa Baban ya tayar da mashin ɗinsa suka nufi makaranta sai da duka fara tafiya kafin Mahaifiyar su Basira tace “malam Atafo mana da kayan miya namu sun ƙare ”. 

To ya amsa mata yana mai cigaba da tafiyar, tafiya sukai mai tsayi kafin suka fara tarar da gidajen mutane harma da mutunen sunata hada hadarsu kasantuwar safiyace. 
Gidan malam Giɗaɗo Acan ƙasan garin JIKAMSHI yake cikin daji domin babu gidan da ya jera da nasa sai ma kayi tafiya sosai kafin ka iske wasu gidajen, filine kawai ya gina ɗakuna biyu aciki sai bukka da makewayin da akai da zana, duka gidan an zagayesa ne da gadon kara irin wanda fulani ke amfani da shi wajen zagaye gidajen su da shi ansare duk wata ciyawa da ta fito a tsakar gidan ya daddale tsaf da shi don a share zaka samesa akoda yau she.
 
Har bakin (Commercial college Charanchi ) wato ( GGTCC) ya ajiyesu sai da yaga shigarsu kafin ya tafi kasuwa ya tsaya dake bakin titi a cikin unguwar kashe nera ya sayi cefane da mai da magi da sauran kayan buƙata ya nufi gida, don ayima yara girki kafin su taso makaranta. 
A nan tasowa yazo ya ɗaukesu, suna tafe suna labari har suka iso gida abin gwanin birgewa, rayuwa suke cike da so da ƙaunar kansu, rayuwa mai tsari da sha'awa kamar ba aƙauyeba suna cikin walwala da jin daɗi basu da wata matsala kuma babu abinda yake damunsu. 
Suna isa ƙofar gidan su suka tarar da mashin a ƙofar gidan ajiye da mamaki suka shiga gidan don ganin wane irin baƙi sukai, 
Washe baki Baba yayi ganin ƙanesa Lamiɗo da wasu mutane su biyu da yayi ya isa garesu da azama suka gaisa, ganin haka yasa Azima da Muheebbah suka gaishe da baƙin kafin suka shige cikin ɗakin su. 
Tabarma Baba ya shinfiɗa masu a ƙarƙashin inuwar bedin dake tsakar gidan suka zauna aka kawo masu ruwan tulu mai sanyi da tuwon masara miyar kuka ya sha manshanu da yajin daddawa. 
“ Yaya Giɗaɗo da fatan mun sameku lafiya ” cewar Lamiɗo 
“ muna lafiya ƙalau Lamiɗo ya waje su inna da sauran mutan ƙauyen fulani? "
Cewar malam Giɗaɗo cikin walwala da fara'a
“ Duk kowa yana lafiya kuma suna gaidaku, Dama iyayen Shamsu na rako gasunan mahaifin sa ne da ƙaninsa kuma sunzo neman auren ƴarka ne Azima da fatan zaka basu batare da sun sha wuyaba. ”
Sai fara'a dake kwance a fuskar Baba ta gushe ya ɗaure fuska tamau kafin yace “ wai ni Lamiɗo yaran nan akanka suke rayuwa da zaka dage ganin sunyi aure na faɗamaka ni yarana karatu zasuyi mai zirfi su taimaki al'ummar ƙauyen nan da sauran mutane don karatun likita zasuyi, kuma suma suna da burin haka saboda wannan dalili yasa bazan iya gajarce masu rayuwa ba zan barsu suyi abinda suke so don farin cikin su shine nawa don haka wannan ya zama na ƙarshe da zaka sake kawo mani wasu a gida da sunan sunzo neman aure, "
“ Amma yaya kasan abinda kake shirin aikatawa yan cikin lalata al'ada bamu taɓa ganin yaran da karatu ya hanasu aure ba bayan gasunan tun suna firamare ake fitar dasu ayi masu aure amma kai ga ƴan mata nan har sun fara jerawa da mahaifiyar su amma kace ba zaka aurar da suba to sai yaushe..... "
“Sai sadda lokaci yayi Lamiɗo bani son muna jayayya da kai don haka mubar wannan maganar ”. 

Haka suka rabu duk ransu a ɓace babu mai walwala. 

                      ABUJA

Birnin tarayya unguwar (JABI) gidan Alhaji Sulaiman Bara'u Gidan Iko, ƙaton falon cike yake da manya - manyan kayan more rayuwa, mutane ne masu kuɗin gaske kuma ƴan siyasa su huɗu zaune a falon sun haɗa taron ne don tattauna wasu matsaloli dake damunsu dan samun hanyar magancesu. 
Alhaji sulaiman gidan iko ne ya soma magana kamar haka “ Dukkan ku dai kunsan maƙasudin taruwarmu anan akan zaɓene don sanin kankune middin aka tafiba haka to jam'iyar adawa itace take da nasa, duba da yadda jama'a suke tururuwar goya masu baya don haka ya zama dole mu kawar da Alhaji Aliyu muhammad middin muna son cikar burikanmu da muradanmu. ”
“ Anya Alhaji wannan hasashe naka zai haifar da ɗa mai ido" Cewar Alhaji Nuhu Dutsi kafin yaci gaba da faɗin “ idon mukai tunani akan wannan lamari da ankawar da Alhaji Aliyu muhammad hankalin jama'a zai dawo kanmu dole za a zargi jam'iyar mu kuma kunsan gwamnati ba a ja da ita, duk wanda ya ja da gwamnati to zai kwana ruwa tsullugudum”. 
Alhaji Iro mai kaita ne ya amshe zancen da cewa “ Tunanin Gidan Iko shine dai dai sai dai akwai ƙarin bayanin da za'a yi akai don kuwa middin Alhaji Aliyu muhammad yana raye to babu ranar da zamu samu zarafin cika muradanmuba middin muna son cikar burin mu sai mun kawar da shi, amma idon an kawar da shi sai aje cen wani ƙauye asamo mutum Talakka wanda bayada yadda zaiyi ace shine yayi kisan ma'ana a ɗaura masa laifin, ta nan zamu fito mu nunama duniya babu sa hannunmu kuma muyi kanfen abinda ya dace”. 
“Gaskiya ne wannan aikinka na kyau ɗan mutan kaita ”. Cewar Alhaji Ado kurfi cike da yaƙini. 
“ To yanzu waye zaiyi aikin cikin kwarewa da sanin makamar aikin " cewar Alhaji sulaiman gidan iko 
“Wanda zaiyi aiki bazaiyi wuyaba don ina da kwararre wanda yake da gogewa akan aikin ya samu trening sosai don haka bari kuga na kira shi don da zafi zafi akan daki ƙarfe, "Alhaji Iro mai kaita ya kai ƙarshen maganar yana ƙoƙarin fito da wayar sa daga cikin Aljihunsa ya danna kiran lambar mai Rakwacam, 
Bugu ɗaya aka ɗauka ana faɗin “Allah ya kare sai da kai Alhaj Allah, sai kahuta ka sarara da ikon Allah, Tsaba kake sai an casa , ka daɗe kai ƙarko uban gida na zuma kake sai an lasa, cikakken jagora sanadinka akejin sunana, waya taɓaka yanzu na farmasa sai dai uwar sa ta haifi wani wallahi, amma tasa ta ƙare.... "
“ Ya isa haka don idon na tsaye saurarenka sai mu kwana kana kanbamani anan, wani aiki nake son aiman amma aikin babbane sai ansa lissaffi da tunani mai yawa don wanda za'a kawar shima shegene akwai tsaro. "
“ Haba Alhaji yakake magana kamar baka san da wakake magana ba ai babu wanda zai gagareni agarin nan don haka kawai turo kayan aiki kukan ka yazo ƙarshe don yau matsalarka ta ƙare . "
“ Yawwa ɗan gari haka nake son namiji ya kasance zanbaka one million idon aiki yayi dai dai kuma zan sake nemanka bari na turama bayanansa, " yakai ƙarshen maganar yana katse wayar sai da ya fara tura masa one million kafin yatura masa poton Alhaji Aliyu muhammad da addreshinsa da bayanan inda yake kafin ya sake kiransa ya buge masa honinng akan yayi aikin kwarewa don basu son asami marsala. 
Sai da ya mayar da wayar sa Aljihunsa kafin ya mai do da hankalinsa kan sauran Abokan nasa yace “ To ni dai na gama nawa saura naku ". 
“Sauran aikin nawa ne kubar komai a hannu na " cewar Alhaji sulaiman gidan iko. 
Ƙarfe biyu da ashirin da biyar na ranar laraba Alhaji sulaiman gidan iko ya kira lanbar wani yaronsa dake garin JIKAMSHI ya sanar dashi aikin da yakeso aimasa da kuɗin da zai bada, sai da suka daddage magana kafin sukai sallama da alamun cin nasara,. 
Wani shu'umin murmushi Alhaji sulaiman gidan iko yayi na samun nasara kafin ya kira lanbar amintaccen ɗan sandansa dake garin Charanchi ya sanar dashi “Yallabai ya yau ya aiki ya fama da miyagu ”
“Alhamdulillah Alhaji gaskiya yau ina cikin sa'a don rabon da kakirani yau ankai wata kullum cikin sauraron tsammani nake, sai ga shi yau jira ya ƙare yanzu meke faruwa ne Alhaji. "
Sai da yaja dogon lumfashi kafin yayi masa bayanin komai akan shirinsu, kafin ya ɗaura da cewa “ idon har amsami wanda ya dace za'a sanar dakai, kai kuma ka tura hilux a ɗauko sa, na gode bari na tura maka na mai. ”
Suna gama wayar Alhaji sulaiman gidan iko ya turama ɗan sandan kuɗi masu yawa.