HANGEN DALA

Chapter 8

by @abdulhakimumar122

Page 8

        
              GWARUNFA ABUJA NIGERIA 

Da misalin ƙarfe sha ɗaya na dare Alhaji Aliyu muhammad ne zaune a cikin motar sa yana zaune ne a gidan baya inda Direba ke tuƙasa, ya sawone daga wata ƙaramar Asibitine dake can cikin GwaGwalada, Asibitin ta talakawace hakan yasa ya kai masu ziyara don taimakon mutane dake jinya da kuɗin aiki wasu kuma na magani, kowa dai da irin taimakon da yake masa suna dai dai da titin ( gidab zoo.) . Zasu shiga cikin gari sai ga wata ƙatuwar mota ta ɗibar yashi ta danno kai aguje duk yadda direban yaso ya kauce masu amma abin ya cutura sai da sukai mummunar haɗewa, domin kuwa sai da motar su ta wuntsula ta kife. 
A ɗari ukku da sittin mai Rakwacam ya bar wajen batare da kowa ya gansaba, kafin kace me tuni gari ya ɗauka, don tuni Allah ya amsa rayuwar Alhaji Aliyu muhammad da direban babu wanda ya tsira a cikin su rai yayi halinsa. 
Aiko nan gari ya haucine da faɗin ƴan jam'iyar adawane don haka sai sun ƙashesu suma kamar yadda suka ga bayan mutumin kirki kamar Alhaji Aliyu muhammad. 
A nan nefa ciki ya ɗuri ruwa tsakanin Abokan nan guda huɗu, kiran wayar Alhaji sulaiman gidan iko da akai shine ya dawo dasu cikin duniyar farin cikin don ɗan sandan ya Tabbatar masu cewa binciken ta hannun sa ya faɗo kuma sunyi nasar samun wanda za'a ɗaura ma laifin. 
          
JIKAMSHI 

Gidan malam Giɗaɗo yau sun wuni cikin farin ciki marar musultuwa sakamakon ƙaramin cikin da akace mama Basira na da shi wanda suka daɗe suna tsammanin zuwan sa don tun tuni suke tanajin wannan rana. 
Malam Giɗaɗo A tsaye yana bama yara sadakar soyayyen Dankali wanda ya sawo a kasuwa don ai sadakar da shi domin yau yana cikin farin ciki, Azima da Muheebbah suna zaune aƙarƙashin inuwar bedin dake tsakar gidan suna gyaran shinkafar da zasu dafa su ci da daddadare sai mama Basira tana ɗaki tana linkin kaya, kamar daga sama sukajiyo jiniyar motar ƴan sanda a unguwar. 
Tsakanin mama da su Azima har rigal ɗin fita ake don ganin abinda ke faruwa, kasantuwar tunda suka dawo garin basu taɓa ganin ɗan sanda ba bare kuma ace motar tasu baki ɗaya da gani kasan ba lafiya ba, tsayawar hilux ɗin aƙofar gidan su yasa gabansu ya yanke ya faɗi su duka baki ɗaya. 
Ba tare da ɓata lokaci ba ƴan sandan suka shiga fitowa ɗaya bayan ɗaya zasukai su goma sukai caraf da malam Giɗaɗo suka fara kiciniyar sakashi mota. 
Tashin hankali wanda ba a masa rana yo ai tuni mama Basira da Azima da Muheebbah sukai ca akan su suna kiciniyar kwace baban daga gare su suna kuka 
“ Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un yau mun shiga ukku kurabu dashi bai da laifi bai aikata komai ba duk yau yana gida zaune baije ko ina ba ” cewar mama Basira tana ƙara kwankwame Baban 
Jikake ta! ta!! Wani marar imani daga cikin ƴan sandan ya ɗauke mama da mari kafin ya saka hannayesa duka biyun ya turata baya ya haɗa mata da halbi da ƙafa har sai da ta kifa ƙasa akan cikin ta, take ko wata azaba ta ratsa dukkan illahirin gabobin jikinta cikin rauni da buguwa tace “ wayyo ciki na zan mutu” kawai sai jini ya ɓareke ya fara bin cinyoyinta.   
Da wani irin zafin nama Azima tai kanta tana faɗin “ mamahhhhh”
Ganin hakan ya ƙarama Muheebbah ƙwarin gwiwa da ƙarfin riƙe Baba matakam tana gunjin kuka 
Kanta wani ɗansanda da ban ya kamo yana shirin buga ta ga bango, da sauri Azima ta saki mama tai kan Muheebbah a firgice ta rungumeta sukai ƙasa atare, hakan ya bama ƴan sandan damar saka Baba bayan hilux ɗin da ƙarfin tsiya. 
Muheebbah zata tashi mama ta riƙo hannun ta tana faɗin“ karki bisu kiman addu'a mutuwa zanyi ciki na kamar ana kunna wuta haka nake ji”
Sai Muheebbah ta rungume maman ajikinta tana faɗin 
“bazaki mutuba mama zaki rayu, ”
Ita ko Azima tuni ta miƙe ta riƙe bayan motar tana faɗin “ Jama'a kuna gani zasu tafi da Babanmu bai masu komai ba kutaimaka mana karku bari su tafi da shi 
Babu imani ko tsoron Allah tare da su sukai ma motar key sukaja aguje, tilas tasa Azima sakin motar don gudun da suke yafi ƙarfin ƙafafunta don kamar zasu balle haka takeji. 
Dabas ta faɗi saboda wata irin juwa da ta ɗauketa, kuka ta fashe da shi tana gunji tana ƙara damƙar ƙasa tana ɗaga hannuwanta tana nuni da motar tana cewa “ Duk taron mutane nan babu wanda zai iya taimakon Baba, jama'a kuyi mana aikin gafara karsu tafi dashi, ” sai kuka yaci ƙarfin ta ganin babu wanda yayi yunƙurin tai makonsu.
      yunƙurawa mama tai da nufin tashi, amma bata ida miƙewaba jini ya ɗibeta ta sake faɗuwa, zafi da zugi da azabar da taji sune suka haddasa mata sakin wata gigitayyiyar ƙara wacce bata san firar raba, da jan ƙafa Azima ta iso inda mama take kwance a jikin Muheebbah, kamota tai kafin tace “ Muheebbah maza kije babban gidan ki sanar dasu halinda muke cikin kinji” tai maganar tana mai share zafafan hawayen dake zubo mata a saman kunci. 
Da sauri Muheebbah ta ɗau hanyar aguje duk nisan dake akwai tsakanin JIKAMSHI da Ƙauyen Fulani da ƙafa Muheebbah taje saboda tsabar tashin hankalin da take ciki, sadda ta isa gidan ko magana bata iya yi sai shassheka da nishin gudun da tai, sai da ta huta kafin ta sanar dasu abinda yake faruwa. 
Suma cikin tashin hankali da firgici suka shiga kawu Lamiɗo sai zufa yake jin ance ƴan sanda haka ya goya mahaifiyar su da Muheebbah a bayan mashin ɗinsa suka nufo JIKAMSHI. 
Sai dai abinda suka iske yafi komai ɗaga masu hankali domin kuwa mutum suka iske lulluɓe da zani a gaban Azima taci kuka har ta gaji idanun nan nata sunyi jajur sunyi luhu - luhu. 
Da gudu Muheebbah taje ta zuƙunna gaban Azima tana murza idanuwanta tana faɗin “meye nan ". 
“ mamace Muheebbah Allah ya amsa abisa mamarmu ta koma ga Allah sun...... "
Kukan da yaci ƙarfinta shine ya hanta ida maganar 
Ita ko Muheebbah hannu na kyarma ta saka ta janye mayafin sai taikaro da fuskar mahaifiyar bata iya lumfashin gata kwance kamar tana bacci “ kai yaya baki gajiya wace maki mama mutuwa tai bacci take idon anjima zata darka, gatanan tana mani murmushi zata tashi zata haifo mana ɗan jariri”. 
“Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un " kawu Lamiɗo ya furta yana goge hawayensa don ya fahinci kamar akwai ruɗewa tare da Muheebbah 
Jawota Azima tai ta rungume tana kuka kafin cikin kukan tace “ sai dai muyi haƙuri Allah yasa mana dangana Amma mama ta rayu ta rugamu gidan gaskiya tai baccin da babu tashi sai a lahira ”. 
“ mahhh mahhh mamar tamuce bazamu ganiba sai a lahira ” cewar Muheebbah cikin in ina kafin ta fara jan lumfashinta yana gushewa, so take lumfashin ya fito dai dai amma yaƙi bata haɗin kai kawai sai ta zube jikin Azima babu rai. 
Bayan komai ya dai dai ta tuni akaima mama sutura zuwa makwancinta na gaskiya. 
Duk inda akasan ƴan sanda na zama ko wata sitasion anje amma babu Baba babu Labarin sa iya tashin hankali da damuwa to wannan zuri'a sun shiga ciki musamman ma Muheebbah da Azima don ko abinci basa iya ci sai dai abinda ba arasaba shima sai an takura masu. 
Ranar sadakar ukku ne sukaji anayin sanarwar ankama wanda ya kashe Alhaji Aliyu muhammad kuma gobe za'a shiga kotu don yanke hukunci. 
              
                          KADUNA STATE NIGERIA 
 
Kasaƙe Namsiyya da Sholy sukai don ganin abinda ya haddasa yin ihun samarin. 
Wata irin Rangatsetsiyar mota ce mai kyan bala'i tai packing a harabar wajen, sai da aka ɗau tsawon mintina biyar kafin matashin gayen dake tuƙin ya fito ya zagayo gudan sashen motar ya buɗe marfin cike da bada girma, ƙaface ta fara fitowa kafin gangar jikin nasa ya fito cikin isa da taƙama da ƙasaita kamar ɗawisu, sanye yake da ƙanan kaya baƙaƙe masu haɗe da falmara an sirka baƙin da (skye blue) inda ita kuma rigar aka zana wasu ƙananan tanbari ajiki jehi-jehi, kallo ɗaya zakai masa ka gano tsantsar kyau da kwarjinin da Allah ya hore masa ga kuɗi da jin daɗi da hutu sungama baibaye yanayin halittarsa yana da shiga rai don bazaka iya gano nakasunsaba a kallo ɗaya, tako ya fara zawa inda ya saba zama kasantuwar wajansa na musamman aka fitar masa dashi a wajan don ba ɗaya yake da kowaba saboda yana da kuɗi. 
“ Subhanallahi ahsanul haliƙin, ƙawa wallahi gayen nan ya haɗu ya tafi da imanina ina sonsa yayiman.”
“ ke Namsy wallahi wannan yafi ƙarfin ki ko baki san ɗan wayeba to ɗan Alhaji Abdurrahman Na'adamine ni kaina nasan yafi ƙarfina bare kuma ke, don haka ki natsu kisan a inda kike don wutsiyar raƙumi tayi nisa da ƙasa , linzami yafi ƙarfin bakin kaza, kuma wajen rijiya ba wajen wasan makaho bane. ”
Mukutt Namsiyya ta haɗiye yawu kafin ta juya don ta saci kallon sa jin cewa ɗan Alhaji Abdurrahman Na'adamine domin kaf ciki da bai na garin KADUNA babu wanda bai san Alhaji Abdurrahman Na'adami ba saboda tarin dukiyar sa domin kuwa idon baifi kowaba to zai zo a nabiyu ko na ukkun masu kuɗin KADUNA kuma ba zai wuce hakan ba saboda irin yadda yayi tsura wajan kasuwani. 
Karaf sukai ido hudu da shi sai tai saurin ɗauke kanta gaban ta na tsananta faɗuwa saboda wani irin kwarjini da yayi mata, tabbas gayen ya hadu kuma ina son sa na shirya fuskantar kowane irin ƙalubali akan samun soyayyarsa na aminta zan jure komai akansa, mai da kallon ta tai kan Sholy kafin tace

 “ Aminiyata ina son sa zan iya komai akansa wallahi bakiji yadda zuciyarta take mani wani irin abuba bansan yadda zan fassarashiba, ”

“ Aiko kina shirin jefa kanki acikin tsaka mai wuya don zaki dakon sone kawai ya wahalar da ke domin wa'inda suka fiki kyau da ilimi sa nasaba da arziƙi sun soshi amma ya ƙisu ya wulaƙantasu don ba kirki ne da shiba saboda haka kiyi gaggawar dawowa cikin hayyacinki don karma ki yadda sonsa ya shiga ranki da yawa don zaki kwana ne da masifar son da bata da mafita, ki manta dashi kawai ki nemi ɗan ƙarya dai dai ke amma ba wancenba. ”
 Anya zan iya barin sa kai never bazai yuyuba dole sai na mallake shi kuma dole yasoni , irin wannan miji na kece raini na nunama sa'a bazan yadda ya kuɓuce mani ba, ai shine irin mijin da nake mafarkin samu wanda na daɗe ina hasashen sa azuciyata kuma na jima ina hangensa a duniya ta sai yanzu kuma yazo na zauna nai sanya, aiko ke Sholy na auri wance sai ɗai ki zamo ƴar maula aguna don haka wannan damatace...... 
“Ki ci abinci mana sai wani tunani kike ” cewar Sholy tana kafe Namsiyya da ido
“ yaya sunannsa? ina son sani” Namsiyya ta jefoma Sholy tan bayar
“ me kuma zaki da sunan sa bakiji abin da na gayamakiba ko, ”
“ ke dai ki sanar dani ina son nima na gwada sa'a ta ”. takai ƙarshen maganar tana mai fari da ido
“Sunan sa Areeyan ”
Batar da tace komai ba ta l miƙe tana mai nufar inda yake tana tafe tana ranngwaɗa tana karkaɗa jiki aiko sai wani irin malolon abu ya tokarema Sholy wuya ganin yadda Namsiyya take sarrafa jikinta, tabbas zai iya jin wani abu akanta ko bai sotaba zai ji sha'awarta don ba kowane irin namiji bane zaiyi tozali da Namsiyya baiji ta burgesaba saboda irin kyawun halittar da Allah yayi mataba sai dai mai ƙarfin imani, kuma tasan Areeyan sarai bai da wannan kawar da kan akan mace don haka sai kishi ya raso ma sholy sosai don bata da wannan ƙirar. 
“ Hello ” Namsiyya ta furta tana mai ƙoƙarin zama bisa kujerar dake gefen sa da sauri ya nunama gayen dake gefen nasa ita da ido da Alamar yayi wani abu akai 
“Kehhhhh ba'a zama nan” ya kwatsa mata tsawa kafin daga bisani yaci gaba da faɗin “da alama dai ke bakuwace anan baki san waye ke zaune a wajan ba ko to maza barnan" yakai ƙarshen maganar yana nuna mata hanya