HANGEN DALA

Chapter 15

by @abdulhakimumar122

Page 15


Tahteef kwance yake akan makeken gadonsa wanda akayi odar sa daga ƙasar dubai, gadon babbane kuma girma ba naa wasaba don atsakiyar ɗakin akai masa mazauni kuma mai runfane inda aka zagaye runfar da fararen labullai masu laushi,
Juyi yake a gadon ya kasa bacci karo na farko a rayuwar sa da wani abu yake ƙoƙarin hanasa bacci domin kuwa da ya rufe idanunsa bai ganin komai sai kyakkyawar fuskarta lokacin da take masa murmushi, ahankali yake tuno surarta da irin yadda take magana cikin muryarta mai sanyi da daɗin sauraro golding voice . 
Ahankali wani irin murmushi ya subuce masa cikin shauƙi da nishaɗin da bai taɓa samun kansa aciki ba bacci ya riskesa. 
Washe gari sai wajen ƙarfe goma na rana ya farka ya hau shiri a gurguje ya bar gidan. 

Muheebbah tun da sassafe ta hau girkama yara ruwan shayi don yau tea da bread zasuci, tana tsaka da aikin sai ga Anty Aina ta shigo kicin ɗin ita da wani mutum wanda zai kai shekara Arba'in da ɗaya. 
Amsa sallamar da sukai mata tayi tana murmushi tare da cewa “ Baƙo kuma mukai Anty Aina ”. 
“ Ai ba bako bane ɗan gida ne yayan mai gidan nan ne kuma ita ce ta turo sa saboda na sanar da ita taimakon kuɗin da muka samu kuma har mun yanke shawarar yarda zamuyi da su shine mukace bari mu tuntuɓeki ko akwai wata shawara da zaki bayar akai ”. 
“ kai amma Anty kinso wahalar da kanki ai dani da dukiyar duk mallakin kune duk hukuncin da kuka zartar yayi ”. 
“ kuma fa hakane” cewar mutumin yana gyara tsayuwarsa 
“To dama ba wani abune mai tsahoba abinda muka yanke shine, Dama wannan bawan Allahr yana da wani rastorent na sayar da abinci shine muka yanke hukuncin sayen wajen aita kasuwar da Zata kawo mana kuɗin da zamu dinga biyan ma'aikatanmu da su da kula da lafiya da cih da sha na yaranmu wajan zai zoma mallakar HALAL CHINDENT HOME, sauran kuɗin kuma za'a biya Albashin ma'aikatanmu sai sauran zamu sayi kayan abinci da duk abinda muke buƙata ”. 
“ kai amma nayi murna ya sunan gidan abincin "
“ TA' AYE RESTORENT zamu jema gobe sai ki gani ”. 
“To Allah ya kai mana rayuwar mu, kuma Allah yasaka maku da Alkhairi, Allah yasa hakane mafi Alkhairinmu baki ɗaya ”
Amin suka amsa su duka ran kowa fes suka fita 

Muheebbah zaune take tana shayar da wani yaro tea a cikin harabar gidan saboda rana ta take kuma nan yafi iska, sai taji kamar ana kallon ta don haka ta ɗago kanta a hankali tana kallon saitin gate ɗin gidan, karaf sukai ido hudu da Tahteef yana kallon ta sai taji duk ta tsargu saboda babu hijabi ajjikinta don ma sauƙinta Atanface ajikinta ko ina asuturce yake. 
Kallonta yake irin kallon nan da yake gusar da hankan mai yinsa domin a zuciyarsa tuni ya fara ayyanota acikin mayafi ta rufe fuska za'a kaita gidan sa a matsayin Amaryar sa , kowa ya kallesa zai iya gane halin da yake ciki na farin ciki, don yanayin da yake ciki ba boyyayyen al'amari bane ga sabon shiga rayuwar soyayya , 
Ajiye yaron tayi gefe ta ɗau hijabinta ta nufi inda yake, amma har ta isa bai san ta zoba yana cen wata duniya ta farin ciki, sai da ta haɗe ɗan yatsanta babba da manuniya ta murza sukai ƙara kafin ya yi firgigit ya dawo duniyar da yake yana sakin wani sassanyan murmushi, 
“ ƴallaɓai sannu da zuwa ai da kasa an kirani zan zo basai ka wahalar da kankaba mu shiga ka ga yaran ”. 
“ A a basai na gansuba sauri nake amma zan sake dawowa, ga wannan saboda shi nazo , ” yakai ƙarshen maganar yana miƙo mata kwalin sabuwar waya Iphone 16 fro . 
“ Ƴallaɓai ni kuma wannan da gani mai tsadace ba zai yuyu na riƙetaba ”. 
“ wayar 2 poinet 5 ɗince bazaki iya riƙewaba ”. 

“ 2 poinet 5 Ƴallaɓai million biyu fa har da dubu ɗari biyar, na shiga ukku rufaman asiri kada a shigo da dare a yankeni ” ta faɗa tana zaro idanunta waje 
Murmushi yayi yana mai kwantar da kansa akan kafaɗarsa don shi atunaninsa wasa take yadda yaga ta razana. 
Sai yaci gaba da cewa “ saboda wannan wayar za a yankaki 2million fa ” ya furta yana mai mamaki saboda shi ji yake kamar ya cire naira ɗari biyu da hamsin 
“ Ƴallaɓai kayi haƙuri bana son ina gardama da kai amma bazan iya amfani da wannan wayarba tafi ƙarfina ” ta ƙarashe maganar tana marairaice masa fuska 
“Anti kizo Ahmad ya tashi sai kuka yake ” cewar wani yaro 
"To muje" ta furta tana mai ƙoƙarin bin bayansa. 
Shima yunƙurawa yayi da nufin bin bayanta sai wayarsa ta hau ruri, da sauri ya dakata da tafiyar da ya fara ya fito da wayar yayi piking ya kara a kunnansa 
“ ok Dad ina hanya ” haka kawai ya furta ya katse wayar ya kira yaron da ya gani yana wasa ya bashi wayar yace ya kaima Muheebbah, ya bar gidan. 

Tuni gidan ya dawo a hannun malam Sufiyanu wanda yayane ga wacce ta ginasa, sai da ikon sa ake komai kuma sai hukuncin da yayanke ake zartarwa. 

Muheebbah ta amsa wayar ganin ya tafi ya batta amma bazatai amfani da itaba sai dai zata ɓoyeta har lokacin da ya dace ta fito da ita. 
Washe gari ma sai ga Tahteef amma wannan karon har da yaransa biyu, tunda ya shigo wajan yake hangen inda zai ganta amma bai gantaba kuma ya manta sunanta bare ya tanbaya, kamar ance ya kalli gabas sai ya hangota ta tagar wani aji tana murmushi tana duƙawa tana ɗagowa da alama dai wani aikin take, da azamarsa ya isa sai dai bai shiga ajinba sai ya tsaya abakin ƙofa yana kallon yadda yaran suke farin ciki sakamakon choculat ɗin da Muheebbah ke rabamasu saboda ƙoƙarin da sukai na kawo haddar hadith ɗin da sukai batare da cin gyara ko gargadaba, baƙaramin birgesa hakan yayiba don haka sai ya sami kasa da shiga ya miƙa mata hannu, babu shi ta ɗago ganin babban hannu sai idanunsu suka sarƙe da juna saboda shima kallon ta yake, sai ta miƙa masa duka ledar kafin ta samu kanta da sakin murmushin itama ta kalli sauran yaran tace 
“ yara kuyi masa tafi da godiya shine wanda ya taimaka mana ”. 
Take suka kaure da tafi da hayaniya amatsayin godiya don har sai da ya toshe kunnuwanshi don bai saba da hayaniya ba 
“Ya isa” ta furta tana mai ɗaga murya ganin yaran suƙi yin shiru. 
Take ko ajin yayi tsit 
Kamar jira yake suyi shiru suna yin shirun ya ce “ ya akai baki kiraniba kuma nakira akashe. "
“ kayi haƙuri Ƴallaɓai bazan iya amfani da wayar ba ne shi yasa ”. 
A madadin yaji haushi sai yayi murmushi kafin ya fito da wani bakin ƙyalle ya bama wani yaro yace“ ka rufema Antynka ido zan mata bazata ”. 
Batai musuba ta tsaya yaron da ya fara wayo ya ɗaure mata idanunta suka fito har bakin gate, suna fita ya buɗe mata sai tayi tozali da wata ɗanƙareriyar mota sabuwa cikin ledarta kalar ja anmata rafin na filawa daga gabanta. 
Take yaran suka hau ihu da tsallen murna ganin sabuwar mota, ganin yadda yaran suke murna yasatai murmushi don ba ƙaramin burgeta hakan yayiba. 
Zatai mafana taji saukar hannunsa akan nata. 
Tai masa wani kallo da niyyar magana, sai yayi sauri ya a za yatsansa akan leɓe alamar tai shiru, sai kuma tai shiru ɗin saboda samun kanta da tai da shiga wani irin yanayi mai wuyar fassarawa, bata iya yi masa musu saboda wani matsayi da girma da zuciyarta ta bashi tun ranar da yayi mata wannan taimakon, binsa kawai ta hauyi kamar wacce aka halitta don bin umarnin sa kawai, motar ya buɗe ya sakata kafin ya koma mazaunin direba ya shiga ya ja suka hau hanya. 
A wannan rana sai da Tahteef ya zagaye garin ABUJA da Muheebbah duk abinda ya gani a hanya sai ya siya mata, tun abin yana birgeta har ya koma bata mamaki, tun abin na bata mamaki har ya koma bata tsoro don gani rake ya fara zautuwa, don haka ta fara tunanin ko dai baya da hankali, 
Dama ina yaga hankali wani sashe na zuciyar ta ya faɗa tunowa da tai da sadda ya ɗibi uwayen kuɗi ya bata a matsayin tallafi da kuma wayar da yasaya da sunanta wacce tunda take bata raɓa ganin kalartaba, gashi yau ya ɗau sabuwar mota yana zagaye fari da ita wai motar ma da sunan tatace . 
“ yaufa sai mu zagaye garin nan har insa baki mafarkin ganiba yau sai kinje wajan, kafin ki saba na fara koyar dake tuƙin, ”
Ya kai ƙarshen maganar yana kallon ta ta gefen ido don ganin irin ri 'acshion ɗin da zata bayar, sai kuma abin ya kasance yadda yayi tsammani don ɗaure fuska tai tana cewa 
“ Badai niba Ƴallaɓai sai dai ko matar da zaka aura”. 
To ai kece, zuciyar sa ta faɗa kafin ya fara mamakin karfa ace har yanzu bata san inda ya dosaba, kar ace har yanzu bata gane sonta yake ba, sai yaji kamar yace ina sonki, tuna cewa ba Lallai ta aminta da soyayyar saba yasa ya fasa domin ayadda yakeji bazai iya jimirin jin kalmar ƙiyayya daga bakintaba, zai iya komai domin ta hatta sa kisan kai haka yake ji a zuciyar sa. 
Taratsatsam wata uwar ƙara ta doki dodon kunnan Muheebbah sakamakon tarwatsewar gilashin motar da suke ciki na gaba, da sauri Muheebbah ta haɗe kanta da gwiwar ta tana makyarkyatar tsoro, inda shi kuma Tahteef ɗin yaja wani uban birki yana kallon mazan dake gabansa zasukai goma kowa ɗauke da makami. 
Yana tsayar da motar ya fita da sauri ya cire gatarin da ya fasa gilashin motar wanda tullosa akai, ya fara sarar wannan gungun samari, shi ɗayane suko su goma ne amma sai da ya nakasa kowa cikin ɗan lokaci batare da shi sunyi masa rauni ko gudaba, abakin na ƙarshen duka ne yakejin cewa turosu akai don su kasheshi kuma matar malamin makarantarsuce take son ɗaukar fansar kashe mijinta da yayi. 
Tun da ya koma cikin motar take kallon sa wani irin tsoronsa takeji, nadamar saninsa da tai ta keyi, don haka cikin kuka tace “ Ƴallaɓai waye kai ”. 
“ zaki san ko ni waye amma ba yanzuba sai lokaci yayi ”. 
To ka mai dani gida ta furta cikin muryar kuka. 
Baice da ita uffanba ya ja motar batare da wani ya sake maganaba har suka isa bakin gate ɗin HALAL CHINDENT's HOME, yana tsayawa tana buɗewa ta fice tana kuka duk jikinta a mace. 
Shima bai bi ta kantaba ya nufi haryar gida don duk jikinsa a gajiye yake.
Tana shiga mai gadin gidan marayun ya tareta da cewa “ hajiya wata ƴar magana nake son na gayamaki”. 
Tsayawa tai tana kallon sa kafin tace “ina jinka baba amma kayi da sauri don bana acikin yanayi mai daɗi. ”
“ Dama cewa zanyi mutane da yawa suna mamakin ganin ki da Tahteef sulaiman gidan iko domin shi kaifi ɗaya ne bai canjawa cikin sauƙi yana da haɗari sosai don duk garin nan ana shakkarsa don bai ɗauki ran mutane da wata darajaba kashe mutum agaresa kamar kashe kiyashine, baya da tausai da sauri imani irin na ƴaƴan musulmai, tarayya da shi kamar jefa rayuwar kine cikin haɗari don haka ina neman alfarma a gareki ki taimaka ki rabu da shi, don idon har kika cigaba sa tarayya sa shi to watarana zakiyi nadama. ”
Tunda Baba mai gadi ya ambaci cikkaken sunan Tahteef gaban Muheebbah yake dukan ukku ukku, tsoro ya kamata sosai akan wanda rake ciki, dagaske ɗan Alhaji sulaiman gidan iko ne, kuma wanda ta sani wanda ya datse mata duk wani farin ciki da shauƙi da dare ake ciki, wanda ya zama sanadin mutuwar mahaifinta, kai ba zai yuyuba, sai kawai taji hawaye na bin kwai da tudun fuskarta suna ɗiga akan wuyanta tunowa da tai da ƴar uwarta Azima, wani irin yanayi mai ɗauke da kwando bakin ciki ta sami kanta kuka take son tayi amma wani malolon bakin ciki da ya tokare ƙahon maƙoshinta ya hana wani irin zafi zuciyarta kemata kamar ana caccaka mata wuƙa Akai , wata irin tsana da ƙiyayya ta fara bin dukkan illahirin jijiyoyin jikinta, sai kawai ta toshe bakinta tai cikin gidan da gudu, sai dai ba inda ɗakunan su suke ta nufaba bayan inda tankin ruwa yake ta nufa ta zauna tana mai fashewa da kuka mai cike da nadama da danasani, kuka mai tarin ma"anoni. 

Tahteef sai da ya hau ƙatuwar kwaltar da zata sadashi da gidan su kafin ya fara samun natsuwa, Titin bubu kowa kamar ba rana ba, bakuma don ba'a binsaba a'a sai don ya kasance Titin da masu tarin dukiyar ABUJA ke da gidajensu wanda suke rayuwa, ko titin baka isa ka hauba idon har ya kasance baka da komai, duk wanda kagani a Titin to wani ƙusane a ABUJA ko kuma ɗan wani hanshaƙin mai arziƙi dake faɗa aji a cikin ƙasa , hon ɗaya yayi aka buɗe masa makeken gate ɗin gidan mai kama da ƙofar masarautar turawa, sai da ya huce gate ukku kafin ya isa conpaut ɗin gidan bai ajiye motar inda aka tanazar ba kuma bawai don babu sipes ɗin da zaiyi hakaba, a'a ra'ayinsane kawai a haka ya ajiyeta bakin barandar da zata sadashi da cikin babban falon gidan tun kafin yayi paking rundunar ma'aikatan dake tsaron gidan sukayo kansa hankullansu duk atashe. 
Yana buɗe marfin motar da nufin fitowa yaji saukar murya a kunnansa inda ɗaya daga cikin ma'aikatan yace “ Ƴallaɓai me ya faru kana lafiya suwaye suka kawo maka hari ki acsidant kayi, ” sai a sannan ya kalli galashin motar na gaba dake a tarwatse kafin tayi magaba wani soja yace 
“ Ƴallaɓai abinda muke nuna maka kenan kana da maƙiya amma kaƙi ka fahimcemu yanzu meye zamuce da Alhaji ko kasan zamu iya rasa aikinmu akan wannan abinda ka aikata ”. 
Kamar badashi sukeba don bai kallesuba bai kuma da niyyar yin hakan, baiyi magana ba kuma babu alamun zai tanka saima tsaki da ya ja ya futo ya fara taka enter lock ɗin dake malale a ko ina na gidan mai kyau da tsada wanda akaima fenti kala kala din ado kawai, sai da ya fara taka stap ɗin farko cikin guda ukkun da zai taka kafin hawa kan barandar, ya juyo ya kallesu suma shi suke kallo sai ya buɗe baki yayi magana cikin izza yace 
“Ni ba raggo bane zan iya kula da kaina, kuma kar wanda yayi gigin sanar da Dad abinda ya faru na magance matsalar kuma zanji da komai. ”
Haka kawai ya faɗa ya mai da kansa akan barandar ya ida hawa inda DoorBell ɗin kofar rake ya nufa ya danna a madadin tai ƙara ko tsuwa sai ta fito da wani ɗan ƙaramin gilashi, faskarsa ya kai cikin gilashin, take taimasa photo tare da yi masa sicaynin, cikin abinda baifi sakon biyu ba ta buɗe da kanta zuwa gida biyu, ya saka ƙafarsa falaon sanyin Ac da wani irin ni'imtaccen ƙamshi ya daki faukarsa ƙamshi mai daɗi da sanyaya rai da zuciya, ƙamshin da bazaka iya gane wane irin turaruka aka haɗa ba, tako biyu yayi cikin falon ya isa inda wata ƴar loka ta aza takalma take, sunkuyawa yayi da nufin cire takalman ƙafarsa sai ga wani gaye yazo wajan da sauri ya duƙa ya kwance masa takalmansa ta saka masa waɗansu masu laushi wanda ake yawo dasu cikin falon domin a dokar gidan ba a yawo da takalmin da aka fita waje da su cikin gidan sai dai a tsaya a sauya wasu masassa datti. 

Falone tanƙameme mai kyau da tsari da ɗaukar ido komai na falon golding ne da baƙi hatta da fentin bangon wanda ya kasance mai zane wati p. o. p , sat na royal chairs ukku ne a falaon banda kujerun daning table, wata tanƙamemiyar plazema ce take maka maraba da ka shigo gefe da gefenta kuma an saka manyan pictures na Tahteef masu kyau da ɗaukar ido daga gefen gabas nan daning table yake da ƙofar shiga kicin ɗin gidan ga kuma wata ƙatuwar prizar mai ƙofa biyu, tundaga labulayen falon zuwa yadin kujerun golding ne masu ɗauke da baƙaƙen filawowi, an ƙawata falon da wani irin kwayakwai masu sauya kala zuwa ja da yellow da blue. Inda wani coredoor yake ya nufa ya buɗe ƙofar ƙarshe, nan ma wani falon ne amma shi kuma komai nasa ja da fari ne har yafi na farkon ɗaukar ido nuna kyalli, na farkon yafi kaya barkatai saɓanin wannan da komai yake a tsare babu wata hayaniya, ƙofa biyu ce daga cen ɓangaren yamma na ɗakin, ta farkon Tahteef ya tura da nufin shiga, sai dai da sauri ya rufe don ba ita zai shigaba gajiyace kawai tasa yaga ƙofar tana sauya masa, kayan geemun ne a cikin kala -kala masu kyau da tsada domin kuwa babu wani nau'i na kayan tada jini da babu a ciki kuma masu kyau da tsada, anan yake trening ɗinsa a kowacce safiya batare da taje inda ake hayaba don shi baijin zai iya amfani da abinda wani yayi amfani da ji yafi son komai ace nasane. 

Ƙafar dake gaba ya buɗe inda wani irin hamshakin bedroom ya bayyana, shima dai kamar falon domin komai na cikin sa ja da fari ne, wani irin royal bed ne a tsakiyar ɗakin wanda a zagaye yake kamar (o) wato sircle an masa runfa doguwa domin kuwa sai da ta dangane da p. O. P ɗin dake saman ɗakin an zagaye runfar da fararen labulaye marassa nauyi dogaye, inda gefen gabas na ɗakin ya kasance kamar wani shago domin wajene aka zafaye kamar ƙaramin ɗaki aka saka masa ƙofar gilas inda ya kasance mai kyan kalla da ɗaukar ido, idon ka zuge glass ɗin ka shiga dafa hannun ka na dama kantace da akai da katako mai zanen filawoyi gida shidda akaima kantar, gida na farko zallar shaddace kala kala masu kayau da tsada, gida na biyu kuma yadine mai zane shima kala-kala ne don zai kai kala hamsin, gida na ukku shima yadinne amma kuma shi mai zanene shima zaikai kala hamsin, sai gida na huɗu nan kuma zallar boyil ne masu taushi da kyau, gida na biyar kuma ƙananan kaya ne masassa nauyi kala kala, gida na shidda shima ƙananan kaya ne amma kuna su suite ne, da rimot ake amfani wajan sarrafa lokokin dama ƙofar glass ɗin shigar baki ɗaya, gefen hannun haggu kuma sauran mahaɗin kayanne gidan huluna ne na farko wanda zasukai kala hamsin suma banda fecincap da sauran hulunan yayi irinsu samarin madina taɓani kaji hadisi da sauransu, gida na biyu takalmane kala kala kama daga plat zuwa kwaba da kanbus da silifas kowane jere da ɗan uwansa, sai inda agoguna suke wanda zasukai kala Talatin kuma duk na Diamond ne da zinari sai na farin ƙarfe masu kyau da sheƙi da tsada domin kuwa wasuma duk daga Dubai akayo odarsu, ga zobina nan barjet kala -kala na Azurfa da Zinare da Tagullah, gida na huɗu ƙanan wandunane da tishart kala kala, sai gida na biyar turarukane masu tarin yawa wanda har iya tsawon rayuwarsa ba zai iya ƙarar da suba, daga cen gefen dake kallon ka kuma wani ƙarfene dogo na silba mai kyau an cikashi daga farko har ƙarse da jallabiya masu kyau na kanti da na saudiyya, komai na wajan a tsare yake kamar wani ƙaramin Boatiqe ko in ce wajen sayar da sutura.