HANGEN DALA

Chapter 18

by @abdulhakimumar122



  Page 18 



KATSINA STATE 
Shagari Low-cous 
Ahanah zaune asaman ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye da falon su tana bama yaronta Ayaba da lemu, sai da yaci ya ishesa kafin yace 
“ mama na ƙoshi ”. 
Ajiye tiran kayan marmarin tai asaman teburin dake gaban kujerar ta ɗau wayar ta tafara cheeting da Aminanta suka fara tattaunawa akan fatin da zasuyi da anjima a babban hall na hill side royal suite da suka kama don gudanar da Dinnar ɗin bikin wanda jibi za'a ɗaura aure, wasu photos ne suka fara tururuwar shigowa cikin wayar masu yawan bala'i , cikin wani irin yanayi mai nuna tsantsar tashin hankali da firgici ta miƙe tsaye daga zaunen da take tana zaro ido kallon poton take wanda ya mamaye fuskar wayar tana zare idanuwa, wani irin bugu zuciyarta ke mata bugu irin na kishi bugu irin na tsoron halin Samir, Afili kuma a bayyane ta furta “ Ni za a tozarta ni Samir zai yima haka ni za a cima amana, wallahi basu isaba sai na hukuntasu ”.. 
Takai ƙarshen maganar tana mai jan wani irin nishi kamar zata shiɗe tsabar bakin ciki sai ta nufi hanyar ɗakin ta ta ɗauko gylen ta ta fice kai tsaye hanyar lea aut ta nufa inda gidan hutawarsa yake wayo ( guis Hause) bugu ɗaya aka buɗe gate ɗin ta shiga saboda mai gadin ya santa, bataji bata gani tsabar baƙin kishi ne kawai ya rufe mata ido. 
Babu kowa a falon sai tanƙamemiyar Tv ɗin daketa aiki ita kaɗai sai kuma sanyin Ac wanda ya garwaye ɗakin mai daɗi ji ga wanda ya tsawo rana ko yaci wuya, sai da ta gama ƙarema ko ina na falon kallo duk da cewa ba yau ta fara shigowa ba sai taga yau ya fita da ban saboda komai a tsare yake babu abinda aka taɓa komai yana mazaunin sa tsaf tsaf gwanin birgewa, batai sallama ba kuma batajin zata iya yin wata sallama saboda yadda zuciyarta ke mata zafi, kai tsaye ta nufi bedroom ɗin cike da masifa. 
Cak ta tsaya tana murza idanu don tabbatar da mummunan ganin da tai zahirine ko gizau shin da gaske Samir take gani a wannan yanayi. 
Tsaye yake daga shi sai ɗan kanfai rungume da wata karuwa wacce taci bilicing ta bugu duk fuskar nan tasha kwailin ɗaure da tawul zasu shiga Toilet. 
Duk wata irin masifa da bala'in da Ahanah ta zo dasu sai ta ne mesu ta rasa wani irin malolon baƙin ciki ya tokare mata ƙahon zuciya sai kawai taji hawaye na zubo mata ta buga ƙofar da ƙarfi tayo baya da nufin fita, sai dai da wata irin azama Samir ya sha gabanta yana cewa
“ ke Ahanah wane irin haukane zai kawoki har cikin falona batare da neman izininaba ke jahilar inace da zaki faɗo gidan mutane batare da kin nemi izinin shiga ba bakisan halin da zaki taddamuba, ko da yake wannan ya huce tunda kinga komai sai dai ina son na tabbatar maki wannan hali na ne kuma ba zan daina saboda keba, kuma zan ja maki kunne abinda kika gani ya tsaya a nan kar naji karna gani , idon har kikai kuskuren sanar da wani sai kin raina kanki maza fice da ganan. "
Mamaki al'ajabi ruɗani sune suka taso Ahanah gaba tama rasa abin cewa ganin abin take kamar a mafarki ganin abin take kamar tunani bawai zahiri ba amma ina zahirin ne saboda yadda take ganin komai baiyi kama da mafarkinba. 
Don haka sai ta daure ta juyo ta kalli Samir ta na magana cikin ɗaga murya “ Da kyau ɗan marassa kunya, dole kake jifata da wannan kalamai tunda kai baka iya borin kunyaba naga halin ka yau nasan kai kowaye, sai dai ina sanar da kai cewa kasa aranka duk abinda ya faru yanzu kamar duniya ta gamaji ne, don barazanar ka bazatai tasiri agareniba, kaji kunya kuma kayi asarar rayuwar duniya da lahira la'ananne mai bibiyan matan mutane ɗan iska ɗabba jahili marar ilimi da izinin ubangiji sai ka shiga wutar ja hannama nai dana sani sanika da nai a rayuwa ta , kuma aurena da kai babu shi don ba zantaɓa auren kaba, don da sannu zan ɗau fansar abinda kai man don ni ba jahila bace nasan abinda nake, don haka bazan iya auren fasiƙi mazinaci mayaudariba ni da kai sai gani sai hange indai nice nan gani nan bari dumamen mayya kuma sai na sanar da duniya ko kai waye middin ina raye. 
“ Da kyau ƴar masassa iya magana naji komai kuma na ɗauka sai dai acikin zancenki akwai mai kama da tanbaya don haka buɗe kunnanki kiji amsa, wannan ɗan abinda kika gani ai bazai isheki hujjaba don abinda na ke aikatawa a yanzu mutane da dama suna aikatashi don haka ba abin mamaki bane don kin faɗama duniya kin kamani da maceba, ki tsaya ki fara nazari da bincike a kaina don baki san komai akai na ba har yanzu , don sai na shayar da ke tafassasshen ruwan mamaki a rayuwarki don ni lunbulubune wurar ƙaiƙai Duk wanda yaci tuwo dani miya yasha, zancen bazaki aureni ba kuma duk bai tasoba don aurena dake kamar anyine don babu mahani ina mai tabbatar maki dole ki aureni kuma kiyiman biyayya ta nan zaki san ko ni waye sai ki shedama duniya cewa ga halin mijin da kike aure ”. 

Wani irin murmushi takaici Ahanah tai kafin ta fara tafa hannayennta tana dariya tana faɗin “ashe Samir baka da hankali haba ai sai yanzu na ɗau haske na gane da wa nake magana, idon ma shaye shayenka kaje kayi ya gusar maka da hankali to inya sakeka zata sanar da kai komai ”, sai ta mai da kallon ta zuwa inda wannan karuwar take tsaye tace “ki sanar masa dacewa Ahanah ta gane gaskiya kuma ta tuba ga Allah, kuma tace ko ana ha maza ha mata bazata auri samir ba don ta tsanesa inko yace zai ta kurata to kotuce zata rabasu. "

“ Dama nasan abinda kike taƙama dashi kenan kice zaki haɗanni da hukuma kuma kin faɗi ƙasa warwas don kotu da ma duk wata hukuma yanzu sun daina gane duk wani yare sai na kuɗi da alfarma da iko don haka zaki kwana aciki, ina mai maki magana da babbar murya idon har maganar nan ta fita to sauran abinda yayi saura a rayuwar mahaifiyar ki zata ida sane a gidan yari kuma ɓangaren laifin da babu beling maza ki bar gidan nan tun kafin nai maganinki jahilar banza kawai . ”
Take wani tunani ya faɗo mata a rai tabbas Samir da gaske yake yanzu andaina fahimtar duk wani yare sai na kuɗi da Alfarma ga wanda ya isa, to dami zata ja da shi da gaske yake sai ya aureta inko hakane tabbas zata faɗama halakar da zata saka ciwon zuciya yayi ajalinta zata san abinyi amma tabbas bazata auri samir ba, hanyar fita ta nufa ta bar gidan batare da tasake cewa komaiba, don ita babu abinda zuwan ta ya haifar mata sai kayan nadama da takaici. 

GENERAL HOSBITAL 

Abbas yana kwance akan gadon Asibitin har yanzu bacci yake, sai dai ƙarfe tara nayi ya farka da wani irin matsanancin ciwon kai da na ƙirji, yace “ hajiya ina Ahanah ta dawo ko har yanzu bata zoba,? ”
“ kayi haƙuri Abbas kamanta da Ahanah don bata sonka kuɗi da Abin duniya yasa bata ganin komai sai dukiya, ƙyale ƙyalen duniya ya rufe mata ido, ka daina tunanin ta Allah zai baka wacce ta fita kaji kayi haƙuri ka daina kuka..... ”
Sallamar da akai abakin kofa aka shigo shine abinda ya dakatar da maganar Hajiya Larai, ta mai da kallon ta kan masu shigowar tana masu maraba ganin manyan mutane ne ko ba a faɗaba tasan masu arziƙi ne daga ganin yanayinsu da shigar dake jikinsu ta Alfarma mutane biyu ne sanye da shadda mai walkiya da walainiya kamar anyi ɓarin mai akanta kalar blue da hula mai tsada ɗinkin tangaram irin wankin nan mai kamar gilas, suna murmushi, fuskar su duk a sake sai likitan da ya fara shigowa da ga farko sanye cikin kayan aiki irin nasu na likitoci sai da suka duƙa har ƙasa suka gaida Hajiya Larai kafin suka tashi sukaima kansu mazauni a kujerun robar dake gefen gadon guda biyu, Alhajin da yafi zati da kwarjini ya fara magana cikin muryarsa mai sanyi yace “ Hajiya mune mukai waya ɗazu na sanar maki zamu zo ganin Abbas ni dai sunana Alhaji Aliyu kuma nine mamallakin gidan man da Abbas yake aiki wannan kuma sunan sa Yahuza shine manager na gidan man, ” yakai ƙarshen maganar yana nuna na kusa da shi kafin ya ɗaura da cewa “ ina da gidajen mai ukku a KATSINA biyu a Kano ɗaya a KADUNA da Sokoto , wallahi kwata kwata bansan yaron nan baya da lafiya ba sai shekaranjiya wacce kuma dalilin samuwar wani Alkhairi ne yasa na sani, akwai wani Aminina da mukai karatu tare da shi a London yanzu haka yana can ABUJA yana Aiki shine Shugaban ( Refineries) a yanzu wato matatar man fetur ta ƙasa baki ɗaya dake birnin tarayya, munyi magana a baya idon an sami opper ta aiki zai bani na bama ƙannena guda biyu to yau tsawon shekara ukku kenan ba a samuba sai cikin satin nan aka samu kuma damar ta mutum ukku ce aka samu, sai dai Allah mai iko ya ɗauki ɗaya daga cikin ƙannan nawa yau tsawon wata biyu kenan ɗayan kuma ya samu aiki a London yanacen yace yafi son aikinsa akan wannan shine nai tunani na yanke shawarar zaɓar zaƙaƙurai acikin ma'aikatana na taimaki rayuwar su na basu aikin, wanda kuma na zaɓa sune masu ilimi da tsoron Allah da riƙon gaskiya da Amana wanda sukai caliafy masu copability akan aiki masu takaddun digree a hannu wanda na yadda da su na sheda riƙon gaskiya da amanarsu, sune zan tura nan da sati biyu masu zuwa A ABUJA don a tantancesu, akwai manager na na katsina wato Yahuza sai Abbas sai wani yaro a KADUNA STATE, ko da nazo da maganar sai aka shedaman cewa Ai Abbas ya jima bai zo aiki ba kuma basu san dalili ba, ina yin bincike sai na samu labarin baya da lafiya shine na yanke yau zanzo na dubasa, idon har Allah ya tashi kafaɗun Abbas ina mai masa albushir da cewa ya samu aiki a ( Refineries), kuma zan ɗauki duk wani nauyi nasa na aikin da za'ayi masa har ya warke da izinin ubangiji.”
“ Kai Alhamdulillah amma naji daɗin wannan albushir Alhaji Allah ubangiji ya tsare gabanka da bayanka, Allah yasa addu'ar iyaye taimaka tasiri Allah yasa Aljanna makoma Alhaji mun gode mun gode har bansan da bakin da zan gode makaba”. Sai kuka yaci ƙarfinta ta fara hawaye da murmushi a laciki guda tabbas ko a. Iya nan aka tsaya to Allah ya nunama Ahanah iyakarta rabuwarta da Abbas bata kaishi ƙiyamaba sai dai takai shi ga hawan maki na Aljannar duniya. 
“ A'a hajiya ba kuka zakiba don wannan ai abin farin ciki ne ya samu kuma bani zaki gode mawaba Allah zakima godiya don shie ya tsara komai kuma ya hukunta akan cewa Abbas zai sami aiki a babban waje irin wannan ”. 
Hajiya Larai daga inda take ta ɗaga hannuwanta biyu sama ta cikin abayarta tana faɗi “ Allah na godema Allah ka ƙarama Annabinka daraja da girma, Allahuma salli wa'sallim ala sayyadina muhammadun sayyidil mursalin, Allahuma salli wa'sallim ala sayyadina muhammadun sayyadil mujaheedin, Allahuma salli wa'sallim ala sayyadina muhammadun sayyadil Abidin, Allahuma salli wa'sallim ala sayyadina muhammadun sayyadil tabi'in, Allah kasa aikin nan ya zama sanadiyyar shigar cikin bayin Allah na gari Allah ya tabbatar mana da duk wani Alkhairin dake cikinsa Allah ya karemu da duk wani sharri da abinƙin da ke cikinsa, ” sai hajiya Larai ta kai ƙarshen addu'ar ta karanta salitul fatihi ta shafa a fuskarta, irin farin cikin da ya fara bayyana a cikin zuciyar hajiya shine ya yaye rabi da kwatar da muwar dake ƙunshe a zuciyar Abbas cikin ikon Allah da yawan addu'a da gatan uwa na nemamasa sauki cikin sati guda ya warke duk wata damuwa ta nisanta da shi, yayi fresh kamar baiyi wani ciwo ba sai dai ya rame kuma yayi haske na zama waje ɗaya da yayi da kuma ƙarancin jinin dake jikinsa, a wannan sati aka sallamesu ba tare da yi masa wani aikiba aka bashi izinin komawa gida, babu abinda yake a yanzu sai ibada da gayama Allah damuwarsa da bayyana masa halin da yake ciki na rabuwa da matarsa, yana fatan mantawa da ita da duk wani abu da yasamesa, yana kuma neman alkhairin da ke cikin aikin da zai fara nan kusa. 
Allah gafurun rahimun cikin ɗan lokaci ƙalilan Abbas ya sauya daga ɗan matsa mai a gidan mai zuwa mai aikin tace mai a Refinerie yayi ƙiba yayi haske kyansa da haibarsa ya sake futowa ya zama cikakken matashi mai zati da kwarjini kuma ɗan gayu mai addini da son ibada. 
Cikin sati na gaba akai masu duk wani gwaji da ya kamata aka turasu ABUJA, sai da Alhaji Aliyu yasa aka gyara ma hajiya turai gidanta da kuɗin aikin da ya fidda kuma ba'ayiba ya ajiye mata duk wani abin buƙata na ci da sha har ma da suturu na Alfarma kafin ya barta da ƙanwarsa da yaronsa da aka maido gidan wai Ahanah tayi aure kuma mijin bai aminta taje da ɗan wani gidansa ba Abbas yaji zafin kalmar Ahanah tai aure sai dai tafiyarsu ta mantar da shi ya shiga sabuwar rayuwa sabon wajen zama dake acikin sabuwar duniya mai tarin daula da ababen more rayuwa, ranar laraba 16 ga watan 7 shekarar dubu biyu da ishirin da biyar Abbas yabar KATSINA STATE zuwa birnin tarayya ABUJA acikin jirgin FADILANCY Air Line. 

ABUJA 
Alhaji sulaiman gidan iko ya kalli Alhaji iro mai kaita yace “ zan fara faɗin matsalata don neman shawarku akan yarona Tahteef don wallahi kullum abinsa gaba yake ci kuma rayuwar nan tamu ta yau babu tabbas idon na rasu a wannan gaɓa ya zaiyi, bana son yayi gidan yari ina son ya shiryu ya dai na ababen da yake marassa kyau domin suna ciman tuwo a kwarya taya za ace ka haifi ɗa amma bayajin maganarka baya gannin kowa da daraja abinda yake so shi yake baya aikata wani abu na khairi, idon nan duniya mun tsaya masa a lahira fa waye zai tsaya masa sai imani da aiki na gari, amma babu ɗaya wanda yake da shi bai da wajen zuwa da ya huce club gidan mata da faɗa da ma'aikata shine sari wancen shine kashe wance, ace yaro ya zama gagararre bai shakkar kowa bai tsoron kowa sai abinda yake so taya rayuwa zata yuyu a haka abin yana bani tsoro zafin Tahteef yayi yawa zuciyar sa ta yi yawa ina son naga ya canja don duk yadda yake tunanin yana da kuɗi kuma nima inada su akwai rigimar da zai ɗakko wacce kuɗi bazai iya maganceta ba ina ƙaunar sa da son sa wanda ya huce musali ba zan iya jurar ganin wani abu ya sameshiba, Duk da cewa Tahteef jarimine mai ƙarfin iko da na zuciya da na damtse amma bai da ƙarfin addu'a, Tahteef bai damu da sallah ba bai aikata wani aiki guda na ibada da zai sashi cikin inuwar ubangiji. ”
“ Lallai Gidan Iko matsalar ɗanka mai yawace sai dai maganinta mai sauƙine don aurar da shi kawai zakayi ni'imar aure itace kawai zata saitashi idon har ya kasance matar tasa ta garice mai addini da tsoron Allah kuma wacce akai sa'a yana yima mahaukacin so to itace zata sauyashi don haka sai ka tintiɓesa idon da wadda yakeso kuma ya calipcanion ɗinta yake sai kawai kayi abinda ya dace. ”
Alhaji Nuhu Dutsi yayi karaf da faɗin “ this is a simple idea, matsalar gidan ka ta ƙare kawai sai kuma abu na biyu kacigaba da yimasa addu'a kuma kasa mamansa ta dinga yi masa ka kuma saka malamai da limamai sitaimasa har a dace, ni matsalata akan wasu kuɗine da nake son yin ƙasa da su amma kuma duk ƴan majalissar suƙi mara mani baya. ”
Nan sukai ta tattaunawa akan matsalolinsu suna sama ma kansu mafita da masalaha har suka kammala kowa ya koma bakin aikinsa. 

Tahteef 
Ƙarfe bakwai na safe ya baro gidan su cikin shirin zuwa wajan Abar ƙaunarsa Muheebbaht ko da ya isa bakin gate ɗin gidan bai shiga da motarsa ba sai sai ya fakata a wajan ya sauke glass yana kallon ƙanan yaran dake wasa a tsakiyar gidan, matan suna tafa hannaye suna tsalle sai su ware ƙafarsu daga ƙarshe ko su matse, sunan wasan da suke tan-tan wasu kuma suna ƴar galagala, yayinda mazan suke wasan kokowa da masu wasan dokuna na itace kamar a ƙauye. 
Haka kawai murmushi ya subuce masa tuno mafarkin da yayi da Muheebbaht , sanye yake cikin ƙana nan kaya wato suite kalar ruwan ƙasa masu duhu da sheƙi kan sa babu hula sai kyakkyawar baƙar sumarsa da ta sha gyara tai baki siɗik gwanin birgewa hannunsa sanye yake da wata irin agogo ta zinare mai kalar kayan, kallon ta kawai zakai ta shedama da kuɗinta saboda yadda take walkiya kamar glass ɗin da rana ta haska, kamar ance ya kalli gabas sai ya hangota tana tafowa da alama unguwa taje don hannun ta riƙe yake da leda kallon yake yana Mamaki don gani yake kamar ba itaba saboda uwar kwalliyar da ta tsara a fuskarta bai taɓa ganinta cikin kwalliya ba sai yau don haka sai yaga ta canza masa saboda uban kyawon da tayi mai kama da na sarauniyar kyau ta larabawa, ya shagala da kallon ɗan ƙaramin bakinta mai ɗauke da jajayen lips, idonta kamar madara don farin cikin su mai tsananin haskene haka ma baƙin mai tsananin duhune ga ɗan siririn hancinta mai kamar an saita da fuskar, wani irin abu ne yaji yana masa tafiyar tsutsa a cikin zuciya wanda bai san yadda zai musultashiba wani irin sontane yake ƙaruwa a kowane second da minti na kowacce daƙiƙa dake bugawa da bugun zuciyar sa, ji kake tas! tas!! wani ya ɗauke Muheebbah da kyawawan maruka guda biyu masu kama da saukar a radu domin kuwa bata san da tafowarsaba babu zato bare tsammani hakan yasa marin ya shige ta sosai don har sai da tai taga taga zata faɗi ta tillar da ledar hannun ta wacce kayan sweet ne da mulkos na yara aciki ta watse saman hanyar, 
Tahteef da wani irin azama ya dafe kuncinsa tamkar shi aka mara ba itaba take idonsa ya kaɗa yayi ja sosai kamar an watsa masa barkono a ciki ya buɗe marfin motar da wani irin sauri ya fito yayo kansu a guje kamar wata Damisar dake farautar rai, dai dai sadda wancen gayen ya nuna Muheebbaht da yatsa yana cewa “ idon har na sake ganin fuskarki a hanyar nan sai na kasheki wawuya matar ɗan daba......... 
Ji kake dam! Tahteef ya saukema gayen naushi a kumatu, bai yi tsammanin jin dukaba hakan yasa yaji bugun kamar a mafarki don har cikin ƙoƙon kansa yaji dukan inda ya watso miyau ƙasa amma sai yaga ja da fari na yawo a saman ƙasar wanda ya tabbata jan jinin bakinsane farin kuma haƙwaransane guda biyu suka cire kafin ya ɗago ya ga wanda yake da irin wannan ƙarfin na duka yaji an kama hannun sa da wani irin ƙarfi kafin Tahteef ya aza hannun akan gwiwar ƙafarsa ya danna da dukkan ƙarfinsa har sai da hannun ya kare, Tahteef na sakinsa ya zura a guje yana ihu tallabe da hannun sa dake a karye sai dai bai yi nasarar guduwaba Afif da wani daga cikin manyan yaran Tahteef da suka biyosa ba da saninsaba suka kama gayen tare da sakashi a mota don tuhumarsa. 

Tahteef na ganin isowarsu Sai ya rungume Muheebbah da dukkan ƙarfinsa yanajin sonta da ƙaunar ta har cikin zuciyarsa kafin ya fara kallon ta a firgici yana faɗin “babu abinda ya sameki ko zomuje Asibiti a duba manke , ”. Yakai ƙarshen maganar yana ƙoƙarin jan hannunta zuwa wajen motarsa, 
Yana faɗin “ waye shi meya haɗaku faɗa ina kika sanshi? ”
Fizge hannun ta tai kafin tace “ bana so kana taɓani don akanka komai yake faruwa ina son rayuwa ta don haka ina mai neman alfarma ka kafita daga harkata waima kai ɗin waye me yasa kake ta bibiyata daga taimako me yasa ake kirana da budurwar ɗan daba kai ɗin waye ina son sani? ”. 
Sai ta nufi hanyar cikin gidan tana kuka, da sauri ya sha gabanta yana faɗin “ haba Muheebbah karkiman haka mana bana son wani abu yasameki ko lafiyarki don inamaki wani irin mugun son da bansan iyakarsaba don haka kibi umarnina bana son gardama muje Asibitin, ” yakai ƙarshen maganar yana kamo hannun ta suka shiga cikin motar sai Asibiti, kamar ta fito tai masa masifa sai kuma ta share, ko da suka isa babu abinda yake damunta amma a dole yasa likitan ya rubutamata maganin rage zafi yako sawosa da yawa kamar za buɗe sabon clinic, A hanyarsu ta dawowa ya tsaya A TA'AYE Rastaurente sai da ya faka motar sa a paking speacs ya buɗe ya fito kafin ya zagayo ya buɗe mata ta fito itama suka shiga cikin wajan a tare , a zahiri ta saki jiki da shi amma acin zuciyarta wata irin tsanace da ƙiyayyarsa suke hurowa acikin ko wane irin lumfashinta sai da suka zauna a wani Teble na musamman kafin yayi umarnin da akawo masa abinda yayima sheda da biro cikin littafin da Aka ajiye gabansa, cikin ɗan lokaci ƙalilan aka kawo masu abinda suka buƙata suka soma ci, yanayin wajan yana birge Muheebbah hakan yasa ta saki jikinta kamar babu abinda ke a ranta. 
Ko da suka gama sai ya ɗauketa zuwa wani sabon waje da aka buɗe na gyaran jiki da salon aka wanke mata kanta aka gyara mata jikinta tsaf gwanin birgewa, ba masu salon ɗin ba hatta ita da akaimawa sai da tai mamakin irin kyawon da tai don bata taɓa zato ko hasashen tana da kyau haka ba, sai kallon kanta take tana murmushi cike da jin daɗi atare suka fito hannun ta riƙe da na mai salon ɗin har inda Tahteef yake zaune saman gaban motar sa yana charting da wayar sa,, suna haɗa ido ta sakar masa murmushi wanda yasake ƙawata kyan fuskarta. 

“ Yallabai gatanan na gama aikina sai a bani tukwici ” cewar mai salon ɗin cikin yaren turanci tana murmushi da alama da zolaya tai maganar 
Shima cikin turancin yace “ wow gskiya kin iya kwalliya da gyaran jiki dole kau na baki tukwici ” yakai ƙarshen maganar yana ƙoƙarin dirowa daga saman motar ya biyasu kuɗinsu yadda suka buƙata kafin yayi mata tukwicin naira dubu 100,000 anan take kash ba lambaba, buɗe gidan gaba yayi na motar yana mata nuni da tashiga yana binta da wani irin kallo mai cike da shauƙi da nuna tsantsar so da ƙaunar da yake mata, sai da tashiga ya rufe ya zagayo gudan gefen ya buɗe ya zauna yayima motar key kansa akan Muheebbaht saɓanin titin da ya kamata ace yana kallo. 
“ Yallabai pleass ka kalli hanya karkasa muyi hatsari, ”
Mulmushi yayi yana faɗin “ kai amma nayi sa'ar samun kyakkyawar mace mai kyau da natsuwa, Allah nagode maka daka bani wannan kyakkyawar a matsayin matar aure na, Muheebbaht kina da kyau i love you we the all my heart, ke nawal ce ma'ana kyauta daga rabbi kuma ke fadila ce ma'ana mai falala ke mufida ce mai amfani acikin rayuwa ta ke Nuriyya ce mai haskaka zuciyata ke Amirace wato ginbiya ginbiyar dake mulkar zuciya ina sonki Muheebbaht ” ya faɗi zancenne cikin shauƙi da nishaɗi har cikin zuciyarsa yana wani kafeta da ido 
Mulmushi tai kafin tace “ wallahi ka iya tsara kalami kamar wani gwanin iya soyayya ”