Chapter 20
Page 20
To me zai hana nabaki tunda kun saba ai shine irin abincin da naga yaran gidanku suna faɗa akansa da alama dai yana da daɗi don haka a bi sannu kar a cije leɓe kinsan tasshin gidan masu kuɗi ba ɗaya yake da nakuba don ko gishiri babu sai magi ”.
Wani kallo taimata mai nuna baƙin ciki sai ta kuma kauda kai gefe
“ ki riƙe sosai dai kar ya zube don da kin zubar dashi to zan kira malam Garba maƙeri ya zo ya kwashe tunda shima mabuƙacine ”.
Ji kake kif Namsiyya ta kifama lateefah filat ɗin garin kwakin a fuska, ta ƙara mata da mari tana faɗin “ Ahir ɗinki wallahi ko mai zakice akaina kice don na aminta da cewa ni nasaya da kuɗina amma ba zan bari a ci mutuncin iyayenaba wallahi ”,
Ita ko Lateefah wata irin muguwar ƙara ta saka tana mai faɗawa kan kujera saboda yadda yajin dake cikin garin ya cika mata idanuwa taja lumfashi ta shiɗe kawai sai ta faɗi sumammiya
Ganin haka ya faranta ran namsiyy taci alwashin barin gidan a yau bayan ta saci duk abinda yayi mata, sai dai bata samu abin ɗauka mai darajaba sai wayar Lateefah wacce Iphene ce sai kuma ƙatuwar sarƙar huyanta wacce ta zinare ce ta fice da sauri ta bar cikin gidan a harabar gidan take ta shawagin ta inda zata fita amma bata samuba sai can ta hangi wata ƙofar bayan gidan a kulle tana isa taga daga ciki aka kulleta don haka hannun ta har ƙarma yake ta buɗe ta fice sai waige take tana bin lunguna har ta bar unguwar ta bullo malali zama tai a kan wani gini na filawoyin wani gida ganin layin babu kowa sai dai abinda bata sani ba ƴan iskan wajane sun shahara hakan yasa ba kowa yake bin hanyarba, sai da ta huta sosai kafin ta miƙe taci gaba da tafiya tana shan kwana wasu ƴan iska suka tareta suna faɗin “ kai amma mun gode maki da kika biyo ta nan mungode da taimakon mu da kikai kika kawomana kanki har nan, ” batare da bata lokaci ba suka zagayeta ƴan iska su goma shabiyar, sai ta fara ɗaure fuka tana faɗin “kukuma lafiya” cike da rashin fahimta
Ɗaya gada cikin su wanda yafi kowa matsayi yace “lafiyar ce tasa haka kuma aike bakiyi kama da mai lafiya ba don haka muna son sanin inda kika sato wayar hannun ki don mu maida masu don kallo ɗaya nai maki na sheda ke ɓarauniyace. ”
“ Ni wallahi ba ɓarauniya bace ”.
To ki tabbatar mana ya faɗi yana fizgo wayar dake hannun ta yace maza ki cire mana pasword ɗin, wannan wani sabon salo ne na ɓarayi Dama haka sukeyima duk wanda wahala da tsautsayi ya haɗasu, idon kacire masu sai su gudu subarka inko kaƙi sai suce kaima ɓarawone su bugeka su barka kwance kuma su tafi da wayar, hakance ta faru akan Namsiyya suka bugeta suka tafi da wayar harma da sarƙar da ta ciro ta huyan Lateefah suka gudu suka barta kwance ƙasa cikin jini.
Sholy na shawo kwana taga kamar mutum kwance a ƙasa sai da tai parking ta fito sai taga macece, cike da tsoro ta isa wajan ta duƙa zata kamota sai kuma tajanye hannunta da sauri tunowa da tai gara tafara sanar da mutane, sai kuma ta ga fuskar Namsiyya cikin kaɗuwa da firgici gami da mamaki ta kai hannun ta takamota don ta gani dagasken itace, itace tabbas don idanuwanta ba gizo suke mataba sai ta fara jijjigata tana faɗin “ Namsy! Namsy !!! Namsy ki tashi ” haka ta dinga girgizata tana kuka tana faɗin Namsy kitashi ganin bazata tashiba ta sakata a mota da taimakon wani mutum ɗaya da ya biyo hanyar ta nufi wani ɗan ƙaramin Asibitin kuɗi dake cikin unguwar Dosa sai dai har tayi nisa sai wani tunani ya faɗo mata koda ace ita ta banketa to bazasu ƙarɓetaba sai taje da police bare kuma ace nan ta sametaba dole ta nufi hanyar gidansu da ita kafin kuma ta fito da wayarta ta kira family Doctor nasu ta ce ya sameta gida yanzu yanzu don babu lafiya.
Ko da ta isa harma ya zo don haka wani ɗaki dabasu amfani dashi ta buɗe aka saka Namsiyya acikinsa aka duba ta dama tare yake da kayan aikinsa don haka har da ƙarin ruwa ya zo ya kuma saka mata Amma sai da aka ƙaro guda, sai wajan ƙarfe shabiyu na rana Namsiyya ta tashi fuskar ta na nuna matsananci tsoro da firgicin da take ciki ganin Sholy a gefenta hakan yai nasarar tattare kaso tis'in cikin ɗari na tarin damuwar da take gabanta cikin wani irin yanayi mai nuna halin mara lafiya tace “ Sholy ashe zan sake saki a idona na zaci na mutu ashe da sauran shan ruwana a duniya, Sholy na tsani Areeyan da shi da aurensa da nayi ina nadamar kasantuwa a cikin wannan inuwar auren da ke kama da zaman gidan kaso Sholy Areeyan ya tsaneni baya sona tun da na shiga cikin gidan can farin ciki ya ƙaura daga gareni ina so na huta na shaƙi iskar ƴanci na gane kuskurena don Allah ki kaini gida na nemi gafarar mama don zama da ita ya fiman daɗi da ni'ima fiye da ɗaukar da nake hange sai yanzu na sheda zancen ƴan magana da kance Hangen Dala ba shiga birni ba na sheda hakan harma na gasgata, don haka aurena da Areeyan ya kare ko shine autan maza bazan koma cikin uƙubarsa ba wallahi na barshi bari kuma na har abada. ” sai wasu hawaye masu zafi suka shiga zubo mata inda kuma da sauri Sholy ta saka diko tana sharemata tana faɗin
“ idon har ina kusa da ke bazaki zibar da hawaye ba ki natsu ki sanar dani komai ta yadda zan magance maki matsalar nan take idon mai magantuwa....
Murmushin takaici da ban haushi Namsiyya tayi kafin ta kwashe komai da ya faru ta sanar da Sholy har zuwa fitowarta daga gidan.
Mamaki da Al'ajabi sun hana Sholy magana sai take ganin abin da yake faruwa kamar a mafarki ko ace a shirin film amma kuma ba a shirin bane wannan da gaske yake faruwa don haka ta hau neman mafita da wuri don samin abinda zasu aikata.
Murmushi Sholy tai na samun mafita da sauri haka batare da tasha wuya ba, matsowa tai har inda Namsiyya take ta dafa ka faɗarta tace “ ba zaki bar Areeyan ba zaki koma garesa don nasama maki mafita wace idon muka bita to Areeyan ma bazaya barkiba zaku rayu tare har mutuwa kuma acikin so da ƙainar junanku har ya zama yana shakkar ɓacin ranki saboda matsayin ki a wajansa ”.
Da sauri Namsiyya tace maza gayaman ƴar uwa me nene mafitar
Raɗa tai mata a kunne, kawai sai suka bushe da dariya har da tafa hannu, daga haka kuma suka cigaba da tsara yadda abin zai kasance inda kuma Sholy ta ja hannun Namsiyya suka shiga cikin gidan anan suka ci abinci kafin kuma daga bisani suka shirya caf cikin shirin fita daga inda Sholy ce ta bama Namsiyya kayan da ta sauya daga cikin kayanta, suka fito atare har inda motar take a fake, wani irin yanayi mai daɗi da sanyi Namsiyya ta samu kanta aciki don rabon da taci abinci haka ta ƙoshi tun tana gidansu sai yau wanka ko kotayi a gidan ta babu kayan sauyawa don sun handame komai sunhnaata amfani da shi kamar tsintota akai ba wai aureba atare suka shiga motar Sholy ta ja suka bar gidan kai tsaye Rafin guza ta nufa inda gidan su Namsiyya yake, suna isa ta faka motar a bakin lungun gidan don bazata shiga da motar ta cikiba saboda jiya anyi ruwa kuma lungun a jagule yake kamar andama ƙazantar dake ciki saboda yadda ya jagwalgwale tana gama parking ta kalli Namsiyya tace “ kiji abinda zakiyi da hanzari ki fito mu tafi kinsan da zafi zafi akan daki ƙarfe bana son jira kiyi da jiki sai kin fito. ”
To kawai Namsiyyar ta iya faɗi da buɗe marfin motar da ke buɗe ta fita ta shiga lungunsu inda anan tai wasan ƙasa aranta ta furta lallai kowa ya ba gida, gida ta barshi domin kuwa ɗan sati ɗayan da tai ba anan ba sai takejin kamar tayi wasu uwayen shekaru bata zoba tana shiga gidan ta samu yaran duk basanan sai mamar kawai da ke zaune tana tuƙa tuwon da ya zame masu al'ada sai dai idon har ba ƙarya idon ta yake mataba taga sauyi don yau tuwon shinkafa taga ana masu kuma miyar taushe don tukunyar miyarma a buɗe take da alama anbarine ta ida tsotse ruwanta ga alayyahu nan sai yawo yake asan miyar.
Sai Namsiyya taji jikinta yayi sanyi don gani take kamar idon ta shigo mama zata koratane ta kulle gidan ta, ita kuma neman yafiya da gafara ta zo tasan harda fushin uwa ya sata a wannan hali duk da cewa ko bataga komai ba,
“ Assalama Alaikum ”
Ta faɗi acan ƙasan maƙoshinta
Sai dai ga mamakinta sai taga mama ta saki fuska tana fara'a tare da buɗe mata hannaye don tazo alamar maraba donko tuni ta saki tuƙin tuwon da take tazo ta kama hannun Namsiyya tana faɗin “ wagga ɗiya sannunki da zuwa mutanen turai ashe har kundawo shigo ki zauna mana ƴar kirki... ”
Sai kuma mama ta tsaya da maganarta tana kallon jikin Namsiyya da wani irin yanayi.
Duk wani abin da ake kira mamaki al'ajabi sune suka sauka a duniyar Namsiyya har sukai nasarar sanyaya jikinta taji kamar an ɗura mata ƙanƙara a jiki saboda yadda ta mutu a tsaye jin mama take da duk illahirin kunnuwanta amma zahiri tunaninta ya sauka a wata duniyar mai nisama kuwa shin da gaskene abinda kunnanta keji ba gizauba to murna zatai ko fashewa da kuka yanzu duk abinda tai ma mama ace har ta yafe mata kai da kwai wani abinda yake faruwa wanda bata sani ba ko tace akwai rina a kaba , a kwai kuma lauje a naɗi.
“ yawwa zauna nan ƴar nan ki huta kunsha hanya amma ya naga ciwo a goshinki me ya faru da ke ne haka? ” mama ta faɗi lokacin da ta zaunar da Namsiyya a saman ƙaramin gadon ta na sulba irin na da can da ake haɗama amare da shi idon anyi masu gadon ƙarfe mai tsawo, idanuwanta kuma kafe akan bandejin dake zagaye da kan Namsiyya.
Namsiyya na zama ta ja wani dogon lumfashi gami da sauke ajiyar zuciya, tace “ faɗu nayi a banɗaki kinsan tayils na masu kuɗi da santsi” .
mama fita tai tare da faɗin “ To Allah ya kyauta ya tsare gaba ” minti kaɗan ta cika gaban Namsiyya da kayan ciye ciye sai da tai dawowa ta ukku kafin ta zauna tana share zufa da gefen zanin ta da ke dukun dukun don tai wujiga wujiga da ita.
Kallon kayan dake tsakiyar ɗakin Namsiyya tai wani murmushi ya suɓuce mata nan duk don ita aka kawo duk da yadda cikinta yake a cike sai taji tana so da buƙatar taci girkin mamarta buɗe kwanikan ta hau yi wanda suka kasance langa tuwo da miya sai wata sulba mai ɗauke da kwaɗon zogala ya sha ƙuli da man gyada, tuwon ma yanzu ta kwasashi sai turiri yake irin na huci, ga kuma fura mai sanyi taji nono, ƙasa Namsiyya ta zauna ta fara cin komai cikin jin daɗi har sai da taji bazata iya ƙara cin komai ba saboda yadda cikinta ya haƙe mata sai da ta wanke hannun ta ta dawo tace
“ yo wai mama duk ina su Auwal naga gidan babu kowa, ina suka tafi ”.
Mulmushi mama tai irin nasu na manya don ta fahimci cewa Areeyan ɗin bai sanar da ita komai ba saboda da dattako don haka mama ta gyara zama tace “ ina so dama na ganki Namsiyya ina da abinda nakeson faɗa da dama akan mijinki amma idon ankiraki ba 'a samu kuma ko anje sai ace baki nan sai jiya zuciyarta ta sami sukuni da sakon mijinki ya iskeni. ”
Wani irin dam! Zuciyar Namsiyya ta buga sai kuma farin ciki ya mamayeta, Fatan ta ɗaya taji mama tace sakon takardar sakintace ta risketa ba wani abunba,
Cigaba mama tai da faɗin “ jiya wani mutum yaxo wanda bamu sani ba yace mijinki ne ya aikosa da kayan abinci niƙi niƙi, su shinkafa taliya garin tuwo makaroni da duk wani abu na kayan abinci irin namu na masu rufin asiri babu abinda babu aciki sai babun, kuma bayan nan yace duka yaran nan akai su makarantar Islamiyya shi zai ɗau nauyin kuɗin watansu duk watan duniya kuma yabama babanku naira dubu ɗari ukku yace ya ƙara jari.....
Mama na cewa dubu ɗari ukku Namsiyya ta ja wani dogon tsaki ta ɗaura da faɗin “ dubu ɗari ukku ɗin ne za a ja jari ni ina jiran naji kince million hamsin haba masu kuɗin nan basa da tausai ace kamar ni ina matar Areeyan Abdurrahman Na'adami ace wai anbama babana nera dubu ɗari ukku kamar dai yaje bara ko maula yadda suke da tarin kuɗi ko million ɗari ya bada ba zai damuba Kujira lokaci kawai na fara fantamawa don wallahi motocin da zaku hauma abin kallone ai Allah ya kashe ya baku tunda kun haifi ƴa mai ƙashin arziƙi mace isassa matar manya ”.
“ inna lillahi wa inna ilaihir raju'un , Subhanall, la haula wala ƙuwwata ..... ni mama yau naga takaina Namsiyya da bakin ki kike faɗar wannan kalamai marassa daɗin j, shiyasa nake nemanki don naji kin sauya ko ko, to na gane har yanzu kina nan da baƙin halinki marar kyau gashi kuma Allah ya baki miji nagari, .
Namsiyya.... ”
Ɗagowa Namsiyya tai ta kalli mama saboda yadda takira sunan muryarta a dake
“ wannan kalamai basu kamata aji su daga bakinki ba a matsayinki na ƴar talaka kuma Allah ya wanke miji kamar Areeyan ya baki sai ki gode masa ki karɓi komai a yadda yazomaki, domin kuwa duk duniya kowa da iyakar wahalar da zai sha kada ki cika baki ko kiyi fariya da bugun gaba da abinda ba nakiba bari na baki wani misali zakiga wajan da ake sai da litattafai na addini ga sunan a yashe duk sunyi ƙura sai mutum ya saya ya kai gidansa ya saka a loka a goge suta sheƙi da burgewa, sukuma masu sai da takalma suna basu gariya da kulane a lokacin da suke so su saida wani takalmin acikin glass yake kuma cikin kwabarsa da an saya ankai gida sai asa aƙafa duk inda za'a shiga za 'a ajiyesa abakin ƙofa, daga haka sai kiga ana tilli da shi a tsakar gida, don haka ki fahimceni ki gane abinda nake son faɗamiki don Areeyan ɗane kuma mijin aure ya zo har nan cikin gidan ya zauna mun tattauna da shi kuma na fuskacesa, wannan dalilin shi yasa na yafe maki, don haka kiji tsoron Allah ki zauna lafiya a gidan mijinki don aure ibada ne ba wajan neman kuɗi ba........
Kukan da Namsiyya ta fashe da shi shine ya kashe mama tai saurin kallon Namsiyya tana cewa “ lafiya me ya faru ”.
Cikin kukan Namsiyya ta kwashe komai da ya faru a gidan ta tunda tasa ƙafarta ciki har yau.
Mama taji babu daɗi amma a yadda taga Areeyan tasan ƴarta ta dace mijin aure sai dai idon dakwai wani kuskuren da yake son ya nuna mata ko kuma jarabata yake don haka ba zatabar ƴarta tai asarar wannan gidaba, sai da takai hannu akan kafaɗar Namsiyya kafin tace
“ kiyi haƙuri komai zai maki na lokaci ne idon har ya zalunceki ki yi sallah ki sanar da ubangiji zai saka maki don Allah ba azzalumin kowa bane, kuma abinda baki sani ba abinda kika aikata gareshi shine yake son ya ɗau fansa zan sannar da ke hanyoyin da zaki mallaki mijinki ku zauna lafiya kamar sauran ko wacce Amarya da ango.......
“Wai ance Namsiyya ta zo ” haka aka faɗa daga can bakin kofar
Mama ce ta leƙo tana kallon Almajirin tace “ waye yake sallama da Namsiyya kuma ”.
Almajirin ya buɗe baki da niyyar magana, Namsiyya tai saurin cewa “jekace gata nan,” sai ya juya ya fice batare da yace komai ba
Juyowa mama tai kan Namsiyya ta mai do hankalinta kanta tace “ Namsiyya ke da wa kuka zo ko har ya dawo ne Areeyan ɗin? ”.
“ A'a mama bai dawo ba Direba ne ya kawoni kuma yace da shi kar mu wuce Awa guda bamu komaba yanzu ko awarmu kusan biyu ya kamata na tafi ”.
“ gaskiya hakan na da kyau indon kin sami dama kin fito sai ki shigo inma hakan bai yuyuba zamu yi waya ki kula da kanki karkiyi abinda zakizo kiji kunya daga baya, ki zama mace ta gari wacce mijinta zaiyi Alfahri da ita ko bayan ranta, zance nan dai da nasaba gayamaki shine zan sake gayamaki a kowane irin lokaci kiyi abinda zai zamemaki abin alfahri wanda za a yaba maki kiyi haƙuri akan komai, inko nace komai to ina nufin komai zaman aure ba abune na wasaba sai an jajurce, kar ki manta da addu'a ki sanar da ubangijin ki komai shi zai maki magani karki haɗa Allah da wani wajan biyan buƙatar abinda ranki yake so, na gode kwarai da wannan ziyarar Allah yayi maki albarka ”.
“Amin mama ”
Haka suka zo har zaure mama na yima Namsiyya nasiha kafin ta fice ta nufi inda motar Sholy take, tana buɗe marfin motar da nufin shiga Sholy ta ja tsaki tsuttt! “wai mi kika tsaya yi ne duk kin wahalar dani da zaman jiran ki ”.
“ kiyi haƙuri Aminiyar mama ce ta tsayar dani tana taman nasiha shi yasa kinsan ba zan yadda na ɓoye mata komai ba na sanar mata amma ta bani haƙuri tace komai mai wuce wane wata rana sai labari ”.
“Ke dai kika sani ” cewar Sholy tana mai yima motar ki suka lula kan hanya, tafiya suke bata wasaba don kuwa Sholy ta dage takai malejin motar ƙarshe sai zuƙa uban gudu suke akan kwalta har hakan ya fara bama Namsiyya tsoro, tun suna bisa kwalta har suka koma tafiya kan burji da jar ƙasa tafiya sukai bata wasaba tafiya irin ta barin gari don garin ma suka bari zuwa local government ɗin batsari dai dai ƙofar wani gida na ƙasa Sholy ta faka motar a wannan lokacin ƙusan ƙarfe biyar na yamma, suna fitowa Namsiyya ta bi gidan da kallo gidane na ƙasa ɗan ƙarami mai ɗauke da ɗakuna biyu masu kallon kudu daga Arewa, na waje na iya ganin hakan saboda rashin tsayin katangar gidan tun daga ƙofar gidan zaka sheda gidan bokane saboda yadda aka yina bangon ado da fatar kura da gashin jimina, kana shiga soron gidan zaka fara karo da ƙulli ƙullin kaya na magungunan mata da kawunan kaji da agwagi, ko da suka isa tsakar gidan matane zauna asaman wani dogon banci na katako suna zaman bin layi, wasu na shiga wasu na fita haka ake tayi kuma wasu na shigowa kamar yanzu garin ya waye ba yamma ba.