HANGEN DALA

Chapter 21

by @abdulhakimumar122

Page 21


Sadda layin ya iso inda suke tuni Namsiyya ta ƙosa har ta fara mitar su tafi gida amma Sholy ta taita bata baki da sanar da ita irin nasar da zasu samu anan gaba, suna shiga ɗakin zuciyar Namsiyya tai wani irin bugawa saboda ba haka tai tsammanin ganin ɗakin ba ga wani wari da ke tashi wai a haka turarene, kayane shirgi guda da komatsai inda mutum biyu zasu zauna ne kawai sararin ɗakin sai inda mutumin yake zaune ƙatone babba irin mutanan nan masu tsayi da kwari yasha babbar rigarsa har da rawani , haƙoransa duk sunyi ja saboda tsabar cin goro tirene a gabansa na katako cike da ƙasa ta duba sai gefe da gefensa duk jikkunan magani da kwalabe na roba suna duk ciccike da magani na ruwa, suna zaunawa Sholy ta ranƙafo tana faɗin “ barka da yamma malam ya aiki ya gida? ”. 
“ me ke tafe da ku ”ya faɗi a takaice yana zare jajayen idanuwan sa masu kama da garwashin wuta. 
“ ƙawata na rako malam ga tanan a taimakamata domin kuwa rana cikin matsala ”. 
Sai da ya kafe Namsiyya da idanuwan sa marasa kyawon ganini tun daga ƙasa har saman kanta yace “ A za hannun ki nan ” yakai ƙarshen maganar yana nuna mata ƙasar dubar da ke gabansa, wani irin magani mai kalar ganye kore shar ya ɗibo acikin wata kwarya ya zuba mata akan hannun nata yana wasu sabbatu da basuyi kama da yaren hausa ba kuma basu yi kama da yaren turanciba ga sunan dai babu daɗin sauraro, sai da suka kwashe kusan mintina biyar a haka kafin wani ƙullin magani ya faɗo a saman rawanin bokan kamar an tulloshi ya ɗauka ya bama Namsiyya yana faɗin “ matsalar ki ta ƙare don ga maganinta nan ya zo kinga wannan ƙullin kwalli ne ki shafa a idonki, middin kika haɗa ido da Areeyan to shikenan sai yadda kika yi da shi matsalar ki ta ƙare sai aninda kikace shi za'ayi acikin gidan zai soki sosai kamar yadda kika tsara a zuciyar ki ” yakai ƙarshen maganar yana bata ƙullin maganin a hannunta. 
“ To mun gode minene tukwaicin ”
“ ba a godiya a nan kuma ba a bada tukwaici sai dai muna da sharaɗi guda duk abinda mukace munaso to dole zaki bayar, kuma ba yanzuba sai buƙatar ki ta biya idon kin dawo sai kizo da shiri. ”
Dam! Zuciyar Namsiyya tai wani irin bugu kamar tace bata aminceba amma kuma wani yanki na zuciyar ta yana bata umarnin ta amince saboda cikar borinta na tsawon shekaru ma su yawa da tai a rayuwar ta. 
Karantar yanayin Namsiyya kawai Sholy tai ta gane tana cikin tunani mai zurfi don haka tai saurin yanke hukuncin cewa ta amince malam . 
Wani kallo Namsiyya taima Sholy da magana a bakinta, amma sai tai shiru ganin yadda fuskar Sholyn ta ayyana mata tai shirun, 

“ kin amince komai muka nema gareki zaki bayar idon buƙatar ki ta biya? ” bokan ya faɗa yana kafe Namsiyya da idanuwansa 
“ eh na amince ” ta faɗi a takaice zuciyarta cike da zullumi suka baro wajan bokon sai kusan ƙarfe tara na dare suka isa cikin unguwar Miloniyan city kuma har a wannan lokacin kafar bayan gidan a buɗe take don haka hankali kwance Namsiyya ta shiga gidan tana murna da farin cikin cewa komai ya zo ƙarshe yanzu zata rayu cikin farin ciki da walwala ita da mijinta ƙarin abin farin cikin ma cikin daula zata rayu. 
Assalama alaikum ta faɗi duk da tasan babu kowa a cikin gidan amma sai taji an amsa sallamar raɗau cikin falon ta mai da kallon ta jin kamar idanuwa na yawo ajikinta yasa ta kalli falon Dam! Dam!! Gaban ta ya yanke ya yi wata mummunar faɗuwa sakamakon ganin Areeyan da Lateefah zaune suna kallon ƙofar kamar masu tsammanin shigowarta 
“Daga ina kiki ? ”
Areeyan ɗin ya faɗi cikin tsawa yana tunkaro inda take 
Take kuma jikinta ya ɗau rawa da karkarwa kamar wacce aka sakama kiɗin gangi zuciyarta na bugawa da ƙarfi kamar zata buɗe ƙirjinta ta fito tsabar tsoro da fargaba. 
A can wajan gidan 
Sholy na ajiye Namsiyya tai gaba abinta da nufin gobe zata shigo su tattauna duk da firar da sukai a mota akan hanyarsu ta dawowa wanda rabi da kwatar firar akan yadda Namsiyya zata mallaki Areeyan ne da kissa da kisisina. 
“Daman..... daman...... Daga gida nake ” Namsiyya ta faɗi muryarta na sarƙewa da in ina 
Wani irin mugun kallo Areeyan yayi mata mai nuna cewa zaki sani zaki yabama aya zaƙinta  
“ Da izinin wa kika fita ya faɗi yana ƙara matsowa daf da ita...... 

KATSINA STATE
 
Shagari lowcous daf da gidan man Aminu maraya adaidaita sahun ta tsaya ta sauke Ahanah 
“Nawane kuɗinka malam ” Ahanah ta tanbayaba tana kallon mai adaidaita sahun lokacin da tasauka. 
“ Dari ukku ne hajiya ” 
Dayake tana da canji a cikin jikkarta sai ta bashi ɗari ukkun tai cikin lungun da zai sadata da ƙofar gidan su tana isa taga yaya Nura da ɗanta Ahmat , Nuran ya riƙe hannun Ahmat shi kuma Ahmat ɗin riƙe da bakon kayansa. 
Da mamaki take kallon su kafin kuma tace “ yaya Nura ina zakuje haka da kaya niƙi - niƙi? ”. 
“ To harkin mance yaune ranar da za a mai da Ahmat gobarau wajan babansu, ”. 
Sai taji babu daɗi tana son ɗanta don haka bazata rabu da shi akan auren Samir ba auren da yake ƙasa yana dabo babu ma tabbacin yinsa ko fasawa amma zata riƙe ɗanta har lokacin da komai zai dai daita don ita tafara shawarar bama Abbas haƙuri ya mai da ita ɗakinta bata acikin yanayi mai daɗi don haka kawai sai ta kama hannun Ahmat tana cewa “ yaya ka basshi kawai zan kaishi da kaina ”. 
Da haka suka koma cikin gidan batare da yaya Nuran yace komai ba. 
Ɗakinta ta nufa ta ajiye kayan Ahmat akan gadonta ta kwanta akan gadon kanta na juyawa kamar zai rabe gida biyu, wani irin zafi zuciyarta ke mata wanda ta rasa dalilin sa amma komai zai faru sai dai ya faru amma wallahi bazata auri samir ba. 
tana zaune a cikin wannan halin mahaifiyarta ta Turo kofar ɗakin ta shigo taima kanta masauki a kan gaɗon dai dai inda ƙafafun Ahanah suke ta kalli ƴar tata kafin tace 
“ Ahanah lagiyarki ɗaya ko maza gayaman me ke faruwa? ”. 
Tashi zaune Ahanah tai daga kwancen da take tana kuka kafin tace “ Mama Samir ya cuceni mama samir ɗan iskane kuma mazinaci, wallahi mama da ido na na ganshi a gida ɗaya da wata ”. 
Sai ta ƙarama kukan nata ƙarfi tana mai faɗowa jikin mahaifiyar ta ta. 
“ inna lillahi wa inna ilaihir raju'un, wannan wane irin bakin labarine kika kawoman marar daɗin saurare shi samir ɗin ne kika kama da wata macen a gida ɗaya. ”
“ inma wannan ne da sauki mama bakiji irin zagi da cin mutuncin da yayi man ba kuma kema bai raga makiba har da yiman barazana akan zai iya sakawa a kasheni idon har na sanar da wani wannan zancen, sai dai ko zai saka a tsireni da raina bazanyi shiruba sai na sanar da ke tunda ke mahaifiyata ce kuma bazaki bari wani abu ya curar dani ba, bare kuma magana ake ta aure da makomar rayuwata. ”
“Ina zuwa bari ki gani” cewar mamar tana mai fitowa da wayarta ta danna kiran lambar samir, bugu ɗaya aka ɗauka kamar dama yanajiran kiran ne, cikin wata irin murya mai cike da bada girma da nuna tsantsar ladabi yace
“ Assalama alaiku mama barka da wannan lokaci ”
“ Amin wa alaika salam yaron kirki, ya kake ya aiki ya fama da hidima? ” 
“ Alhamdulillah mama sai godiya ”
“Dama wani baƙin labarine ya riskeni yanzin nan marar daɗin ji bate kuma sauraro, ina son idon kana da dama kazo yanzu don Allah gida na na son ganinka ”. 
“ Aiko mama sai dai kiyi haƙuri muyi maganar A waya domin a halin yanzu maganar da muke ina ƙasar Dubai naje ne akan kasuwancina zanyo sayayya bana Nigeria, amma idon maganar bamai yuyuwa bace a waya zan gabe zan dawo da na sauka sai nazo mu tattauna. ”
Wani irin sanyin daɗine ya mamaye zuciyar mama jin abinda samir ɗin ya faɗa kafin ta cigaba da cewa “ Haba nidai nasan badai kaina wallahi bazaka iya aikata wannan abin ba”. 

“Ni fa mama kin barni a cikin duhu ki sanar dani komai ke faruwa. ”
“ Kwantar da hankalinka yarona dama wani ɓakin sharrine naji za ayimaka wani ne ya kira Ahanah waya yake shedama ta cewa wai anganka da wata mace kuna yawo a gari har ta hau ta zauna gata nan sai kuka takeman, niko nasan badai kaiba shiyasa na kira na ji daga bakinka don nasan Sharri a kaima. ”
“ Amma dai ko waye yake son haɗani da Ahanah bai kyautaba, wata ƙilama tsohon mijin tane ya saka ayiman sharri don Ahanah taji haushi ta tsaneni ta koma gidan sa mai kama da gidan ƙaddara, amma Alhamdulillah tunda dai mama kinsan abinda zan iya da wanda ba zan iya ba, da zarar na sauka ƙasar nan sai na saka anjamasa kunne domin wallahi bazan bassa a haka yana ƙoƙarin ɓata mani suna a gariba ”. 
“ kar kasa ayi masa komai ni kaɗai na ishesa don yanzu zanije na cima mahaifiyarsa mutunci kuma nasaka taja masa kunne, idon kunne ya ji to jiki ya tsira sai anjima zamuyi magana. ”
Mama na kaiwa nan ta katse wayar tana kallon Ahanah tana cewa “ To ƴata kin dai ji sharri akamasa ”. 
“ wane irin kuma sharri bayan na sanar da ke da idona naganshi, to koma dai miye wallahi bazan auresa ba, yau naga ƙarfin iko yanzu mama ace kin yarda dashi kin ƙaryatani kawai don yana da kuɗi ko wallahi mama kiji tsoron Allah ni dai na gane gaskiya, Abbas zani nemo na basa hakuri ya mai da ni ɗakina....”
“ ke tsaya Ahanah waike wacce irin yarinyace mai kunnen ƙashi na sanar da ke aurenki da Abbas ya ƙare amma kina son maido hannun agogo baya, to buɗe kunnanki da kyau kijini bazaki taɓa komama Abbas ba, aurenki kuma daga yau ki fara shiri domin babu fashi sai anyi, yo ke inbadama rashin wayonki ya za'ayi kice zaki guji miji ɗan arziƙi kamar samir kin ban kunya wallahi ”. 
“ Mama komi zakice kice amma wallahi bazan auresa ba”. 
Ganin yadda ran Ahanah ya ɓaci yasa mama ta kwantar da murya ta fara maga kamar haka “ haba ƴata ki dubafa ki gani yadda yaron nan yake ta ƙoƙari akanmu tunda al'amarin nan ya faru komai ya ɗauke mana ya sauya mana gida ya ɗauki nauyin cinu da shanmu ga Alƙawarin saudiya da yayi man da zarar kin tare idon baki auresa ba ni kikaimawa ba kowa ba wallahi, baki san yanzu an wayeba anbar wannan rayuwar yanzu duniya komai sai da kuɗi ake yinsa ki natsu kiji abin da zangaya maki da kunnen basira don mu mukaga jiya mukaga yau namiji ba ɗan goyo bane duk wacce ta riƙe miji uba to zata mutu marainiya, ai yanzu don kuɗi ake aure idon ma baki sani ba ki sani yanzu, domin don kuɗin samir zaki auresa ki samu kema ki kwashi rabonki ki zama hamshaƙiyar hajiya duk inda ki kai ana duƙawa har ƙasa ana gaisheki ko ba don Allah tunda kin tara antara maki don haka ki ɗau mataki ki takanki wannan shine gaskiyar magana idon ya aje riga ɗan Aljihun nan lalube, ɗan kuɗin cefane rinƙa ragewa, ƴar shinkafa idon ankawo Auni tiya biyar ko goma ki sayar bazai ganeba tun da yana da kuɗi, kinga Atika sadda akai aurenta bata da komai sai tarin talauci da tsiya amma da ta ɗau mataki bakiga garken awakinta ba sai haihuwa suke suna ƙara yawa ta zama hamshaƙiya jiya jiya aka buɗe mata ƙaton shaga anan cikin kasuwar CENTARA tasa yaro anatayi mata business saima kinga motar da take hawa tazama wata ƴar gayu abin kallo ga ƙauyawa irina to haka nake fatan ki zama nan gaba kaɗan daga ankaiki ɗakin nan naki duk abinda kika samu maza ki aiko gida da shi atara maki ko ma a shigar maki adashe hannu bibbiyu daga an kwasa sai asai gida asamaki ƴan haya dan danan zaki zama hajiya ”. 
Shiru Ahanah tai takasa magana don tarasa abin cewa sai saƙa da warwara take a cikin zuciyarta, duk abinda mahaifiyarta ta faɗa haka take son ta kasance a rayuwa taga tazama hajiya ana mutunta ta agari ko don dukiyar da ta tara, gefe guda kuma tana kallon irin yadda zata zauna da mazinaci kuma maƙaryaci. 
***
Daga marubucin 
nace ke duniya ina zaki da mu wai ƴa za ayima aure ake mata wannan nasihar saboda tunanin iyaye da yawa shine zaman aure don duniya ake yinsa ba don ladaba, wannan Shi yasa kuke ganin hulaƙanci a rayuwar ku ta yanzu, ku kalli yadda maza suka maida mata kamar turaman Atanfa, matar bata da kima don yasan saboda kuɗinsa aka bashi, ya saketa yayi mata hulaƙanci na ƙarshe domin yasan yana da kuɗi kuma ko ina yaje za abashi tunda ya tara ƴa'yan banki, ba a kallon wane irin hulaƙanci yayima matar ka ga mutum yayima matarsa dukan tsiya ya karyata tadawo gida a kwasheta a mai da ana cewa kiyi haƙuri ƴarnan kinga tunda kika yi auren nan mun zama cikin rufin ashiri, ya riƙemu hannu bibbiyu ina zamuyi wasa da shi. 
Duk abinda zai sami ƴar ba damuwarsu bace tunda suna samin tallafi daga wajan miji . 
Yana da kyau mu natsu musan cewa mutuncinmu yafi mana komai a rayuwar duniya kare darajarmu shi zai sa a kallemu da mutunci Don haka mukare mutuncinmu sai mu zauna lafiya ba kyara babu tsangwama. 
****
Ahanah zatai magana sukajiyo sallamar yaya Nura a tsakar falonsu tun kafin su gama Amsa sallamar ya hau faɗin 
“ mama fito ki ga kayan arziƙi. ”
Atare suka iso falon suna kallon kayan abincin dake tsakiyar falon, buhun shinkafa da katan ɗin taliya dana makaroni da jarkar mai olga, kafin mama tai magana yaya Nura ya miƙomata kuɗi rafar ƴan dari biyar biyar yana faɗin “ Samir ne yace nazo na amsa wai kayan abincin bikine kuɗin kuma ayi cefane kuma ga rago can a harabar gidan nan yace wai a yankashi a samu naman miya ”. 
“ Ahhh masha Allah ” cewar mahaifiyar Ahanah tana washe baki kafin taci gaba da cewa “ kaji ɗan arziƙi irin Albarka kace akwai shagali yau. ” 
Ahanah zatai magana wani saurayi yayi sallama ya shigo yana cewa ina za 'a ajiye kayan 
Ajecan cewar mama tana mai rawar jiki irin na mutanen da suke da son abin duniya kuma suka samu, yana ajiye kayan ya fita bayan ya bama Ahanah wata takadda a hannunta, 
Kayan da saurayin ya akiye mama ke kallo cikin ɗoki da zumuɗi, bandir ɗin Atanfane da na shadda sai sheƙi suke da ƙamshi irin na sabunta, da sauri mama ta ce “ karanta mana da sauri muji abinda ya rubuto ”. 
Afili Ahanah ta fara karanto ɗan rubutun dake akan takardar kamar haka “ Wannan sakone daga mijin da zaki aura Samir shaddar ta su yaya Nura ce harma da abokansu, suyi ankon biki haka itama Atanfar ta mamace da danginta waɗanda suke da alaƙa ta kusa suyi anko suma su fito shar, Akwatin kuma komai na ciki nakine kiyi kwalliya sosai idon anjima za a zo ɗaukarku zuwa wajan Diner ”. 
Atake Ahanah ta buɗe Akwatin tana kallon kayan dake ciki masu kyau da tsada, tuni ta manta da duk wani baƙin cikin da yake damunta ganin komai da zata buƙata akwai cikin Akwatin tun daga kayan sawa kayan kwalliya da turaruka da mai kala kala duk masu kyau da tsada. 
“ kingani ko Ahanah ga irin abinda nake gwadamaki nan ki kwantar da hankalinki komai ya kawo kici ki mirsisi tusa gaban uwar miji. ”

Da dare misalin ƙarfe takwas na dare 
Tuni gida ya cika da ƙawayen Ahanah duk sunci kwalliya cikin ankonsu na Diner wanda ya kasan ce matiriyal kalar ja da filawoyi farare ko wa ka kalla yayi shar abinshi gwanin birgewa. 
Mota ukku ce tazo ta kwashe su daga shagari lowcous zuwa gidan dawa a Hill side royal suite, tunda motocin su suka shawo kwanar wajan suke buɗe baki da ido suna kallon wajen saboda kyau da tsaruwarsa, Suna gama fakin Amarya Ahanah ta fito sanye take cikin wata fitinanniyar doguwar riga fara irin ta Amaren turawa,  
Wawoo ta furta acikin zuciyarta tana mai ƙara ƙaimi wajan kallon wajan da ƙamshi kawai yake tashi ga sweeminfull tar da shi ruwan ciki sunyi kalar sky blue, tsabar haske ko wajan kamar rana don ko Allura ka yadda to zaka duƙa ka ɗauki Abin ka. 
“ ni Ahanah wai yau nice za'a Diner ta bikina a wannan babban wajan, inda daga farko ni da nan sai gani sai hange gashi yanzu ta dalilina ma wasu ke shigowa ”. Ta ayyana hakan a cikin zuciyarta tana murmushi 
Hannun Samir da taji ya saƙo cikin nata shine ya dawo da ita hayyacinta ta kallesa cike da burgewa ganin kalar kayan dake jikinsa suite ne bakaƙe sun karɓi jikinsa sosai gwanin birgewa. 
Suna fara tako ɗaya aka fara zazzago masu filawoyi daga sama masu kyau da ƙamshi har zuwa cikin ƙayataccen Holl ɗin, kowa ya sami waje inda ya dace da shi ya zauna aka fara gudanar da shagalin bikin cike da wayewa Anci Ansha Anyi hani an. 
Da misalin ƙarfe shabiyu saura taro ya watse kowa ya kama gabansa. 

Washe gari ma ansake yin wani fatin A can Liyafa cikin nuna wadata 
Ranar Asabar da misalin ƙarfe biyu da rabi aka ɗaura auren Ahanah da Samir, Anyi biki irin na manyan mutane kamar yadda suka tsara a cikin zuƙatan su. 
Ranar lahadi da misalin ƙarfe bakwai na safe jirgin su Ahanah ya ɗaga sai ( Sweetherland). 
Firgigit Ahanah ta dawo hayyacinta sakamakon shigowar wata Gamdiroba a cikin kurkukun da take kulle.