Chapter 23
Page 23
KATSINA STATE
Da misalin ƙarfe bakwai na yamma danƙareriyar motar Abbas PRADO ta ja birki a gobarau bayan firamare, sai kallon motar mutane suke baƙi da ƴan gari kasantuwar ba a saba ganin irin wannan motar a wajan ba sai dai idon sayayya akazoyi ko hucewa.
Da taimakon wasu Almajirai Abbas ya samu ya shiga da kayansa cikin gida.
Ba ƴan gidan su ba duk ƴan unguwar murnar dawowarsa suke da ganin ci gaban da ya samu a Rayuwa, sai da yaje ya gabatar da sallah magariba ya jira akai isha'i kafin ya dawo gidan.
Yana zaune a kan katifar da hajiya ta fito masa da ita a tsakar gida An baje kayan tsarabar da yazo da su ana fidimar rabama makwabta sai ga mahaifiyar Ahanah ta shigo ɗauke da sallama a bakinta hannunta kuma ɗauke da jikkar kayan Ahmat ɗayan hannun kuma riƙe da hannun Ahmat ɗin.
Turus ta ja wani uban birki.......
“Ya kika tsaya ki shigo daga ciki mana ”
“ dole na ja birki na tsaya ” cewar mahaifiyar Ahanah tana ƙara mitsittsike idanunta tana kallon Abbas kafin ta ɗaura da cewa “ Wai da gaske Abbas kai ne ka zama haka, kai ne ka koma ɗan gayu, don Allah ku tasheni daga wannan baƙin mafarkin da nake taya za ace Abbas yayi arziƙi cikin wannan ɗan lokacin, wai don Allah kuma kuna ganin yadda nake gani wai ko dai ba gidan Hajiya larai bane ”.
Mulmushi Hajiya Larai tayi kafin tace “ nan ne wallahi bakiyi ɓatan kai ba kuma Abbas Allah ya yarda arziƙi ya sauka, tsiya da talaucn da kuke liƙamasa sunji bugun arziƙi don wallahi aguje suka barshi ƴan baƙin cikin sai dai su mutu, yau dai ai kinga ishara kuma kibga ikon Allah mai saka tulu yai gashi, ai dama na sha gayama ki arziƙi rabo ne wai A fasa kwai a tsinci mota ”.
“ Dama Ahamat na kawo don mungaji da kiwon da ba riba sai faɗuwa, kuma Alhamdulillah ko yanzu Ahanah ta yi gaba don mijin da ta aura har abada Abbas ba zaiyi irin arziƙin sa ba don yanzu haka sun isa ( Sweetheart), yawon buɗe idon don haka bakuda abinda zanyi baƙin ciki da shi sai dai ni ayima ƴata don nagaba yai gaba, na baya sai cintar takalmi ”.
“ ke dai ake ji kuma ke kaki ya kama tun da kin haɗiyi sauro ɗan mu kika kawo mana kuma mun gode Riƙon da kikai masa Allah ya biya ki ”. cewar hajiya Larai tana kamo hannun Ahmat
Dogon tsaki Mahaifiyar Ahanah ta ja ta fice ba tare da ta sake cewa komai ba, A ƙofar gidan ta tsaya tana kallon motar dake ɗaukar mata ido tsabar sheƙi da sabinta, kallon bai mata ba har sai da ta isa wajan ta leƙa cikin motar ta kai hannunta tana shafawa a ranta tana cewa bari na koma na kira Samir wallahi na fasa zuwa hajjin kalar wannan motar zai sawo wani ni ma na kece rai ni na zama abin kallo a cikin unguwa.
Haka har ta isa gida tana sabbatu kala -kala a fili duk ta rikice da ganin arziƙin da Abbas yayi lokaci guda, ko msyafinta bata cire ba ta ɗauko waya ta hau kiran lambar Samir sai dai a kulle sai da tai masa kura yakai goma ba'a ɗaukaba kafin ta hau kiran lambar Ahanah ita ma dai shiru duk kanwar ja ce babu sauyi. Sai da tai masu kira ya kai shabiyar su duka kafin ta haƙura tare da ayyana ma ranta cewa inda suke babu Network, amma dai taci alwashin sai ta sai motar PRADO irin ta Abbas.
Daga wannan rana riƙon Ahmat ya dawo a hannun kakarsa Hajiya Larai, Aka sauya masa mskaranta daga Global zuwa ( Arraghibun Academy) dake nan filin sukuwa kuma gaɗe boko da Islamiyya.
Da safe Hajiya Larai tana ƙoƙarin kunna wuta a murhu Abbas ya shigo yace “ mama sako Abayar ki zaki rakani unguwa ”.
“ kai ko Abbas da jan magana kake ina zamuje da sassafe haka ko kalaci ba muyi ba ”.
” ke dai mama ki shiryo kawai muje nan kusa ne babu nisa ki tafo da Ahmat ”.
To kawai tace don tasan halin yaron nata da kafiya yanzu zasita jayayya da kace nace, don haka Hijabinta kawai ta sanyo ta kama hannun Ahmat don tuni tai masa shirin makaranta sai da suka fara ajiye Ahmat A makaranta kafin suka nufi Le aut dai dai wani katafaren gida suka tsaya, yai hon aka buɗe ya danna motar a ciki sai da ya nunama Hajiyar ko ina na gidan tanata yabawa da sa albarka kafin yace ta zauna yana zuwa A falon ta zauna shi kuma ya nufi wata ƙofa ta glass ya fice mintina kaɗan sai gashi ya dawo yana tafowa wata mace na bayanshi hannunta riƙe da Tire ɗauke da kayan karin ku mallo kalar na ƴangayu .
Sai da mai aikin ta fita kafin Abbas yace “ Hajiya kinga gidan nan da duk abinda yake ciki to naki ne da sunanki aka ginashi kuma na mallaka maki a kwai komai na buƙata.
Farin ciki da murna tuni suka baibaye zuciyar Hajiya Larai sai tama kasa magana sai kukan farin ciki.
Hajiya ki dai na kuka don Allah ai wannan abin farin ciki ne idon da akwai wani abu da bai makiba kiyi magana sai a sauyashi akwai mai aiki da me gadi, komai akwai a gidan nan har freezer da kayan kallo.
“ Amma dai Abbas kayi mani bazata, Allah ubangiji ya yi maka Albarka Allah yasa yaranka suyi maka irin yadda kai mani Allah ya ƙaro arziƙi da wadata Allah ya baka mata ta gari ”.
Amin Hajiya
“ Amma amma.... " sai ta kasa ƙarasawa
Murmushi Abbas yayi tare da dawowa kusa da Hajiyar yana cewa “ Akwai magana a cikin zuciyarki Hajiya ki faɗi ko mai zaki faɗi ni ɗanki ne komai nawa mallakinkine kuma kina da ikon yanke mani ko wane irin Hukunci”.
“ na sani Abbas amma kuma duk da haka bana son na ɓatamaka rai ”.
“ Babu abinda zakiyi ki ɓataman Hajiya ki faɗi komai zaki faɗa zan karɓa kuma na gode maki ”.
“To Abbas Ina son in sanar da kai nayimaka mata, abinda nake nufi na zaɓa maka matar aure ”.
Dam! Dam! Zuciyar Abbas ta buga da wani irin ƙarfi, yanzu fa yake shirin sanar da ita ya samu yarinya mai hankali wacce ta dace da shi don yau yake shirin zuwa garin charanchi ne man gudansu Muheebaht don wasa wasa ganinta kawai yake son ya sake abinda zuciyarsa take nufi da shi shine ta kamu da ƙaunar yarinyar, amma kuma ba zai iya musu da mahaifiyar sa ba don haka sai ya sami kanshi da cewa“ Hajiya dama saboda wannan batun kika damu kanki, bani da wani zaɓi da ya huce naki kuma ina godiya ga Allah da ya bani uwa kamarki, kuma ina mai tabbatar maki na karɓi zaɓinki hannu bibbiyu, me ne ne sunan yarinyar? Kuma wacce unguwa take?. ”
Sai da Hajiya Larai tai murmushi kafin tace “ sunan ta Muheebaht a charanchi take a ƙauyen fulani, kar kuma ka damu kanka don kaji nace ƙauye tana da ilimi da wayewa kuma tana da tarbiyya yarinyar kirki ce zakai Alfahari da ita ”.
“ Amma kuma hajiya taya kika santa,? ”
“Cen dangin mahaifinka ce yarinyar ma marainiya ce mahaifin ta ne kwanaki na sanar da kai anma sharrin kisa a ka kaishi kotu a ka kasheshi ba da haƙƙinsa ba ”.
“ wayyo Allah, Allah ka sakamasa ka bimasa haƙƙinsa ”.
“Amin yaron kirki to yau she zamuje kaga yarinyar? ”
“Duk lokacin da yayi maki Hajiya kisa mana lokaci kawai .”
KADUNA STATE NIGERIA.
Gidan Areeyan
“ fara bani wayar Lateefah da sarƙar wuyanta don su ba kayan wasa bane ” cewar Areeyan yana ƙara ɗaure fuska
Wani irin bugu zuciyar Namsiyya tai wanda har ƴan hanjinta sai da suka motsa ta shiga cikin tashin hankali marar musultuwa,
Ganin tayi shiru yasa Areeyan ya ƙara matsowa kusa da ita yana cewa “ Dake fa nake magana kar ki bari rai na ya ɓace don ba zaki ga da kyau ba don ba ƙaramin hukunci zan maki ba ”.
Kuka Namsiyya ta fashe da shi tana rawar jiki tace “ Don Allah Don Girman iyayenka kai mani rai wallahi wasu miyagu na haɗu da su a hanya suka tare ni suka kwace wayar da sarƙar har ma ciwo suka jiman ”.
A madadin ɓacin rai sai ya fashe da dariya yana cewa
“ kamar dai yadda na tsara arai na amma yarinyar nan kina da wayo da basira kin san salon yau dara, to bara kiji nan ba inda ƙarya da munafurci ke tasiri bane nan kar ta san karce ki gaggauta fito da wayar nan tun kafin rai na ya ɓace. ”
“ wallahi ba ƙarya na gayamaka ba iya gaskiya tace na sanar da kai ka yarda da ni ”.
“ yaya bafa zata fito da wayar nan ba a haka kasan halinta zata iya jure komai don ta tsira da kuɗin wayar ”.
Sai da ya ja baya kafin yace “ ok na fahimta ”. Ya faɗa yana fito da wayarsa daga cikin Aljihun sa ya kira lambar (D. P. O)
“Yellow ƴallabai muna da mai laifi a gida don Allah kazo da sauri mace ce kuma ”.
” Ok sir yanzu zamu iso insha Allah ”
Cikin mintina ƙalilan sai ga D. P. O da wata mace ƴa sanda sai wani namiji shima ɗan sanda.
kuka Namsiyya ta fashe da shi tana mai faɗuwa ƙasa tana gunji da magiya, amma sam Areeyan ya kauda kansa gefe ya ɗaure fuska sai ma yace “ ku bugeta sosai har sai tayi magana, kar ku bari ta kira kowa kuma kar kubari wani ya ganta kuyi duk abinda ya kamata har sai ta fito da wayar da sarƙar. ”
Namsiyya tana ji tana gani aka danƙara mata hangcock a hannu aka fita da ita, karo na farko a rayuwar ta da ta hau motar ƴan sanda da sunan mai laifi.
Ko da suka isa suka sata a sell suka hau dukanta sai da sukai mata jina jina kafin suka barta ta huta domin taƙi magana.
Kwatsam sai ga Sholy a cikin sitation ɗin a rikice, Namsiyya tayi mamakin ganinta, ko da ta tanbayi ba asi sai ta shedama ta taje gidan yanzu mai gadin ya sanar mata da komai bayan ta bashi naira dubu biyar, nan acikin sitasion ɗin ta bama Namsiyya kwallin ta shafa takuma ƙara jaddada mata cewa aikin zai yi sai dai komai bokon ya buƙata to ta tabbata ta bashi in ba hakaba komai zai zahule.
Ko da Areeyan ya iso cikin sitasion ɗin fuskar sa a murtuke amma kuma yana yin tozali da Namsiyya sai yaji duk wata damuwa ta kaura daga cikin ransa, hassalima faɗa ya hau yima ƴan sandan akan dukan da sukai mata yayi yawa daga ƙarshe kuma ya buƙacu su fito da ita, daga sitasion ɗin Asibiti ya nufa da ita aka dubata, ganin irin yadda yake riritata da bata kulawa yasa taji a duk duniya bata da masoyiya kamar Sholy kuma babu masu kauda matsala a cikin sauri kamar bokaye.
Ko da Aka sallamesu dagga Asibiti suka koma gida a ranar Lateefah ta bar gidan ganin zuciyarta zata fashe tsabar baƙin ciki ganin yadda Areeyan ya koma kamar ƙaramin yaro sai yadda akai da shi.
Cikin murna da ɗauki Namsiyya ta kira Sholy ta sanar mata yadda kwallin yayi aiki kamar yankan wuƙa, ai ita ma Sholy 'n cikin farin ciki ta zo ta ɗauki Namsiyya suka nufi gidan boko.
Iya tashin hankali da ruɗani Namsiyya ta shiga jin abinda bokan ya buƙata amadadin ladar aikin sa.
“ ladar aikina ɗaya ce zamu kwanta da ke ni da Aljani Ayiya ”.
Ji tai kamar an watsamata tafassasshiyar Dalma a kunne, jikinta ya fara rawa kamar ana kaɗa mata gangi tai baya tana makyarkyata, sakamakon jin kalaman bokon masu kama da albushir da shiga wutar Jahannama,
“ Allah yayi man tsari da haɗa jiki da kai haka kawai kana ƙazami sai wari kake da ƙarni kuma na haɗa jiki da kai to wallahi baka isa ba, ” haka Namsiyya tai ta masifa taima bokan tas tai tafiyar ta, cak kuma ta ja birki ta tsaya jin abinda bokan yake faɗa.
“ Idon har baki kwanta da ni ba zaki rayu cikin duhun da baya da magani indon har baki haɗa jiki da ni ba to zaki makance. ” yakai ƙarshen maganar cikin bada umarni.
Sai dai ko juyowa Namsiyya batai ba ta bar wajan.
Bayan ta koma gida tai wanka ta fito tana shafa Areeyan ya shigo yace “ ginbiyar mata har kin fito daga wankan?. ”
Sai da tai murmushi kafin tace “ nayi sauri ko my Husband ”.
Takai ƙarshen maganar tana shafa kwallin a idon ta don ƙara samun kan mijinta ya manta da kowa sai ita da danginta.
Shahararren baƙin duhun da ya mamaye dukkan illahirin ganinta shine ta jefa rayuwar ta a cikin tsoro da zullumi, da sauri ta kai hannun ta akan fatar idon ta tafara mirzawa tana buɗewa Amma shiru babu abinda ya canza bata ganin komai sai duhu.
Ji kake kwaratsatsam ta watsar da kayan shafar dake akan mirrow ɗinta tai hanyar waje tana faɗin
“ Areeyan! Areeyan!! Bana iya ganin komai na makance ”.
Kamar wanda aka saka majaujawa aka tillo haka naji hannun sa akan fuskata yana shafawa yana faɗin
“ wane irin baki gani ga idanuwanki nan buɗe tangaram kamar na kowa? ”.
Faɗawa Namsiyya tai jikinsa tana sakin wani irin kuka mai ban tausai da rikita mai saurare ta ce “ Areeyan wallahi bana iya ganin komai kuma yanzu abin ya faru ina tsaka da yin shafa abin ya sameni tun ina ganin gizau har abin ya mamaye ni duka. ”
“ inna lillahi wa inna ilaihir raju'un yau munga baƙar rana makanta kuma da kuruciyar ki dai dai kina cin Amarcinki, wannan wacce irin baƙar gaddarace haka. ”
“ Areeyan meye abinyi yanzu baka san yadda nake ji ba lallai makafi suna cikin jarabtar ubangiji, Ba ƙaramin taimako ido yake mana ba a rayuwar duniya, ashe haka abin yake, ashe haka ake ji lallai babu wani abu mai daɗi a rayuwa kamar ido, wanda ya sami kansa a cikin makanta shine zai iya fahimtar abinda ake ji. ”
“ maza muje asibitin zama bai ganmuba ”.
Zaune na ke a bayan motar shi kuma yana mazaunin direba ya na ja duk hankalinshi a tashe sai surutai yake kala - kala na fita hayyaci, ni ko uffan na kasa cewa sai kukan zuci na ke da tashin hankalin da ya mamaye kwanyata lallai nayi gudun gara na faɗa gudan zago.
basake cewa komai ba har muka iso gaban likitan, duk wani awo da gwaji an mani amma ba a gano wani ciwo a ido na ba , a cewar likitan ma lafiya ta lau kawai muna rai na masa hankali ne, haka muka dawo gida jiki babu kwari, a wannan ranar kwanan bakin ciki nai, tun da safe na kira Sholy na sheda mata halin da nake ciki, daga farko sai ta shareni sai daga ƙarshe tazo ta ɗaukan muka koma wajan Bokan.
Wata gigitacciyar dariya da bokan ya ke ita ce ta shedaman mun iso wajen sa don bana iya ganin komai har yanzu.
“ Dama ai nasan zaki dawo don maganin da na baki ƙaryar namiji yace an ɗaura aurenku ya barki sai yaji sonki a ransa amma kuma nayi mamaki da har ni na kasance cikin masu buƙatarki, yanzu kin shirya kwantawa da ni ko kuma zaku dauwwama a cikin makanta. ”.
“ Na amince ”.
Na faɗi cikin muryar kuka ina mai ci gaba da cewa “ wa iyazu billah naga takaina ”.
Wani uban wari da ya zirayarci hancina shine ya shedaman yadda bokan yake a baya , bai da sutura a jikinsa sai walki wanda yayi amfani da shi wajan boye tsiraicinsa da shi, zata iya rantsuwa akan bai taɓa wankaba saboda yadda dauɗa ke fita a jikinsa, bakin sa cike ya ke da dussar goro wasu haƙoran ma duk sun ɓalle, ga yanan da babu kyan gani.
“ Sholy yanzu ya zanyi ina son budurcina kuma na son idanuna bana son rasa ko ɗaya a cikinsu, don bansan irin kalaman da zanyi amfani da su ba wajan kare kaina a gaban mijina Idon ya tanbayeni ta yadda na rasa shi, kuma da na rayu bana ganin komai gara na mutu wallahi.
“ zo kiji ”.
Sholy tai ma Namsiyya raɗa a kunne
“ ke gara ki amince idon har buƙata ta biya sai a kulle bakin mijin naki ki sakata ki wala ayi komai a cikin sirri.
Babu musu Namsiyya ta amince da shawarar ƙawarta ta toshe hanci suka aikata masha'a da Boka, sai da ya gama biyan buƙatarsa kafin yayi gefe yana mai da lumfashi.
Da kyar Namsiyya ta iya miƙewa tana dukkuƙewa kamar Tsohuwa, ta lalubo kayanta ta saka cikin wani irin yanayi na tausayin kanta ta tsinkayo muryar bokan yana wasu soki burutsu wanda ko za a yankata batasan abinda yake cewa ba.
Andaɗe ana abu guda Amma babu sauyi, cikin zaƙuwa da ƙosawa Namsiyya tace wai haryanzu.
“ inna lillahi wa inna ilaihir raju'un,” sune kalaman da nake ta furtawa cikin tsoro da zullumi ganin bokan yayi iya yinsa amma ganina bai dawoba
Abu kamar wasa Gani ya ƙauracema idanuna kuma a yadda bokan yake nunawa shima ba daga garesa bane.
Daga ƙarshe dai ya bani wani magani yace nayi amfani da shi tsawon kwana bakwai ganina zai dawo kuma a kullum sai na kawo masa kaina middin ina son ganina ya dawo.
Bayan wata Takwas
Namsiyya ce zaune a ɗaki cikin kunci da takaici, a hankali ta furta “ lallai hausawa sunyi gaskiya da sukance duk tsuntsun da yaja ruwa to shi ruwa kan doka, garin neman gira na rasa idanu, babu mijin ba idanun babu arziƙin, na zama makauniya tuburan, ga kuma tsohun cikin boka da yake jikina, don yayi amfani da damarsa wajan ɗirka mani ciki.
Tun bayan wata ɗaya da makantata asirin da nai ma Areeyan ya karye yayi mani saki ukku.
Tabbas naga izinah a rayuwa ta don na rasa ido na kuma na rasa mijin da nake ta fafutukar jawo hankalin sa a kaina, ni kaina na rasa me ne ne makomata, rashin yadda da ƙaddara ya kaini ga halaka, ga shirka ga makanta ga kuma cikin shege ni Namsiyya naga ta kai na kaico da wannan rayuwa da duniya ta zama abin nema ga kowa kamar ba za'a mutuba, bubu irin taimakon da mama bata nemo mani ba amma shiru babu nasara sai Asara, a dole na koma ga Allah ina roƙonsa da ya yafe mani laifina ya kuma kawoman mafita a rayuwa ta .
Yadda da ƙaddara shine cikar imani, Allah ka azurtamu da tarin imanin da babu kafirci a bayansa, Allah ka mucigaba da aikata kyawawan Ayyuka, har ƙarshen rayuwarmu, Allah kasamu a cikin masu fidima ga Addininka, har zuwa lumfashinmu na ƙarshe.
Allah mafi jin roƙon bayinsa ya amshi addu'a ta bayan na haifi yaron baizo da rai ba kuma ganina ya dawo, sai nake jin Ina ma ace tun farko Allah na bayyana ma damuwata ba wani mushirikiba, da duk hakan bata faruba, HANGEN DALA shine hangen da ya buɗenman shafin baƙar ƙaddara a rayuwata, daga ƙarshe dai wani Gurgu na aura kuma nai haƙuri da Talaucinsa.
ABUJA NIGERIA
JABI
Tunda Muheebbaht ta bar gidansu Tahteef ya fito a guje yana nemanta amma bai gantaba har waje ya fito amma ko mai kama da ita bai ganiba, ( oh short ) ya furta yana kaima iccen lemun da yake ƙofar gidan bugu da ƙarfi kafin ya koma cikin gidan a ruɗe ko takalma babu a ƙafafunsa ya nuna mahaifin sa da yatsansa manuniya yace “ kagani ko Dady kaine silar duk abunda ya faru ta tafi ta barni, idon har wani abu ya sameta ba zan yafemaka ba, ”.
Yana kaiwa nan a maganar sa ya fice daga gidan baki ɗaya a motarsa da ya shigo da ita, kansa tsaye gidan marayu ya nufa amma yana zuwa Atika ta sheda masa ta tafi gida garinsu, duk wata tashar mota dake garin ABUJA sai da yaje amma bai sami Muheebbaht ba kawai sai ya nufi hanyar garin nasu ga marece yayi sosai ga gajiyar da ya tarama kansa ga damuwa da tunanin da sukaima kansa yawa yana dai dai kauyen Banguwa yakusa shiga KADUNA mummunan hatsarin ya faru inda yayi karo da wata ƙatuwar mota Tirela da ƙyar aka iya fitowa da shi ko ina na jikinsa jinine yake fita duk fuskarsa ta ɓace da kwalbar glass ɗin motar da ta caccakai kamar an tsittsira masa abin dai babu kyan gani ga wani yanka a baya da wani ƙarfe yayi masa haka aka fito da shi daga cikin motar bai san inda kansa yake ba.
Dan da nan maganar wannan mummunan hatsarin ta zagaye garin ABUJA da KADUNA, domin kuwa ko wane gidan Tv da jarida abinda suke haskawa kenan.
Alhaji sulaiman gidan iko na zaune a falonsa duk abin duniya ya taru ya ishesa sai ga sako ya shigo ta wayarsa yana buɗewa ya ga wannan mummunan hatsarin nan take ya yanke jiki ya faɗi babu rai,
Tahteef ko da aka kaishi Asibiti Aka Amsheshi da kula mai kyau sai dai an kasa ceto rayuwar shi kwana ya ƙare haka ya amsa kiran mahaliccinsa.
Da sakon mutuwar Tahteef ya riskesa ya sake shiga wani halin sama da wanda yake ciki, ciwo yayi tsanani har ƙasar waje Aka fitar da shi amma Lafiya ta gaza samuwa duk wata daula da aka tara ta gaza samamasa lafiya, daga ƙarshe dai ya kamu da cutar mutuwar ɓaren jiki.