OMRI HAYATII

18

by @asmybaliyu

OMRI HAYATII 

by.
Asmy b Aliyu 

18...

zaman da sukayi da noor na ya'n awanni 
ya rage mata damuwar da take aciki
noor ta taimaka kwarai wurin rage mata damuwa.bayan sunyi lunch Suna kwance 
akan bed ,noor dake kwance akan bed tana chart .ta dan kalli malaak din
kafin tace bazaiyuyu ki xauna babu waya ba babe.idan mun fita a biya a siya sabuwa gaskiyya.murmushi kawai malaak din tayi.kin San me?"nifa har na fara tunanin xaki bini Abuja a gobe ki samu ki dawo walwalarki .yau sauran kwana 10 birthday dina kinga duk wasu shirye shiryen da zamuyi muyi kafin zuwan ranar.dan shiru malaak din tayi kafin ta amince Zata bi noor din a gobe kamar
yadda tace Sai ta sauka gidan yayarta maleeka.kamar yadda ta saba duk lokacin da ta xiyarci Abuja.duk da Suna da gida
a abuja babu kowa aciki Sai maigadi
suna dadewa ma basuje gidan ba,
ko taje Abuja gurin maleeka take zama,
Sai inda mum ne suke sauka a gidansu.

wuraren 4 suka fita.malaak ta tsaya wani shop Wanda ake siyarda wayoyi
noor ta matsa mata ta dauki iPhone 18
ba yadda ta iya haka ta dauki iPhone 18
dan ko a ido batayi mata kyau ba kamar 
yadda iPhone 17 tafi kwanta mata arai,
tana kokarin cire card dinta ta bada
noor ta rigata dora nata da ido
take kallon noor tana dan bude ido
akan noor din,juya mata ido noor din tayi.
bayan Sun fito ta kalli noor Cike da class take fadin."thank you my girl friend,
hannu noor din ta saka akan bakinta
alamar tayi shiru,yadda tayi din ne
yasa malaak din ta saki murmushi.
haka suka rinka yawo cike da farinciki da sakewa,Sai bayan ishaai malaak ta maidasu hotel tace lallai Sai noor din ta kwaso kayanta Sun dawo gidansu,
haka suka kwashi kayan noor suka koma gidansu malaak din koda suka koma
mum na a falo.tana danna waya
maikaikinta na zaune kusa ga kafafunta
tana dan jamata su.cike da fara'a mum
ta tarbesu,musamman da ta kalli malaak din taga ta dan rage damuwar da ta shiga
mum ta kalli noor tana mata sannu da zuwa.da sauri mum ta umurci maiaiki
da takai kayan noor din dakin malaak.

mum zamu shiga cikin muyi wanka.
malaak ta fada a tsaye ,kuje kuyi wanka ku huta kafin nasa mai aiki ta shigo maku da abincin dare.......no mum a koshe Muke
fruits kawai ya isa.in Sha allahu.mum ta fada cike da kulawa ,koda suka nufi dakin malaak din noor ta fara rage kayan jikinta
tana watsar dasu a tsakiyyar room din
kasancewar itama ya'r gatace gaba da baya. Kanwar maza Kuma,komai Sai anyi 
Mata kusan masu aiki biyu gareta 
komai da komai su suke mata hatta da wankin pant.sangartatta CE ta karshe
tun kafin zaliha ta fita daga room din
ta durkusa ta fara tsince kayan noor din....bayan sunyi wanka wuraren qarfe 9
aka shigo masu da fruit kadan suka Sha suka haye kan makaken Turkish bed din
malaak din na ya'yan gata ko wace da waya a hannunta.ta leqa Whatsapp yafi sau nawa babu alamar mu'azzam Yana online,rabonsa da online tun jiya.
haka takai zuciyarta nesa bata nemesa ba kamar yadda noor din ta tsaramata
akan tabari shi ya fara nemanta.
irin wannan soyayyar da take nuna masa
shiyasa yake amfani daita Yana huting din feelings dinta,noor ta runtse ido
tana fadamata ita bata ga shegen namijin da Zata zauna tana yiwa wannan tsinanniyyar soyayyar ta gairi babu dalili ba.
shiyasa dating dinta baya nisa ya lalace
saboda kwata kwata bata daukar nonsense da izgilancin namiji.ita dai malaak jin noor din kawai take 
bata samu namiji mai kyau da class irin mu'azzam marafa ba da duk wata izza tata Sai ta sauketa ta bada Kai......tun daren ranar noor ta siya masu tickets 
Sai da safe malaak ta gayawa mum 
tafiyarta Abuja.bakarmu Th,zzn farin ciki
mum din tayi ba,itama mum shirye shiryen tafiya Us take taje ta xiyarci dad dinsu
malaak din.dan tafi yawan Kai masa ziyara ,sabanin shi Yana wata 3 bai leko Suba.

mum din ta kaisu airport da kanta 
lokacin tashinsu nayi jirginsu ya daga birnin tarayya.....koda suka isa driver da zai dauki malaak ya iso ,itama noor drivern ta ya iso tun a airport suka rabu akan Sai sunyi waya.tsadaddiyyar unguwa ce 
Wanda masu kudi Abuja suke kewaye 
acikinta Wanda suka koshi suka tada Kai da naira ,masu wata irin power da daukaka.tun a babban parking lot 
maikatan gidan suka San da zuwan malaak din saboda matsayin da take dashi a wurin matar gidan Sai sannu da zuwa ake mata da respect Cike da class da basarwa take amsa gaisuwarsu,
maleeka da kanta tazo ta tarbi kawartata
a kofar shiga babban falon gidan
ta jawota ajikinta ta rungumeta tana mata sannu da zuwa da tsananin so da wata irin kewarta da tayi.itama malaak tuni ta manta wani sabanin da ya shiga a tsakaninsu sosai take murnar ganin ya'r uwarta.

masu aiki suka dauki trolley bags din malaak din babba da karama da suke a hade suka nufi babban dakin da malaak din ke sauka duk lokacin da ta kawo ziyara gidan Yayartata.babban dakine mai hade da toilet a ciki Sai babban Turkish bed,
Sai babbar wardrobe dinsa da ta kusa cinye Rabin dakin saboda girma da tsayi.
tuni maleeka ta fita shopping ta hadawa malaak din duk kalar suturar da takeso 
da abubuwan da tasan zatayi using dinsu
Sai da ta tabbatar an tanadarwa malaak din komai Sannan hankalinta ya kwanta.
Kai tsaye malaak ta kalli yayarta tana fadin."Ina nadir?"Yaronta dan shekara 8 Wanda tun daga nadeer din bata Kara samun wani ciki ba,daman Kuma ba son haihuwa take ba uwa uba maigadin Kai tsaye ya fada mata daya ya ishesa tareda ita uwar gidansa tana da kusan yara biyar tare dashi.itama saboda tsananin sonsa
da take bata wani damu ba.tunda Zasu cigaba da Rayuwa a karkashin innuwar Aure.zan wuce daki na watsa ruwa na huta.daga mata Kai maleeka din tayi
tana sakin murmushi tana fadin."a fito lafia babyn mum.kai tsaye malaak din ta nufi bedroom dinta.
bayan wucewarta itama maleeka sukayi waya da mum akan malaak din ta iso.

######
Sai wuraren 4 bayan ta tashi baccin da bata samu tayi ba ajiya dan raba dare sukayi Suna hira da noor ko yanxu Yunwa ce ta tasheta.kai tsaye toilet ta nufa
wani wanka ta sakeyi.bata damu da sallolin da suka hau kanta ba daga azzahar ,har la'asar wata English gown 
ta fitar cikin kayan da aka jera mata cikin 
wardrobe mai ratsin baki da fari ajikinta
da kadan ta sauka akan gwiwowinta
ta Kara gyara parking din gashinta dan babu laifi Sunada gashi saboda mum dinsu
asalin kabilar ghana ce Kuma su basu Kai haske mum dinsu ba duhun fatan mahaifinsu suka dauko duk da Suma baa saka su cikin jerin bakake Suna da dan haske.haka Suna da wani irin sanyayen kyau.casuall slippers ta xura a kafafunta
ta dauki wayarta ta fita daga dakin 
Kai tsaye dinning area ta nufa
gabaki daya ta tattara hankalinta kan wayarta.tunda ta iso wurin mijin maleeka din ya kureta da ido wasu mayun yawu
ya hade tsananin maitarsa akanta da son kasancewarta na bayyanar masa 
afili duk da a haife zai haifi malaak din
Dan ba yaro bane ya baiwa arbain baya,
ganin yanayinsa maleeka ta saka 
kafarta ta danna tasa tana saka masa kumbarta ta kafa da yasa ya kalleta 
agigice Yana jin wani zafi da radadi 
na shiga cikin kafarsa.daidai nan malaak din ta karaso taja kujera still hankalinta
na kan waya take fadin"Hiii Abban nadir sannu da gida.cikin washe baki Alhaji Jamil
naira yake fadin"sannu da zuwa baby malaak da fatan kinzo lafia."lafia lau
ya kake ya aiki ta fada cike da class 
cike da takaici maleekan ke kallonsa,
duk ya wani ya daburce akan malaak
batada wani haufi kan malaak din dan komai nacinsa .malaak ba irin matan da Ake samu cikin sauki bane.sai an sha wahala da gwagwarmayaaa.tasan kuwa
ko acikin mafarki baizai taba samun
malaak farook Rano ba........ maleeka ta kwalawa mai aikinta kira da sauri maiaiakin ta karaso ,kiyi serving nata
nan akayi serving malaak din da kalar cimar da akasan tana so.malaaak 
ta aje wayar hannunta tana dagowa
idanunta cikin nashi,wani irin abu taji
Yana soka mata zuciya akan mayen kallon da taga Yana mata.sai ta fasa cin abincin akan table din kamar yadda tayi niya 
ta kalli maleeka tace ya'r aiki ta hadamata 
komai a tray akai mata a daki.da haka 
ta juya tabar dinning area din duk rai 
a bace.

"kaji dadi yanxu tabar ma wurin hankalin ka ya kwanta.?"maleeka ta fada cikin rawar murya da wani irin daci a muryarta,wani shegen kallo ya rika aikawa ta saitinta kafin ya miqe tsaye Yana kwashe wayoyinsa Yana Jan wani shegen tsaki yabar wurin tamkar zai tashi sama saboda bakin cikin da malaak tayi masa
na barin kan table......


#ASMY B ALIYU 
#LOVE/FATE
#HOT LOVE
#OMRI HAYATII 
#***