Forever favorite book 2

Chapter 51

by @reeeyarh

Forever favorite 51

  Baby na kwance around 10:00 ta fara bacci wayan ta yayi ringing, a kira na biyu ta farka a hankali ta daga jin muryar al’amen yasa ta dan bude ido a hankali tace good evening cikin muryar bacci, babyyyy, ummmmm, kin fara bacci ne, ehhh, ohhh sorry, a hankali tace ya al’amen, babyy, i’m mad at you.

   Da akai me, mai yasa kake yimin fada kuma bayan bani da laifin komai, babyy but I told you bana son alkarar ki da maza, but ya al’amen he’s my brother babu yadda zai yuwu na rabu dashi, shiru yayi sai kuma yace kunyi magana da mami, ahah what happened.

  Okk shikenan, mai ya faru, za kuyi magana da itaa, shiru tayi yace kiyi bacci gobe zanzo zamu je school, tam bye, bye love you ya kashe wayar.

   Kamar Kwai haka sultan ya ringa lailaya shahida, a ranar babu kunya ya kira mom ya fada mata sosai sukai farin ciki ya fadawa ammi da daddy shi su mimi sabir babu wanda bai fadawa ba, kayan ta ta hada da shima ya tatara nashi suka koma gidan ammi dan itama ammi yana fada mata tace su dawo gida.

  Al’amen around 10 yazo gidan lakacin bata dade da gama breakfast ba suna zaune da mami ya shigo, gaida mami yayi sannan yace ta tashi su tafi sukaiwa mami salama suka, suna cikin tafiya tace wana school zamu je, inda su meerah sukai.

 Kai ta daga mishi hannun ta ya riko yace babee, ummm, mami bata miki magana ba har yanzu, kai ta daga mishi yayi murmushi tace please ka fada min, kai ya girgiza mata tace pleasessssss, kallan ta yayi sai kuma yace su abbah sunyi magana, magana kuma ta mai.

  About us, kallan shi tayi yace an saka ranar aure mu, ban gane ba, meye baki gane ba nace an saka ranar aure mu, shiru tayi ya matsa hannun ta yace are you not happy, kai ta girgiza mishi yace zaki zauna dani nan ma ta daga mishi kai yace thank you.

  Shiru sukai for moment sannan tace yaushe, next year, kallan shi tayi ya daga mata kai, amma ya al’amen school fahh, hararar ta yayi yace maiya faru da school din, taya zan hada aure da school, murmushi yayi yace zaki iya, shiru tayi yace toh yanzu keda karatun da za kiyi na shekara 7 ne sai kin gama za kiyi aure.

  Kai ta daga mishi yace you’re not serious, yaya, ummm, promise me something, what za kayi blocking din coworker dinnan taka, murmushi yayi yace why should I, please ni bana so tana kiran ka, nothing between us, but har gidan su kake zuwa.

  Dan naje gidan su aiki ne ya kaini, tohh ni gaskiya yaya bana sonta, tohh aure tama fa za ayiii, but her sister don’t tell me, ki tambaye ta kiji we’re just friends, shiru tayi yace that is all, kai ta girgiza mishi tace baza ka kara aure baaaaa, zaro ido yayi yace dalili, one side looks tayi mishi ta dauke kai.

  Magana yake ta mata amma taki kula shi har suka je, yana parking ya juyo ya kalle ta yace da wasa nake miki my Mon cœur (my heart), hararar shi tayi ta dauke kai, trust me babyyyyyy, haba kema kinsan ke kadai ce babu kari sammm, hmmm, wallahi da gaske, ya al’amen duk ranar da kace zaka auri wata zan tafi na bar maka gidan ka.

  Haba dai ai babu wurin wata a wannan zuciya, zuciyar taki ce ke kadai my Mon cœur,
Murmushi tayi yace oyya muje suka fita hannun shi na cikin nata har suka gama komai ya maida ta gida.

  Haka sukaci gaba da rayuwa soyayya tsakanin baby da al’amen kamar ba gobe shi yake kaita school shi yake dauko ta sun kara shakuwa iya shakuwa.

  Meerah ta koma gida tun bayan 40 days da haihuwa wata sabuwar kauna dee yake nuna mata suna rainon dan su wanda suke kiran shi da Abutt, sosai suke nunawa juna soyaya.

  Shahida a yanzu cikin ta yana 8 months kusan karshen 8 months dinma haihuwa yau ko gobe, tunda ta dawo gidan ammi take shan kula daga wurin kowa dake gidan sultan badda rashi kunya babu abun daya karu babu ruwan shi a gaban kowa yake nuna mata soyayya.

  A wannan lokacin abubuwa da yawa sun faru kamar mutuwar hajja da mama fulani amma har yau usman bai dawo ba sam shahida da diyya sunci gaba da rayuwa kamar babu abun daya faru maman su ma yanzu tayi hankali, a yawan zuwan da diyya take yi nan Asad ya ganta soyayya suke sosai, aaliya ta haifi yan biyu su sabir an zama maya.

  Yau suna zaune sultan da shahida a palon yana zaune kanshi a kanta yace princess, ummm, anjima fa zamu je taron bude lab dinan, i don’t think zan iya zuwa, nooo zaki iya in sha Allah, yaushe ne, da yamma, okk toh Allah ya kaimu, amen.

   Koda suka shirya da yamma ba wani dadi take jiba haka ta shirya, kallan ta yayi yayi murmushi yace perfect princess kinga yayyda kikai kyau, dan yamutse fuska tayi tace nifa ba wani dadi nake jiba kar naje na haife maka danka a yawo, dariya yayi yace da kuwa miss suhana ta zama babbar mai sa’a a duniyar nan.

  Murmushi tayi ya rike jakar ta ya kama hannun ta saida suka biya part ammi tace kaga sultan akan yawon nan hmmm babu ruwana idan ta haihu a titi, murmushi tayi tace nima abun dana gama fada mishi kenan ammi, toh Allah ya kiyaye ya dawo daku lafiya, amen ammi na bye suka juya suka huce.

  Driver yayi driving dinsu suna isa aka fara gudanar da taro da addu’a sosai lab din ya hadu ba iya lab bane an hada da clinic mai kyau kamar wani baban asibiti, anci ansha sosai a wurin taro yayi kyau.

   Tunda suka zo yana gefen ta sai yanzu ya tashi yaje wurin doctor fahad suna magana, a hankali yace ni na rasa maizan maka fahad in biya ka da wanan abun daka ke min, murmushi yayi yace ka bani angel dinka kawai shikenan, kallan shi yayi yace how did you know her.

  Murmushi yayi yace she’s my sister friend, ohh really, ummm, da gaske you like her, kai ya daga mishi yace tam shikenan magana ta huce.

   Jin kamar abu yana mata motsi yasa ta juya lokaci daya taji kamar an daure ta, suhana data lura da yanayin ta yasa ta karasa wurin tace maiya faru, cikin ta ta nuna mata, tsugunawa tayi tace mai yake miki kai ta fara girgiza mata tana hawaye da sauri taje inda suke, kallan ta sultan yayi yace what happened.

  Da hannu ta nuna musu inda shahida take ai bai jira tace komai ba ya huce a guje zuwa inda take, wani gumu ne a goshin ta sai juya kai take, doctor fahad da suka karaso wurin yanzu yace sultan dakko ta muje ciki, daukan ta yayi suka huce Allah ya taimaka a wurin akoi doctor mata na asibintin fahad nan da nan aka shiga duba ta.

  Sultan ya kasa tsaye ya kasa zaune fahad da kanshi ya kira ammi babu bata lokaci sai gata tazo asibitin, haka sukai ta zaune ana jiran haihuwar ta amma sam taba haihu ba sallah ce kawai take sa sultan yabar wurin, abu kamar wasa har washe gari shahida bata haihu ba, da yamma tayi kawai daddy yace a mata cs.

  A clinic din aka hada komai domin mata cs din sultan gaba daya ya fita a hayyacin shi su dad da mami all her family sunzo, lokacin da aka gama hada komai da sultan aka shiga cs din amma babu uwar da yake tabukawa sai aikin shafa kan shahida yama rasa ya zaiyi ji yake dama za’a iya dawo da ciwon kanshi amma babu dama.

  Haka aka mata cs aka fitoh mata da danta namiji koda aka gama sultan sam baibi ta kan baby ba shi kawai ta matar shi yake hanun shi yana nata har aka yi komaii a wurin ta ya zauna sam bai fita ba sai lokacin sallar asuba.

  Daya dawo wurin ta ya kuma komawa ya zauna, hannun shi na cikin nashi ya kwantar da kanshi lokaci daya yaji hawaye nabin fuskar shi kamar wani karamin yaro ya fara kuka sosai duk da kukan nashi babu sauti a hankali yaji hannun ta a kanshi tana shafawa.

  Dagowa yayi idon shi yayi ja sosai cikin karfin hali ta sakar mishi murmushi, murmushi yayi mata yana kara rike hannun ta, a hankali takai dayan hannun tana goge mishi hawayen nashi hannun ya rike yayi kissing hannun nata yace thank you princess thank you ina sanki i love you you’re my FOREVER FAVORITE princess ina sanki.

  Murmushi tayi a hankali tace you’re also my FOREVER FAVORITE ta fada hawaye nabin face dinta, goge mata hawayen yayi yace it hurts ko, kai ta daga mishi yace kiyi hakuri princess I don’t have anything to do about this but I wish ciwon a jiki na yake princess.

  Sun dade a haka kafin yaje ya amso baby da tunda aka haife shi sai yanzu ya taba shi ya kawo mata, murmushi tayi ta nuna mishi forehead din baby sanna ta nuna bakin ta lokaci daya ya gane mai take nufi dan haka yakai baby daidai bakin ta tayi mishi peck sann ta nuna shi,Shima tsugunawa yayi tayi mishi, a haka dai su mom suka shigo suka duba ta.

  A asibitin suka ci gaba da rayuwa saida sukai kwana 5 sannan suka huce gida, a part din ammi ta zauna sosai take shan kulawa saida tayi 3 weeks ranar tana zaune meerah tazo da baby Abutt da mijin ta ranar a gidan suka yini har dee din suna tare da sultan a part dinshi.

  Da yamma shahida na zaune meerah ta shigo da wasu kaya a leda, kallan ta shahida tayi tace wanann fa, naki ne ki saka, nayi me,yaya dee ne yace ki shirya yau ki dan fita, kinga nifa ba wani dadi nake ji ba, dan Allah ki shirya ba dadewa za muyi ba, haka ta shirya, suka fito ammi murmushi kawai tayi tace saikun dawo, suna fita tace ina ya dee din, zuwa za muyi mu same shi, nan driver ya dauke su suka huce.

  Dee kuwa tun dazu yasa sultan ya shirya suka fita sam sultan bai kawo komai a kanshi ba wani babban event suka shiga, kallan shi sultan yayi yace mai za muyi anan kuma, I want to visit a friend, okk, suka shi lokacin su meerah suna zaune a mota.

  Kiranta yayi yace are you ready, ehh kawai tace yace go, wani red kelle ya dauka ya rufewa sultan ido itama meera haka ta rufewa shahida ido ta dauki baby sannan ta bude motar ta fitoh da ita, kusan tare sukace mai yake faruwa jin muryar juna yasa yace princess, haka dai meerah da dee suka shigar dasu event din.

   Suna bude musu ido suka kalli kowa dake wurin their both family are here har ammi da suka bari a gida yanzu su mimi da sabir family kowa is here, an tsara wurin yay kyau sosai an saka hoton babyy mai sunan dad din shahida, suna ce mishi moha, daddy ne yay musu alama da dee da meerah ne suka tsara komai meerahhh data mikawa ammi baby shahida ta juya tayi hugging dinta kamar yadda sultan yayi hugging din dee.

  Canza direction akai shahida tayi hugging din dee shi kuma yay hugging din meerah, dago shahida dee yayi daga jikin shi yana goge mata hawayen da take, sanna ya kama hannun ta kamar yadda meerah ta kama hannun sultan suka kaisu wurin zaman su.

  Sosai akai shagali a wurin shahida tayi accepting gift kala kala golds, gida, mota, babu wanda bata samu ba, anyi bidiri meerah ya gayaci masu karatu har sultan ya basu tukuci na bandir din dollars per person.

  After event sultan ya gudu da matar shi kuma ya kashe wayar shi, aiko yasa mita wurin ammiii duk da bata same shi ba, aiko ranar ya gane Allah daya ne dan sam ba suyi bacci ba moha yayi ta musu kuka cikin dare.

 After 3 months week din bikin baby da al’amen anyi shagali kwana hudu akai ana biki sultan shi yayiwa baby komai kamar yadda yake yiwa sauran sisters dinshi biki iya biki bikin yan gata har gift din ticket din honeymoon dee ya basu Allah ya taimaka dama suna cikin hutun school.

 After some years 

Rayuwa tayi nisa wanda a yanzu shakarar moha 10 kuma har yanzu sau daya shahida ta kuma haihuwa because cs aka kuma mata rayuwa suke cikin farin ciki da kaunar juna a lokacin baby tana da two baby’s itama meerah kuma uku gare ta.

  A shikarun anyi bikin diyya da Assad, angel da fahad, duk uban shekarun da aka dauka har yau usman bai dawo ba sam, yau suna zaune shahida da sultan sabrin mai sunan mom tana kwance kan sultan yace yau babu shopping ne, da sauri sabrin tace za muje appa.

  Okk let me dress you up yana tashi ya huce da ita dakin ta nan shahida ta huce da moha dakin shi shima danta shirya shi suka gama shiryawa suka shiga mota driver yana driving nasu.

  Suna isa suka huce wurin teddy dan siyawa sabrin sabrin akoi surutu, da karfi tace shahida, gaba daya juyowa sukai suka kalle ta, wata yarinya da age mate dinta ce ta juya tana tafiya da wani mutun sanye da pcap da alama baban tane.

  Sabrin tayiwa sultan alamar ya sauke ta, sauke ta yayi ta kuma kolla kira shahida, lokaci daya yarinyar ta juyo tace sabrinnnnnnnn ta fizge hannun ta daga na mahaifin nata ta taho a guje tayi hugging dinta, tsale suke da farin cikin ganin juna.

  A hankali shahida ta daga kai sukai ido hudu da usman da yake sanye da p cap, da hannu ta nuna shi tace ya us man a rarabe, kallan ta yayi sai kuma ya juya, da sauri tabi bayan shi tace ina zaka je ina zaka tafi.

  Ya usman some people don’t deserve ka rabu dasu yes mun maka laifi meye laifin diyya mama, dad mai yasa zaka tafi ka barsu, a hankali ya juyo ya kalle ta cikin idon ta da yake zubar da ruwa ya girgiza mata kai yace no don’t cry shahida if not idan na tafi for now I will never come back.

  Goge hawayen tayi sultan ya karasa inda yake ya rike hannun shi yace why usman mai yasa ka tafi mai yasa, mai zanyi idan na zauna mai kuke so nayi na kashe kaina a tunanin ka da ina garin nan zan kasance cikin salama i will never bazan taba zama cikin farin ciki ba.

  Shahida ya kalla yace princess kamo yaran nan mu huce yana jan hannun usman, wuri suka samu suka zauna sultan yace usman ina kaje, kai ya girgiza mishi yace usman kayi hakuri for what i do to you, karka damu sultan haka rayuwa take wani baya taba auren matar wani ni ban taba kullatar ka ba.

  Sun dade a zaune suna bawa juna hakuri kafin shahida tace a lallai sai sun kaishi gida komai zai faru, no shahida bazan je gida ba, no you have to tayi ta rokan shi suna isa suka shiga ranar diyya tana gida.

  Mama farin ciki ta shiga wanda bata taba tsammani ba ita ta cire dawowar shi a zuciyar ta, nan ya basu labarin ranar daya tafi kasar ya bari gaba daya sai after two years ya dawo nan yaje aka daura mishi aure da marry, ya nuna musu yarinyar su da suka haifa.

  Sun dade basu garin sai year back ya dawo, a hankali ya kalli sultan yace ina umar, shiru yayi sai mama ce tace mishi umar Allah ya mishi rasuwa baka dade da tafiya ba, kallan ta yayi lokaci daya hawaye ya fara bin fuskar shi, sosai yayi kuka kuma ya nemi yafiyar iyayen shi nan suka bashi labarin rayuwar da sukai a baya.

  Ranar a gidan su shahida suka yini sai dare suka watse har usman din yacewa mama gobe zai kawo mata matar shi dad yayi farin ciki sosai sultan saida ya kuma neman yafiyar usman sanan suka huce.

  Suna zuwa gida bayan sun kwantar da yaran su ta huc tayi wanka, lokacin data shigo dakin yana zaune gaban mirror, kallan ta yayi ta mirror yadda take kallan shi yace princess, dauke kai tayi ya dawo inda take a hankali yace did you still love usman.
 
  Rufe mishi baki tayi tace so kake mala’ikun Allah su tsine min, toh what about the look and you look worried, babu komai kawai ina tunanin rayuwar mu ta baya ne too much has happened, murmushi yayi yace ummm haka ne princess kowa da kike gani a cikin rayuwar shi akoi kalubale kala kala.

  Kai ta daga mishi yace kowa da irin kaddarar rayuwar shi, murmushi tayi tace kamar yadda tawa kaddarar ta makale maka, murmushi yayi shima ya janyo ta jikin shi yace ummmm haka ne princess kaddarar mu a tare take har abada you will always be my number one.

  You’re my forever favorite princess, murmushi tayi tayi kissing kumatin shi tace nima you’re my forever favorite.

  Wasu masoya suna son juna da zuciya ɗaya, amma duk da irin son da suke yi wa juna, ba a rubuta ƙarshen labarinsu da zama tare ba. 🥺💔

Abu mafi ciwo ba wai ka rasa wanda ba ya sonka ba ne… a’a, shi ne ka rasa wanda yake sonka, wanda yake fahimtar zuciyarka, wanda kake ganin rayuwarka ba za ta yi kyau ba tare da shi ba… amma duk da haka, rayuwa ta ƙi ba ku damar kasancewa tare. 😭🥀

Wani lokaci, soyayya ba ta ƙarewa saboda an daina ƙaunar juna ba. Tana ƙarewa ne saboda akwai abubuwan da suka fi ƙarfin son da suke yi wa juna. Sai su zama baƙi ga juna, alhali zukatansu har yanzu suna tuna duk wani lokaci da suka taɓa zama farin cikin juna.

Abin takaici, ba kowane masoyin da ya cancanci zama tare da kai ne zai zama rabonka ba. Wasu mutane Allah yana kawo su rayuwarmu ne domin su koya mana yadda ake ƙauna, yadda ake haƙuri, da kuma yadda ake rayuwa da ciwon rashin wanda zuciyarmu ba ta taɓa son rasa wa ba. 💔🥹

Perhaps, in another life, under different circumstances, they would have been each other’s forever. But in this life… they were just two hearts that loved each other in a story that was never meant to have a happy ending. 🥀😭


Alhamdulillah ya Allah na gode maka da ka bani mata mai hankali da kamala ya rabbi ka biya ta da gidan aljannah, Ameen my man kaima Allah ya biya ka da gidan aljannah.

Alhamdulillah Alhamdulillah ala kullu halin🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉
 
 _nagodewa Allah SWA daya bani damar kammala wannan littafi cikin koshin lafiya, ina godiya ga mosoyya na na gode ga soyayyar da kuka nuwa ga wannan littafi, idan akoi wanda na batawa rai ta sanadiyar wannan littafi ina neman yafiya Allah yasa mu dace yasa mu cika da 
imani 🙏🏻🙏🏻🙏🏻.

   Da fatan kunji dadin wannan littafi, Allah ya kara hada saduwar mu wani lokacin zanyi kewarku sosai da sosai sisters 👯‍♀️ ❤️


Da fatan kunji dadin novel dinnan ina jiran comment dinku da shawarwari ku inda kuka ji dadi da abun da bai muku dadi bah 

Ga masu bukatar advert zaku iya min DM ta number ta ***.