RU'UYAA (The dreams we never lived)
43. ... Graduation...🖊️
by @autum17
43. ... Graduation...🖊️
Khalil yake takun shi cikin natsuwa kamar babu mutum a jikin shi,har dariya ma abun yake bashi
Sai kuma ya tuno hirar su akan Abeedah,ya girgiza kanshi
He's has never fallen in love..sannan alaƙar shi da Abeedah ƙawance ne kawai
She's the most genuine person a rayuwar shi bayan Roman..and he likes her alot ba so na soyayya ba
kallon Diyaam yayi data haɗe fuskarta da ƙirjin shi,she look like a little red velvet saboda pajamas ɗinta
bada daɗewa ba ya kawo gida,a maimakon ya kaita ɗakin su sai ya wuce da ita sashen shi
Ɗayan ɗakin dake sashen shi ya buɗe ya kunna ƙaramar wutar ɗakin ya sauke ta saman gado yaja mata blanket ya rufe
ya kunna Ac,yaja da baya yana kallon ta na ɗan lokaci kafin ya kashe wutar ɗakin ya fita
tana jin ya rufo ƙofa ta yaye blanket ɗin ta tashi zaune tana kaɗa rigarta tsabar yanda jikinta ya ɗau zafi
Tun daga sanda ya sunkuya ya ɗauke ta a beach ta tashi daga baccin,sanda ya sauke ta saman gadon yayi mata runfa yana rufa mata blanket ta riƙe numfashinta, trying so hard not to make any movements
Kwantawa tayi tana kallon ceiling da murmushi a fuskar ta
'' wannan ne ɗakina idan munyi aure!" ta faɗa a fili murya ƙasa tana dariyar kunyar abinda ta faɗa
____
sanda na farko tsakar dare banga Diyaam ba amma da safe sai naganta kwance kusa dani,koda na tambaye ta ina ta tafi bata bani amsa kai tsaye ba sai kame kame da take
Taɓe baki nayi, idona ya sauka akan rose hair clip ɗin dake gashinta,taɓawa kawai nazo inyi ta daka uban tsalle tare da rufewa da hannunta tana zarar min ido kamar nace zan ƙwace
Naja baya tare da ɗaga hannu..i come in peace
A hanyar mu ta zuwa sai da muka bada sadaƙa..nayi sallar dare da kuma addu'oi da yawa akan wannan jarabawar... Diyaam kuwa babu abinda take sai yaƙar haƙori kamar gonar auduga
sanda naga tambayoyin idona sun kusa faɗowa...na taune lips ɗina hawaye suka ciko idona..ban san ko amsa ɗaya ba...kowa sai rubutu yake banda ni,daga lokaci zuwa lokaci invigilators ke leƙowa suna faɗa mana sauran lokacin daya rage mana..naji wani irin abu a ƙasan ciki na...share hawayen nayi ina tattaro duk wani abu dazan iya tunawa game da wannan topic ɗin amma abu yaci tura,,,in rubuta,in soke haka nayi ta yi har ya rage saura minti talatin mu gama ..sai lokacin naɗan fara tuna abubuwa
Wani daga cikin invigilators ɗin yake tayima masu rubutu suna kansilewa faɗa har ya kawo wurina..
'' eweyyy! see diz girl ooo? wetin b diz?'' ya ɗauki paper ta yana jijjigawa a gaban aji...ya dawo yana min ihu a kai '' be looking at me with your eyes wey b like winch own...'' ya wurga min paper a fuska...hawaye suka dinga sauka kamar ana koro su...idona suka yi ja naji kamar in fice in bar masu exam hall ɗin
Duƙawa nayi na ɗauki paper ..na kasa cigaba da rubutun har lokaci ya ƙare...ana kirana nayi submitting na fita da sauri ko diyaam ban jira ba na kama hanya ina tafe ina kuka...abun har ya zame min jiki...duk danayi addu'a da komai..akwai ƙoƙonto da yawa raina...meyasa nima bazan zama kamar masu cewa 'nidai na barwa Allah komai ba,duk abinda yayi shine daidai' ba?
meyasa nake damuwa koda yaushe? meyasa komai yake taɓo ƙahon zuciya ta?
farar motar data tsaya gefena na kalla,Khalil ne ya fito daga back seat saye da baƙaƙen kaya.. shigar Roman...
'' Oh...Kitten what happened?" Ya tambaya yana kallona ko akwai inda naji rauni... girgiza kaina nayi..bazan ma iya faɗa mashi cewa tsoro na kada ya kasance addu'a ta bata karɓu ba kuma sai na sake maimata SS 3
'' oh okay...zo mu tafi gida!" Ya riƙo hannu na,nan ma girgiza kaina nayi '' bana so in tafi gida yanzu...'' na share hawaye da suka jiƙa mun fuska...
'' bari in kaiki wani wurin daban ...'' ya buɗe min ƙofar na shiga ya zagaya ya shigo driver ya cigaba da tuƙa mu yana bashi direction har muka kawo wani park...
Parking driver yayi a parking lot bayan an siya ticket daga bakin gate...fitowa yayi ya buɗe min ƙofa na fito...nayi wuƙi wuƙi da ido...ƙaton fili ne,mai ɗauke da hakukuwa masu laushi...wani sashe na wurin akwai masu ƙwallo...wani daban wurin wasan yara..a wani wurin kuma masu sayar da abubuwa ne harda ice cream...ga bishiyoyi birjik
babu rana amma kuma babu hadari...hakan ya ƙara ma wurin tasiri na musamman...can can akwai wurin da ake wasar takalmin tayu da inda ake wasa da kala da alamu wani abu ake celebrating...
abubuwa da yawa..kowa sai harkar gaban shi yake...kowa na murmushi banda ni...ban wani ji raina ya saki ba...
muna tsaka da tafiya wasu yan mata suka tare mu suna gaisawa da Khalil, Allah yasa musulmai ne yan kano hakan yasa bana buƙatar yin tsalle in shiga tsakanin su gudun a rungume shi... Duk da shigar su sai a hankali
'' wannan yarinyar fa?yar aiki ce?" Ɗaya daga cikinsu ta tambaya
'' tafi kama da irin yaran nan da basu da gida...mema ake kiransu?" Wata daga cikin ukun ta tambaya da rainin wayo tana yamutse fuska
'' almajirai..yeah that's the word,kun san Abraham da tausayi na tabbatar ya ganta tana yawo ne shine yace bari ya ɗan kawo ta ta shaƙata!" Ƙasa nayi da kaina,hawaye suka taru a idona....kallon da suke bina dashi cike da ƙasƙanci...
'' be respectful will you?!" Khalil ya ɗaura hannunshi a kafaɗa ta ya jawo ni kusa...fuskar shi ba walwala...yan matan suka kalli juna kafin suka kalle ni wata tace
'' come on,kada ka faɗa min saboda wannan idon nata da suke kamar na mayu kake tare da ita...ina nufin akwai classic ladies kamar mu,mai xakayi da wannan trash ɗin?" doguwar cikin su ta faɗa tana harare Harare
'' kallonta kaɗai yana jima idona ciwo pls Abraham.. she's so ugly!" Wata daban ta faɗa
'' Then look elsewhere,and she's beautiful.. atleast a idona tafi kowace cikin ku!!" Maganar shi tasa na ɗago idona dake kallon ƙasa suna tsiyaya na kalle shi,shima kalllona yake da kulawa kamar nice mafi daraja a idonshi...ya share min hawaye na
'' yanzu ku gafarce ni akwai inda zanje!" Yaja ni muka bar wurin,hakan da yayi ya ɗumama zuciya ta..ban taɓa tsammanin wani zai ɗauke ni da muhimmanci har haka ba...ya kare ni a gaban su,nasan maganganun ƙanana ne amma a wurina suna da girma da daraja...
Hawayena a wannan lokacin badan abubuwan da suka faɗa bane sai dai dan na fahimci cewa nima akwai wanda ya damu dani...dena tafiyar nayi...idona ƙasa...hakan yasa shima Khalil tsayawa gabana '' kiyi haƙuri akan duk abinda suka faɗa...da maza ne da mun fafata!"
Murmushi nayi tsakanin hawaye...yanda yayi maganar da kuma expression ɗin shi yasa naji rauni...share min hawaye na yayi sai kuma ya jawo ni hugging me tight...nima na ƙanƙame shi,ban yi tsammanin zan taɓa iya yin hakan ba...
'' meyasa kike kuka?" Ya tambaya
'' bayan Jay d,ban yi tsammanin wani zai damu dani ba har ya kare ni ba... I'm grateful to you...'' dariya yayi ya raba jikinmu'' yanda kike kukan nan ya kamata in siyo kwalba dan in dinga tara hawayen ki a ciki!" Lumshe ido nayi...one last time ya ƙara goge min fuskata da lallausan hannun shi...
section ɗin masu wasa da kala na nuna mashi bayan ya tambaye ni inda nake so mu fara zuwa...sosai wasar su ta watsi da kala ta burgeni...ina tsaye ina kallo bakina ya kasa rufuwa '' kitten...'' Juyowa nayi Khalil ya shafa min kala a fuska yanda na zaro ido yasa shi sakin dariya
Nima kala na damƙa a hannu na...na shafa mashi a fuska yayi buɗun buɗun..daga nan muka haɗe da sauran masu wasa... yake bina da kala a hannun shi ina gudu....
'' ki tsaya mana....'' wai in tsaya kai...kafin in sani uniforms ɗina sun koma rainbow, shima kan shi yayi buɗu buɗu da kala da badan baƙaƙen kaya ne jikin shiba...
wurin da ake wasa takalmin tayu muka tafi daga nan...nida nayi tsaye daga gefe ina kallo ya saka takalmin ya shiga cikin rukunin masu wasar tserarra...kuma yazo a na farko...ina tsalle ina clapping...munyi wasanni da yawa harda wanda ake ɗaure ma mutum biyu ƙafafa ɗaya ɗaya ayi yar tserarra...
wurin ƙarfe shida muka zauna a ɗaya daga cikin bencin dake wurin...hannu na riƙe da ice cream ina kallon mutanen dake guje guje Khalil zaune daga gefe na ya kafe ni da ido kamar ya samu TV
Juyowa nayi na miƙa mashi ice cream ɗin da hannu biyu '' kana sone?" girgiza kanshi yayi bakin shi a ɗage '' toh kada ka shaƙeni da idonka inji Romo...'' mu biyun mukayi dariya nace '' na rasa taya ido zai shaƙe mutum...ko suma suna da hannu ne?"
'' it's a metaphor...'' taɓe baki nayi '' nasan wannan ma figures of speech ne amma ban san meye shiba kaji?"
'' kin lura da cewa yanzu idan nayi maki magana da turanci kin dena cewa ' nifa bana so anamin magana ana haɗawa da turanci!" na ɗan waro ido na yan sakanni kafin nayi dariya sosai kamar wacce ta zauce yake bina da murmushi kawai...
'' yanzu ai naɗan iya turancin amma ba can can ba!"
'' hmmm!" yayi humming...mukayi shiru
wayarsa ce tayi ringing yayi excusing kansa
Ina bin bayan shi da kallo..naji an zauna kusa dani, na juyo naga wani gaye da wata bugaggar fuskarshi can duk ta kwaye tsabar bleaching... ya washe min bakin shi da haƙoran suka gama dafewa
'' yan mata mai idanun mage...'' na ɗaure fuska,na rasa dalilin dayasa idona suka shama kowa kai...
na tashi zan bar wurin ya riƙo hijabina '' tsaya mana magana nake fa....'' ya furta tare da miƙewa..yana da manyan ido da sukayi ja kamar gauta...nidai bai min kama da mutanen kirki ba..tsoro ne ya ɗan shige ni ganin yanda yake kalllona...kuma mutane hankalin su baya kanmu ga Khalil yayi nesa kaɗan
'' wai Mey haka dalla sake min hijabi!" Nayi maganar ina ƙoƙarin ƙwace hijabina... taune leɓenshi yayi yana matsowa kusa tare da naɗe hijabin a hannun shi...na shiga tashin hankali
'' w...wa..m..ye...ha..k'' nayi maganar rarrabe hawaye kwance a idona '' magana kawai nake so muyi..Kinga mota ta can!" ya nuna min wata jar mota parke a gefe
'' suna na HASSAN...zo muje ba daɗewa zamuyi ba!" Kallon sashen da Khalil yake nayi,kamar wacce aka ɗaure ma baki na kasa kiran shi
'' nidai ban zuwa ka rabu dani dan Allah..'' nake jan hijabina da yake naɗewa a hannu
'' hmmm...yanda kike magana har tsumani yake..'' ya faɗa yana lumshe ido...ni ban masan me hakan ke nufi ba,burina kawai ya rabu dani
Hannunshi dake riƙe da hijabina aka wazga da ƙarfi kafin naushi mai nauyi ya sauka a haɓar shi dayasa shi baya baya kafin ya faɗi ƙasa warwas Idonshi waje
Babu abinda Khalil yake sai huci
Jan hannu na yayi muka bar wurin...da alamu yayi fushi ko kallona bai yiba har muka shiga motar,wannan abune da bai taɓa faruwa va
Jikina ya ƙara yin sanyi sanda muka iso gidan ya fita yayi tafiyar shi batare da ya kalle niba...nayi tsaye a wurin...kafin kuka mai ƙarfi ya ƙwace min...
naji duniyar tayi min faɗi fiye da koda yaushe..Meye laifina?
Babu kowa a parlor na shiga elevator kafin ta rufe Roman ya shigo ya tsaya can gefe bai kalli inda nake ba, fuskarshi a matuƙar haɗe,ga wani scar a gefen wuyan shi..mara zuciya
Jiki ba ƙwari na fito daga elevator zuwa ɗakin Diyaam..tana ganina ta miƙe tayo kaina take tambaya ta mai ya faru...kasa amsawa nayi na cigaba da kuka...
Kwanakin da suka biyo baya Khalil ya cigaba da share ni,zan iya rantsewa wannan shine mafi tsananin lokaci a rayuwa ta...kusan kullum sai nayi kuka,na dena fitowa sai in takama dole... har yanzu na kasa fahimtar me nayi mashi...
Ina cikin wannan yanayin naji ana announcing wai aure za'ayi ma manya maxan gidan harda Roman a ciki wai za'a bashi Mardiyya yar Hajiya Momma... Seraphina ba ƙaramar hauka tayi ba
Nima kaina ji nayi kamar ina nutsewa a cikin ruwa...
Harda zazzaɓi nayi da naji wannan maganar...da daddare duka an hallaro dining... Mardiyya babu abinda take sai murmushi kamar gonar auduga haka ma Hajiya Momma...fuskar Farzan kamar hadari ya tsuke ta tamau ba sauƙi, Roman ne na ƙarshen zama a table ɗin
Babu abinda ake sai maganar bikin da za'ayi bada daɗewa ba... hankalina ba ƙaramin tashi yayi ba musamman dana ga shi bai da ja akan batun..kamar in mashi ihu a ka...maƙogarona sai kai kawo yake na kasa haɗiye koma meye ya tsaya min a wurin...silale wa nayi nabar wurin zuwa parking lot...
Matan gidan dai kowa ta ciki na ciki basu wani yi farin ciki da wannan abu ba,alhazawan kuma su gani suke wannan hanyar zumunci zai ɗaure,
ajiye cokalin shi Roman yayi yana kallon Hajiya Momma dake maganar shida Badariyya da sauran ma su ƙara sasanta kansu yace '' yaushe nace na yarda da wannan auren?" wurin yayi tsit! Badariyya ta kalle shi, Seraphina da daƙyar take tura abinci taji wani irin sanyi ya saukar mata a zuciya
'' ban gane ba..dama ra'ayin ka ake nema?" Hajiya Momma tayi maganar tana zare mashi ido...
su Alhaji suke bin Roman da kallo haka ma sauran waya'nda ke wurin..mayarda kallon shi yayi akan Alhaji Mansir slowly yace '' na gode kawu,amma babu wannan tunanin a raina...''
Alhaji Mansir ya kalli yan uwan shi kafin ya dawo da kallon shi akan Roman '' meyasa? Mardiyya'r ce batayi maka ba ko yaya?"
'' eh,sannan bana ra'ayi '' yayi maganar straight forward dayasa kowa kallon shi
'' yanzu yar tawa zaka kalla kace bata yi maka ba? baka da mutunci ko? Toh wallahi ko mutuwa xakayi sai an ɗaura auren nan!"
Miƙewa Roman yayi yana kallonta yace '' zamu gani...da in haɗa zuri'a dake..Gara na mutu a gauro!" Kamar an sauke Bomb... Hajiya Zeenatu da Hajiya Wareesha suka kawar da kawunan su gefe suna dariya...Hajiya Hafsah fuskarta babu wani expression akai...
Hajiya Ruƙayyah ta taɓe baki... Mardiyya idonta suka yi jawur kamar garwashi.. Farzan yayi baya a kujerar shi yana kallo dajin daɗi...Khalil kuwa kanshi ya cika da tunani fal Bama jinsu yake ba...
'' Roman...meyasa kai baka da tarbiyya baka da mutuncin kake iya faɗawa kowa magana yanda kaga dama?" Alhaji Hussein ya faɗa a zafafe
'' da ace ka sauke nauyin ka a matsayin uba,da ban kasance haka ba PADRE!!!"
yana faɗar haka yasa kai ya fice yabar su da baki sake... Alhaji Hussein ya tsani wannan PADRE ɗin da Roman ke kiranshi dan Roman bai ɗauke shi a matsayin uba ba so he uses that word Instead ...ƙirjin shi sai sama da ƙasa yake.. idonshi sunyi ja
Alhaji Hussein yabar wurin...babu wanda yace komai...amma kuma table ɗin bai kasance the same ba...
Tsaye nayi a harabar gidan da hasken wata ya haskaka..na rasa inda zan kama...sama nayi da kaina..ina jan dogon numfashi..hawaye suna fita daga gefe da gefe...kamar inyi ihu...ƙasa nayo da kaina zuciya ta tayi nauyi sosai...sai kuma na durƙusa wurin na saki kuka...
Da jan jiki na shiga tsakanin motocin dake pake a wurin ina tsananin kuka batareda na damu da duhun dake ɓoye da abubuwan da zasu iya cutar dani ba..
can naji takun mutum...leƙowa nayi daga inda na ɓoye na hango Roman saye da baƙaƙen kayanshi kamar kullum..gashi tufke a tsakiyar kai..yanda yake tafiya ya bambanta da kullum...zuciyata ta fara bugu da ƙarfi... nunfashina na fita da sauri sauri
nayi shiru ina sauraren bugun zuciya ta... hawa saman mashin ɗin yayi tare da kifa kanshi a sama na tsawon lokaci..ko yayi bacci ne?
jan jiki na fara yi zuwa wurin mashin ɗin..bayan na iso na miƙe ina leƙa fuskar shi... ganin bai motsa ba yasa na ɗauka bacci yake yi...sai da nayi ƙoƙarin taɓa jan abun nan ya damƙe hannu na..hakan ya firgita ni ya ɗago kanshi idonshi straight cikin nawa...'' me kike yi anan?" yayi tambayar da ƙatuwar muryar shi data sa nayi fitsari kaɗan cikin pant ɗina
'' uh...d..dana...UHM..''
'' uh..d...meye haka? You like pretending to be innocent.. I don't trust you one bit! I kissed you once and now you can't get over it?"
Ya sakar min hannu tsumammun idonshi na kalleni daga sama har ƙasa...
nikam sai nayi sake da baki jin abinda ya faɗa wai na kasa mantawa da kiss ɗin shi amma wannan mutumin
'' ni nace haka?" nayi maganar da ɗaga murya haushin sa na cika Ni
''.your actions did! kinga...'' ya dakata tare da zaro pendant ɗin shi ya nuna min
'' idan ma akwai wani abu a zuciyar ki gara ki yayyafawa kan ki ruwan sanyi cuz I already love somebody else!"
yayi maganar fuska a tsuke,naji kamar duniya ta tayi summersaulting kafin ta kife
Idona suka sake cikowa da hawaye
'' ai nima ina da wanda nake so! k...kawai kana ban tausayi ne!"
nayi maganar batareda tunani ba,gani nayi ya sauko daga saman mashin ɗin shi eyes blazing with fury
Kafin inyi ta kaina ya damƙo hannu na ya murɗe shi ta baya,ƙirjina ya haɗu da nashi
Voice devilishly cold yace '' idan kika ƙara yin amfani da 'tausayi' cikin maganar ki dani,i will chew your lips and swallow them raw!"
sosai ya bani tsoro har naji fitsari na yana zirara,numfashina ya ɗauke,naso in mayar mashi da martani amma na kasa saboda yanda naji shakkun shi ya dirar min ga hannu na dake ciwo
can ya sake ni batareda ya sake kallona ba ya haye mashin ɗin shi ya fita daga gidan
'' mugu kawai Allah ya isa ban yafe ba!" Na faɗa ina kuka sosai kafin na juya na koma ciki da gudu
Cikin gida Hajiya Momma sai sababi take wai Roman bai isa ba... Seraphina ke kare shi kamar rayuwarta...saura kaɗan ta karɓi duka daga kitiɓeɓen hannun Hajiya Momma... Hajiya Wareesha ta jaye ta..abu yaso ya zama faɗa tsakanin matan gidan sai da Alhaji Mansir ya tsawatar
Sauran ranakun haka suka biyo baya... Khalil ya cigaba da share ni.
jarabawar mu saura ɗaya mu gama... hankalina a tashe yake...rayuwa ta a hargitse... kullum jan jiki kawai nake ƙarfina ya kusa ƙarewa....
Da sassafe kafin in wuce makaranta na fara biyawa sashen Khalil dai dai ya fito daga ɗakin shi saye da ƙananan kayan ciki
Tsayawa yayi da ya ganni..nayi ƙasa da idona murya a sanyaye nace '' na maka laifine Khalil?"
'' A'a!"
'' meyasa kake share ni?" idona suka ɗau zafi hawaye suka ciko su taf
'' ba komai...''
'' Oh...'' na gyaɗa kaina na haɗiye baƙin cikin daya taso min na juya na fita...halin nasu na masu kuɗi zai nuna min bayan yasa na saba dashi ko? Ba matsala...ni Abeedah zan nuna mashi cewa nasan darajar kaina...
Da ƙarfe huɗu da rabi muka gama jarabawar ƙarshe data kasance math,nake ji kamar inyi kuka saboda damuwa...duk da kowa na murnar gama jarabawa ana sign out ana wasa da kala...na laɓe gefe ina kallo...idan fa saina maimaita aji bayan duk wannan murnar?
Share hawaye nayi daidai su Jay sun ƙaraso
'' yau ranar farin ciki ce Bee!" Jay d ta faɗa tare da shafa min kala...ta jawo ni muka shiga cikin yan ajin mu,muna wasa da kala tare da ɗaukar hoto...da gaskiyar ta..me zai sa in ƙuntata kaina akan wa'yanda basu damu dani ba?
sakin raina nayi muna murnar...duk kowa uniforms ɗinsu babu inda ba'ayi signing da maka ba...wasu suka zo paint irin wanda ake fesawa kamar turare
'' Congratulations!!!!'' ake ta faɗi nan da can...
Bayan wani lokaci Jay d tace in Zo in raka ta tayi fitsari,
a maimakon muyi hanyar toilet tajani zuwa wani wuri da ba mutane sosai ta juyo tana kallona
Nima ita nake kallo
'' Girl spill the beans! naga yanda duk kika bi kika damu. Of course nasan kin damu da result ɗin jarabawa but beyond that meya faru ne? Duk kin canja"
Ta matso kusa tare da riƙon hannu na cike da damuwa,tun kafin in ɗauke idona gefe hawaye suka fara wanke fuskata
Kafin na fashe da matsanancin kuka,ta rungume ni tana lallashina kamar yanda uwa ke lallashin ya'yan ta
Ya Allah what would I ever do without Jay d?
Sai dana gama kuka na ta tabbatar na nutsu sannan ta tambaye ni meya faru
naja dogon numfashi kafin na faɗa mata komai harda kiss ɗin da Roman yayi min da kuma abinda ya faɗa jiya sai Khalil da yake share ni shima
'' i feel overwhelmed,ban san yanda zan yi ba... ina so in bar komai in fara daga farko amma sai koda yaushe nake ji kamar akwai abinda yake riƙe ni i don't know what to do!"
Ta sake rungume ni,her warm comforting hugs '' it's okay,ba dole sai kin san abinda zakiyi ba next saboda kina dani Bee...you don't always have to carry it alone koma meye zaki iya faɗa min kin ji! I'm and will always be there for you
Now and forever!"
ta share min hawayen dake sintiri a fuskata
'' Oh Jadeedah ya xanyi idan babu ke ''
'' You live on Abeedah!" Ta amsa
mukayi wa juna murmushi