PAGE 29
SAWU BIYU
Khadijah Sulaiman
YOTA
Book 1
Page 29
Sadauki ya zubawa takardun ido yana sake nanata abinda ke rubuce,jin kanshi na neman hargitsewa ya sa shi dafe kai ya ce"Ya Allah".
Bai sake rintsawa ba har asuba,yana idar da sallah ya hau shirin office.
Bilal dake zaune yana shan tea ya bishi da kallo,a ƴan kwanakin nan ya kasa fahimtar abokin nasa,gani yake kamar akwai abinda yake ɓoye masa.
Bayan ya gama sa socks ya sa booth ya ɗago ya ce"idan ka gama ƙare min kallo ina waje".
Bilal ya watsa mishi harara ya ce"in kalle ka in gane me?ga ƴan mata nan kala kala a gari in rasa abin kallo sai ɗan uwana namiji".
Bai kula shi ba ya fita,a mota ya same shi har ya kunna yana addu'a,bai ce komai ya buɗe kusa dashi ya zauna .
Har suka isa office babu wanda yace komai a tsakaninsu.
Yana shiga office ya tarar da basket saman table,ya ɗan bi basket ɗin da kallo ya taɓe baki.
Bai daɗe da zama ba Bilal ya shigo,ya ja kujera ya ce"what do we have here?"
"Idan kana so ɗauka ka tafi".
Bilal ya ce"ya za'a yi in ɗauki abin masoya?sai dai in ɗanɗana kawai".
Sadauki ya ce"kai ma ka san babu abinda zan yi dashi,ɗauka ka tafi".
Bilal ya ɗauka don ya san idan bai ɗauka ba wasu zai kaiwa a waje.
Yana ganin fitarsa ya ajiye pen ɗin hannun shi ya fita,direct office ɗin jiya ya koma.
Bayan sun gaisa ya ce"Colonel Yaqub Tafida ya rasu a operation right?zan iya sanin sunayen team ɗin shi?"
Bai yi musu ba ya miƙe ya duba file ɗin ya mika mishi,sai da ya isa office sannan ya buɗe.
Ɗaya bayan ɗaya ya dinga bin sunayensu da kallo,su goma ne a team ɗin.
Colonel Yaqub Tafida,shi ya jagoranci Operation ɗin saboda shine mai highest rank a cikinsu,sojoji guda bakwai,mai kula da lafiyarsu guda ɗaya sai Captain Barau.
Gabaɗaya babu mai rai a cikinsu sai Captain Barau da ya zama Colonel a yanzu.
Ya tsurawa sunan Barau ido kafin ya sauke wani wawan ajiyar zuciya,ya cigaba da duba file ɗin.
Mutane bakwai suka rasu a ranar ciki har da Colonel Yaqub Tafida,sai mutum biyu da suka rasu a hatsarin mota bayan operation ɗin.
Ya hargitsa suman kanshi jin ciwon kan dake taso masa sama sama.
**********
The Dark Network
Ɗakin bai taɓa cika irin na ranar ba,duk wadda ka kalli fuskarsa za ka hango wani irin tension mai wuyar fassarawa.
Su kusan goma sha biyar ne a ɗakin ko ma fiye,sai babban kujera dake tsakiyar wurin,Chief ya zauna kusa da kujerar kanshi a ƙasa.
Ƙaramin kofar dake wurin aka turo da saurin gaske,wasu jibga jibgan bouncers guda biyu sanye da baƙaƙen kaya suka fara shigowa,daga bayansu wani ne sanye da manyan kanya da babbar riga ya nufo wurin fuska ɗaure,duk suka miƙe da sauri.
Ɗaya daga cikin bouncers ɗin ya ja kujerar da zai zauna ya goge mishi ya koma bayan shi ya tsaya.
Sai da ya zauna sannan suka haɗa baki gabaɗaya suka ce"Elder !".
Ɗaya bayan ɗaya ya gama ƙare musu kallo sannan ya ce"sit".
"Thank you Elder".
Bayan kusan minti biyar ya sauke numfashi ya ce"me ke faruwa,wani labari na ke ji haka?"
Duk su kayi tsit,ya buga table ɗin a fusace ya ce"will you open your mouth and say something?what the hell is going on ?"
Chief ya sauke numfashi ya ce"nothing serious Elder....?"
Da mamaki Elder ya ce"nothing serious?,could you hear yourself Chief,ƙaramin yaro na ƙoƙarin tono abinda ke binne za ka ce min nothing serious,are you for real?"
Ya karasa maganar da ƙarfin gaske har sai da ɗakin ya amsa.
"Ina son wani ya buɗe baki ya sanar dani abinda ke faruwa".
Wani daga cikinsu ya miƙe yayi gyaran murya ya ce"Captain Sadauki ya fara bincike a kan case ɗin Colonel Yaqub Tafida,wanna shine abinda ya faru daga jiya zuwa yau Sir".
A nutse ya dinga bubbuga hannun shi a kan table ɗin,yayi guntun murmushi ya ce"kun san abinda hakan ke nufi?"
Duk suka zuba mishi ido,ya ƙyalƙyale da dariya kamar taɓaɓɓe ya ce"Yaqub Tafida ya tafi,wani na son ɗorawa daga inda ya tsaya?
Shi kan shi Tafida sarkin taurin kai yana ina,na ce yana Ina?"
Ya buga musu tsawa gabaɗaya.
Scorpion ya ce"an gama dashi Elder,ya zama labari".
Ya gyaɗa kai ya ce"good,balle wannan ƙaramin alhakin,ina son binciken shi ya tsaya iya haka,idan ba haka ba zai jefa kansa cikin masifa da bala'i".
Ya juya ya kalli Chief ya ce"a tura mishi gaisuwa,gaisuwa mai rikitarwa".
Gabaɗaya suka haɗa hannu wurin cewa"IGWE".
*************
Ƙarfe huɗu ya tashi a office,sai da ya tsaya yayi Sallah a Headquarter sannan ya kira Bilal suka fita.
Dai dai wurin wani roundabout Bilal ya hango mai fura da nono,ya juya ya kalli Sadauki ya ce"tsaya Captain,bari in tuno gida".
Ya kalli wurin ya ɗauke kai ya ce"ni za ka tsayar a wannan hanyar?"
"Haba Captain,yaushe rabona da sha dan Allah,na kwana biyu wallahi,ka san mawuyacin abu ne bafulatanin asali yayi sati bai sha madara ba".
Ya taɓe baki ya samu gefen hanya yayi parking.
Bayan Bilal ya fita ya kwantar da kanshi ya lumshe ido,kanshi wani irin ciwo yake kamar zai tsage.
Yana buɗe ido ya hango pharmacy a tsallaken titi,ya ɗauki wayar shi ya buɗe motar ya fito.
Yana tsallake titi ya ji wani mugun ƙara,juyawar da zai yi ya hango motarsu na ci da wuta.
Ya tsaya kamar gunki yana kallon motar, Bilal ya juya da sauri hankalin shi tashe ya ruga zai tafi wurin motar don duk a tunanin shi Sadauki na ciki.
Jin an riƙe hannun shi ya sa ya juya da sauri,ganin Sadauki ya sa ya rungume shi.
Sadauki ya hau bubbuga bayan shi idon nan jazur.
Lokaci ɗaya wurin ya cika maƙil da jama'a ana kallon motar,sai da ta cinye tas sannan wutan ya fara raguwa.
**********
Ta sake daliling number shi for the countless time amma haka ya ƙaraci ringing bai ɗauka ba.
Abin ya bata mamaki sosai don so ɗaya take kiran shi,kuma nan da nan zai katse ya kirata.
Bai taɓa missing call ɗinta ba sai idan Sallah yake,amma ko yana office ta kira he'll surely call her back.
Tun jiya take kira amma ko sau ɗaya bai ɗauka ba kuma bai kira kamar yadda ya saba ba.
Ta koma ta zauna gaban mirror tana kallon fuskarta,can ta tashi da sauri tuna by this time yana gida.
Ta ɗauki hijab ta sa saman guntun rigar jikinta ta sa slippers ta fita,ganin motar shi a parking space ya sa tayi murmushi ta wuce garden ta tsinko wani red flower mai kamshi ta bar wurin tana sake shinshina flowern.
Cike da dabara ta isa part ɗin,ta tura ƙofar da sauri gudun kar wani ya ganta,ta tsaya jikin bedroom ɗin ta ƙwanƙwasa a hankali,jin bai amsa ba ya sa ta sake bugawa.
Can ta ji alamar ana buɗe ƙofar da key,ta koma gefe ta maƙale tana murmushi.
Ya fito sanye da jallabiya riƙe da kanshi da ke masa wani irin ciwo.
Ta fito daga inda ta ɓuya tayi ihu ita a dole tsoro take son bashi.
Ya sauke hannun da ƙyar yana kallonta.
Ganin yanayin shi yasa ta yarda flowern da sauri ta matso ta ce"Ya Sudais are you okay?"
Ya koma baya da sauri ya ce"lafiya?"
Ta tsaya cak tana kallon shi ta ce"Are you sick,Ya Sudais?"
"And how does that concern you?"
Da mamaki ta ce"Ya sudais,lafiyar ka kuwa?"
Ya ɓata fuska ya ce"ke zan tambaya lafiya,menene haɗina da ke da har za ki biyo ni nan,akwai bashin da ki ke bina ne?"
"Wani irin wasa ne haka Ya Sudais,laifin me na maka,tun jiya nake kiran wayarka but you aren't picking".
Ya ce"babu abinda ya haɗa ni dake,ban san akan me kike magana ba so please excuse me".
Ya buga ƙofar da ƙarfi ya barta sake da baki.
Dariyar da ta ji yasa ta juya da sauri,Hajiya Mama ne tsaye tare da ƙawarta Hajiya Zainab,sai Mami daga can bayansu.
Don dawowarta daga asibiti kenan ta hango fitowar Zarah daga garden,har za ta ƙwala mata kira ta ga ta nufi part ɗin Sudais.
Da mamaki ta tsaya tunanin abinda zai kai Zarah can sai ta hango Mama da ƙawarta sun nufi can.
Da sauri ta bi bayansu, gabanta in banda faɗuwa babu abinda yake.
A idonsu komai ya faru,Hajiya Mama da Hajiya Zainab basu san da tsayuwar Mami ba.
Ta ba ƙawarta hannu suka tafa ta ce"to uwar naci,dangin kaska,sai a bar min ɗana ya huta ya sarara,a sake mishi mara yayi fitsari haka nan,yanzu dai tunda da bakin shi ya sanar dake baya yi ai sai ki haƙura ko?"
Ran Mami in banda tafarfasa babu abinda ya ke,ta kirata da wani irin kaushin murya ta ce"Fatima".
Da sauri ta ɗago har fitsari na son kufce mata,ta nuna mata hanya ta ce"zo ki wuce".
Ta fashe da kuka don ta san yau kashinta ya gama bushewa,ta yarfe hannu ta ce"Mami don Allah".
A fusace Mami ta ce"idan ba ki min shiru ba sai na karya ki Zarah,zo ki wuce".
Su Mama suka fashe da dariya suka sake tafawa ta ce"a kai kasuwa,ɗana ya yafe".
Da gudu ta wuce su hankali tashe Mami ta bi bayanta,tana isa parlour Mami ta fincikota.
Ta ƙwala wani uban ihu hankali tashe,ta kai mata wani wawan mari ta ce"yi min shiru don ubanki".
Ta fincike hijabin jikinta tayi jifa dashi,ta janyo igiyar charger ta watsa mata,ta ƙwala ihu gashi guntun riga ne a jikinta iya gwiwa.
Mami ta sake watsa mata wani sai yawo take a parlourn Mami na binta,tana ƙoƙarin sake zuba mata wani ta ruga da guda zata fita waje ta faɗa jikin mutum.
Lokaci ɗaya ta koma bayan shi ta ƙanƙame shi hankali tashe tana kuka.
Rai ɓace Mami ta ce"turo min yarinyar nan Faruq,sai kin gane shayi ruwa ne Zarah,wallahi ba ki san wacece ni ba".
Ta sake rungume shi ta ce"dan Allah,dan Allah ka ba ta haƙuri".
"Ki yi haƙuri dan Allah Mami".
"Zan watsa maka bulalan nan Faruq,ka matsa ko in haɗa da kai".
Ta sake ƙanƙame shi hankali tashe ganin Mami ta nufo su,ya matsa da sauri yana ƙoƙarin riƙe chargern hannunta.
"Ranka zai ɓaci Faruq,ka bani yarinyar nan kafin in haɗa da kai".
A hankali ya ce"ki haɗa dani Mami".
Ba tayi wata wata ba kuwa ta zuba musu bulalan,ya sauka a damtsen hannun shi gashi har lokacin Zarah ta ƙi rabuwa dashi.
Sai da ta gaji dan kanta sannan ta zauna kan kujera tana sauke numfashi,da gudu Zarah ta nufi hanyar waje yasa hannu ya janyota ya nuna mata hanyar ɗaki.
Ta fashe da kuka ta ce"wallahi dukana za tayi".
Ya watsa mata wani harara ya ce"wuce ciki".
Ya ƙarisa dining ya buɗe fridge ya ciro bottle water ya ɗauki cup ya tsiyaya mata ruwan ya miƙa mata.
Babu musu ta sa hannu ta karɓa,ta shanye duka ta miƙa mishi cup ɗin,sai da ya koma ya ajiye sannan ya zauna kan carpet yana kallonta.
A hankali ya ce"ki mata afuwa Mami,duk da ban san abinda tayi ba amma na san ta ɓata miki rai,dan Allah kiyi haƙuri".
"Zarah na ja min magana Faruq,idan bata ɓata min rai ba hankalinta ba zai kwanta ba,could you imagine bin yaron nan Sudais tayi har part ɗinsa,for what?
A matsayinki na ƴa mace menene abinda zai kai ki wurin saurayi for God sake har ya tsaya yana faɗa miki maganganu son ran shi?"
Ya ce babu abinda ya haɗa shi da ita,ya buga mata ƙofa ya barta a tsaye,Allah yasa soyayya bai rufe mata ido ta miƙa mishi kanta ba don ba ta da hankali".
Da sauri ya ce"kar ki ce haka Mami,ki kyautata mata zato,dan Allah ki yi haƙuri kar ki sake dukanta Mami".
Ta ce"shikenan Faruq".
Tun daga ranar Zarah da Mami suka fara wasan ɓuya,ko makarantar ma daina zuwa tayi,za ta jira sai Mami ta fita aiki sannan ta fito ta shiga kitchen tayi abinda za tayi kafin Mami ta dawo.
Daga Hajja har Daddy babu wanda ya san abinda ya faru,Hajiya Mama bata faɗa ba Mami ma ba ta ce komai ba.
A ɓangaren Sudais wani irin rashin sukuni ke damun shi,ya kan rasa abinda ke mishi daɗi,abu ɗaya dai ya sani shine ko sunan Zarah bai son a ambata.
Ya daina fita aiki,ya rame ya lalace amma ko a jikin Uwar,Ita dai tunda ya rabu da alaqaqai duk zai gaji ya hakura ya koma normal life ɗin shi.
Daga gefe suna nan suna shirya aure tsakanin Sudais da yar wajen Hajiya Zainab mai suna Aabida.
Book 1 ya kusa ƙarewa,Book 2 na kuɗi ne.
Pay 1k into *** Khadijah Sulaiman Opay.
Evidence of Payment via
***.
Thank you.