Riya

Riya Chap 8

by @lariryatouaziz

YACE ok tafi ki zawna ….
Koh kadan babu wanda yayi mamakin rashin bular late din da beyi mata ba dan yanzu dayawa daga cikin yan ajin sun san cewa mallan Abdul nasan Riya… 
Ranar da ya fada mata cewa yana sonta babu irin haoukar da Riya bata yiba dan cewa tayi zata fadawa mallan baba kuma ita duka nawa take da zaicewa yana sonta anya mallan Abdul bah mayaudari bane ,,, 
Riya tacewa kawayenta… 
Tana zawnawa kusa da Amina ta saki wata  siririyar kwalla tana kife kanta a table din !!!
Maryama ta dafata tace …. Dans Allah Kawata kiyi hakuri sawra kadan ammy ku ta dawo , kuma kumai zai huce insha’Allah !!!
amina tace «  waii bazaku tafi gidan kakar kuba » Riya ta dan zabura tace “ Innalilahi… Takuma cewa subhanallah ”  
Cikin dan bacin Rai tace .. Amma daii Amina baki kauna sam wallahi…
Amina tace Yi hakuri na manta cewa bakison maganar su….
     Maryama ta dan kama hanun Riya tana dan kwantar da ita a gefen kafadar ta dan sun saka Riya ne a tsakiya !!!!

Duk Abinda Duke Mallan abdul ns kwallansu tunda Riya ta zawna har kwalla da tayi, zuwa kwantawar da tayi akan Maryama, Saidai baya jin me suke fada , Amma ya sakawa Zuciyar shi 
cewa ana fita break ze tambayi Amina kawar ta dan duk tafisu hankali , dan Maryama kam ita da Riya saida daya ta gwadawa daya jiki, Maryama irin yan matan nan ne masu fadin da tsayi fara fatt dan tayi Riya fari nesa bah kusa bah sanan itama kyaukawace dan buzuwar Agadez ce gaba da baya Aiki ne yaka mahaifin su garin, yayin da ita Amina asalin yar tchad ce ita ma mahaifinta aiki ne ya kashi garin dan kasuwanci yake… 
Amina batada wani tsaho sosai dan itace karama a cikin su saidai duk ta fisu shekaru daga ita sai Maryama Riya ce karamar su amma duk ta fisu wayoo da iya yi sai kace babar mace…
ana fita da break Mallan abdul ya hadu da Amina bakin kofar shiga ajin , sanan ya dan jata gefe yana tambayar meke damun kawarta ne kwana biyu  … Yace koh dan nace ina santa ne , Koh wani ke takura mata …. Ya kare magana yana tsarawa Amina ido kamar me ??

     Amina ta danyi  Jimmm… tana tsoran fada mishi Kawayan nata suga laifin ta… 
Ta dan numfasa Dan gara ta fadamishi saboda idan Riya tayi late ya daina mata fada duk da yanzu ya rage!!!
Har mallan Abdul zai kuma cewa wani abun yaji tace….
   
   Wallahi mallan Riya ya cikin wani irin halin , Dan Allah Mallan idan tazo late kadaina mata fada koh duka, mamar suce batanan tayi tafiya  kuma, ga aikin gida , Duk da cewa akoy wata cousin dinta a gidan toh ita da cousin din ce suke samun matsala !! Amina ta kwashe komai ta fada mishie….
Mallan abdul yayi shuru wani abu me kama da tawsayi da soyeyar Riya na mamaye duk wani sako da lungu na zuciyar shi Yace Shikenan nagode kije kaway…
Tana shigowa duk suka tsira mata ido dan sunga lokacin data tsaya da ustaz din su kuma dunga adadin mintinan data kwashe tayi mishi bayani….  Takaraso ta zawna …
Maryama tace Kaii amy  me kikayiwa mallan yake miki tambayoyi !!!
Saidai Amina taban dedeta maganar da zata fada musu ta yadda zasu fahimceta sanan tace, 
Kuyin hakuri na fadawa Mallan Abdul abinda ke farawa da Riya kuma banyi dan in tuna miki asiri bah a’a dan ya daina dukanki in kinyi late kuma ya daina miki fada duk da nasan cewa yanzun ya rage tunda ya riga daya fallasa miki abinda ke ranshi,!! !!!
Ta rashe maganar cike da yakinin zasu fahimceta…
   Riya daii shiru tayi !!! 
Yayin da Maryama tace Toh Shikenan amma nan gaba dan Allah karkiyi kumai ba tare da shawarar muba….. 



 Anatashi daga makarantar tuni kanin Riya sun huce dan ana riga sakin rayan kafin su dan rage sai a saki manya, saboda kar tsunkoso yayi yawa…. 
    
 Riya ce ke sawri a cikin lungun bayan makarantar Ita da Maryama dan Amina zata huce kasuwa ne ….
Sawri suke dan Riya ce ta lura da Mallamin nasu daga biyar bayansu !!! Bata koh kadan wata magana ta shiga tsakaninta da shi dan ita bah wata soyeya da zatayi wallahi ga karatun boko ga jarababiyar cousin dinta dan ana dawoo daga hutu. zasuyi exam duk da tacen cewa bata karatu yada ya kama amma zatayi kokari ta huce ajin nan dan bata si ta maimaita shi tasan irin rashin jin da take da kawayenta na boko bah lalle ne bah tayi karatun Amma zata yiwa kanta karatun tanatsu ta kokarta….
Suna kawowa bakin kofar fita Abdul ya cin musu yace !!! 
Riya tun dazu sai biyar bayanki nake ina miki magana amma kinki tsayawa please meye lefina dan nace ina sanki????
Ya fada cikin yanayin dan Riya taji tawsayinshi…
kamar bah Mallan Abdul bah wanan hadadan gayan me jiji da kaii , wanan sawrayin da yan mata suke mutuwar so , 
sai gashi yar yarinyar shekara 14 na  Walagigita da zuciyar shi….
  Ya kwalli Maryama yace … koh zaki dan balu minti 5 … 
Maryama ta dan matsa tana cewa a zuciyar ta gwara ta fadawa Riya Gaskiya wallahi ta yarda da soyeyar ustaz dan a dan karamin wayonta ta fahimci cewa yana kawar ta da gaskiya…

 
Abdul yadan nisa … cikin cool voice dinshi yace … 
Dazun Amina ta fadamin komai … ya dan kwalleta yace kiyi hakuri kinji bzh abunda zan iya miki face adu’a amma duk idan kina bukatar  wani abun ki min maga indai befi karfina ba insha’Allah zan miki… Sa nan tun wace Ranar har yanzu biki tsemin komai bah ..  
ya dan sunkuyar dan kanshi yana kwallan fuskarta da tayi ja !! 
Kuka take so tayi amma sai basarwa take 
yace Riya!!  koh kin amince da maganata ne … 
wallahi da gaske nake sonki… 
Ta rince idaninta hawayen da bata son dalilin su bah suna zubawa akan fuskarta…
Ta bude baki da kyar tace Toh nagode zan tafi… 
sana dan Allah mallan kah daina tsedani dan kar wani yaje ya fadawa mallan baba  koh Abban mu …. 
Ta huce ta barshi cikin zullumi da taradadin zuciya saboda bega alamun ta yarda da soyeyar shi ta.. 
 Tana zuwa Maryama ta rike hanunta tana bata hakuri sukayi gaba dan taji komai tunda bah wani nisa tayi dasu sosai bah!!!
har kusa da kwanar gidan su Ta kara Kawar tata…. 
Ta kuma bata hakuri tace komaii zai huce insha’Allah da zaran ammy ku ta dawoo … 



  Riya na shiga gidan ta tarar da kanwar ta Nadja har ta fara wanki dan dama yau sukayi da ita idan sun dawo su wanke kayan su dana kaninta na su … 
har ta shiga daki ta cenza kaya bayiwa kowa magana bah …. 
Ta huce ta dawko wanki  ta ita ma ta soma farawa ,, Cousin dinta na zawna dan kusa da inda suke wanki tana daka yajin da zasuci wanken da ta dawra …. 
Yasmine ce tacewa yayar tasu Ummy zanci abinci yunwa nake ji …. 
haka suke cewa Riya dan haka abban ke ce matan a waje daii kuwa da Riya yasanta amma cikin gida zasuce mata ummy .. 
Riya tace yi hakuri bari a gama … 
yarinyar ta fara kukan tana cewa yunwa … Yunwa … ni wallahi yunwa nake ji Riya ta shiga kichten din ta duba taga girkin ya kamala zyy tun dazun sai ta dawku dan karamin bool ta zuba mata ta dan sa tama maggi da man gwada tace ungo ayy… Sa’adatu na ganin haka ta tashi da hanzari dayi kzn Riya kamar za’ta kaii mata duka tace !! Kekikayi abinci da zaki zuba mata be??? 
cikin fisata dan Riya  tace … No bani na girka bah Amma abinci na gidan mu neh kuma nan shineh gidan mu  haoushin yada ta kwale kanwar tata tana ta kukan yunwa bayan tun tunin ta kamala abinci .. 
Cikin wani hargagi tace ni kike fadawa hakan ??  
Riya cikin Rai tace Ehh !!!! keh din … 
sa’adatu  ta shamaci Riya ta tsakumu Rigarta ta bugata jinkin ginin katangar kichten din… 
Riya taji ciwo sosai dan har hanunta ya gurje… 
nan suka fara dambatuwa dan Riya najin haoushin ta sosai duk da cewa tafi karfinta haka tayi ta kai mata duka ta koh ina da cizo…. 
kanninta naso raba fadan amma abin yafi karfin su dan dama Nadja ce mai wayon cikin su…. 
dede nan Allah yaba sa’adatu  ikon kai Riya kasa … 
cikin bacin Raii Riya ta tundumu yajin dakai gefenta ta watsawa sa’adatu akan fuskarta ta kuma tundumuwa ta watsa mata akan jikin tayi wani itin ihuuu azaba da radadi da ciwon ta kwanta ta yin wani irin abu kamar mai Aljanu dede nan Abban su ya shigo gidan dan dawowar sa kenan daga aiki .. . 

sakk ya tsaya ganin abunda ke faruwa ….