MIJIN AMAL

Chapter 22

by @reza12

(HIV Research)

Chapter 22
Tana shiga ɗakin Anty Maryam ma na shiga. Ta ce "Amal meye haka? Mai kikeyi ne? Kina wasa da ikon Allah kenan ko mai? Ta yaya za'a miki aiki kice baki so?". "Anty dan Allah ki fita, kar na faɗa miki abun da zaki ji kamar ban kyauta ba. Please Anty". Ta karasa tana ƙoƙarin yin kuka. Anty Maryam ta ƙura mata ido wani irin tausayin yarinyar na kamata. Ta ce "Na fahimce ki Amal. Amma dan Allah nima ki fahimci abun da zan faɗa miki". Cikin kuka ta ce "Bana son ji, nace bana son ji, shin mai kuke so dani, ku fita a rayuwata mana haka". Anty Maryam ta ƙaraso ta riƙe ta tana hawaye. Sai kawai ta faɗa jikinta tana wani irin kuka na fitar haiyaci. Kukan da bata samun damar yin irinsa ba, kukan da ba wanda ya taɓa rungumeta Kamar haka domin ya ƙara mata kwarin gwiwa. Anty Maryam na bubbuga bayanta itama tana hawaye. Sai kuwa ta fara faɗin abubuwan da yake ranta. "Taya zan sake yarda da wani mutum a duniya Anty, taya zan iya kallon wani har na yarda da shi? Kuma Anty ba'a warkewa a cutar hiv, duk wanda yace ana warkewa karya ne, dan haka ba zan yarda a sake min aikin Komai ba. Idan kwanana ya kare babu makawa zan mutu ko ina da cutar ko babu, dan haka ku daina wahalar da kanku". Sosai Anty ta barta tai ta faɗin abun da bata samu ta faɗa ba. Sai da ta gama kafin ta raba jikinsu. Ta ce "Duk na saurareki, kuma tabbas haka ne ba'a warkewa a cutar hiv, sai dai idan mutum na shan magani ana iya rayuwa ba tare da matsala ba. But idan har cutar bata zauna a jikin mutum sosai ba, ana iya masa aikin da zai rabu da ita. Na san ba zaki yarda da abun da zan ce miki ba. Amma ina so muje gurin likitan idan yayi miki bayani in baki gamsu ba to zan fadawa yaya a hakura". Amal ta share hawaye tace "Anty bana so, wallahi bana bukatar ganin kowanne likita, gaba ɗaya basu da amana, wacce aka haɗa baki da ita aka cuce ni Mace ce, bata duba hakan ba". "Wannan ba abun da za'a muki Amal, ai muna tare da ke". Sai da ƙyar Amal ta yarda zata je gurin likitan. Bayan tafiyr su Yaya ta sake tashi zata fita Mama ta tare ta tana tambayar ina zata je? Dan Allah kar ta gudu, ta rufa musu asiri ta tsaya ayi wannan aikin. Bata ce mata komai ba tayi waje da sauri. Sabulun wankanta ne ya kare, Kuma akwai abun da take buƙatar saya. Bayan ta dawo ta tarar da Nana a gidan zaune tana bawa Mama labari, cikinta bai fara baiyana ba har yanzu. Bata ce mata komai ba ta shige ɗaki, daga wajen Nana ta fara gaidata tana ya jiki. Kaman yadda ta yarda ranar Monday suka ɗauke ta zuwa wani ƙaramin asibiti na kuɗi a bayan gari, domin bata taɓa zuwa gurin ba, ashe wai asibitin na masu irin cutar me. Bayan sun zauna Likitan ya fara musu bayanin cutar da yadda ake samunta da kuma adadin da take iya kaiwa ayi aki, da kuma lokacin da take kawai a jikin mutum ta wuce yin aiki.

Ya ce "Kaman yadda nai masa bayani zan sake yi muku yanzu. Domin a dokance aikin da kuke su ayi mata yana da haɗari sosai da sosai, domin abu ne mai yiwuwa da mara yiwuwa. Saboda sauyin jini baya warkar da HIV nan take. Wannan labari ne da wasu mutane suke yaɗawa amma ba gaskiya bane a likitance. But amma ita da aka tabbatar da cewar bata daɗe da samun cutar ba akwai abun da zamu duba. Amma idan har ta haura wannan adadin a jikinta gaskiya ba zamu iya ba. (Ga dalili) Na ɗaya. Ita ƙwayar HIV ba a jini kaɗai take da zama ba muddin ta daɗe a jikin mutum. Ƙwayar cutar tana ɓoye ne a wurare da yawa a jiki da cikin kwakwalwar ɗan Adam da cikin ɓargo (bone marrow) a cikin Lymph nodes, da kuma cikin ƙwayoyin halitta da ake kira ("reservoir") Idan ka kwashe jini ka sauya, to waɗancan wuraren da yake ɓoye zasu sake cika sabon jinin da kwayar cutar kamar yadda kuka ce ayi mata yanzu.

Na biyu. An taɓa samun mutane 1-2-3 ne kacal a tarihin duniya da suka warke saboda an yi musu irin wannan aikin dashen jini (bone marrow transplant) ba sauya jini kadai bane. Kuma suma ba wai anyi musu don cutar HIV bane kawai, an yi musu ne saboda suna da cutar sankara (cancer) mai tsanani. Kuma ɓargon da aka dasa musu yana da wata garkuwa ta musamman (CCR5-delta32) wacce HIV ba ta iya shiga. Wannan aiki ne mai hatsari sosai, yana da tsada, kuma mutane da yawa sun mutu yayin gwadawa. Ba magani bane da ake yi wa kowa.

Na Uku. Hanyar da ta dace tabi idan har ta riga tabi jinin jiki da ɓargo ita ce maganin (ART) Ita kadai ce hanyar da WHO da likitocin Najeriya suka amince da ita ga mai wannan cutar da tabi jikin mutum saboda aiki ba zai fitar da ita ba. Maganin yana danne kwayar cutar har ta zama bata iya yaɗuwa ga kowa. Kuma mai cutar yana iya rayuwa lafiya lau a cikin mutane muddin an kiyaye shan maganin. Saboda haka yanzu zamu bata wasu magunguna wanda zatayi amfani dasu na sati ɗaya. Daga nan zamu tabbatar da yiwuwar aikin a tare da ita. Idan har cutar ta mamaye jikinta kaman yadda nace a bayanin farko, to sai dai a ɗora ta amagni, idan kuma bata mamaye jikin nata na, to za'a iya mata aiki ina sha Allah. Muna mata fatan nasara". Likitan ya mikawa Yaya hannu. Ya kalli Amal ya ce "Ki kwantar da hankali, cutar hiv bata hana rayuwa. Har aure ana iya yi da wanda bai da ita kuma a aihu ba tare da an haifi yara masu cutar ba, ko kuma mijin ya samu cutar ba. Mutukar an bi dokokin likita. Ni nan da kike gani mahaifiyata tana ɗauke da wannan cutar tsawon lokaci mai tsayi. Kuma bai taɓa tashi mata ba, saboda maganin ART wanda babu wani magani da ya fishi a halin yanzu. Dan haka ki kwantar da hankali". 

Tun da da ya fara jawabin ta rikice saboda yadda taji bayanin. Sai dai izuwa yanzu ta ɗan samu yar natsuwa ba dan ta yarda da cewar zata warke ba, sai dan yadda ya kwantar mata da hankali. Haka ya haɗo musu maganin Kamar yadda ya faɗa. Yace kullum da safe tasha biyu, da rana biyu. Haka idan zata kwanta. Sannan yace su saita lokacin shan maganin saboda gwaji ne za'ayi. Hakan yasa Yaya ya wuce da ita gidan sa kaman yadda suka yanke hukunci da Anty. Wanda bata lura ba sai da ya shiga da motar cikin gidan da yake babban gida ne dan harda get. Anty ta riƙo hannunta akan ta fito sai ta tsaya tana kallon gidan. Ta ce "Dan Allah Anty ku kaini gida Please dan Allah anty?". "No wannan sati ɗayan zakiyi shi ana ne saboda shan magani, bama so ki bamu matsala ne, dan Allah ki kwantar da hankali, nan da cen duk ɗaya ne". Haka ba yadda ya iya ta bita. Aka bata daki ɗaya wanda iya gado ne a ciki. Sai dai yayan yace gobe zai sayo Komai ya saka mata. Kuma washegarin ya sayo komai ya saka mata. 

A karon farko da Amal ta fara tunanin abun da bata taɓa tsayawa ta tuna ba. Shin a garin yaya ma ta samu hiv? Sannan a garin yaya ta samu larurar ƙoda duk bata sani ba. Batun ƙoda ta ajiye a gefe tana nazarin samun hiv ɗin. Sosai take tunani. Kawai ta bari akan sun haɗa baki da wannan likitar ne da shi sun saka mata, idan ba haka ba bata san ta inda zata samu ba, ko kuma shi yana da ita ne. Haka dai take ta tunanin amma ta bari a hakan. Tana cikin haka Aunty ta shigo da plet ta ajiye mata abinci. Ta zauna kusa da ita ta ce "Ki samu kici wannan sai kiyi wanka ki fito falo, dan Allah Karki dinga rife kanki a ɗaki kinji? Ki fito ayi hira dake nan ma kamar gida ne". Amal ta ce "Anty ai dole na rufe kaina saboda ni ba ɗaya nake da ku ba, saboda zan iya cutar da ku, ko kema bana so kina raɓata haka dan Allah". Anty ta ce "Waye ya faɗa miki zama kusa da mai hiv yana sa a samu? Ai hiv ba'a taɓa samunta a mu'amala irin wannan. Kinga kamar zama guri ɗaya, ko runguma da cin abinci tare harda wanka tare da sauransu basa sawa a samu, har ma da yin kiss haka. Ita ana iya samu ne kawai ta hanyar gudanar jini. Misali kamar kiyi amfani da wuka ko reza kuma jini ya taɓa sai nima nayi amfani da shi. Ko ta hanyar ƙarin jini, ko kuma mu'amalar aurataiya da dai sauransu". Amal tayi shiru tana tunanin wannan maganar tata, hakan yasa ta faɗa tunanin baya domin gano wani abu, sai ta ce "to amma mai yasa..." Sai tayi saurin kawar da wannan tunanin. Anty ta ce "Akwai wata ƙawata mai wannan cutar, amma idan kika ganta ba zaik taɓa cewa tana da ita ba, kuma ba abun da bama yi da ita, idan tazo gidan nan tare nuke cin abinci da hira sosai. Saboda idan ana gudun masu cutar shine yake ƙara sa suji sun muzanta". Wannan jawabin ma ya sake kwantar mata da hankali sosai. Hakan yasa bata kuma zama a ɗakin sosai. Lokacin shan magani nayi zata sha, ko Anty ta tuna mata, har shi yaya ɗin ma ko baya gida zai kira ya tambaya ta sha. Wani lokaci haka suna hira yaran zasu kunna Film ɗin Indiya. Tana wanda zai tuna mata da wasu abubuwan haka zata fara hawaye ita ɗaya. Ko ta tashi ta bar palon. Idan abun ya ta so mata haka zata kwana a zaune tana kuka. Sosai taji daɗin zama a gidan. Babu takura babu ƙyama babu hantara. Gashi ba wanda ya taɓa mata maganar Yasir ko da gwaji. Yaran kuma suna zama da ita suyi hira suyi kallo. Haka har kwana bakwai sannan suka koma asibiti.

Bayan ya gama duk gwajin da zai mata ya ce musu tabbas cutar bata daɗe a jikinta ba, dan haka za'a iya mata aikin. Kuma zata iya rabuwa da cutar in sha Allah. Sannan ko bayan an yi aikin akwai gwaji uku da za'a mata idan har Allah yasa lafiya to ya tabbatar an dace. Sai dai ba ƙaramin kuɗi bane za'a kashe. Amma haka Yaya ya ce zai biya. Sosai ya dinga shige da fice da yake shi ɗin gadon manyan kasar ne tuni ya yaɗo kuɗin aka sa ranar aiki. A ranar da za'a fara aikin ta bar wasiyya cewar idan ta mutu a fadawa duk wanda ya zalunceta zasu haɗu a lahira gaba Allah, gurin da Ubangiji zai ƙwatar mata hakkinta. Kowa yasan da wa take yi. Sosai ta bawa Kowa tausayi a gurin ciki kuwa harda kikanta da yake ta kwantar mata da hankali. Nan aka shiga aiki yayin da yaya da Anty Maryam suke zaune a bakin gurin suna jiran ikon Allah. A kalla awa biyu kafin ɗaya mace ta fito. Bata daɗe ba ta dawo. Haka suka dinga jira har kusan awa Biyar kafin likitan ya fito ya sanar dasu anyi aiki. Amma ba zasu samu ganinta ba sai gobe saboda bata farko ba. Hakan yasa suka tafi sai washegari suka zo harda Mama. Suka sameta kwance idanunta a buɗe. Tana ganinsu kuwa ta saki murmushin ƙarfin hali tana bunsu da kallo. Sosai murna harda hawaye Mama jin aiki yayi. Haka suka yi sati kafin aka sallame su. Nan ma gidan Yaya ɗin suka wuce akan sai ta warke. Aka cigaba da dorata akan magani har wata guda. A gwajin farko aka tabbatar da cewar ta tsallake wannan. Sai bayan wani wata dayan za'a sake yi. Daga haka tace zata koma gida, amma Yaya yace sai fa anyi gaba ɗaya Gwajin. Haka na biyu ma aka tabbatar da cewar bata da shi. Yanzu suara gwajin karshe. Wanda daga shi za'a tabbatar an dace ko ba'a dace ba. A daren ranar ne idan batayi ƙarya ba kamar Muryar Yasir taji Anty tana magana da shi. Hakan yasa gabanta ya faɗi, ta taso a hankali ta boƴe tana sauraron wuyan nata. Amma ta tsinkayayo muryar Antym ɗin tana zagi da kutuntuma ashar ta cikin wayar ranta a mugun ɓace. Hakan ya tabbatar mata idan ma shine to anty zaginsa take yi. Kwana tayi tana Sallah. Tana addu'ar Allah ya dubeta, ya tabbatar mata da cewar babu wannan ciwon. Ƙurajen nan kuwa tuni suka ɓace, yanzu sai dai alamunsu wanda suma suna ta tafiya, tabbas tun daga aka mata wannan aikin taji sauyi sosai duk bata yarda cewar zata iya warkewa gaba ɗaya ba. Haka kuwa suka tafi wannan karan harda Nana da cikinta ya kai wata biyar kusan na shida. Bayan sun zauna shima ya sake kwantar musu da hankali ganin ta a rikice. Haka aka shiga gwajin nan cike da tsoro da fargaba da tashin hankali, domin idan har ya tabbatar bata warke ba dole haka zata rayu da wannan cutar. Jikinta har ɓari yake lokacin da aka gama mata likitan ya tafi domin gwajin da za'ayi. Tabbas Amal zata ce bata taɓa shiga fargaba da tashin hankali irin wannan ba tun ranar da ta tabbatar tana da cutar. Lokacin da likitan ya buɗe Kofar ya shigo sai ta kasa kallon fuskarsa saboda tashin hankali...📝

To fa.