Chapter 23
*_The Amazing Pen_ ✍️..........*
*Ba ni da Madogara*
(Sai Allah...)
023
Kamar walƙiya boka mai Zaki ya juyo yana daka musu wata uwar tsawa mai matuƙar firgitarwa wacce bai taɓa yi musu ba. Nan da nan hantar cikinsu ta kaɗa, tsoro da firgici ya ɗarsu a zukatansu lokaci guda. Babu zato babu tsammani suka ji amon muryarsa mai firgitarwa yana cewa
"Mu bayinsu neeee! Muna ƙasan ikonsu neeee! Karku sake zuwa nan! Matsiyataaaa!"
Da sauri suka ɗago kansu daga duƙyen da suka, zuciyar kowannansu na bugawa. Cike da ƙarfin hali Hajiyan sama ta ce
"Boka yanzu babu wani taimako da..."
Wata uwar tsawa ya daka mata wanda hakan ya haifar da ɗaukewar wutar da take ci a tsakiyan ɗakin, lokaci guda wutar ta kawo kamar almara. Cikin kausasshiyar murya ya fara magana
"Babu wani taimakon da za ku nema ya yi aiki, ko bani ba babu wanda ya isa ya yi muku aiki, domin sai sun lalata shi, sun wargaza komai, suna da matuƙar ƙarfin da babu wani shaiɗanin aljani da ya isa yafi ƙarfinsu! Ku bar min waje karku sake dawowa! Sannan ku jira sakamakonkuuu! Ku tashi naceee!!! "
A zafafe ya ƙarashe maganar, babu shiri Hajiyan Sama da Hajiya Zinatu suka miƙe jikinsu na rawa suka bar ɗakin bayan sun yi surkullen da zai sa ƙofar ta buɗe. Bayan sun baro dutsen kafin su isa inda motarsu take, sai Hajiyan Sama ta dubi aminiyarta ta ce
"Aminiya nifa har yanzu ban haƙura ba wallahi"
Hajiya Zinatu da ke sauke tagwayen ajiyar zuciya ta ce
"Ko nima nan ba haƙura zan yi ba, haka nan wata bazata zo ta haihu cikin gidan mijina ba, a raba gado da yaronta. Yarana kaɗai za su ci gadon ubansu, Yanzu kawai mu nemi wata hanyar"
Shiru Hajiyan Sama ta yi tana tunani, sai can ta dubi Hajiya Zinatu ta ce
"Na samu wata lafiyayyar hanya mai ɗaurewa Aminiya"
Cike da zaƙuwa Hajiya Zinatu ta ce
"Wace hanya kika samo mana?"
Murmushi a fuskar Hajiyan Sama ta ce
"Ba dai boka mai Zaki ya ce duk asirin da za mu yi sai aljanun yarinyar nan sun lalata shi ba?"
Jinjina mata kai Hajiya Zinatu ta yi suna tafiya. Wani ƙasaitaccen murmushi Hajiyan sama ta saki sannan ta ce
"Hanyar ita ce yin amfani da guba wacce kamar ruwa take bata da launi, mu zuba wa kowanne a cikin abincinsu hankali kwance"
Waro idanu Hajiya Zinatu ta yi tana cewa
"Aminiya guba kuma, Ni dai tsoro nake ji idan kuma ta mutu fa"
Wani wawan tsaki Hajiyan Sama ta saki sannan ta ce
"To idan ba wannan hanyar ba wace hanya kike tunanin zata ɓulle mana. Karfa ki manta bamu da damar yin asiri tunda wannan shaiɗaniyar yarinyar zata iya karyawa. Amma kinga wannan gubar da zamu samo ba mai aiki bace lokaci guda. A hankali take bin jikin mutum tana lalata ƙo'ina tun daga kan kayan cikinsa da jijiyoyinsa, daga baya sai mutum ya mutu, kinga babu wanda zai yi zargin wani abu. Bayan haka Hujayrah bata isa ta lalata wannan aikin ba tunda ba abin da ya shafi asiri ba ne, balle aljanun kanta su ce za ku lalata mana aiki"
"To indai irin wannan gubar ce ina maraba da ita, Ina zamu samo ta?" cewar Hajiya Zinatu cike da farin ciki
"Kibar komai a hannuna zuwa gobe za ki ga saƙo ko anjima, ni kisan wa san zuba wa gubar nan kuwa " cewar Hajiyan sama.
"Ba Hajiya Mubina za ki ƙarasa ba?"
Girgiza mata kai Hajiyan Sama ta yi sannan ta ce
"Ko ɗaya Aminiya, tushe farin cikinsu zan halakar"
"Ban gane tushe farin cikinsu za ki halakar ba?" cewar Hajiya Zinatu.
"Arqam!!! Arqam shi ne tushen farin cikinsu, ba Hajiya Mubina im kaɗai ba har da Alhaji, duk burikansu akan Arqam yake kinga kuwa idan na gama da babinsa shikenan komai zai dawo hannuna"
"Hannunki kuma Aminiya taya?" Hajiya Zinatu ta ce cike da mamakin daya kasa barin fuskarta, domin a dunƙule Hajiyan sama take maganar, ita kuma ta kasa fahimta. Suna gab da isa inda motarsu take Hajiyan Sama ta dubi Hajiya Zinatu ta ce
"Kar ki damu Aminiya ta hanyar Khalil komai zai dawo hannuna kuma cikin sauƙi, naki kawai zuba ido ne kiga Ikon Allah, sannan idan mun koma gida zan yi tunanin yadda za mu kawar da yarinyar nan a cikin sauƙi"
"To shikenan Aminiya, Ni wani lokacin tsoron shu'umancinki nake Aminiya, Kinsan kan duniya sosai" cewar Hajiya Zinatu tana dariya ita ma Hajiyan sama dariyan ta yi sai suka ƙarasa inda motarsu take cike da farin cikin samun mafita cikin ƙanƙanin lokaci.
Basu suka dawo gida ba sai wurin Asr,bayan sun sauke Hajiya Zinatu sai suka wuto gidansu. Hajiyan Sama na isa sashenta ko hutawa bata yi ba ta sake wani sabon wankan ta fito cikin shirin fita, sanya take da atamfa Holland ɗinkin boubou tasha adon stones, gyalen data yafa ya yi matching da atamfarta , bata shiga part ɗin Hajiya momma ba ta wuce abinta tare da amintaccen dribanta. Kai tsaya suka nufi wata unguwa mai kyau amma bata kai Estate ɗinsu haɗuwa ba. Umurtar dribanta ta yi ya yi parking a gefan hanya, babu musu ya yi parking sai ta fito daga motar ta nufa wani gida. Bata wani daɗe a gidan ba ta fito ita da wata mata suna dariya, har motar ta rakota. Hajiyan Sama na shiga motar ta leƙo ta windon motar ta ce
"Yanzu zan wuce gidan Hajiya Zinatu na kai mata nata saƙon, zuwa gobe nakeso kowannanmu ya fara aiwatar da ƙudirinsa, Kinsan da zafi-zafi ake dukan ƙarfe"
Ƴar dariya matar ta yi sannan ta ce
"Hajiya baki da dama wallahi, ku dai yi komai cikin taka tsantsan"
"Haba ni har sai an cemin wannan, ke dai kawai ki jira daddaɗan labarin da zan faɗa miki zuwa gobe idan komai ya kankama"
"Allah ya nuna mana, sai na jiki goben"
Daga haka matar wacce bata wuce sa'ar Hajiya a shekaru ba ta komai gidanta su kuma suka ja motarsu, kai tsaye Hajiyan Sama ta wuce gidan Aminiyarta Hajiya Zinatu bata saƙo gubar data amso wurin ƙawarta wacce ta gwada gubar taga ta yi aiki sosai, wanda hakan yasa Hajiyan sama take son amfani da gubar kasancewar ƙawartata da yawa ta siya gubar in case za ta iya amfani da shi nan gaba. (Oh Allah! Mutane babu imani kwata-kwata a zukatansu. Allah kasa mufi ƙarfin zukatanmu)
Bata wani daɗe a gidan aminiyarta ba ta fito suka wuce gidan rasuwa don ta yi ta'aziyyar Sabrin, don gobe bata da lokacin fita saboda ƙudirinta da take so ta aiwatar. Ba Ita ta dawo gidan ba sai wurin 8:12pm na dare. Bayan ta yi wanka sai ta yi zaman cin abinci wanda tun safe rabon ta da abinci sai zirga-zirga take. Kasancewar Alhaji ba a ɗakinta yake ba sai kawai ta yi kwanciyarta don tasan ko ta ce za ta kwana part ɗinsa ba yarda zai yi ba duk da Hajiya momma bata da lafiya. Yafi ƙaunar ya kwana shi kaɗai... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
A can gidan Alhaji Sambo dala kuwa, zaune yake a farfajiyan gidan shi da Senata sai wasu abokansa biyu suna amsar gaisuwa. Daga jiya zuwa yau har ya fita hayyacinsa, har ƴar rama ya yi, idanunsa sun shige cikk, hancinta ya ƙara tsayi. Senata ne ya dubesa muryarsa can ƙasa ya ce
"Linkaku zo mu zagaya garɗen mu tattauna"
Alhaji Sambo Dala da yake zaune kamar mutum-mutumi ya dubesa da jajayan idanunsa ba tare da ya ce komai ba ya miƙe. Senata ne ya dubi sauran abokansu ya ce suna zuwa. Basu kawo komai a ransu ba suka jinjina masa kai, daga haka ya ja hannun Alhaji Sambo Dala suka nufi garɗen wanda yake a bayan gidan. Zama suka yi a kujerar da ke cikin garden ɗin. Babu laifi garden ɗin ya taru sosai, baka jin motsin komai sai kukan tsuntsaye masu launi jiki mabambanta,flawowin da ke shuke a cikin garden ɗin masu ɗaukar hankalin ne, bayan haka a wani gefan garden ɗin akwai bishiyun kayan marmari da dama irinsu Apple, ayaba, lemu, black berries da dai sauransu.
Bayan sun zauna sai Senata ya dubi Alhaji Sambo Dala fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce
"Linkaku har yanzu baka ji wani labari ba daga yaran ka?"
"Ina nake cikin kwanciyar hankalin da zan kirasu Senata, mutuwar Sabrin ta tarwatsa duk farin cikina baki ɗaya, Ina tsaninin son Sabrin, gashi ta tafi tabar ni."
Wasu zafafan hawaye ya share sannan ya ci gaba da cewa
"Senata na rasa inda yarinyar nan ta shiga a duk faɗin garin nan, na yi kuskuran barinta secret house ɗina har ta samu damar guduwa. Da a ce a lokacin dana ɗaukota daga garinsu kai tsaye na wuce da ita ƙungiyar da ban rasa sanyin idaniyata ba Sabrin."
Sauke ajiyar zuciya Senata ya yi sannan ya ce
" Ni dai addua'ana idan mun haɗu a ƙungiya kar demon king ya ce zai sake hukuntaka. Nafi son su ƙara mata lokaci tunda ai ba yanzu DODO ƘURNUSSA zai aiwatar da aikinsa akan yarinyar ba, sai ta cika shekara 23 cif-cif. Yanzu haka a ɗan kwai sauran lokaci"
"Nima Ina fatan haka don bana son su sake taɓa ahalina, yanzu yara biyu suka rage min a duniya, zan yi iya ƙoƙarina na ganin na nemo yarinyar in har za su ƙara min lokaci, nima na huta da tunani da taraddudin da nake ciki akodayaushe" cewar Alhaji Sambo Dala.
"Yanzu mu koma ciki zuwa can dare sai ka kira ka ji ko an samun labarin inda take" yana maganar yana miƙewa, shi ma Alhaji Sambo Dala miƙewan ya yi sai suka fito daga garden ɗin zuwa cikin gida.
A can cikin gida Hajiya Mariya ce da ƴan uwanta waɗanda basu jima da isowa ba, sai Hajiya Ramla da aminiyarta Hajiya Lubna wacce ta zo musu ta'aziyya . Kowa ya yi jugum-jugum babu mai cewa komai. Hajiya Ramla da aminiyarta suna a wani gefan ɗaki su kaɗai,ganin basa kusa da mutane sai Hajiya Ramla ta yi amfani da wannan damar don ta sanar wa aminiyarta halin da take ciki. Gyara zama ta yi sannan ta dubi Hajiya Lubna murya can ƙasa ta ce
"Aminiya wallahi akwai wata babbar matsala da ke shirin kunno min"
Waro idanu Hajiya Lubna ta yi waje, lokaci guda hankalinta ya tashi, cike da tashin hankali ta ce
"Matsala Hajiya? Wace matsala? Zuciyata har ta fara dukan tara-tara bama uku-uku ba, sanar min meke faruwa"
Hajiya Ramla bata ɓoye wa Hajiya Lubna komai akan abin da ke faruwa a gidan yayanta Alhaji Imran, komai ta sanar mata har da asirin da take tunanin Hajiyan Sans ta yi wa Hajiya momma saboda mugunta. Wata nauyayyan ajiyar zuciya Hajiya Lubna ta saki sannan ta ce
"Gaskiya akwai kuwa matsala babba, yanzu dai bayan addu'ar uku sai mu zauna mu san abin yi tun kan wankin hula ya kaimu dare, Ni tsorona kar wannan yarinyar ta yi nasarar karye asirin da muka yi wa Hajiya momma na auransu Tahseen daga baya ta ce ba za a yi auran ba "
" Nima tsorona kenan wallahi, dole mu yi gaggawar kawar ya yarinyar daga baya sai mu san abin yi, bana so a ɗau lokaci mai tsayi kinga auransu bai fi ƴan kwana sha biyu ba. Bana so a fasa auran, yau zan koma gida sannan zan sanar wa Senata abin da ke faruwa, nasan zai bani shawara mai kyau sai zuwa jibi mu san abin yi" cewar Hajiya Ramla tana gyara zamanta.
"To shikenan zuwa jibin sai ki sanar min yadda kuka tsara,amma a gaskiya Hajiya Izzatu shaiɗaniyar mata ce"
Murmushin takaici Hajiya Ramla ta yi sannan ta ce
"Barta kawai baƙin ciki ke ɗaiwaniya da ita, amma zan yi maganinta, da zarar an ɗaura sauransu Tahseen na kawar da wannan yarinyar zan koma kanta"
"Gaskiya kan don idan baki kawar da ita ba to za ta hana yarinyar zama da mijinta lafiya"
"Hakane" cewar Hajiya Ramla tana hamma tare da miƙe babu salati balle salallami. Daga haka suka ci gaba da wata hirar ta daban.
A can sama ɗakin Sakhiyya kuwa, Tahseen da wata budurwa sa'arsu ce zaune suna sanye da wasu yagalgalun kaya wanda dasu da babu duk ɗaya. Tahseen na kwance a jikin budurwa ta yi lamo, ita kuma budurwar sai shafa bayanta take yi tana lumshe idanu. Sakhiyya ce ta fito daga bayi da alamu wanka ta yi. Watsa musu ruwa ta yi tana dariya, firgigit! Suka dawo cikin hayyacinsu, watsa mata mugun kallo suka yi suma suna dariya. Tahseen har idanunta sun sauya kala saboda tsabar shawa'ar da ke cinta a rai.
"To Mayu ai sai ku bari a yi addu'ar uku ko! Shegu baku da aiki sai ƙwaƙular juna" cewar Sakhiyya tana zama a saman kujerar mirror.
"Ai ke dai bari kawai I'm just squeezing myself Zuwa bayan addu'ar ukun nan, na yi matuƙar matsuwa Sakhiyya" cewar Tahseen tana sake rugumar budurwar a jikinta tana lumshe ido.
"Yanzu idan kin auri Ya Arqam daina harkar les za ki yi ko?" cewar Sakhiyya.
"Never wallahi, kawai don ina mutuwar son Ya Arqam ne yasa zan auresa if not ko auran ma ban tunanin zan yi, don nafi samun biyan buƙata a les sosai ko ya kika ce Mardy zuma" cewar Tahseen tana kallonta. Wacce aka kira da Mardy Zuma na kai dubana gareta, kyakkyawa ce sosai daga ganinta kaga ƴar uhu irinsu Tahseen .
"Sosai ma Kuwa Tahseen, mai za a fasa mutuwa ko hisabi"
"Koda yake nima nafin jin daɗin les gaskiya" cewar Sakhiyya tana ciro kayan da za ta saka. Kwashewa da dariya Tahseen da Mardy Zuma suka yi har da tafawa.
"Ashe Kema kinsan kan duniya Sakhiyya, " cewar Mardy Zuma tana dariya. Ci gaba da hirarsu suka yi wanda yawanci akan harkarsu ta lesbian ne. Kamar ma mutuwa aka yi jiya-jiya ba, har sun manta Wa'iyazubillah. (ke duniya ina za ki damu🤔, Allah kasa mu yi kyakkyawan ƙarshe)... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Ƙungiyar Black Pythons Society*
*ƙarfe 1:35am na dare*
A daidai wannan lokacin kowani member na ƙungiyar ya hallara har da Demon king da uban gidansu DODO ƘURNUSSA sun iso.Bayan sun zauna a kujerarsu ta mulki sai Demon king ya dubi Linkaku (Alhaji Sambo Dala ) fuskarsa a ɗaure babu kyawun gani ya fara magana cikin amon muryarsa mai firgitarwa
"Linkakuuuuu! "
Alhaji Sambo Dala da ke tsaye cikin layi ya ji kamar zuciyarsa za ta faɗo tsabar firgicin da ya shiga jin Demon king na kira sunansa da kakkausar murya. Cike da raunin murya mai nuni da tsantsan firgici ya amsa masa
"Nnnaaaa'aaaammmm Dddemon kinggg!"
Wani killing smile Demon king ya saki yana watsa masa mugun kallo, bai ce dashi komai ba har na tsawan wasu ƴan sakanni daga bisani ya fara magana.
"Kwanakin da DODO ƘURNUSSA ya ɗeban maka suna gab da ƙarewa amma ka gaza nemota?"
Alhaji Sambo Dala da ke Share gumin da yaa tsattsafo masa ya ce
"Demon king har yanzu muna kan bincike, zan yi iya ƙoƙarina wurin nemota. DODO ƘURNUSSA ya yi min rai kar ya taɓa ahalina saboda laifina."
Hannu bibbiyu yake roƙan demon king idanunsa na zubda ƙwalla. Miƙewa demon king ya yi ya nufo inda Alhaji Sambo Dala ya ke,shi ma DODO ƘURNUSSA wanda ke a suffar Mesa ya biyo bayansa har tsakiyar ɗakin inda kungin macijin yake. Da sauri Alhaji Sambo Dala ya koma cikin layi, tsoro na sake lulleɓe shi. Kamar walƙiya DODO ƘURNUSSA ya rikiɗa zuwa ainin suffarsa ta aljani,kowa ƙasa ya yi kansa cike da tsoro.
Idanuna na kai duba ga wannan halittar don na sake ɗauko muku rahoto ko kun manta suffarsa da matuƙar ƙarfi ƙirjina ya bada Dammm! Dammm ! Dadammmm! Lokacin da na ɗago kaina na dubi dodon, tabbas! Wannan dodon ya ci sunansa DODO ƘURNUSSA suffarsa ba abin kallo bane ga mutum, don idan mace mai ciki da kalli Dodon nan to da wuya bata yi ɓari ba tsabar firgici, ,yanada matuƙar tsawo sosai don duk girman Demon King sai naganshi ɗan ƙarami a gabansa,balle a je gunsu Alhaji Sambo Dala, kamar ƙananun ƙwari suke a gabansa, suffa biyu ne dashi,suffar maciji da suffar mutum, gangan jikinsa na mutum ne, mabanbanta macizai bakwai ne akansa,a tsakiyar kansa akwai ido ɗaya mai girman gaske sannan ƙwayar idon kalar na macizai ne, babu alamar baki balle hanci,kan macizan sai juyi suke suna fidda harshensu, Sannan harshen kowannansu tsaga biyu ne,yatsun hannayansa da na ƙafarsa ba irin na mutane ba ne, don bindin macizai ne a madadin yatsun.A tsakiyar randameman cikinsa zanan baki ne mai faɗi da girma,sai a sannan ne naga bakin har da haƙora.Haka ya tsaya ƙiƙam! Da wata iriyar murya ya fara magana cikin wani irin yare na daban wanda Demon king yake fassara ma su Alhaji Sambo Dala da cewa
"Lokaci ya kusa na cimma ƙudirinmu wanda muka yi tsawan shekaru muna jiran zuwansa! Gashi ɗaya daga cikinku ya ɓata mana shiriii! Saura wata biyu yarinyar ta cika shekarar da muke buƙatar don cimma ƙudirinmu akan taaa! Yanzu aikin ya koma kan kowaaaa! Daga yau zuwa nan da wata daya dole a kawota ƙungiya don na shirin aiki kafin shekarun nata su cikaaaa! Nan da wata ɗayaaaaa! Ɗayaaaaa! Ɗayaaaaa! Idan kuka Gaza samo ta to shikenan za ku TALAUCEEE!!! Za ku TALAUCEEE idan kuka Gaza kawota nan da wata ɗayaaaaa! kowa ya fara shiriii! Daga yauuuuuu!!!! Sannan wanda ya yi sanadiyyar ɓatanta zai fuskanci tsattsauran hukunci mai tsananin gaske da shi da ahalinsaaaaa! Ku kawota ƙungiya nan da wata ɗaya ko ku koma matsiyataaaaa!!! "
Haka Demon king ya ci gaba da fassara wa members ɗin ƙungiyar abin da DODO ƘURNUSSA yake faɗa. Babu wanda a cikinsa hankalinsa bai yi matuƙar tashi ba, jin idan har basu kawota ƙungiya ba zasu TALAUCEEE, wannan kalmar ta girgiza kowa a cikin ƙungiyar har da shi kansa Demon king kasancewa aikinsa fassara abin da DODO ƘURNUSSA ya faɗa. Lallai dole kowannansu ya fara shiri a cikin daren nan ko kuma ya fuskanci hukuncin mai tsauri a wurin DODO ƘURNUSSA. Bayan ya kammala fassara musu abin da DODO ƘURNUSSA ya faɗa. Kamar kodayaushe masu kawo jini a ƙwarya da farfesun yaran mutane suka zo, kowani member ya miƙa ƙoƙonsa mai kwalliyar maciji suka zuba mai jini sai ya amshi wani sashe na daga sassa jikin yaran wanda aka yi pepper soup ɗinsu. Koda suke cikin tashin hankali hakan bai hana su santin farfesun da aka kawo mu ba. Suna kammala ci da sha sai mutanen suka koma inda suka fito, kowani member ya ɓace sai daga bisani Demon king da DODO ƘURNUSSA suka ɓace. Nan take gidan ya nutse cikin ruwa kamar bai taɓa wanzuwa ba... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Ƴan Majalisu, Unguwan Dosa, Kaduna state. Nijeriya*
*Ƙarfe 1:29am na dare*
A daidai wannan lokacin Hassana matar Abdul ta tashi da naƙuda kasancewar har ta wuce watan haihuwarta, sosai hankalin Abdul ya tashi. Da sauri ya sanya Jallabiya ya zuri makullin mota ya cicciɓota zuwa cikin mota. Sai fama matsaar ƙwalla take tana cije lips ɗinta kamar za ta ciresu. Da sauri ya tada mai gadi wanda yake cikin ɗakinsa yana sharɓar bacci. A gigice mai gadin ya farka daga daddaɗan baccin da yake ya fito tare da wangale musu gate. Jan motar ya yi da ƙarfi suka bar gidan. A hanya ya kira mahaifiyarsa yana sanar mata da suna hanyar asibiti. Hankali tashe take tambayar wane asibiti suke. Faɗa mata ya yi Dialog Hospital zai kai ta inda take awon ciki tunda babu da nisa daga gidansu. Ce masa ta yi gata nan zuwa.
Suna isa cikin asibitin aka wuce da ita labour room, basu daɗe a ciki ba wata nurse ta fito ta ce ya kawo kayan haihuwa don har ƙan yaro ya fara fitowa. Lokacin ya tuna kayan suna ɗaya ɗakinsu bai ɗauko ba. Miƙewa ya yi da sauri ya fito zuwa mota bayan ya faɗa mata gidansu babu nisa daga nan zai je yanzu ya ɗauko,kama hanyar gida ya yi a sauri.
A can gidansu Abdul bayan fitowarsa da kusan mintuna ashirin yaran Sheikh Munnir (Demon king) suka dira cikin gidan bayan sun yi parking motocinsu a waje. Su shida ne suka zo, ƙwanƙwasa gate ɗin gidan suka yi, mai gadi da ke ɗaki yana zaune ya miƙe a tunaninsa ko uban gidansa ne ya dawo ɗaukar wani abu da ya manta. Da sauri ya buɗe ƙofar gidan wanda lokaci guda gabansa ya yi mugun bugawa ganin ƙattin maza kusan su shida suna nuna sa bindigunsu masu hatsarin gaske. Tuni hantar cikinsa ta kaɗa, cikinsa ya bada sautin ƙulululuuuu! Babu zato babu tsammani ya ji zufa na kwaranyo masa a duk ilahirin jikinsa. Wata uwar tsawa ɗaya daga cikin yaran ya daga wa mai gadin da cewa
"Matsaaaa! Wurin uban gidanka muka zo!!!"
Da sauri ya matsa suka shigo cikin gidan su duka,sai waige-waige suke. Wani a cikinsu ya ce
"Kai fatan Uban gidanka na ciki ko?"
Waro idanunsa ya yi waje ya kasa cewa komai
"Ba waro min idanu na ce ka yi ba, Uban gidanka na cikiii?"
Cikin inda-inda mai gadi ya ce
"A'a baya garin"
A daidai wannan lokacin da yaran Sheikh Munnir suke wa mai gadi tambayoyi, lokacin Abdul ya shanyo kwana da motarsa cikin layin. Before yana gudu sosai, sai kuma ya fara tuƙi a hankali. Mamaki ne ya ci kasa gadin motoci har biyu a ƙofar gidansa. Su waye? Meya kawo su? Nan take ya ciro wayarsa tare da kunna data ya cika App ɗinsa, kasancewar akwai CCTV camera a kowani lungu da saƙon gidan, yana isa ɓangaren mai gadi yaga abin da ke faruwa a ciki. Dummmmm! Ƙirjinsa ya bada lokacin ya ya duba ɓangaren mai gadi yaga ƙattin maza har shida da bindugu sun tsare mai gadi da tambayoyi. Tuni ya shiga ruɗu da tashin hankali,da sauri ya juya kan motarsa ya jata a sittin yabar layin. Tuƙi yake zufa na kwaranyo masa a jiki, he can't believe a ce a cikin gidansa wasu za su zo su shida kowanne a cikinsu da bindiga mai hatsarin gaske. Waye ya turo su? idan da Hassana bata farka da naƙuda ba da shikenan tasu ta ƙare? .Babban tashin hankalinsa karsu cutar da mai gadinsa tunda basu gansa ba. Har ya iso asibitin bai daina zancen zucinsa ba. Koda ya iso asibitin sai ya samu har mahaifiyarsa ta iso ita da ƙanwarsa budurwa. Da sauri ya iso inda mahaifiyarsa take can ƙasa da murya ya ce
"Mom wasu mutane da bindigogi sun shiga gidana yanzu haka suna ciki, na je ɗaukar kayan haihuwa ne na tsaya a farkon layi ganin motoci har biyu, Ni kuma ban yi da wani zai zo gidana ba, Ina kunna App ɗina na yi connecting da CCTV camera na gansu"
Waro idanunta ta yi waje tana faɗin
"Gidanka Abdul me ka yi musu! !"
"Nima ban sani ba Mom, Ni tsorona karsu cutar da ɗan Asabe, idan da Hassana bata farka da naƙuda ba da shikenan wani zancen za a yi ba wannan" cewar Abdul fuskarsa shimfiɗe da damuwa. Dafe ƙirji mahaifiyarsa ta yi tana salati haɗi da salallami.
"Yanzu dai Ubangiji ya kuɓutar daku Alhamdulillah, shi ma ɗan Asabe Allah zai kuɓutar da shi, mun ari kayan haihuwa na wata mata zuwa gobe sai muje mu siyo mata, bazaka koma gidan ba..."
Bata ƙarasa abin da ta yi niyyar faɗa ba wata nurse ta fito da jariri a hannunta daga cikin Labour room ɗin. Da sauri su Abdul suka ƙarasa inda take. Mom ce ta amsa jaririn fuskarta ɗauke da tsantsan farin ciki tana cewa
" Maa shaa Allah! Tabarakallah mace ce ko namiji? "
"Mace ce Hajiya yanzu haka Patient tana bacci, zuwa asuba data farfaɗo za mu kaita ɗakin hutu"
"OK Toh godiya muke" cewar Abdul ynaa amsar jaririyar "
Wuri suka samu suka zauna, can Abdul ya dubi mahaifiyarsa ya ce
" Mom gidanki Hassana za ta koma ko? "
" Har da kai Abdul, ai kun gama zama gidan, sai an yi bincike an gano wanda ya turosu an ɗauki tsattsauran mataki sannan zaku goma"cewsr Mom tana rirriga jaririyar saboda ta fara mutsu-mutsu.
" Gobe zan sanar wa ƴan sanda su zo gidan su duba ɗan Asabe "
"Allah ya kaimu" cewar Mom tana miƙawa ƙanwar Abdul jaririyar... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Kwanar Faru ƙwai, Kaduna state. Nijeriya*
A ɓangaren Zaliha bayan Alhaji Zakari yabar ɗakin, fita ta yi ta wanke fuskarta ta dawo cikin ɗakin. Sutura ta canja sannan ta saka hijab ta fito zuwa sashen Murja. So take su tattauna da ita ta ji wace shawara za ta bata. Da sallama ta shiga sashen, a can ciki Murja ta amsa mata. Cikin ɗakin ta shiga tare da samun wuri ta raƙube kamar wata munafuka. Shiru ɗakin ya yi kowa na zancen zucinsa, can Zaliha ta yi ƙundumbalar cewa
"Innar Balki ni na gaji da zaman auran, so nake Zakari ya bani takardata "
Bushewa da wata mahaukaciyar dariya Murja ta yi har tana riƙe ciki kamar wata zautatta, galala Zaliha ta yi tana kallonta zuciyarta na yi mata suya kamar ƙosai, a ranta take faɗi 'Ba laifinki ba ne Innar Balki ni na kawo kaina, duk abin da kika min ni naja wa kaina' Murja ta daɗe tana busar daeiyarta daga bisani ta dubi Zaliha cikin dariya ta ce
"Haba Zaliha ƴar Innar! Tun yanzu har kin karaya? Karaya ba naki ba ne Zaliha, bari na yi miki wata waƙar yara da suke yi wa amarya mai kuka da cewa *_Yeeeeee yiyalleee!!! Ke kika ce kina so! Da baki ce kina so ba da ba a baki shi ba!!! Yeeeeee yiyalleee_* Malam Tani mai allon ƙarfe, ni da innarki har da Kawu Isah sai da muka baki shawara akan kar ki auri Zakari amma kika yi burus! Da kalamanmu, ke ala dole ƴar soyayya, ai ga irinta nan tun ba a je ko'ina ba Kin fara cikin karo da madarar tashin hankali tare da shayin kuka "
Sosai ran Zaliha ya ɓaci jin kalaman ƴar uwarta wato dai ba za ta taimaketa ba ke nan. Shanye ɓacin ranta ta yi sannan ta ce
" Innar Balki yanzu bazaki taimake ni a warware auran ba? "
Waro idanu Murja ta yi waje tana riƙe haɓa ta ce
" Ni Murja wane ni da shiga faɗan masoya, ce nike saboda so da ƙaunar da yake miki ya saki Hannatu uwar ƴaƴansa. Ni dai babu ruwana, Ina zaman-zamana ki sakani shiga lahaula.Ni yanzu ta yadda zan ci galaba akan su Zaytuna da Hannatu nake, bani da lokacin irin waɗannan abubuwan "
" Shikenan tunda ba za ki taimake ni ba, Ni
Kinga tafiyata, da zarar an yi sadakar bakwai zan koma wurin Malam Tani mai allon ƙarfe ya warware asirin da ta yi wa Zakari na mallaka, kinga shikenan sai ya sakeni, don wallahi ba an zauna da Zakari ba, ya dawo da uwar gidansa su ƙara ta can! " Zaliha na gama faɗi haka ta miƙe tabar sashen Murja, dariya Murja ta shiga yi kamar wata mai shafar jinnu, dariya take tana girgiza.
A ɓangaren Alhaji Zakari fadar mai unguwa ya nufa, ya ko ci sa a shi kaɗai ne. Bayan sun gaisa sai ya samu wuri ya zauna tare da cewa
"Mai unguwa wurin na zo"
"To lafiya Zakari?"
Share zufan data tsuttsugo masa ya yi sannan ya ce
"Ina fa lafiya mai unguwa, daga wancan sai wancan, kullum ina cikin tashin hankali da taraddudi. Na gama da ɓangaren Alhaji Sambo Dala yanzu kuma Innayi ta taso da maganar zuwa gidan auran Hujayrah"
Waro idanu mai unguwa ya yi waje sannan ya ce
"Toooo babbar magana! Wata sabuwa inji ƴan caca"
Cire hular kansa Alhaji Zakari ya yi yana fiffita sannan ya ce
"Kai dai bari gashi Zalihatuwata ta ce saina saketa, Ni kuma Allah ya ji ya gani bazan iya sakinta ba"
Wani wawan tsaki mai unguwa ya saki sannan ya ce
"Idan kun mutu a burneku a tare tsabar soyayya. Ni yanzu ba wannan ba wace mafita ka samu na zuwa wurin Hujayrah"
"Hmmmm ai mafitar na zo wurinka ko zan samu, kaga dai shi karan kansa Alhaji Sambo Dala bai san inda Hujayrah take balle na tambayesa" cewar Alhaji Zakari. Ɗan tunani Mai unguwa ya yi sai can ya ce
"Yanzu mai zai hana kace wa Inna Hujayrah da mijinta sun yi tafiya Saudiyya Umra sai nan da wata biyu za su dawo"
"Yawwa amininaaama mai unguwa, gaskiya wannan shawarar ta yi ɗari bisa ɗari, zuwa gobe zan sanar mata, shikenan na huta da tashin hankali" cewar Alhaji Zakari fuskarsa ɗauke da tsantsan farin ciki wanda baya misaltuwa. Daga haka suka ci gaba hirarsu cike da nishaɗi... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Gidan Prof. Abdulrahman Saminu Kwankiyal*
*Washe gari*
*ƙarfe 9:12am na safe*
A ɓangaren Hajiya Zinatu da wuri ta tashi ta shirya breakfast lafiyayye kasancewar Prof a ɗakinta yake. Bayan sun karya ya miƙe zai fita sai Hajiya Zinatu ta yi saurin cewa
"My prof ga pancake(kalallaɓa) na yi wa Nafisa, nasan masu ciki da son ƙwalam da maƙulashe" Tana maganar tana miƙa masa wata haɗadɗiyar kula. Lokaci guda ya washe bakinsa ya amsa kular yana cewa
"Ai kuwa ta gode"
Fita ya yi daga ɗakin zuwa part ɗin Hajiya Nafisa. Hajiya Zinatu na ganin ya fita sai saki wani ƙasaitaccen murmushi tana cewa kanta 'Sai dai wata Nafisa ba wannan ba, sai faman rawar kai yake saboda cikin kamar bai taɓa haihuwa ba, Mts!' tana gama maganar ta koma bedroom ɗinta ta kwanta dama baccin bai isheta ba.
A ɓangaren Hajiya Nafisa ita da Nazima da Halima suna zaune cikin shirinsu na fita zuwa gidan Alhaji Imrana duba Hajiya momma daga bisani ta wuce gidan Alhaji Sambo Dala gaisuwa. Suna tsaka da shiri Prof ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama. Amsa masa sallamar suka yi sannan ya ƙaraso cikin ɗakin. Za ma ya yi kusa da Hajiya Nafisa fuskarsa lulleɓe da murmushi ya ce
"Nafisa ya jikin naki" yana maganar yana miƙo mata kular da Hajiya Zinatu ta bashi ya bata. Amsa ta yi tana murmushi ta ce
"Jiki Alhamdulillah, Ina muka samu kula haka? "
"Zinatu ta soya miki Pancake, tasan ku da son ƙwalam da maƙulashe" cewar Prof yana murmushi.
Bambaraƙwai Hajiya Nafisa ta ji maganar 'wai ta yi mata pancake, ko yaushe suka fara hakan da ita oho" bayan ta amsa kula ta bude kula, tana shaƙar ƙamshin abincin nan take zuciyarta ta tashi amai ya taso mata. Wurgar da kular ta yi ta nufi sama da gudu, bata tsaya ko'ina ba ta wuce bayi, sosai take aman tana riƙe cikinta, ta daɗe tana aman daga bisani ta wanke bakinta ta canja kaya ta sauko ƙasa. Lokacin har Prof ya umurci Nazima ta kai kula cikin kitchen da alamu bata son warin pancake ɗin. Nazima na ɗaukar kular ta wuce kitchen ta zuba pancake ɗin a cikin dustbin ta ajiye kula a wurin wanke-wanke ta fito. Lokacin har Hajiya Nafisa ta sauko daga sama ta zauna kusa da Prof. Dubanta ya yi cikin tausayawa ya ce
"Sannu ashe baki son pancake ɗin?"
"Bana son warinsa wallahi" tana maganar tana yamutsa fuska. Murmushi ya yi sannan ya ce
"To ai shikenan na saka Nazima ta kai kitchen, yanzu gidan Imran za ku fara zuwa ko?"
"Eh, Nazima za ta ja mana motar yau saboda Mas'ud office sun kira Mas'ud yana aiki urgently sannan ba a garin nan ba ne" cewar Hajiya Nafisa.
"To ai shikenan, Ni yanzu zan wuce makaranta" yana maganar yana miƙewa. Su ma miƙewan suka yi. Halima ta riƙo jakar Hajiya Nafisa suka fito. Nazima ta zauna a mazaunin driba, Halima kuma front sit sai Hajiya Nafisa ta zauna a baya. Motar Prof ne a gaba,sai nasu Nazima a baya suka ɗauki hanya... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Gida-dubu, Gubi Housing Estate, Bauchi State. Nijeriya*
A ɓangarensu Hujayrah Alhamdulillah Hajiya momma bata farka cikin dare ba. Washe gari da asuba Hujayrah ta taimaka ta yi brush,ta sha tea sannan ruwan addu'ar ta bata ta ɗan sha ƙadan sannan ta shafa mata sauran ruwan a duk ilahirin jikinta. Sosai Hajiya momma take jin azaba da raɗaɗi a ko'ina na jikinta. Kamar ana mata suyar hanci haka take ji a cikinta,kusan mintuna goma tana a wannan yanayin daga bisani bacci ya ɗauketa. Sauke ajiyar zuciya Hujayrah ta yi sannan ta miƙe zuwa falo, tana zaune tana karyawa kasancewa yau Razina ta tafi makaranta, su suka haɗa wa kansu breakfast. Tana gama ci ta miƙe ta kai kayan kitchen sannan ya wuce ɗakin yin wanka. Tana fita da kusan mintuna ashirin sai ga Arqam ya shigo ɗakin, kai tsaye ya wuce bedroom ɗin Hajiya momma ya duba ta sai ta dawo falo ya zaune. Sai waige-waige yake yana tunanin ina Hujayrah ta je ton yunwa yake ji, ya zo da Sandwich ɗinsa yana so da dafa masa ruwan zafi. Shiru-shiru bata dawo ba, har ya miƙe zai fita sai ka Talatu ta shigo falon bakinta ɗauke da sallama, ciki-ciki ya amsa mata sannan ya ce ta dafa masa ruwan zafi yanzu. Babu musu ta wuce kitchen farin ciki fal! Ranta za ta samu damar aiwatar da aikin Hajiya sama cikin ƙanƙanin lokaci da samu maƙudan kuɗi. Bata daɗe ta dafa masa ruwan zafi bayan ta yi yadda Hajiyan Sama ta umurceta ta yi da gubar. Fitowa ta yi da flask a hannunta ta kawo masa har gabansa sannan ta koma ciki ta ɗauko plate wanda ke ɗauke da kayan shayi da ajiye. Sai ta sake komawa ciki don ta gyara kitchen ɗin. A hankali Arqam ya haɗa tea ɗinsa Mai kauri, ya ɗaukaka zai kai bakinsa sai wayarsa ta yi ƙara ya ajiye mug ɗin a gefe, ya ɗauki kiran kasancewar P.A ɗinsa ne Bilal ya kira, da yake yana can Germany yana kula da business ɗinsu na can kafin Arqam ya koma. Sun daɗe suna waya har Hujayrah ta dawo cikin falon melonta na biye da ita. Hujayrah na ganin Arqam na wuce wurinsa fuskarta ɗauke da murmushi daman abincin magenta ya ƙare sannan magen bata son wani abinci sai wannan. Ta tarar dashi yana waya sai ta ɗauki Mug ɗin shayin don tsokana za ta sha tashi yadda yake. Tana kaiwa bakinta kanta yayi mugun sarawa. Da sauri ta dafe kanta tana addu'a,shayin ta kalla na tsawan wasu sakanni sannan ta buɗe flask ɗin ta kalla shi ma na ɗan wasu sakanni. Lokaci guda annurin fuskarta ya sauya, jira take ya kammala wayar ta tambayi wsya dafa masa shayin. Yana kammala waya hannunta riƙe da Mug ɗin ta ce
"Ya Raqam qam waya dafa maka ruwan zafi?"
Wani kala ya ji maganar tasa, bai kawo komai a ransa ba ya fara magana cikin cold deep voice ɗinsa.
"Wacce ta dafa ruwan tana kitche... "
Bai ƙarasa abin da ya yi niyyar faɗa ba sai ga Talatu tsulum kamar an jefota za ta fita daga falon. Lokacin da Hujayrah ta haɗa ido ta Talatu gaba ta sai da ya yi mugun bugawa har tana safe ƙirjinta. Cike da tsawa haɗi da umarni Hujayrah ta ce
" Ke! Zo nan"
Wani mugun kallo Talatu ta jefa wa Hujayrah ganin Arqam na kusa sai kawai ta iso inda suke. Miƙa mata Mug ɗin shayin Hujayrah ta yi fuskarta a ɗaure ta ce
"Gashi ki sha"
Dummmmm! Haka ƙirjin Talatu ya bada, ai ko hauka take bata ta yi gigin shan wannan shayin ba. Lokaci guda Talatu ta rike, Arqam ɗai kallon su kawai yake yana so yaga yadda wasan zai fara. Kafin Talatu ta ce wani abu sai ga Alhaji da Hajiya Sama sun shigo ɗakin bakinsu ɗauke da sallama. Da sauri Talatu ta amsa musu sallamar a tunaninta tunda ga uwargijiyanta tasan bazata bari asirin su ya tonu ba. Ita kuwa Hajiyan Sama ba don duba Hajiya momma ya kawota ɗakin ba ne, ta zo dubawa ta gani ko Talatu ta aiwatar da aikinta data bata. Ko kallon inda Hajiyan Sama Hujayrah bata yi, cike da girmamawa ta gaida Alhaji amma taƙi gaida Hajiyan Sama, sosai Hajiyan Sama ta ƙulu duk da gabanta na faɗuwa ganin Talatu a gaban Arqam. Kafin ta yi magana sai ga su Hajiya Nafisa sun shigo falon, a nan suka yi wata sabuwar gaisuwan daga bisani ɗakin ta yi shiru. Ganin Talatu na tsaye Alhaji ya ce
"Lafiya Talatu na ganki tsaye, Arqam ko kai kace ta tsaya"
Caraf Hujayrah ta caɓe da cewa
"Abbu ni nace ta tsaya tambayarta zan yi"
"OK"
Miƙewa Hujayrah ta yi ta zo kusa da Talatu tana miƙa mata Mug ɗin shayin da cewa
"Ungo Kisha"
Da sauri Talatu ta ce
"Taya zan sha a kofin Ya Arqam, ai bai dace ba"
"Wai lafiya Hujayrah kika wani tsare mai aiki, Ina ruwan ki da ita, naga Kema ƴar aikin ce kamarsu, ko dan kinga an kara ki cikin dangi shi yasa kike yin yadda kika so" cewar Hajiyan Sama tana watsa wa Hujayrah mugun kallo. Madadin Hujayrah ta ji haushi sai ma murmushi data saki tana cewa
"Hajiyan sama idan kinga matar nan tabar ɗakin to shayin nan ta shanye duka..."
"Dallah malama tafi can ki bamu guri, ke har kin isa ki sakata sha shayi a kofin Arqam, ƴar aiki ne za ki sa tasha shayin Arqam"
"Ban yarda da shayin ba ne kuma ita ta dafa masa shiyasa nace tasha, idan kuma taƙi sha to tabbas abin da nake tunani haka ne" cewar Hujayrah tana saukar wa Hajiyan Sama ƙasaitaccen murmushi har da kace mata ido. Su dai ƴan ɗaki da ido suke kallon idon Allah, kowa ya masu yaga yadda wasan zai kaya.
"Babu wani abu da Talatu ta saka a cikin shayin, matar da takai shekera da shekaru tana musu girki a ce ta saka wani abu a cikin shayin Arqam, meyasa a da can bata saka ba. Wani daɗi Hujayrah ta ji, a ranta tana cewa *'Da kyau an zo wurin'* Hujayrah barin Talatu ta yi ta wuce wurin da Hajiyan sama take zaune ta miƙa mata Mug ɗin shayin tana cewa... ✍️
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
***