20
by @asmybaliyu
by
Asmy b Aliyu
20.......
Yana zaune gefen bed Yana danna wayar hannunsa yaji karar bude kofar bathroom din.ya daga Kai Yana kallon kofar.tana tsaye a bakin kofa.daga ita sai mini towel ajikinta fari kal Wanda ko gama sauka akan cinyoyinta baiyi ba.tasani da ganga
ta dauro towel din dan ta Kara birkitasa da kallonta tayi nasara kuma.dan kasa dauke idonsa yayi akanta tamkar an kafe
idon nasa wani abu yaji ya tsaya daidai makoshinsa haka ya kasa wucewa.
lokaci daya yaji abunda yakeji a mararsa
Yana kokarin dawowa.hannunsa daya
ya saka daidai mararsa ahankali cikin
takun natsuwa.malaak ke tunkarosa
da duk duk takun da take tana qarasowa
wurinsa Kara birkitasa yake da idonsa yake girgiza mata kai.haka idon nasa na kankancewa lokaci daya,bata fasa tun Karosa ba har lokacin ruwan da tayi
wanka da gashinta da ya jike a hankali suke sauka Suna zuba akan jikinta.
Kai tsaye akan cinyoyinsa tayiwa kanta masauki.
da wata irin kwarewa da salo mai Jan hankali da kissa ta duka daidai kunnensa,ta fiddo harshenta ta lashi kunnensa kafin ta bude baki cikin saukar da murya take fadin."I want you
I want to marry you doctor na."wani irin tashi tsikar jikinsa ta farayi da gaske
malaak neman kashesa take sonyi
Kara laso fatar kunnensa tayi da gangan
take kokarin zame dan towel din jikinta
da albarkartun kirjinta suka dan fito sarari......kansa yaji Yana mugun juyawa
haka iskan da yake shaka a dakin yaji ya fara yimasa kadan ,da wani irin sauri
ya mike tsaye daita a jikinsa.duk kokarin
son takai jikinta cikin nasa ya hana
hakan dan da sauri ya katseta Yana fadin"
ki xauna anan zanje na dubo mai delivery idan ya kawo sakon kayanki da nayi oder ta shop dinsu.da haka ya juya ya nufi
kofa bayan ya fita ya rufo mata kofar a natse ta zube kan gado........tana sauke wata irin ajiyar zuciya Banda murmushi babu abunda takeyi bata taba tsintar kanta cikin farin ciki irin wannan ba
haka mu'azzam bai taba bata farin ciki kamar wannan ba wannan shine best moments din da ta taba samu tareda mu'azzam din tsawon rayuwar da sukayi a tare......murmushi take saki ita kadai
cike da shauki.batasan ta dauki lokaci a haka ba taji an murda kofar dakin an shigo
da sauri ta mike tsaye har lokacin da ruwa akanta ta karbi bag din hannunsa mai dauke da sunan kantin ajiki.ta nufi toilet
Sai da ta Kara daukar lokaci wurin shirya kanta.dan sai da ta saka drayer ta busar da gashin kanta.
koda ta fito Yana zaune a dakin
ya daga kai ya kalleta yadda kayan suka zauna daidai jikinta tamkar dan ita akayi
Turkish abaya din.gaban mirror ta karasa
ta dauki daya daga cikin turarrukansa da ya jera ta shiga fesawa......ya mike tsaye
Yana kallonta Yana fadin."zanje nayi sallar
magrib kema kinyi sallah idan na dawo zamu fita muyi dinner yunwa nakeji.
da haka ya fice daga dakin tana binsa
da kallon so jin take tamkar ta jawosa
ta boye acikin jikinta ta yadda babu
maccen da ta isa ko kallonsa tayi.
kan bed ta koma tayi kwanciyyarta
batareda tunanin yin wata sallah ba
datar ta ta bude taci sa'a noor
na online......anan Suka fara hira ta fadamata idan tagama da mu'azzam Zai sauketa a gidansu anan Zata kwana.
bakaramin dadi noor din taji ba
jin malaak din xata kwana a gidansu
batareda kowa ya xaba mata hakan ba.............
#########
Bayan ya dawo daga sallah suka Kara fita suka sauka down stairs suka nufi wani VIP dake cikin hotel din Mai dauke da babban balcony aka kawata wurin da wasu irin fitullu da kujerun zamani harma da table
kallo daya xakayiwa wurin kaga wurin
masoya.wurin yayi shiru sosai babu wata hayaniya,gaban table din da aka axa card mai dauke da sunan sa suka nufa,tuni aka cika wurin da abububuwan motsa baki
Yana zama ya bude mug din da aka hadamasa turkish tea din da Sai tiriri
yakeyi.ta tallabe chins dinta kawai
tana famar kallonsa tamkar an bata aikin
yin haka.babu wata yunwa da takeji
ganinsa kawai ya wadatar ban da drink
din da ta tsiyaya cikin cup glass
ta dauki cup din ta fara sipping cikin
natsuwa da wani irin class,Yana dago
kansa yaga shi take kallo Sai ya Kashe
mata ido daya.dan juya masa ido
tayi Sun dauki lokaci babu mai magana
acikinsu.kafin mu'azzam ya motsa shirun da Kiran sunan malaak din.wanda yasa ta tattara hankalinsa akansa.tun Ranar kince
zamuyi magana bamu samu damar maganar ba.ga daman ya samu ko zamuyi iya yin maganar a yanxu.??"da gaske
ka shirya jin abunda zan fada?"ta tambaya da wani yanayi a muryarta tana kallonsa
a natse ya dagamata kai.wani irin murmushi ta saki.............Yaushe zamuyi Aure??"ya kamata iyayenmu su San da maganar duk da Sun sani mu fara
taka matsayin da xai kaimu gayin Auren,
kamar yin baikonmu sadaki da saka rana......wani irin kwarewa yaji yanayi
da tea da yayi sipping yaji Yana Shirin biyo
masa ta cikin hanci da sauri ya aje cup din
ya shiga tari sosai a rude malaak din
ta mike tsaye ta zagaya bayansa tana dan bubbuga bayan tana famar jera masa sannu.sai da tarin ya lafa ta bude water bottle Kai tsaye ta nufi bakinsa babu musu ya bude bakin ya fara sha.
bayan ya sha ta Jaye water bottle din
a hankali yake fadin"Thank you ta dan matsa kafadansa cike da kulawa da tattalinsa take fadin......."sorryyy!!!"
jin yayi wani abu na karyewa acikin zuciyarsa lokaci daya.musamman da ya kalli malaak din wani irin tausayinta
yaji ya lullubesa lokaci daya.bai San me zataji ba idan ya fadamata da bakinsa
maminsa bata raayinta wata takeso
a matsayin suruka daban ba malaak din ba..........wani irin mugun nauyi harshensa
yayi masa haka kalaman Mami na dawo
masa na wancan Ranar.jin yayi baxai
iya fadawa malaak wannan gaskiyyar da zatayi hurting dinta ba gaskiyyar da idan taji yadda yasan malaak din da mugun rauni musamman akansa zuciyarta Zata iya tarwatsewa........
da gaske kin shirya aurena?"tambayar taji a bazata.da sauri ta daga Kai tana kallon
cikin idanunsa Kai tsaye idanun dake
Kara Kashe duk wani kuzarin ta.
mezai hana idan ka shirya nima na shirya.
ya dan girgiza Kai Yana so ya fadamata
kalaman da Zata rike na wani lokaci
kafin ya shawo kan Mami....akwai wani project da bamu Kammala ba yanxu ma Zaa fara aikin zai daukemu a kusan shekara ko xaki dagamun kafa.zuwa
lokacin an Kammala komai Sai muyi koman acikin kwanciyyar hankali.
kallonsa take tana jin wani iri a zuciyarta
ta fara tambayar kanta wane irin project ne mu'azzam zaiyi da zaiyi shekara yanayinsa.?"ganin yanayinta yasa ya Kara fadin"project din Yana da matukar amfani
cikin rayuwarsa yafison agama dashi
Shima hankalinsa zaifi kwanciyya.ajiyar zuciya malaak din ta sauke Yana kallon
yanayinta.da sanyin da tayi lokaci daya
Sai yaji duk babu dadi Kara yayi mata
wannan Karyar da ya fadamata gaskiyyar
da zatayi hurting dinta......Allah ya kaimu
ta fada tana kallon cikin fuskarsa
tamkar maison gano wani abu acikin fuskar.ya saki murmushi Yana fadin Amin
"matar mu'azzam marafa.sunan da ya Kirata dashi din yasa taji kanta ya Kara mugun girma.a natse yaci abincinsa,
Yana gamawa suka Kara taba hirarsu ta masoya.sai da yayi sallar ishaai sukabar hotel din Kai tsaye ya nufi unguwarsu
noor.suna isa first gate kawai suka
tsaya saboda security dake first gate
idan baa kirasu daga ciki akace
zaayi baki ba basa bude get ta biyu
saboda tsaro............ya Kashe motar
Yana kallonta ,ganin yanayinta yasa
ya kamo hannunta Yana murxawa cikin
nasa hannun.kafin ya kira sunanta a hankali daga Kai tayi tana kallonsa,
duk Sai yaji jikinsa yayi sanyi musamman da yaga yanayinta ya canja.wani irin tausayinta yaji ya cika masa zuciya.
acikin shekara dayan nan da ya diba
in sha allahu zaiyi kokari ya shawo
kan Mamin.haka alkawari ne
ya daukarwa kansa wata shidda data dibar masa komai zai faru babu matar da xai fitar
a haka Mami Zata hakura tabarsa da zabinsa dan har abada baya tunanin
Mamin zatayi masa auren dole.......wayarsa
ce ta fara ring.fareeda ce mai Kiran batareda ya dauka ba ya kife wayar
Yana rarrashin malaak Yana fadamata
shekara kamar gobe ce zataga tazo.
haka aka Kara Kiran na biyu nan ma
bai daga ba ,bayan wasu mintunan
aka Kara Kiran da sauri malaak ta cire
hannunta cikin nasa.a matse take fadin."Ka daga wayar mana nan take
mood dinta ya canja Yana daukar wayar
ya haska mata wayar sunan Queen 👑
ta gani sunan da ya tsayar da bugun zuciyarta na dan wani lokaci.nan take
mugun kishi ya rufe mata zuciya
babu xato yaji ta fisge wayar cikin
bacin rai Zata daga ya rike mata
hannuwa ya hanata daukan Kiran
cike da tashin hankali yake kallon malaak din da take neman xarewa.me xakiyi?"
idan Suna agaban Mami fa?"me xakice."
duk a rikice ya jera mata tambayoyin
fisgen kanta tayi daga rikon da yayi
mata.........
meyasa Sai ita?"me Zata fadamaka a wannan lokacin ya'r aikin gidanku fa mu'azzam?"meye alakarku meyasa
kuke nuna matsayinku daya daita
meyasa kullum wannan Yarinyyar
tana gefenka ka fadamun....Her voice rose with every question, each word sharpened by jealousy and resentment.
ta birkice masa hausar ma gaba daya gagararta ta farayi ta juye masa ta koma
masa asalin baturiyyarta.a hankali ya rike
fuskarta Yana ta kokarin tsiyarda fushin da ya rufe mata ido,Yana ganin kwallar da ta taru a idanunta baida zabi ya hade bakinsa da nata ya tsotse bakinta da Sai da ya tabbatar da duka jikinta ya karbi sakonta ya saketa.
kanta kawai ta hade da gwiwa tana sauke numfashi.wata irin mugun tsanar Yarinyyar
taji tana cika mata zuciya tsanar da bata taba yiwa wani biladama ba.sai da ta dan dawo daidai ta kallesa tana fadin
ya bude mata kofa.ya kwantar da kansa jikin seat Yana kallon cikin idanunta
baki hakura ba kenan?"ke a tunaninki
zan taba soyayya da queen din ne
sa'an fa fareeda.wanda da nayi aure da wuri da zan haifeta allah ya kiyaye kima daina wannan tunanin yadda kika San babu aure tsakanina da fareeda haka babu
aure a tsakanina da Ayusherh har abada....dan sanyi taji a zuciyarta Sai da ya tabbatar ta hakura sa'annan yayi mata
sallama ya tafi.....
#ASMY B ALIYU
#LOVE/FATE
#HOTLOVE
#MU'AZZAM MARAFA
#MALAAK FAROOK RANO
#OMRI HAYATII
#***