FADIANA

Chapter 6: Two different worlds

by @hauwajaywrites

Ƙarfe bakwai na safe, Rayyan yana kwance a kan gadonsa lokacin da wayarsa ta fara ringing bayan ya dawo a masallaci, da farko bai damu daya ɗauka ba, sai da ta sake ringing karo na biyu sannan ya miƙa hannu ya ɗauko ta


Yana ganin sunan da ya bayyana a screen ɗin, murmushi ya subuce masa ‘My Peace’


Ya amsa video call din “Good morning, Sleeping Beaut” ya faɗa cikin muryar wanda bai gama farkawa ba


A ɗaya ɓangaren, Safiyya ta ɗaga gira tana kallonsa “Sleeping Beauty? Habibi have you looked at yourself in the mirror this morning?”


Ya buɗe idanunsa sosai, sannan ya mike ya zauna “What’s wrong with me?”


“Everything! Look at your face kawai, kamar wanda aka yi wa dukan tsiya a mafarki fah”


Ya fashe da dariya, ita kadai kuma ke iya sashi dariya duk da anger issues dinsa “Wow! Wannan ce good morning ɗin da zan samu daga wajen princess?”


“Me kake so in ce maka? Good morning my handsome prince?”


“Exactly!”


Safiyya ta yi dariya ta girgiza kai “Dream on, my dear”


Rayyan ya yi murmushi yana kallonta, wannan ɗaya ne daga cikin abubuwan da yake so a tare da Safiyya, tana iya zolayarsa ba tare da ta ɓata masa rai ba, tana iya sa shi dariya ko da kuwa yana cikin damuwa, sannan tana da wata nutsuwa da yake jin daɗinta


Sun shafe kusan shekara biyu suna soyayya

Rayyan yana son yadda Safiyya take fahimtar burinsa. Ba ta cika takura masa ba, kuma tana ba shi damar yin abubuwan da yake ganin za su inganta rayuwarsa. A ganinsa, Safiyya mace ce da zai iya gina rayuwa da ita


“So, Yau ɗin zaka zo?” Safiyya ta tambaye shi


Rayyan ya duba agogo “I have a meeting by ten. I’ll call you when I’m done”


Safiyya ta yi shiru na ɗan lokaci “That’s what you said yesterday”


“And I called you”


“At eight-thirty in the evening ba!”


Ya sauke ajiyar zuciya “Safiyya, munyi magana akan wannan ai”


“Yes, and we’ll keep talking about it until you understand that being in a relationship means making time for the other person”


Fuskarsa ta ɗan canza, ba wai bai damu da abin da take faɗa ba ne, amma shi yana ganin yana ƙoƙari. Yana aiki tuƙuru, kuma yana ƙoƙarin gina rayuwar da yake son su more tare a nan gaba


A tunaninsa, duk wannan ya Isa yasa tasan cewa yana sonta, ba lalle sai suna haɗuwa kullum ba


“Look, I know I’ve been busy, okay? Amma zan kokarta I’ll make it up to you today In shaa Allah”


Safiyya ta zuba masa ido ta screen ɗin “kayi alkawari?”


“I promise”


Ta runtse idanunta kaɗan “Habibi alkawarinka da yana expiring”


Ya yi murmushi “Then I’ll renew this one”


Safiyya ta yi dariya “There! That’s the Rayyan I know”


Ya ci gaba da kallonta na ɗan lokaci, murmushin da ke fuskarsa har sannan yana nan “Have you had breakfast?” ya tambaya


Ta ce “No”


“Why?”


Ta ce “Because I’m talking to someone who thinks a video call is more important than food”


Ya girgiza kai “Go and eat Safiyya”


“Only if you eat too”


Kamar mai tunani ya ce “Toh”


Ta ce “And send me a picture”


Rayyan ya ɗan zuba mata ido “Of my breakfast?”


“Of yourself genius, I want to see what you’re wearing”


Ya ce “Why?” ta ce “Because I want to”


“That’s not an answer”


Ta ce “Okay, wato sai ma na fad’i dalilin?”

Ya yi dariya “You’re impossible”


“And yet, you love me”


Murmushinsa ya ƙara bayyana a fuskansa “Yes, I do”

Safiyya ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta murmusa “I love you too” a haka har suka gama waya


Ya ajiye ta a gefe, sannan ya jingina da gadon yana tunani, yana son Safiyya


Yana son nutsuwarta, kyawunta, yadda take fahimtar burinsa da kuma yadda take ƙoƙarin zama wani ɓangare na rayuwarsa though suna samun saɓani a wasu lokuta


Me kuma zai nema fiye da haka?


Da ya sauka ƙasa, sai ya tarar da iyayensa a dining room, while Rameez yana zaune yana cin abinci kamar wanda za a kwace masa plate din


Rayyan ya tsaya yana kallonsa “Ikon Allah! Are you being chased by someone?”


Rameez ya ɗago kai yana tauna abincinsa “Me?”


“Kana cin abinci kamar wanda rayuwarka tayi depending akai”


Rameez ya haɗiye abincin, sannan ya ce “Eh my life does depend on it ba kamar kai ba, I don’t spend forty-five minutes admiring myself in the mirror”


Rayyan ya ja kujera ya zauna “Good morning


Rameez ya ce “Good morning, Mr Handsome”


Mahaifiyarsu ta girgiza kai tana murmushi

“Ba za ku iya yin breakfast ɗinku lafiya ba sai kun fara da tsokana?”


“No Mom” Rameez ya amsa da sauri “It’s against our family tradition”


Rayyan bai kula shi ba, ya miƙa hannu ya ɗauki bread


Mahaifinsu ya ɗago kai daga abincinsa

“Ya meeting naku na jiya ya kasance?”


“Fine Dad, already mun riga da munyi settling din issues din, I just need to review the revised proposal before we proceed”


“Yauwa, amma kada kayi gaggawan yanke hukuncin, make sure you examine the figures carefully”


“I will”


Mahaifinsu ya gyada kai cikin gamsuwa, yana jin daɗin yadda Rayyan yake iya sarrafa kansa idan ya fuskanci matsala. Ba ya yanke hukunci cikin gaggawa, kuma yana ƙoƙarin bincika abubuwa kafin ya ɗauki mataki


Sai dai wani lokacin wannan natsuwar tasa tana haɗuwa da taurin kai, musamman idan ya riga ya yanke shawarar cewa shi ne yake da gaskiya


“Are you meeting Safiyya today?” mahaifiyarsa ta tambaya


Rayyan ya ɗago kai “Yes, why?”


“Nothing, kawai na tambaya ne” Rameez ya ɗan ajiye cup ɗinsa a hankali “Ahhh Safiyya!”


Rayyan ya kalle shi “What about her?”


“Aa fah, babu komai bro I was only appreciating the name”


“Appreciate your breakfast instead”


Rameez ya yi murmushi mai nuna cewa bai gama ba fad’in abunda ke cinsa ba “shekaru biyu kuna tare and you’re still behaving like a newly married man”


“Rameez!”


“What? I’m happy for you! Love is beautiful. Love is sweet. Love makes a grown man smile at his phone before brushing his teeth”


Mahaifiyarsu ta fashe da dariya, Rayyan ya ajiye sandwich ɗin da ke hannunsa “Ka gama?”


“Aa da saura amma karka damu I’ll save it for your wedding”


“Save your speech for your own wedding”


Rameez ya dafe ƙirjinsa kamar wanda aka yi wa rauni “That hurt! I was only celebrating your love”


“Celebrate it quietly”


Mahaifinsu ya koma duba tablet ɗinsa, amma murmushi ne bayyane a fuskarsa


Duk da yawan tsokanar da suke yi wa juna, akwai soyayya a tsakaninsu. Rameez ya san yadda zai ɓata wa ƙaninsa rai, shi kuma Rayyan ya san yadda zai nuna kamar bai damu ba


Bayan sun gama breakfast, Rayyan ya ɗauki key ɗinsa yana shirin fita


A ransa yana ayyana yau zai ba Safiyya lokacinta yadda ya kamata, zai gama aikinsa, ya je ya ɗauke ta, sannan su ɗan fita date


Rahama ta tsaya cak a cikin ɗakinta, ta kalli ƙofar, sannan ta kalli agogo “Ya Allah! What have I done again?”


“RAHAMA!”


“Coming, Mammy!” Ta yi saurin ɗaukar handbag ɗinta, while da take ƙoƙarin gyara ɗankwalinta, edge d’in ya kama jikin wardrobe d’in


Ta ja da ƙarfi, sai kuma taga kamar zai yage, ta sake ja, wayarta ta faɗi kan gado, lip balm ɗinta kuma ya mirgina ya shiga ƙarƙashin dressing table


Rahama ta tsaya tana kallon abubuwan da suka faru, sannan ta ɗaga kai sama “Subhanallah! Is this how my day is going to start?”


“Rahama!”


“I’m coming Mammy! Ko kina son in sauko ba tare dana shirya bane?”


“Ke kika sani, kar ki bari na hauro saman nan tahm”


Rahama ta buɗe baki “Wow! So this is how mothers treat their innocent daughters?”

 Ta ƙwace ɗankwalin, ta gyara shi da sauri, sannan ta ɗauki wayarta ta fita daga ɗakin


Bayan ta sauka sai ta tarar da mahaifiyarta a tsaye kusa da dining table, ta haɗe hannayenta a ƙirji


Rahama ta rage saurin tafiyarta bcos ta san wannan look ɗin


Ba look ɗin tambaya ba ne, look ɗin da ke nuna cewa an gama haƙuri ne


“Good morning Mammy” ta faɗa cikin muryar mai taushin Hali


Mahaifiyarta ba ta amsa ba, Rahama ta ɗan karkatar da kai “Silence? Mammy kina azumin magana ne?”


“Rahama”


“Yes, ma?”


“Ki kalli time din nan”


Rahama ta juya ta kalli agogo, ta yi shiru, ta sake kallon agogon, kamar tana tsammanin lambobin za su canza idan ta yi musu kallon ban tausayi “Oh”


“Oh?” mahaifiyarta ta maimaita, Rahama ta yi murmushi “I can explain”


“Ina jinki, yi bayani”


Rahama ta gyara tsayuwarta “That depends on how we define preparing”


Mahaifiyarta ta lumshe idanunta “Ya Allah, ka ba ni haƙuri da yarinyar nan”


“Ameen!” Rahama ta amsa da sauri “Da lafiya, arziki, da tsawon rai ma Mammy”


Mahaifiyarta ta buɗe idanunta ta kalle ta “Rahama!”


“Sorry, ma” Ta nufi dining table ta zauna, ta ɗauki bread


“Ki ci abinci a nutse kuma, bana son wannan rashin nutsuwar taki” mahaifiyarta ta faɗa


“I know, Mammy”


“Kada ki ce kin sani alhali gobe za ki sake maimaitawa”


Rahama ta ɗan yi tunani “shikenan barin sake cewa I know ba”


Mahaifiyarta ta kalle ta, Rahama ta ci gaba da cin sandwich ɗinta “Problem solved”


“Wlh wata rana za ki kashe ni da shirmenki”


Rahama ta ajiye sandwich ɗin, ta miƙa hannu ta rungume mahaifiyarta “No Mammy! First, zan yi kuɗi sosai, in saya miki gida mai kyau, in kai ki Umrah, sannan ki riƙa yi mini faɗa cikin kwanciyar hankali”


Mahaifiyarta ta yi ƙoƙarin ɓoye murmushinta“Wane ne ya ce ina son gida?”


Rahama ta zaro ido “You don’t want a house? Fine! I’ll buy you two”


“Rahama!”


“Three then, Let’s not limit Allah’s blessings”


Mahaifiyarta ta kasa daurewa, ta fara dariya tana girgiza kai


Rahama ta yi murmushi, sannan ta koma cin abincinta


Ita ce Rahama. Ko tsawatarwa za ta iya mayar da ita abin dariya, kuma idan aka ba ta dama, za ta iya mayar da tambaya ɗaya ta zama lecture na tsawon mintuna talatin


Amma duk da shirmenta, ba ta son zalunci, kuma idan ta ga ana zaluntar wani, sai ta ji kamar ita ake yi wa


Bayan ta gama breakfast, Rahama ta samu saƙo daga ƙawarta Maryam


Da ta karanta saƙon, sai fuskarta ta canza


Maryam: Rahama please, ina buƙatar taimakonki. Something happened at my training centre. Ana zargina da abin da ban yi ba, kuma babu wanda yake son ya saurare ni


Rahama ta karanta saƙon sau biyu, ta ɗaga kai ta kira mahaifiyarta “Mammy?”


“Me kuma?”


Rahama ta ɗan yi shiru “Can I go out for a while?”

“Fitan namu fah, ina zaki yanzun?”


“Wani waje”


Mahaifiyarta ta juyo ta kalle ta “Rahama”


“Okay, somewhere with an address”


“Kada ki fara”


Rahama ta ce “I’m trying to be a responsible adult Mammy. Responsible adults suke tambayar iyayensu kafin su fita a gida”


“Responsible adults also suna fad’in inda zasu je wa iyayensu”


Rahama ta yi murmushi “Exactly, that’s the next stage of my development”


Mahaifiyarta ta ajiye abin da ke hannunta “Me ya faru?”


Rahama ta nuna mata saƙon “Maryam ce, ta ce ana zarginta da wani abu a training centre ɗinsu, kuma tana buƙatar in je”


“Kin san abin da ya faru ne?”


“No Mammy”


Mammy ta ce “Ki je, amma ki yi a hankali, kada ki shiga abin da ba ki fahimta ba”


“I won’t, Mammy”


“Kuma kada ki yi musu gardama ko tsiwa”


Rahama ta buɗe baki cikin mamaki “Me? Ni?”


“Eh, ke”


“Mammy, I’m offended”


“Good ki tuna da wannan feeling ɗin idan kin je can”


Rahama ta dafe ƙirjinta “I am a peaceful person”

Mammy ta ɗaga gira “Rahama halinki fah Kenan, ko ba ke bane watan da ya wuce kika yi gardama da wani a supermarket saboda ya tsallake layi”


Rahama ta ce “He was wrong!”


“Kuma and still a watan kin yi gardama da neighbor dinmu sbd ya ajiye mota a gaban gate”


“He was also wrong!”


Mahaifiyarta ta buɗe baki za ta ƙara magana, amma Rahama ta yi saurin katse ta “ Mammy! Me ya sa kike sake bin duk tarihin rayuwata haka? Akwai wani shari’a ne da ake yi a kotu wanda ban sani ba?”


Mahaifiyarta ta girgiza kai tana murmushi “Ki dai yi hankali”


Rahama ta matsa kusa da ita ta sumbaci kumatunta “I will Mammy, I promise” Ta ɗauki handbag ɗinta, sannan ta juya ta nufi ƙofa


“Rahama!”


Ta tsaya “Yes, ma?”


“Kada ki jawo matsala ko magana pls”


Rahama ta yi murmushi “Me? Ni zan dawo da matsala? Mammy haba mana do I look like a problematic person?”


Mahaifiyarta ta kalle ta daga sama har ƙasa “Yes”


Rahama ta buɗe baki “Wow!” Sannan ta juya da sauri kafin mahaifiyarta ta sake faɗin wani abu

Da Rahama ta isa training centre ɗin, ta tarar da wasu mata a tsaye suna raɗa-raɗin magana. A cikin ɗakin kuma, wata mata mai kama da supervisor tana yi wa Maryam magana cikin fushi


Maryam idonta sunyi jajayen idanu saboda kuka


“Maryam!” Rahama ta kira ta


Maryam ta juyo, da ta gan ta sai ta ƙaraso gare ta “Rahama, thank God kin zo”


“Me ya faru?”


Maryam ta yi mata bayanin abin da ya faru, an samu kuskure a wasu documents, sai supervisor ɗin ta zargi Maryam da cewa ita ce ta canza bayanan da ke ciki


Maryam ta dage cewa ta yi abin da aka umurce ta ne kawai, amma babu wanda yake son ya saurare ta


Rahama ta saurara har ta gama magana “Kin ajiye copy ɗin document ɗin da kika aika?”


Maryam ta gyada kai da sauri “Eh, yana cikin wayata”


“Good! Kina da saƙon da suka aiko miki da umarnin?”


“Eh”


“Show me”


Maryam ta miƙa mata wayar, Rahama ta duba saƙonnin, ta kwatanta su da bayanan da ke cikin document ɗin. Bayan ɗan lokaci, sai ta ɗaga kai


“Wait… sun aiko miki da wannan instruction ranar Talata?”


“Eh”


“Ke kuma kika aika document ɗin ranar Laraba?”


“Exactly”


Rahama ta sake duba saƙon “To, idan ke kika bi umarnin da suka ba ki, ta yaya za su zarge ki da kin canza document ɗin da kanki?”


Maryam ta sauke muryarta “Supervisor ɗin tana cewa ba ta amince da wannan version ɗin ba”


Rahama ta yi shiru ta ji fushinta yana tasowa, amma ta tuna da maganar mahaifiyarta ‘Kada ki yi musu gardama’ Ta sauke numfashi a hankali


Ta gyara hijab ɗinta, sannan ta nufi wajen supervisor ɗin “Good morning, ma”


Matar ta kalle ta“Yes? Who are you?”


“Sunana Rahama ni ƙawar Maryam ce, dan Allah Ma, ina so in fahimci abin da ya faru”


“This is an internal matter. You should stay out of it”


Rahama ta gyada kai “I understand Ma, ba na son tsoma baki, amma ina ganin akwai yiwuwar an samu misunderstanding”


Matar ta haɗe hannayenta “What misunderstanding?”


Rahama ta nuna mata saƙonnin da ta duba, ta yi mata bayanin abin da ta lura da shi


Da ta gama, sai supervisor ɗin ta ce “ Hakan bai canja komai ba, ya kamata ta san abin da ya dace tun da far.” 


Rahama ta zuba mata ido ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta yi murmushi

Murmushin nan nata da yake nuna cewa tana ƙoƙarin riƙe bakinta kada ya jawo mata matsala


“With all due respect ma, how was she supposed to know better than the instructions she was given?”


Fuskar matar ta canza “Are you questioning my authority?”


Rahama ta ji zuciyarta ta buga “ A’a fa, ina tambayar sahihancin hukuncin da aka yanke ne, they’re two different things”


“Young lady, you need to watch your tone”


Rahama ta haɗiye yawu, a ranta tana ma kanta mgn ‘Rahama, remember Mammy. Kada ki yi gardama. Ki yi magana cikin ladabi’


Ta sake numfashi “I’m sorry if I sounded disrespectful ma, that wasn’t my intention amma please, idan akwai wata hujja da ke nuna cewa Maryam ce ta sauya takardun da kanta, muna son mu gani. Idan kuma babu, watakila ya kamata ki sake duba saƙonnin kafin ki yanke hukuncin cewa ita ce mai laifi”


Matar ta zuba mata ido na ɗan lokaci, sannan ta karɓi wayar ta fara duba saƙonnin da kyau


Rahama ta tsaya a gabanta, tana jin bugun zuciyarta amma ta ƙi nuna hakan


Bayan wasu mintuna, supervisor ɗin ta ce “Leave this with me, I’ll review the matter”


Rahama ta gyada kai “Thank you, ma”


Ta juya ta koma wajen Maryam, Maryam ta kama hannunta “Rahama, what if she gets angry with you?”


Rahama ta kalle ta “Then sai na sake bata hakuri”


“Really?”


Rahama ta ɗan yi shiru “No”


Maryam ta zaro ido, Rahama ta ɗaga kafaɗunta

“If I’m wrong, I’ll apologise. If I’m not wrong, I’ll speak politely and let her be angry in peace”


Maryam ta fashe da dariya duk da jajayen idanunta, Rahama ta yi murmushi, tana jin daɗin ganin ƙawarta ta samu sauƙin damuwa

Da suka fito waje, Maryam ta tambaye ta “Yanzu me za mu yi?”


Rahama ta kama hannunta “First, we’ll find something to eat”


Maryam ta kalle ta cikin mamaki “Food?”


“Yes, food! You can’t cry on an empty stomach”


Maryam ta yi dariya “Is that your solution to everything?”


Rahama ta tsaya kamar tana tunani mai zurfi

“Of course. Food has solved many of humanity’s problems”


“Name one”


Rahama ta yi shiru ta ɗaga yatsa “Mine whenever I get angry, feed me”


Maryam ta girgiza kai tana dariya


Su biyun suka ci gaba da tafiya, Rahama tana ba ta haƙuri da ƙarfafa mata gwiwa


Meanwhile, Rayyan yana zaune a cikin wani babban conference room, yana nazarin wani rahoto da aka kawo masa


Taron da ya kamata ya zama na yau da kullum ya rikide zuwa tattaunawa mai zafi bayan wani babban client ya nuna rashin gamsuwa da figures ɗin da aka gabatar masa


Bayanan da ke cikin sabon rahoton ba su yi daidai da waɗanda aka nuna masa a baya ba, wannan ya jawo tambayoyi da yawa


Wasu suna zargin finance department, wasu kuma suna ganin an canza figures ɗin ne bayan an riga an aika rahoton


Kowa yana magana a lokaci guda, Rayyan ya ajiye pen da ke hannunsa “Everyone, one at a time”


Duk suka yi shiru, ya juya wajen finance manager “Ka nuna min original report din”


Manager ɗin ya buɗe laptop ɗinsa ya nuna masa bayanan


Rayyan ya nazarce su, sannan ya nemi a nuna masa sabon version ɗin. Ya kwatanta su a hankali, yana duba inda aka yi canje-canje da lokacin da aka yi su “Who authorised this revision?”


Manager ɗin ya yi shiru na ɗan lokaci “ Ya fito ne daga sashen gudanar da ayyuka, ranka ya daɗe”


Rayyan ya ce “From whom?”


“Ina so nayi confirming ne”


Rayyan ya jingina da kujerarsa “Then confirm it, I don’t want assumptions, I want facts”


Ya juya wajen client ɗin “We understand your concern, and we’re not going to ask you to accept figures that haven’t been verified. Za mu sake duba takardun, gano inda aka samu saɓani a cikin alkaluman, sannan mu ba ku cikakken bayani mai gamsarwa kan abin da ya faru”


Ya ci gaba da ba wa kowane department aikin da zai yi, sannan ya sanya musu deadline na gabatar da sakamakon binciken


Ba ya son a ɓoye kuskure don kawai a kare sunan kamfani. Idan an yi kuskure, yana son a gano inda aka yi shi, a gyara, sannan a tabbatar ba za a sake maimaitawa ba


A lokacin da aka tashi daga taron, an riga an san matakan da za a ɗauka


Rayyan ya ci gaba da duba rahoton lokacin da wayarsa ta yi ƙara


Saƙo ne daga Safiyya


Safiyya: Are we still meeting today, or should I assume your office has adopted you?


Rayyan ya yi murmushi


Rayyan: We’re still meeting. I’ll be there


Safiyya: You said that yesterday


Rayyan: And today, I’m saying it again


Safiyya: Very convincing


Ya girgiza kai yana murmushi, sannan ya ajiye wayar


Duk da yawan aiki da nauyin da ke kansa, Safiyya tana ɗaya daga cikin mutanen da suke tunasar da shi cewa rayuwa ba aiki kaɗai ba ce


Akwai soyayya, ga fam and akwai lokacin da mutum yake buƙatar ya ajiye duk wata damuwa gefe domin ya kasance tare da mutanen da yake so


Kuma a yau, ya yi niyyar ba Safiyya wannan lokacin gsky