KOWA DA RABONSA

Chapter 11

by @mamyywriter

╔══════════════════════╗
  🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝

 🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺

 ✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

✨ FIVE STAR WRITERS✨

📞 ***

📚 BOOK 1

📖 Page 11
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ


Bismillahir Rahmanir Rahim.

> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.

~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━



"Haka ne Daada Shatu ita ce rabonsa shi ma kuma shi ne rabon da Allah ya zaɓa mata..."

Shiru ya yi bai iya cewa komai ba, dalilin bugun da zuciyarsa ke yi, daga ƙarshe su Daada fita suka yi daga ɗakin, zama suka yi a gadon suna kasa magana kowa kallon ɗan uwansa yake tsawon lokaci sai da Baba Malam ya shigo yana sanar da su tafiya gida za su yi.

Jiki a sanyaye duk suka fito a ɗakin, Shatu na ganin fitowarsu ta nufu su, tana shirin rungumo M.Madawaki, A Maina ya riƙeta, fashewa ta yi da kuka tana son ƙawace hannuta.

"Shatu M Madawaki Abbanki fa ba shi da lafiya kina faɗawa jikinsa ai ƙarasa shi za ki yi, ko ba ki san ki girma ba ne?"

Daada ce ta kamo hannunta suka shiga mota, shi kuma suka shiga da A Maina, har suka isa gida Shatu na kuka
A falon Daada suka zauna Abubakar Madawaki yana aiki rarrashin, Baba Malam kuwa cewa ya yi su rabo da ita har ta haƙura ta yi bacci.

Tun da Baba Malam ya yi magana babu wanda ya sake kulata, Mummy kuwa zama ta yi a gefenta tana shafa kanta har ta yi bacci, kallon Daada Mummy ta yi tare da cewa.
 "Daada ta yi bacci ko Rima za ta taimaka min na rakata bedroom ɗinta..."

"A'a Hajarah ki tafi sai da safe mijinki yana ciki kuma alamu sun nuna yana buƙatar kulawa."

Tashi Mummy ta yi ta nufin ɓangaren M Madawaki, a falonsa ta tsaya ganin baya nan hanyar nata falon ta nufi, tana son sani abin da yake damun M Madawaki da har aka kai shi asibiti.

A ranar Shatu sai ɓangaren Daada ta kwana, washegari ranar kuwa ƙalul ta tashi har ta yi shirin tafiya school, a dinning room ɗin suka haɗu da Abbana nata, cikin farinciki ta gaida shi, ya amsa kamar yadda ya saba, sai da suka gama za su tafi school ne ta kalleshi tana turo baki ta ce.
 "Abbana da wacce motar zan tafi?"

Lumshe idanuwansa ya yi domin baya ƙaunar magana yau Daada ce ta yi saurin cewa.
 "Ina motar taki? Da alamu school ɗin ne bakya son zuwa ko?"

Tashi tsaye ta yi tare da ɗaukar phone ɗinta ta sake turo baki ta ce.
 "Gaskiya Daada babu ruwanki, ai da Abbana nake magana, kuma ba jiya ne ya ce na bawa Inayaa motar ba...."

Tashi ya yi tare da cewa.
 "Ku same ni a mota."

Da farinciki ta ɗauki school Bag ɗinta Rima, Meerah ma da murna suka tashi domin suna ƙaunar M Madawaki ya kai su school yana ƙara kankaro musu girma sai da suka je bakin ƙofa Baba Malam ya kallesu tare da cewa.
 "Shatu M Madawaki dawo ki sauya hijabin jikinki Hajarah a bata hijaba babba na hana saka wannan daga yau."

Tun fara maganar Baba Malam M.Madawaki ya tsaya jin abin ya faɗa ne ya saka shi fita daga falon, Shatu kuwa kallon hijabin ta yi sannan ta sake kallonsu Meerah ta ce.
 "Baba Malam wannan ne hijabin school ɗinmu fa kuma gaskiya Ni ba zan saka babba hijabi ba kamar wata matar Malam ai sai a yi min dariya yau a schoo...."

Dariya Rima ta yi tare da cewa.
 "Yau da mun sha dariya, shi fa Baba Malam bai san wannan hijabin ma ya yi miki girma ba.."

"Eh mana To ni ko wannan ma, ya yi min girma a dole nake saka shi Rima mu tafi."

Tashi Baba Malam ya yi yana kallon fuskar Abubakar Madawaki ya ce.
 "Shatu M Madawaki ba za ta fita ba yau mundun bata sauya hijabin jikinki ba."

Rima da Meerah, Abubakar Madawaki ya nunawa hanya ita kuma Shatu Anne ce ta kama hannayenta tana kallon Mummy ta ce.
 "Hajarah kawo mata wani hijabin lokaci yana wucewa..."

Fashewa da kuka Shatu ta yi tana cewa ba za ta sauya hijabin ba, duk yadda Mummy ta yi ta rararsheta kin yarda ta yi, da suka takura mata ne ta ce ba ta je school ɗin ba, ta kwanta tana fama da kuka, Nanny ce ta zauna kusa da ita tana yi mata faɗa da yake ta jin maganar Nanny sai ta tashi zaune tana cewa.
 "Allah Nanny ba zan sauya hijabin nan ba, kawai na shiga cikin school a na nuna Ni, na yi faɗa da yarinya a zo ana cewa bana jin magana."

A Maina ne ya shigo da saurin domin message ɗin da M Madawaki ya yi masa na Baba Malam ya hana Shatu fita, tana ganin shi ta fashe da sabon kuka, dafa kansa ya yi yana tunanin abin da zai yi.

Baba Malam ne ya fito daga falonsa, zai fita A Maina ya riƙe hannunsa yana ba shi haƙuri akan ya yi haƙuri Shatu ta tafi school ɗin, hannunsa ya cire yana sake tabbatar masa mundun bata sauya hijabin jikinki ba za ta fita ba, shiru ya yi sanin halin Baba Malam in ya yi magana babu mai musawa sai Shatu da take da masifar taurin kai.

Daada ya kalle ga bata ce komai ba, hijabin hannun Hajarah ya karɓa tare da riƙewa Shatu, yana haɗe fuska, karɓe ta yi tare da guduwa ɓangarensu, da kallon suka bi ta suna girgiza kai, murmushi Baba Malam ya yi tare da cewa.
 "Ta haƙura Abubakar ka tafi wajen aikinka ba ta son zuwa school ɗin ne."

Fita A Maina ya yi ba tare da ya sake magana ba, a hankali Mummy ta bi bayan Shatu, a kwance ta sameta tana kuka sosai, rarrashinta ta yi tare da cewa.
 "Kin burge ni sosai da kika ƙi saka wannan ƙaton hijabin kamar ba buduwa ba, ban san abin da yake damun Baba Malam ba da zai haka ki fita bayan su Rima ma irinsa ne a jikinsu..."

Cikin kuka ta ce.
 "Ai wallahi sai dai na haƙura da school ɗin gabaɗaya, dama haushi nake ji jiya Abbana ya ce na bawa Inayaa key ɗin motata."

Zugata Mummy ta yi sosai sannan ta fita daga bedroom ɗin.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━
M.Madawaki kuwa yana dawo daga kai su Meerah school gida ya shigo A.Maina ya samu a bakin Gate, tare suka shigo ciki bayanin abin da ya faru A.Maina ya yi masa, tare da cewa.
 "Dole ne Shatu M Madawaki ta yi biyayya ga abin da Baba Malam yake so, ina so zan sanar da ita wacce ita yanzu ka yi min wannan alfarma."

Shiru ya yi tsawon lokaci sannan ya kalle A.Maina.
 "Ba haka muka yi da ku ba, ku bani lokaci zai samo mafita...?

"Mafita kuma akwai wata mafita ne bayan ku karɓi abin da kaddararku ta zaɓa muku? MAMUB bana so ka sawa zuciyata wani abu da ban, dole ne duk ku zauna da juna a yadda kaddararku ta nuna."

Shiru M.Madawaki ya yi yana kallon fuskar A.Maina, cikin ɓacir rai A Maina ya nufin falon Hajarah, tashi tsaye Hajarah ta yi ganin ya shigo mata falo babu ko sallama, bedroom ɗin Shatu ya shiga, yana shiga M.Madawaki ya shigowa kallon fuskar Hajarah ya yi kai tsaye ya ce.
 "Fita za mu yi magana."

Cikin nadama da danasani ta ce.
 "Akwai maganar da zaku yi wacce bai kamata na sani ba? M.Madawaki ka yi haƙuri don Allah ka maida ni ɗakina nagaji na tuba..."

Katseta ya yi ta hanyar cewa.
 "Ba na sha'awar zama da mace fiye da ɗaya, jiya na yi aure ki yi haƙuri ki komai gidanku....."

"Aure aure kuma M.Madawaki wacce wanda ka aura 
"Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un!"

"Eshaa...."
━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━
A ɓangaren Shatu kuwa mamakin ganin A.Maina ta yi a bedroom ɗinta, tashi zaune ta yi tana tunanin ko shi ma duka zai yi mata irin wanda Abbanta ya taɓa yi mata, zaro ido ta yi ganin ya zauna a gefen bed ɗin tare da janyota.

Fashewa ta yi da kuka tare da cewa.
 "Don Allah Abbansu Nadiya kada ka dukeni na yadda zan saka hijabin..."

Hannunsa ya ɗora saman lips ɗinta yana murmushi, janyota jikinsa ya yi tare da cewa.
 "Ni ba dukanki zan yi ba, magana za mu yi."

Sauke ajiyar zuciya ta yi tana kallon fuskarsa,
"Shatu M Madawaki, ina so sanar da ke wani muhimmin abu wanda nake da ya ƙinin ba za ki bani kunya ba, a yau gani gabanki a matsayin Uban da ya haifeki, da fatan za ki yi min biyayya?"

Jikinta ne ya yi sanyin ta saki baki tana kallonshi, ɗaga mata kai ya yi alamar ta yi magana.
"Zan yi amma sai na sanar da Abbana..."

Girgiza kai kawai ya yi tare da cewa.
 "A jiya na karɓawa Abban naki aurenki a wajen Baba Malam.."

Da saurin ta miƙe tsaye tana fito da idanuwanta cikin ƙaramin sauti ta furta.

"Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un!.Shi ne sautin da iya fitowa daga bakinta tare da zabura tana kallon fuskar Mahaifin nata da yake murmushi ciken da farinciki marar misali.

Rawa jikinta ya fara hawaye na zuba daga kyakkyawar fuskarta tana ƙoƙarin fahimtar abin da Abbansu Nadiya yake faɗa, cikin kamala da kame fuska yake sake jaddada mata auren da aka ɗaura mata da Muhammad Madawaki (MAMUB)wanda yake tamkar uba ko kuma ta kira shi da uba ma gabaɗaya.

Cikin tashin hankali da firgici take kallon Abbansu Nadiya wanda bakinsa ya sake faɗar abin da take ganin masifa ce babban a rayuwarta gabaɗaya, domin ta san ta gama rayuwa daga yau ɗin nan.

Tsayawa zuciyarta ta yi da aiki, lokacin ɗaya tana ji sama da ƙasa na juyawa idanuwanta na rufe wa, numfashinta na ƙoƙarin tsayawa.

A lokaci guda hankalinta ya fita daga jikina, tunanin makomarta ne ya sakata fashewa da kuka haƙiƙa tana cikin wani halin da bata san waye zai fitar da ita ciki ba.

Amma duk halin da take ciki Abbansu Nadiya farinciki ne kwance a kan fuskarsa har wani tattausan murmushi yake yi yana sake kallonta.

Suna cikin wannan yanayin ne suka ji ihun Mummy ta na cewa.
"Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un!. Na shiga uku! Me kake faɗa min haka M.Madawaki me ya sa za ka yanke wannan ɗanyen hukuncin?"... 

Ba ta ƙarasa maganar ba ta yanke jiki ta faɗi, da gudu duk suka fita zuwa inda suke jiyo ihun Mummy kwance a ƙasa suka ganta a sume, M Madawaki na tsaye a kanta.

 Jiri ne ya ɗebeta ko taku ɗaya bata yi ba ita ma ta faɗi a sume, masu aikin gidan ya kira suka saka masa Mummy a mota, shi kuma ya ɗauki Shatu a kafaɗarsa, yana fitowa security guards ɗinsa sukai saurin buɗe mota.

Da mugun gudu suka fita daga Madawaki Dynasty mintinan kaɗan ne suka kaisu Madawaki Special Hospital, security Hospital ɗin na ganin motocin M Madawaki suka buɗe Gate tare da zagaye motar suna jiran fitowarsa.

A.Maina ne ya fara fitowa yana kiran nurse, kafin ya rufe baki, nurses ɗin asibitin suka fito da gadon ɗaukar marasa lafiya, Mummy aka fara shiga da ita, sannan M Madawaki ya fito da Shatu a jikinsa wacce take sume.

Taimako gaggawa aka fara basu, wasu daga cikin nurses ɗin suna mamaki abin ya saka uwa da 'ya suma lokacin guda cikin ƙwarewa aka ceto rayuwarsa tare da kaisu ɗakin hutu.

M.Madawaki ne ya buƙaci a raba musu ɗaki, umarninsa suka bi na abin da ya buƙata ɗin Dr Nadraa ce ta yi wa A. Maina bayani, domin ta san shi ɗaya ne yake iya faɗa wa M.Madawaki magana ba tare da an ji kansu ba.

Fita M Madawaki ya yi daga office ɗin yana shiga ɗakin da aka kwantar da Shatu, ya jima a tsaye a kanta ya zuba mata idanuwansa masu kaifi, A Maina ne ya shigo tare da zama gefen gadon ya shafa fuskarta.
"Rigimar yau ta da ban ce ina tausayawa M.Madawaki."

Lumshe idanuwansa ya yi tare da juyawa ya fita daga ɗakin, ɓangaren Mummy ya nufi, bai jima da shiga ba ta farka tana kuka sosai ɗago manyan idanuwansa ya yi yana kallonta sannan ya ɗauke kai yana miƙe wa zai fita.

Da sauri Mummy ta riƙe hannayensa za ta yi magana, cire hannunsa ya yi daga nata ya fita ba tare da ya ce wani abun ba, dama ta san ba magana zai yi ba, da gudu ta fita tana tambayar in Shatu take, nuna mata ɗakin da aka kwantar da ita wata nurse ta yi.

Da ƙarfi ta buɗe ƙofar babu kowa a ɗakin sai Shatu M Madawaki da take kwance, ido a rufe Mummy ta fara dukanta, wahala ce ta farfaɗo da Shatu, ganin Mummy na dukanta ya sakata fashewa da matsanancin kuka dama ta san sai Mummy ta yi alajinta duba da yadda Mummy take kishin Mijinta.

Cikin fitar haiyaci Mummy ke dukanta tare da cewa sai ta kasheta kowa ya huta, nurse ɗin da ta shigo ce ta ga abin da yake faruwa, da gudu ta koma tana sanar da A Maina da suke magana da M Madawaki, cikin hanzarin suka shiga ɗakin.

Cikin ƙaramin sauti ya furta,
"Assagafirllilah." Tare da kamo hannayen Mummy ya fitar da ita daga ɗakin, Dr Nadraa ya kira ta sake duba Shatu wacce ta sake sumewa hauka Mummy ta fara yi masa a Hospital ɗin, Yusuf ne ya kawo masa wayoyinsa da ake kira cikin girmamawa.

Da ido ya yi wa A Maina magana yana so a maida Mummy gida fahimtar abin yake nufi ne, A Maina ya kira Baba Jamila da suka zo tare, bayanin komawar Mummy gida ya yi mata tare da haɗa su da Yusuf.

Duk haukan Mummy sai da aka maida ita gida, shi kuma ya zauna har Shatu ta dawo haiyacinta a lokacin A Maina ya koma gida, tun farkawarta take kuka marar sauti ganin iya M Madawaki ne a ɗakin, duk rigimarta tana tsananin tsoronsa duk Madawaki familys babu wanda take shakka irinsa.

Sautin kukanta ne ya fara damunsa ya kira Dr Nadraa ta sallamesu, Dr Nadraa wayeyar macece tana jin daɗin aiki da M Madawaki shi yasa take masa biyayya sosai, murmushi ta yi tare da rarrashin Shatu da take kuka taimaka mata Dr Nadraa ta yi tana kama hannunta domin rakata mota, ƙamshin turaren M Madawaki ta ji a kusa da ita ta yi saurin ɗago da kanta.

Ganin irin kallon da yake wa Shatu ne ya sakata matsawa gefe cak ya ɗaga Shatu yana fita da ita kamar yar bebe Yusuf na ganin fitowarsu ya yi saurin buɗe mota.

Yusuf ne ya jan motar suka fita daga hospital ɗin tun da ya shiga motar ya fara amsa wayoyi, yana magana cikin ƙaramin sauti, ko Shatu da take gefensa bata jin abin da yake faɗa.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
A compound ɗin gidan Yusuf ya faka motar cikin fargaba da tashin hankali Shatu ta fito jikin a sanyaye.

Baba Isa mai gadi ne ya ƙaraso bakinsa a washe yana cewa.
 "Shatu sannu da jiki ai yanzu Inayaa ta fita tana kuka...."

Shiru ya yi dalilin M Madawaki da ya fito ita ma da gudu ta ƙarasa cikin babban falon gidan,Madawaki Dynasty ne gabaɗaya a falon zaune da alama magana suke mai mahimmanci, shigowar Shatu ne duk suka zuba mata ido kowa yana kallonta.

Cikin sanyin jiki ta tsaya daga bakin ƙofa tana mai jin tsoron shiga, Mummy ce ta fito da wani ƙaton sanda a hannunta za ta rafka mata cike da ɓaci rai Daada ta ce.
 "Kina dukan Shatu M Madawaki a bakin auranki ko 
M. Madawaki bai sake ki ba,sai na sake ki yau ɗin nan..."

Fashewa Shatu ta yi da kuka tare da zuɓewa a ƙasan wajen zan ta fara sana'ar ta ta, wato rigimar banza,tana ji shigowar Abbanta cikin rawar jiki ta tashi tare da goge fuskarta.

Shiru falon ya yi kowa yana kallon fuskar M Madawaki da ya zauna ba tare da ya yi wa Shatu magana ba, Baba Malam ne ya kamo hannunta yana goge mata fuskarta cikin sanyin murya kamar yadda ya saba yi mata magana ya ce.
  "Shatu M Madawaki......"

Dariyar Aminu H Madawaki ce ta saka Baba Malam shiru yana kallon gefenshi da yake cewa.
  "Sai yau sunan ya zama cikakke...."

Ganin kallon da Baba Malam ya yi masa ne ya hana shi ƙarasa maganar yana murmushi.

Zaunar da ita Baba Malam ya yi a kusa da shi suna zama suka ji cikakkiyar muryasa wacce a kowane lokaci take saka Shatu cikin nutsuwarta ya ce.

"Ko da wasa bana son jin ko ganin irin hakan ta faru."

Sai da ya ɗan huta sannan ya cigaba da cewa
"What is really bothering you? Are you the first woman to have kishiya? Shin ke kadai aka fara yiwa kishiya a duniya? Listen to me very well, I will not tolerate any nonsense from you. Bazan lamunci wani rashin hankali ba, kin ji ko?"

Farinciki ne ya bayyana a kan fuskar Madawaki Dynasty sosai. Wasu daga cikinsu ma dariya suke yi suna hararar Mummy.

Cikin ɗaga murya Mummy ta ce,
"Wai kana da bakin magana Muhammad Madawaki? Ni zaka cuta yarinyar da na rike ita zaka auro min? To wallahi baku isa ba daga kai har shi shegen Uban nata. Ashe ma saboda haka ya baka ita? To wallahi sai dai ka zaba ko ni ko ita dan ba zan zauna da yarinyar cikina ba."

Fashewa Shatu ta sake yi da kuka domin tun da take da Iyayenta, bata taɓa ganin sun yi fada ba sai yau. Kuka take sosai ganin suna irin wannan maganar kuma Baba Malam ya yi shiru ga Daada ma bata saka baki ba.

Tsayawa ta yi da kukan sakamakon wata mummunar kaddara da ta ji tana fita daga bakin Abbanta. Cikin bacin rai ya ce,

"Za ki iya tafiya, but Eshaa is now part of Madawaki Dynasty She is mine, babu rabuwa a tsakaninmu. Try touching her again and you will see the other side of me."

"Ni zaka saka a kanta? Wai wane shegan ne ya baka shawara auranta?"


"Nothing. I just need it to be so."

Yana gama fadar haka ya tashi tare da nufar hanyar bangarensu. Sake fashewa ta yi da kuka tare da rungume Daada.

Cikin bacin rai Mummy ta bi bayan M.Madawaki. Baba Malam yana mata magana, amma ko juyowa bata yi ba.

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━

Tun fitar M.Madawaki daga falon Daddyn Meerah yake rarrashin Shatu amma da yake tana da rigima bata saurareshi ba. Har wani bacci ya ɗauketa tana aikin kuka.

"Alhamdulilah yau M Madawaki ya nunawa matarsa shi cikakken Madawaki familys ne."

Jijiga kai Baba Malam ya yi alamar hakan ya yi masa, Abubakar Madawaki ne ya kalle su Shamsudeen da suke zaune gefen Daada ya ce duk su fita.

Magana suka yi iya manyan sai matansu waɗanda suke mamaki abin da M Madawaki ya yi wa Hajarah na aure Shatu da ya yi.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━
A ɓangaren A Maina kuwa yana shiga gidan ya samu Zulaihah da Rahmah suna faɗa, Innayi na gefe sai Muhammad da yake bawa Umminsu haƙuri, cikin sanyin murya Rahmah ta kalle A Maina tare da cewa.
  "Da gaske ne abin da Zulaihah take faɗa? Wai Shatu aka aurawa M.Madawaki? Don Allah ka yi min bayani.."

Kallon Zulaihah ya yi tare da cewa.
 "Waye ya kawo maganar nan gidan nan?"

Muhammad ne ya yi ƙasa da kansa yana cewa.
 "Abba Inayaa ce yau bata je school ba, kayanta ma duk ta kwashesu daga gidan nan shi ne Mama take yi wa Ummi gori suke faɗa."