KOWA DA RABONSA

Chapter 12

by @mamyywriter

╔══════════════════════╗
  🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝

 🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺

 ✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

✨ FIVE STAR WRITERS✨

📞 ***

📚 BOOK 1

📖 Page 12
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ


Bismillahir Rahmanir Rahim.

> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.

~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━



Muhammad ne ya yi ƙasa da kansa yana cewa.
 "Abba Inayaa ce yau bata je school ba, kayanta ma duk ta kwashesu daga gidan nan shi ne Mama take yi wa Ummi gori suke faɗa."

Hannayen Innayi ya kama tare da zaunar da ita, tsakiyar falon Rahmah ta dawo tana son ji gaskiyar maganar ba tare da ya kalli kowa ba ya yi musu bayanin komai har zuwa ɗaura auren, zaman yan bori Rahmah ta yi tare da cewa.
 "Amma dai zai saketa in ka samu wacce za ta zauna da shi tsakanin da Allah k....."

Katseta ya yi cike da ɓacir rai yana nuna mata yatsa.
 "Ko da wasa bana so bakinki ya sake ambata irin wannan maganar, ke ina ruwanki ne?...

Ita ma katse shi ta yi tare da cewa.
 "Maina ina ruwana fa ka ce? Ni ce fa na haifi Shatu...

Cikin tsawa ya ce.
 "Ya isa haka Rahmah ya isa.."

Falonsa ya shiga ba tare da ya sake cewa komai ba, Innayi ce ta yi wa Rahmah faɗa sosai tana nuna mata abin ta faɗa wa A Maina bai kamata ba, goge hawayen fuskarta ta yi sannan ta nufin falon nasa domin su tattauna.

A kwance ta same shi haƙuri ta ba shi sosai, har ta samu ya sauko suka yi magana ta fahimtar juna, a lokacin ya nuna mata auren Shatu da M Madawaki ƙaddara ce wacce babu wanda ya isa ya kwaice, shiru ta yi alamun maganar ta shiga zuciyarta.

Inayaa kuwa A.Maina da Rahmah na shiga falon ta fito daga inda ta boya ta fara ihun kuka, tana cewa ita da Abbansu ya aure mata M.Madawaki tana son shi,duk da girmansa, tashi Innayi ta yi tana fita daga gidan gabaɗaya domin ba za ta iya ɗaukar haukan Inayaa da Zulaihah ba.

Rarrashinta Zulaihah ta yi tare da cewa.
 "Ki yi haƙuri na san wannan auren ba nisan zangon zai yi ba, yanzu dai ki fara komawa gidan ki takura masa sosai mu samu ya sakar miki dukiya kamar yadda ya yi wa waccan shegiyar, daga baya za mu yi maganar auren da A.Maina tun da har ya ambata zai iya aura masa yarinyarsa ai abun ya zo da sauƙi."

Goge hawayen ta yi Zulaihah na rakata da sauran kayanta har ƙofar falon Daada, sannan Zulaihah ta dawo har lokacin A.Maina da Rahmah suna falonsa yana yi mata bayanin tare da nuna mata ƙaddara ce ta haɗa auren Shatu da M Madawaki.

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━
A ɓangaren M.Madawaki kuwa ko da Mummy ta bi bayanshi ba ta samu damar shiga ko falonsa ba, knocking ta fara yi da iya ƙarfinta, amma M.Madawaki bai buɗe ba.

Falonta ta koma tana kiran number Amina, tana ɗagawa ta fara kuka tana sanar da ita abubuwan da suke faruwa, cike da masifa Amina ta ce ga ta nan zuwa.

Ba a ɗauki tsawon lokaci ba, sai ga Amina tana zuwa bedroom suka shiga, labarin abin da yake faruwa Mummy ta sake bata tare da fashewa da kuka.
"Amina na shiga uku M.Madawaki fa aure ya yi da bakinsa yake sanar da Ni, abin da yafi ɗaga min hankali shi ne wacce shegiyar Yar riƙon tasa wai ya aura...."

"Uhm Hajarah Ni ma abin da yake ɗaga min hankali kenan wai Shatu yarinyar cikinsa yarinyar da duniya take yi mata kallon 'yar ɗaya tilo a gareshi, kai! Mun shiga uku muna so ya maida ke sai ga wata masifar ta shigo......"

"Amina kashe Shatu zan yi kowa ya huta, ba zan yi ganin M.Madawaki yana sharing one bed da wata mace ba,kin san waye M.Madawaki kuwa wajen iya sarrafa mace wayyo Allah na shiga uku..."

Rufe mata baki Amina ta yi tare da cewa.
 "A'a Hajarah ba zan baki shawarar aikata kisan kai ba, yanzu dai mafita nake so mu samu, yawwa ina Shatu?"

Kallon tambaya Mummy ta yi mata, murmushi Amina ta yi tare da cewa.
 "Ta hanyar Shatu ne za mu samu abin da muke so, Shatu yarinya ce ƙarama tana daukar duk abin da kika ɗora mata, dan haka nake so ki janyota jikinki ki nuna mata wannan aure bai halarta ba, ki sanar da ita babu aure tsakaninsu domin Ruƙayyah ta shayar da ita nono ita Yar ce ga matarsa....."

"Sai me zai faru bayan yin haka ɗin?"

"Uhm daɗina da ke ba ki da haƙuri, Shatu na sanin haka ba za ta taɓa yadda wani abu ya faru tsakaninsu ba, za ta san yadda za ta yi auren ya rabu shi kuma zai yi mata abin da take so domin kowa ya san ita ce zuciyarsa.."

Da wannan shawarar Mummy ta samu yar nutsuwa domin sun shirya haukatawa Shatu ƙwaƙwalwa, ta hanyar sanar da ita M.Madawaki ya saki Hajarah saboda ita, domin sun san Shatu za ta iya komai akan Mummyn nata, tare da Amina suka zama har dare.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Dawowarsu Rima ne Shatu ta farka, babu wanda ta yi wa magana, bedroom ɗin Rima ta shiga sallah ta yi tare da sanarwa Allah halin da take ciki domin ta san shi ɗaya zai fitar da ita.

Meerah ce ta shigo tana tambayarta abun da ya faru ta yi kuka irin haka duk fuskarta ta yi yellow, kallon Meerah ta yi tare da fashewa da kuka, rungume juna suka yi ita ma tana taya ta kukan, a haka Daada ta shigo ta same su.

Hawaye ta ji ita ma yana zubo mata, ta san Shatu tana cikin wani halin ƙwaƙwalwarta ta yi ƙarama da ɗaukar abin da yake faruwa, fita ta yi daga bedroom ɗin domin ba za ta iya cewa komai ba.

Inayaa da Rima ne suka shigo da sauri Rima ta ƙaraso tana rungumosu cikin sanyin murya ta ce.
 "Me yake faruwa ne? Shatu M Madawaki Meerah A Madawaki wani abu ya faru ne ku sanar da Ni ba zan iya ganinku cikin damuwa ba...."

Tsaki Inayaa ta yi, tare kwanciya a saman bed ɗin Rima, kallonta duk suka yi Rima ta ce.
 "Inayaa A Maina."

Tashi zaune Inayaa ta yi tana turo baki tare da cewa.
 "Na'am Rima Sayyid Madawaki."
 
"Ke ce ba je school ba wani abu ya faru bayan tafiyarsu?"

Yatsnine fuska Inayaa ta yi tare da cewa.
 "Ya faru kam, Yar riƙo ce ta aurin Uban riƙonta abun dai babu kunya wallahi..."

Zaro ido Shatu ta yi tana mamaki inda Inayaa ta samu labarin, tashi tsaye Meerah ta yi domin ta fi su zafin zuciya ta ce.
 "Wai a kan wa kike wannan haukan?"

Ita ma Inayaa tashi tsaye ta yi tare da yin dariya ta ce.
 "Da Shatu M Madawaki nake wacce ta aurin Uban riƙonta wato M.Madawaki waye bai sa..."

Sautin kukan Shatu ne ya hana Inayaa ƙarasa maganar jiki na ruwa Meerah da Rima suka riƙe Shatu wacce take kuka kamar za ta haɗiye zuciya, duk kuka suka fara ganin irin kukan da take yi.

"Shatu M Madawaki wai da gaske....?"

Ciki kuka sosai ta ce.
 "Rima haka Abbansu Nadiya ya faɗa min ban sani ba ko mafarki nake yi, zuciya kamar ta fashe Rima ki taimaka min wayoo Allahna na shiga uku....

Duk fashewa suka yi da kuka, Inayaa kuwa tana tsaye a kansu, ƙamshin turaren M.Madawaki Inayaa ta ji ta yi saurin juyawa, a tsaye ta ganshi ya naɗe hannayensa a baya, ciki nutsuwa ya ƙaraso inda suke a rungume suna kuka.

Meerah ya cire daga jikin Shatu, kallon fuskarsa duk suka yi da mamaki hannayensa ya miƙewa Shatu, da saurin ta faɗa jikinsa tana fashewa da sabon kuka, lumshe idanuwansa ya yi tare da saka hannayensa ya rungumota da kyau, fita ya yi da ita daga bedroom ɗin.

Bayansa su Rima suka biyo suna kuka mai ratsa zuciya, a falon suka samu duk yan family da alama sun jima a falon da gudu suka faɗa jikin Daada, hawayen fuskarta Daada ta goge tana kallon bayan M.Madawaki da ya nufi ɓangarensa da Shatu.

Ciki ƙarfin halin Baba Haruna ya ce.
 "Wai kukan me kuke yi haka? Duk kun ɗagawa mutane hankali wani ne ya mutu?"

Shiru suka yi da kuka suna sauke ajiyar zuciya, Omar Aminu H Madawaki ne ya yi tsaki tare da cewa.
 "Allah Baba Haruna da ka yi shiru duk na zane su, wanne irin hauka ne wannan? ku da ya kamata ku rarrashinta shi ne za ku zaunar da ita kuna mata kuka.."

Hajiya Safiya ce ta katse Omar tana kallon su Meerah tare da girgizar kai, cikin ƙasaita tare da taɓe baki ta ce.
 "Kukan da kuke yi ne zai sauya mata kaddarar da Allah ya rubuta mata? Ke Yar Yaya Maina ki kama bakinki mu ji abin da kika faɗa wato Zulaihah bata baki tarbiyya ba ko?"

Ƙasa Inayaa ta yi da kanta, sanin Ammie ba mutumci ne da ita ba duk Madawaki Dynasty ta fi kowa isa da jin kai haka ma yaranta basu da mutunci ko kaɗan, shiru falon ya ɗauka kowa da abin yake saƙawa a ransa.

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Sallama ya yi cikin ƙaramin sauti, tashi tsaye A.Maina ya yi ganin Shatu a jikinsa tana kuka, girgiza kai yana kallonsu har ya kwantar da ita a saman kujerun falon, ruwan da fara sha kafin a sanar da shi abin da yake, ya ɗauko tare da ɗora mata a saman lips ɗinta, dole ba dan ta so ba ta sha tana sauke ajiyar zuciya, A.Maina ne ya zauna a gefenta yana kamo hannayenta.
Cikin sanyin murya ya ce.
 "Eshaa bana son wannan kukan tun safe kike yi hakan bai isheki ba?"

Ɗago idanuwanta ta yi da suka kumbura sakamakon kukan da ta sha, A.Maina ne ya goge mata fuskar yana yi wa M.Madawaki magana da ido, tashi M.Madawaki ya yi tare da nufar bedroom ɗinsa.

M.Madawaki na shiga bedroom ɗinsa A.Maina ya kalle Shatu, tausayinta ne ya kama shi sosai, cikin karfin halin ya ce.
"Shatu wai me ke damunki? Kina so MAMUB ya sake kwanciya a Hospital ne? Kin san abin da ya saka shi suma jiya?"

Girgiza kai ta yi tana kallon fuskar A.Maina.
 "Tunanin halin da za ki shiga bayan sanin ƙaddarar da ta same ku, ke yake tausayawa bayan ke ɗin ba abar tausayi ba ce, shi ne wanda ya kamata a ce kina tausayawa, Shatu Abbanki fa yana cikin damuwa sosai..."

Zaro ido ta yi tare da riƙe hannayensa muryarta na ruwa ta ce.
 "Abbansu Nadiya wacce damuwar ce take damun Abbana?"

Murmushi ya yi mai ciwo yana dafa kanta ya ce.
 "Ke yarinya ce bai kamata ki sani ba, amma ina rokonki don Allah ki daina zubar da hawayenki a banza domin duk kukanki ba zai sake komai ba, sai ɗagawa MAMUB hankali na tabbata jiya ba iya yi bacci ba, yanzu haka ciwon kai yake fama da shi ga kuma damuwaki...."

Goge hawayen fuskarta ta yi tare da cewa.
 "Na daina Abbansu Nadiya, ba zan sake ba, bana so Abbana ya shiga damuwa saboda ni, Allah ba zan sake kuka ba, don Allah Abbansu Nadiya ka raka Abbana Hospital a duba shi..."

"Okay zan raka shi, amma sai mun yi alƙawarin ba za ki sake kuka ba..."

Fashewa ta yi da kuka tana cewa.
 "Ba zan sake ba Abbansu Nadiya Allah na daina.."

Rarrashinta ya yi har ya samu ta yi shiru sannan ya ce.
 "Shatu M Madawaki, bana so kina musu da Baba Malam daga yau ki sauya hijabin school ɗinku Yusuf zai kawo miki wani shi za ki cigaba da amfani da shi Abbanki ne ya sake miki ki fahimta?"

Ɗaga masa kai ta yi,hawaye na zubowa da idanunwanta, wayar M.Madawaki ya kira sai ga shi ya dawo zama ya yi kusa da ita ya yi shiru, tsawon lokaci suna tare babu mai cewa komai shi ma A.Maina shiru ya yi yana wani aiki mai muhimmanci a system ɗin gabansa.

A hankali M.Madawaki ya kalle Shatu da ta yi shiru kanta a ƙasa, hannayenta ya kamo yana matsawa, ɗogawa ta yi tana kallon fuskarsa ɗaga mata gira ya yi, ta san duk wani motsinsa, shi yasa ta matso jikinsa tare da kwantar da kanta a kafaɗarsa, cike da tausayawa ta ce.
 "Abbana wai baka da lafiya? Ka yi haƙuri ba zan sake kuka ba na daina kuma Abbansu Nadiya ya ce zai rakaka Hospital a baka magani...."

Yatsan hannunsa ya ɗora saman lips ɗinta yana murmushin jin daɗin abin da da faɗa, lumshe idanuwansa ya yi tare da ɗaga mata kai ciki ciki kamar ana yi masa dole ya ce.
 "Good Yusuf zai kawo miki motarki zuwa dare and sabon Unifrom ki yi amfani da shi.."

Ɗaga masa kai ta iya yi kawai,domin sabon kukan da ya kamata, ita ba komai ne ya sakata kukan ba sai maganar Uniform da Abban nata ya yi mata ta san ya zama dole sai ta sauya kamar yadda Baba Malam ya faɗa, duk taurin kanta bata iya yi wa Abban nata musu, domin gudun ya sake mata dukan da ya yi mata a shekarun baya.

A.Maina ne ya ɗago kansa yana kallonsu ya san magana suke a haka, amma baya jin abin da suke faɗa murmushi ya yi yana cigaba da aikin gabansa.

Ɗago mata da kanta ya yi tare da nuna mata hanya, cikin sanyin jiki ta miƙe tsaye tana kallon fuskarsa ɗaga mata kai ya yi, a hankali ta juya za ta nufin hanyar falon Mummynta sai kuma ta tuna abin da yake faruwa da gudu ta nufin hanyar falon Daada, murmushi A.Maina ya yi tare da juyowa yana kallon fuskar M.Madawaki da ya kawar da kai.

"Shatu M Madawaki fa tsoron tsohuwar matarka take."

 Shiru ya yi,bai yi magana ba, bai kuma ɗago ba, shi ma aikinsa ya cigaba da ya yi sai bayan ya gama ne ya tattara takardun wajen ya miƙe zai fita M.Madawaki ya buɗi baki a hankali yana cewa.
 "A satin nan za ta koma gidansu ni ma na gaji."

Murmushi kawai ya yi tare da fita shi ma bai ce komai ba,