KOWA DA RABONSA

Chapter 13

by @mamyywriter

╔══════════════════════╗
  🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝

 🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺

 ✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

✨ FIVE STAR WRITERS✨

📞 ***

📚 BOOK 1

📖 Page 13
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ


Bismillahir Rahmanir Rahim.

> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.

~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━ 




━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Zaune Shatu ta same su suna cin abinci, su Rima kuma sun yi shirin islamiyya, kallonta duk suka ba tare da sun yi magana ba, wayarta ta ɗauka a saman kujera tana dubawa, ajiyeta ta yi tare da kallon Meerah ta ce.
 "Meerah ku jira mu tafi islamiyyar."

Hajiya Maryam ce ta yi murmushi tana kallon Shatu ta ce.
 "Mamana babu gaisawa?"

Lumshe idanuwanta ta yi hawaye na zubowa, gogewa ta yi ganin A.Maina ya fito, murmushi gefen baki ya yi domin ya ga hawayen, cikin sanyin murya ta ce.
 "Umman Banisha sannu da zuwa ina Banisha?"

Girgiza kai A.Maina ya yi, yana buɗe ƙofa yana fita ta fashe da kuka tare da shiga bedroom ɗin Daada, murmushi Baba Malam ya yi, sanin Shatu ba daina kuka za ta yi ba, suna, zaune ta fito cikin Uniform ɗin islamiyyar tana goge fuska wacce ta koma jajir da ita har yellow take.

Cike da tausayawa Daada ta kamo hannayenta tare da zaunar da ita abinci Nanny ta zuba, Daada ta fara bata a baki ba da ta so ba ta fara ci tana hawaye Baba Malam ne ya kalle su Meerah ya ce.
 "Rima ku tafi makarantar mana...."

Kafin ya rufe baki Shatu ta fashe da kuka tana cewa.
 "Allah sai na je ai Abbana ne ya ce na shirya Uncle Yusuf ya kai Ni.."

Shafa kanta Baba Malam ya yi tare da yin ƙasa da murya ya ce.
 "Ni ba hanaki zuwa makaranta zan yi ba,shigar jikinki nake so ki sake a bay....."

Daada ce ta katse Baba Malam ta hanyar cewa.
 "Don Allah Malam ka barar yarinyar nan ta ji da abu ɗaya,haka da safe ka hanata fita ina kallo ko kunyata ba ku ji ba kai da Abubakar Madawaki, shi ne yanzu ma za'a hanata fita."

Tashi Shatu ta yi tare da goge fuskarta ta fita da gudu dariya duk suka yi, Meerah ta bi bayanta, sai Rima ce ta ɗauko masu Bag ɗin islamiyyar, Yusuf da yake tsaye a jikin mota yana jiran fitowar Shatu mamaki ne ya kama shi ganin ta fito da gudu duk da ya san halinta gudu baya mata wahala.

A jikin motar ta tsaya sai da ta huta sannan suka tafi sun yi nisa da gida Shatu ta buɗe baki a hankali ta ce.
 "Uncle Yusuf."

Amsawa ya yi kamar baya so domin zama da M. Madawaki ya koya masa body language, kuma yana kiyaye magana da zuciyar Uban gidan nasa wato Shatu.

 "Abbana ya ce zaka kawo min Uniforms don Allah ni bana son masu girma, sannan motar ma fara nake so.."

Yana kallon hanya ya ce.
 "Uniforms an gama komai,kuma Sir M.Madawaki manya ya ce a yi motar kuma za'a kawo...."

Gate ɗin makarantar da aka shiga ne ya hanata magana, tana turo baki ,Nadiya ta gani tsaye a gabanta tana yi mata murmushi, rungume juna suka sannan duk suka shiga class, babu laifi zuwa makarantar ya ɗauke mata hankali, ba ta sake tuna maganar auren ba sai da ta dawo gida ta samu Mummy na nemanta.

Jiki a sanyaye ta ƙarasa kusa da Mummy da take ƙoƙarin rungumota, Hajiya Safiya ce ta shiga tsakaninsu tare da janyo Shatu tana ɗagawa Mummy gira.

"Hajarah wai me kike jira ne a Madawaki Dynasty? Ki tattara kayanki kafin na saka security su fita min da ke.."

Zaro ido Shatu ta yi baki na rawa ta ce.
 "Ammie Mummy na ce fa...."

Yatsan hannunta ta ɗora saman lips ɗin Shatu tana kallon fuskar Hajarah ta ce.
 "Hajarah magana nake miki, sanin kanki ne bana wasa da makiyi don haka kafin rai na ya ɓace ki fita mana daga gida.."

Ƙwace jikinta Shatu ta yi tare da kamo hannayen Mummy ta ce.
 "Allah babu inda Mummyna za ta tafi ai muna sonta ni da Abbana...."

"Ita kuma bata son Abban naki ba, maza sakar mata hannu ta fita mana daga gida.."

Fashewa Mummy ta yi da kuka tare da janyo Shatu jikinta cikin kuka ta ce.
 "Shatu Abbanki ya sake ni, babu aure tsakaninmu ina zaman kula da ke ne sakamakon ƙaunarki da nake yi...."

"Mummy saki kuma?Mummy tun yaushe ban sani ba wayyo Allahna...."

Maganar ta tsaya ne sakamakon M.Madawaki da shigo, da gudu Shatu ta faɗa jikinsa tare da cewa.
 "Abbana wai wai babu aure tsakaninku da Mummy?"

Cireta ya yi daga jikinsa yana kallon fuskar Hajarah sannan ya kalle Shatu yana cewa.
 "Eshaa, get out of the living room."

Da gudu ta shiga bedroom ɗin Daada tana kuka sosai, Hajiya Safiya ya kalla tare da cewa.
 "Bana son damuwa Hajarah za ta zauna har sai Eshaa ta samu nutsuwa abubuwan sun yi mata yawa."

Fita ya yi ba tare da ya jira amsar kowa ba, hamdala Mummy ta yi tare da nufar ɓangarenta, baƙinciki ne ya kama Hajiya Safiya ta zauna tana masifa, a hankali Daada ta tashi bedroom ɗinta ta shiga tana sanar da Shatu M.Madawaki ya ce Hajarah ta zauna, farinciki ne ya kama ta fito tana nufar ɓangarensu.

Waya Hajarah take amma tana jin sautin kukan Shatu ta fashe da kuka, rungumeta Shatu ta yi suna kuka sosai tsawon lokaci sannan Hajarah ta tsarawa Shatu ƙarya da gaske akan sakin da yake tsakaninsu ita da M Madawaki.
Goge mata hawaye Shatu ta yi tare da cewa.
 "Yanzu Mummy sai an ƙara ɗaura auren tsakaninku da Abbana?"

Cikin kuka Hajarah ta ce.
 "Eh Shatu na jima ina so ya maida ni ɗakina amma ya ƙi yadda don Allah ki saka baki kin ga duk duniya Ni ɗaya ce zan iya zama da Abbanki tsakanin da Allah duk matan da suke sonshi saboda da dukiyarsa ne."

Tashi Shatu ta yi tare da cewa.
 "Yanzu zan faɗa masa gobe da safe a ɗaura muku aure ko?"

Murmushi ta yi tare da cewa.
 "Eh yawwa Shatu kin san wani abu? Wani sirri zan faɗa miki amma sirri ne domin babu wanda ya sani sai M.Madawaki Ni ma shi ne ya faɗa min."

Zama Shatu ta yi tana fuskantar Mummy da take cewa.
"Ba jiya A.Maina ya sanar da ke wai an yi miki aure da Abbanki ba? To ƙarya ne babu aure tsakaninku sakamakon shayar da ke nono da Ruƙayyah ta yi lokacin kina jaririya, amma fa babu wanda ya sani daga Ni sai M.Madawaki, Ni ma abin da yasa na sanar da ke bana so na ganki kina kuka ki kwantar da hankalinki..."

Farinciki ne sosai ya kama Shatu ta rungume Mummy tare da sauke ajiyar zuciya sai yanzu ta ji ta dawo cikin mutane sosai farinciki ya bayyana akan fuskarta ta ce.
 "Na gode sosai Mummy sai yanzu na sami nutsuwa, kuma na yi miki alƙawarin gobe sai Abbana ya sake auranki mu yi zamanmu tare."

Da gudu ta nufin hanyar falon Abbanta, dariyar samun nasara Mummy ta yi tare da kiran Amina ta bata labarin abin da ya faru, Shatu kuwa bata samu M.Madawaki a falon ba shi yasa ta je bakin ƙofar master bedroom ɗinsa ta fara bugawa kamar za ta cire ƙofar.

Fitowarsa kenan daga bathroom ya ji bugun ƙofar sanin ita ɗaya ce za ta iya shigowa falon nasa a lokacin, ya saka shi nufu ƙofar ɗaure da towel a ƙugunsa, a hankali ya buɗe bai yi tunanin a jikin ƙofar take ba, yana buɗewa ta faɗu jikinsa, saura kaɗan towel ɗin jikinsa ya zame.

Ƙanƙameshi ta yi tana turo baki ta ce.
 "Alhamdulilah dama na sani babu wani aure tsakaninmu kai Abbana ne, kuma ko Mummyna ba ta shayar da ni nono ba ai na san kai ma a Yar kake kallona ko?"

Tun fara maganarta yake kallon bakinta murmushi gefen baki ya yi domin ya gano Hajarah ce ta kitsamata wannan zancen, ɗaga mata kai ya yi alamar amsar tambayar da take masa, cusa kanta ta yi a ƙirjinsa sabo da murna, cike da farinciki ta ce.
 "To don Allah Abbana ka sake auran Mummy gobe sa mu yi zamanmu bana so Ammie ta sake yi mata magana irin ta ɗazu..."

jin tana son kassara masa sauran lafiyar da ta rage masa ne ya yi saurin cireta daga jikinsa yana nuna mata hanya, sai a lokacin Shatu ta kalle jikinsa da saurin ta rufe fuska tare da cewa.
 "Sorry Abbana amma..."

 "Eshaa."

Jin muryarsa da yanayin da ya kirata, ta yi saurin matsawa daga gefensa ta juyawa da gudu, girgiza kansa ya yi tare da rufe ƙofar, zama ya yi gefen bed ɗinsa yana sauke numfashi a hankali, cikin sanyin murya ya furta.
"Auzubillahi! Subbahanallhi! Subbahanalli! Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un! Me ke faru da ni Subbahanallhi! ?."

Da saurin ya koma bathroom yana sakarwa kansa ruwa ya jima yana tunanin abin da ya ji, a tare da shi a lokacin da Shatu take jikinsa, girgiza kansa ya yi yana fitowa daga bathroom ɗin.

Har ya shirya yana saƙesaƙe, wayarsa ya ɗauka suka yi magana da Yusuf da yake faman kiransa, bayan su gama magana ne ya kwanta yana yi kansa alƙawarin hana Shatu sake rungumarsa tun da har sheɗan ya fara kawo masa farmaki.

A ranar dai haka ya kwana da yana tufka da warware.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━
A ɓangaren Shatu kuwa Mummynta ta kaiwa labari mai daɗin, tare suka zauna har sha ɗaya na dare suna magana, sannan Shatu ta koma ɓangaren Daada domin ta bata labari, lokacin da ta shiga Daada ba ta nan tana ɓangaren Baba Malam.

Sai ta yi kwanciyarta a ɗakin kusa da Umman Banisha, ko da asuba ita ce ta fara tashi tana idar da sallah ta shiga bedroom ɗin Rima tare da kamo hannayents suka shiga bedroom ɗin Meerah, dariya ta yi tana kallon fuskarsu ta ce.
 "Kun san wani abu, to Abbansu Nadiya ƙarya yake min babu aure tsakaninna da Abbana...."

"Ke Shatu Abbansu Nadiya ne yake ƙarya?"

"Ai na manta, ashe Mummyna ta shayar da ni nono kun ga ai babu wani aure tsakaninmu da Abbana ko? Tun da ni 'Ya ce ga matarsa kuma na tambayi Abbana jiya ya ce min da gaske ne amma babu wanda ya sani sai shi.."

Farinciki ne ya kama su duk suka rungume juna, sosai suka yi murna hakan, har bakwai na safe suna ɗakin suna tsara fitar da za su yi zuwa yamma tun da jama'a ce babu islamiyya, Daada ce ta leƙo tare da bawa Shatu kayayyakinta da Yusuf ya kawo, tana turo baki ta saka sabon Unifrom ɗin.