Chapter 14
by @mamyywriter
╔══════════════════════╗
🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝
🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺
✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
✨ FIVE STAR WRITERS✨
📞 ***
📚 BOOK 1
📖 Page 14
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Bismillahir Rahmanir Rahim.
> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.
~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
> Farinciki ne ya kama su duk suka rungume juna, sosai suka yi murna hakan, har bakwai na safe suna ɗakin suna tsara fitar da za su yi zuwa yamma tun da jama'a ce babu islamiyya, Daada ce ta leƙo tare da bawa Shatu kayayyakinta da Yusuf ya kawo, tana turo baki ta saka sabon Unifrom ɗin.
Lokacin da suka fito kowa yana dinning room ɗin har M Madawaki, gaida su suka yi,sannan kowa ya zauna har za su fara cin abincin Shatu ta fara dariya tana kallon Baba Malam girgiza kansa ya yi domin da asuba M.Madawaki ya faɗa masa abin da Hajarah ta kitsamata.
" Daada na baki labari?"
Farinciki ne ya bayyana a fuskar Daada gani farinciki a fuskar Shatu ta ce.
"Ina ji Shatu M Madawaki me yake faruwa ne yau kike cikin farinciki?"
Dariya ta yi tana kallon fuskar Baba Malam ta ce.
"Kuma Baba Malam na san wani abu wanda baka sani ba, daga ni sai Abbana muka sani kuma iya Daada zan farawa sai Abbansu Nadiya."
Girgiza kai Baba Malam ya ba tare da kulata ba, kunnen Daada ta kamo tana faɗa mata abubuwan da Hajarah ta shuka mata a zuciya, cike da mamaki Daada ke kallon fuskar M.Madawaki sannan ta kalle Hajarah sai kuma ta yi murmushi alamun tana taya Shatu murna.
A bakin Gate suka haɗu da A.Maina, wanda yake magana da Yusuf, hannayensa ya ji Shatu ta rungume juyowa ya yi a ɗan zafafe domin ya hanata rungumarsa, sai kuma ya ga M.Madawaki tsaye yana lumshe masa idanuwansa, Shatu ya kalla sannan ya ce
"Shatu M Madawaki da alama yau akwai labarin mai daɗi?"
Nuna masa Yusuf ta yi da hannun, alamar bata so ya ji, sallamar Yusuf ya yi yana kallon su Rima da suke dariya.
"Abbansu Nadiya albashinka, ashe babu aure tsakaninna da Abbana Mummyna ta shayar da ni nono ka ga ai ni "Yarta ce ko?"
Buɗe idanuwansa ya yi da suka sauya lokacin ɗaya fuskar Shatu ya kalla da take dariya zai magana M.Madawaki ya dafa kafaɗarsa yana girgiza masa kai, murmushi dole ya yi tare da cewa.
"Good na taya ki murna, maza ku tafi school ga key ɗin motarki."
Karɓar key ɗin ta yi tana murna tare da nufar M.Madawaki, yana ganinta ya yi saurin shiga mota yana rufewa, A Maina ne ya nuna mata mota tare da cewa su tafi, ita ce ta ja motar suka fita, Yusuf ne ya shigo motar ganin A Maina ya shiga.
Suna fita daga gidan A. Maina ya ce.
"MAMUB daga ina wannan maganar ta fito?"
"Hajarah ce amma mu bar maganar a haka Baba Malam ya ce na yi shiru mu ga abin da take shirin shiryawa."
Shiru A Maina ya yi yana tunanin abin da zai faru gaba, shi ma M Madawaki tunani ya tafi har suka isa office babu wanda ya sake magana.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
A ɓangaren Shatu kuwa karfe biyu na rana suka shigo gida motar Inayaa ce a gaba sai ta Shatu da su Nadiya suke ciki, duk fitowa suka yi suna dariya, Inayaa suka ga a tsaye a jikin motata tana murmushi.
Hannayen Nadiya,Shatu ta kamo tare da cewa.
"Ki shigo mu shirya sai mu kira Umminsu Nadiya mu sanar da ita...
"A'a Shatu M Madawaki Umminmu za ta yi min faɗa kuma kin ga ban sanar da ita za mu fita ba...."
Tsaki Inayaa ta yi tare da cewa.
"Munafurcin banza wallahi ko ta shiga ba za ta shiga bedroom ɗin da nake ba....."
Hararar Inayaa,Meerah ta yi,Rima kuma ta kamo hannun Nadiya tare da cewa.
"Don Allah Nadiya A Maina ki shigo mu ga ko ita ma bedroom ɗin da take magana a kai ko nata ne."
Dariya Nadiya ta yi tare da rungumo Shatu ta ce.
"Ki yi kwalliya mai kyau sai na fito."
Tana gama faɗar haka ta juyawa tana fita daga gidan, Inayaa ce ta fara shiga ciki,sai su da suke magana, suna shiga babban falon gidan suka fara ihun murnar ganin Banisha da Nimrah, sai rufe kunne su Hajiya Safiya suka yi Anne kuma ta fara masifa.
"Wai ku baku da hankali ne? Kullum kuna girma amma...."
"Wait a minute Anne, why ba zamu yi murnar ganin juna ba....?
Bugawa Nimrah baki Ammie ta yi tare da nuna musu hanya, suna dariya suka nufin ɓangarensu Shatu da take murnar zuwansu, ko da suka haɗu da Mummy a falon bata kula su ba, iya Shatu ta yi wa welcome, bedroom ɗinta suka shiga.
Cike da farinciki Shatu ta ce.
"Welcome Banisha Al Hamzawi and Nimrah Al-Zubair..."
Rungumeta duk suka yi Rima ta ce.
"Welcome Baby's yau muna da fita...."
Ihu suka yi suna rungume juna, tsaki Inayaa ta yi tare da kallonsu, kamar ba za ta yi musu magana ba sai kuma ta tuna Nimrah ba mutunci ne da ita ba.
"Hey Nimrah Al- Zubair barka da zuwa Madawaki Dynasty."
Kallonta Nimrah ta yi tare da cewa.
"Hey Inayaa A.Maina".
Murmushi Banisha Al Hamzawi ta yi,tana kallon Shatu da ta miƙe tsaye dariya Banisha da Nimrah suka yi tare da nuna Shatu, kallon tambaya ta yi musu ita ma tana kallon jikinta, dariya Rima ta yi sannin abin da suke yi wa dariyar.
"Shatu M Madawaki kin ganki kuwa waye ya saka miki dokar saka wannan manyan kayan?"
Tsaki Shatu ta yi tare da shiga toilet, wanka ta yi sannan ta fito ɗaure da towel tana ɗaure gashinta a gaban miro ta zauna tana kiran number Rahmah cikin shagwabe take faɗa mata Nadiya ta shirya domin yanzu za su fita.
Rima ce ta shiga toilet ɗin domin ta yi wanka tana fitowa Meerah ta shiga a bedroom ɗin Shatu suka shirya kuma duk kayanta suka saka, har su Banisha, Inayaa na ganin fita za su yi da gaske ita ma ta shirya.
Cikin shagwabe suka ji tana magana, kamar wacce a ka yi wa dole ta ce..
"Abbana Allah bana son Uncle Yusuf ya raka ni tare da su Rima, Nadiya, Banisha,Nimrah...."
" Eshaa."
Dariya Shatu ta yi domin sanin dalilin kiranta da ya yi, shi yasa ta yi shiru tana turo baki.
"Ki kula."
Shi ne abin da ya faɗa tare da kashe wayar dariya ta yi tana ɗaukar ƙaramin handbag ɗinta za su fita
Meerah ta ce.
"Wallahi Shatu yau kin yi kyau."
Baki Shatu ta turo tana kallon riga da sikat ɗin jikinta wanda ya kamata sosai sai ɗan ƙaramin mayafi a kafaɗarta ta ce.
"Ni fa yau ba ruwana da kyau ɗin kawai son nake mu fita."
Nimrah ce ta miƙe tana ɗaukar wayarta ta ce.
"To ina za mu?"
Da sauri Rima ta ɗaga hannu.
"Ni na san wajen akwai wani sabon recreation park da aka buɗe kusa da city center akwai games, bowling, arcade, rides da food court yara da manya duk suna zuwa."
Tsalle Shatu ta yi tare da cewa.
"Yes na tuna."
"Mota fa!"
Meerah ta tambaya tana gyara ɗaurin ɗankwalinta.
Dariya Nimrah ta yi tare da cewa.
"Akwai ta Ammie tun da Shatu M Madawaki ta hana Uncle Yusuf ya kai mu."
Taski Shatu ta yi tare da cewa.
"Ni fa bana son tuƙin Uncle Yusuf har gara Baba Jamil da wancan marar mutuncin."
Ihunsu ne ya cika bedroom ɗin domin sun san wanda Shatu ta kira da wancan marar mutuncin, Baba Jamil direban Abubakar Madawaki ne, shi kuma wanda Shatu ta kira da wancan marar mutuncin, Mamman ne shi ne direbansu wanda yake kaisu school.
Kowa ya san Shatu bata son Mamman tun farkon zuwansa gidan ta ce wai wari yake yi, shi ma da kansa ya san Shatu bata ƙaunar ta hau mota yana ciki, shi yasa M.Madawaki yake saka Yusuf ya kaita ko kuma ta tafi da motarta.
Su na dariya suka fito a falon Daada suka tsaya domin sanar da Daada inda za su fita, kafin Daada ta fito Shatu ta fita domin kiran Nadiya, ko da Daada ta tambayi Shatu cewa suka yi ta fita addu'ar dawowa lafiya ta yi musu suka fito.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
A harabar Madawaki Dynasty kuwa, motoci biyu suka samu an gyara su da alama Shatu ce ta saka a wankesu tana tsaye a gefe Baba Isa mai gadi yana bata labari.
Nadiya ce ta shigo sannan duk suka shiga motocin Meerah da Rima,Nadiya suka shiga ɗaya, A ɗayan motar kuma Inayaa, Banisha da Nimrah sai Shatu da Nimrah ta riƙe dole sai sun tafi tare a mota ɗaya.
Suna fita Shatu ta sauke ajiyar zuciya,ta buɗe baki tana dariya.
"Yau kam zan manta da komai."
Inayaa ce ta kalle ta tare da cewa.
"Har maganar jiya?"
Shiru Shatu ta yi na ɗan lokaci sai ta girgiza kai.
"Yau ba na son tunani yau ranar shaƙatawa ce."
Banisha ce ta dafa kafaɗarta.
"That's my girl."
Dariya suka yi, har Nimrah da take jan motar.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Suna isa wajen, babban Gate ɗin recreation park ɗin ya buɗe musu, wurin cike yake da hasken fitilu, manyan kayan wasa, bowling alley, arcade games da wuraren zama.
Shatu ta sauke gilashin motar.
"Wow!"
Suna fitowa daga motoci, sai wasu daga cikin mutanen wajen suka juyo suna kallon motocin da suka shigo, da yawan mazan wajen kallonsu suke yi, ganin yadda suke farinciki.
Shatu ce ta kama hannun Meerah tana cewa
"Mu fara da games!"
Banisha ce ta yi saurin cewa.
"Da farko mu ɗauki hotuna."
Wayar Shatu Rima ta karɓe, dukkansu suka tsaya a gaban babban alamar wajen.
"One, two, three!"
"Cheese!"
Duk suka fashe da dariya, a cikin mutanen wajen ne wani ya zo yana cewa Ruma ta kawo wayar ta shiga cikinsu ya yi musu hotunan, babu musu ta bashi ya yi musu hotuna sosai.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Bayan sun gama hotuna, ne suka shiga arcade Shatu ta tsaya gaban wani game tana kallonsa.
"Me ake yi a nan?"
Meerah ta nuna mata.
"Ki gwada."
Shatu ta saka kuɗin wasan, amma kafin ta fahimci yadda ake yi sai da aka cinyeta kuɗaɗe masu yawa
"Wayyo!"
Dariya ta kama duk mutanen wajen ganin zallar shagwabe a wajen Shatu, turo baki ta yi tare da cewa.
"Meerah! Ki taimaka min!"
Dariya Meerah ta yi.
"Ki danna nan!"
"Na danna!"
"Ba wannan ba!"
"To wanne?"
Dariya duk suke yi ganin Shatu ta gagara yin.
A ƙarshe sai da Shatu ta ci wasan ba tare da ta san yadda ta yi ba, ta juya tana alfahari.
"Kun gani?"
Rima ta riƙe ciki tana dariya.
"Ba ki san abin da kika yi ba amma kin ci!"
"Nasara dai nasara ce."
Shatu ta faɗa tana hararar Rima.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Bayan wasanni suka je wajen bowling Nadiya ce ta fara jefa ƙwallon amma ta bi gefe.
"Zero!"
Nimrah ta fashe da dariya haka kowa ya fara gwada wa, sosai suke farinciki sai da suka gaji sanna suka nufin food court suka fara cin abinci.
Shatu na jingina da kujera tana kallon su.
"Na ji daɗi sosai yau."
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Sai misalin ƙarfe takwas na dare suka fito daga wajen.
Shatu ta tsaya tana kallon wurin.
"Wallahi ba na son mu tafi."
Rima ta ce:
"Za mu dawo."
Shatu ta shiga motarta tana murmushi a lokacin da motar ta fara tafiya ne, wayarta ta yi ƙara tana duba sakon da ya shigo.
Abbana:
"Kun gama? Ku dawo gida lafiya?"
Murmushi Shatu ta yi sannan ta rubuta.
"Eh Abbana muna hanya na ji daɗi sosai yau."
Bayan ɗan lokaci ya rubuta mata.
"Alhamdulillah. Ki yi hankali."
Ajiye wayar ta yi, a gefenta tana murmushi.
"Abbana ne."
Meerah ta kalle ta.
"Me ya ce?"
Dariya Shatu ta yi.
"Ya ce mu dawo gida lafiya."
Rima ta ce.
"To mu je."
Motocin suka ci gaba da tafiya cikin dare, fitilunsu suna haskakawa a kan titin.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
A zaune suke dukkaninsu kamar wanda suke family meeting,sallamar su Rima ce tasa duk suka ɗago suna kallonsu, Abubakar Madawaki ne ya kalle agogon hannunsa sannan ya nuna su da yatsa.
Ƙasa duk suka yi da kai babu bakin magana Baba Malam ne ya kallo gefen da M.Madawaki yake zaune sannan ya kalle Shatu da take tsaye girgiza kai ya yi yana nuna Shatu da hannayensa.
"Shatu M Madawaki, ban hanaki irin wannan shigar ba?"
Kallon jikinta Shatu ta yi sannan ta kalle gefen Abbanta ta turo baki tare da karɓar key ɗin motarta a hannun Nimrah ta nufin hanyar ɓangarensu.
Da kallo duk suka bi ta har M.Madawaki ganin bata bawa Baba Malam amsa ba, sai da buɗe ƙofar falon Mummynta sannan ta juyo.
"Ni gaskiya Baba Malam ka faɗa min abin da na yi maka sai na baka haƙuri duk ka takura min ai kana ganin Abbana bai yi min magana sai kai......"
Da gudu ta shiga falon tana rufewa da ƙarfi, ganin Baba Malam ya taso, murmushi manyan gidan suka yi Abubakar Madawaki na bawa Baba Malam haƙuri.
"Don Allah Baba Malam ka rabu da Shatu M Madawaki har yanzu yarinya ce ƙarama, akwai lokacin da za ta daina irin wannan shigar Yan matan ......."
"Kai! Kai! Abubakar tsaya ni a wajena Shatu M Madawaki ba yarinya ba ce, kune kuke ganinta a haka kuma zan ɗauki mataki sosai daga ita har wanda ya ɗaure mata gidi."
Faɗan Shatu da Baba Malam ne ya hana Abubakar Madawaki yi musu faɗa akan dare da suka yi, babu wanda ya nemi abinci a cikinsu haka suka kwanta duk a bedroom ɗaya, saboda ƙunara juna, sai asuba suka tashi, lokacin ma knocking ɗin Mummyn Shatu ne ya tashe su.
Hannayen Shatu ta kamo suka koma ɓangarensu a nan Mummy take tambayar ya maganar sake ɗaura auren tsakaninsu da Abban nata, sai lokacin Shatu ta tuna ta yi sallar asuba ta nufin ɓangaren Abbanta.
Hausawa dai suna cewa mai hali baya fasawa to haka ne a bangaren Shatu ma, domin tana zuwa bakin ƙofar master bedroom ɗinsa ta zauna tare da fara knocking tun tana yi a hankali har ta koma da ƙarfi kamar yadda ta saba, cikin bacci ya ji bugun ƙofarta babu shirya ya saka jallabiya ya buɗe.
Yana buɗewa ta faɗo cikin bedroom ɗin hannayensa ya miƙe mata ta kamo ya miƙar da ita, kallon fuskarta ya yi tare da lumshe idanuwansa, cikin ƙaramin sauti ta furta.
"Good morning."
Ɗaga mata kai ya yi, yana matse hannayenta cikin ɗan ɗaga sauti ta furta.
"Wayyo."
Kunnuwanta ta ya kama da ɗaya hannunsa yana tsareta da idanuwansa, ƙasa ta yi da kanta tana kamo hannunsa da yake kunneta, langwaɓe da kai ta yi tana furta.
"Sorry Abbana da ciwo..."
Yatsan hannunsa ya ɗora saman lips ɗinta yana sake riƙe kunnuwanta, baki ta turo tana son guduwa, hannunsa ɗaya ya saka yana kamo ɗan ƙaramin ƙugunta tare da sakata a jikinsa, a hankali ya motsa bakinsa.
"Eshaa ba kya jin magana ko?"
Rungumoshi ta yi da kyau tana kwantar da kanta a ƙirjinsa cike da shagwaɓeɓiyar muryata ta ce.
"Abbana."
Lumshe idanuwansa ya yi yana cirota da jikinsa tare da kallon kayan baccin jikinta wanda yake bayyana ilahirin jikinta lips ɗinsa na ɗan haɗuwa ya furta.
"Baba Malam bai hana ki saka irin wadannan kayan ba?"
Da sauri ta dawo jikinsa tare da buɗe baki ta fara kuka cikin kuka ta ce.
"Abbana wannan fa kayan bacci ne don Allah ka da ka hana ni sakawa,ban san da wane zan na yi bacci ba."
Goge mata hawayen fuskarta ya yi yana kamo hannayenta suka fito daga bedroom ɗinsa, a falo suka zauna suna fuskantar juna yana riƙe da hannayenta har lokacin, kallon hawayen fuskarta yake, ya san shi ɗaya take tsoro a Madawaki Dynasty, shi yasa take kuka saboda ya yi mata maganar da ya san dole ne sai ta yi biyayya akan abin da ya buƙata.
"Yusuf will bring you hijabs everyday, that is what you will be using inside this house."
Tun da ya fara maganar take kallon lips ɗinsa hawaye na zubowa, goge mata hawayen ya yi yana girgiza mata kai.
"Sorry Abbana amma ban da in zan fita ko? Domin dariya mutane za su yi min."
Ɗaga mata kai ya yi tare da tambayarta abin da ya kawota cikin sanyin jiki ta matso jikinsa tare da langwaɓe da kai tana taɓe baki ta ce.
"Abbana please remarry Mummy, I don't want people to know that my Abba and Mummy are not together, I won't be happy, and my Abba's respect will be affected and I don't want that..."
Murmushin gefen baki ya yi yana ɗago da kanta tare da furta.
"Is that what you want?"
Cike da farinciki ta furta.
"Yes Abban Shatu."
Lakace mata dogon hancinta ya yi tare da miƙewa yana kallon agogon hannunsa, ita ma tashi tsaye ta yi tana tsayawa a gabansa kallo ɗaya ya sake mata ya ɗauke idanuwansa, yana girgiza kansa.
"Okay ki sanar da ita, and ban son sake ganin ki shigo min da irin wannan shigar ba tare da hijabi ba ki fahimta?
*The End*
Sai mun haɗu a littafi na biyu domin jin yadda za ta kasance
✍️ MAMYY WRITER CE