GADON ZINA

1-2

by @oumhairan1

*💧💧GADON ZINA💧💧....*
_*(romance & destiny)*_


*Oum Hairan*


*long story*

*1-2*
Ranar juma'a ta kama yau da wuri ake tashin yan makaranta inda kowa yake ta saurin isa gida domin samun sauÆ™i daga Æ™walleliyar ranar da gari ya tashi da ita, cikin ranar wasu yammata ne su biyu sanye da kayan makarantar koyon aikin jinya tsaye a bakin titi rungume da takardun su da alama abin hawa suke jira, A hankali mafi sanyi a cikinsu ta sawa wani me mota hannu har yayi gaba ya dawo baya ya tsaya ya isa gareshi cikin takunta ne jan hankalin Mazaje ta É—an duÆ™a daidai window na motar daya zuge tace “Sannu mal da alama miÆ™ewa zakaji don Allah ka saukemu a kwanar É—ambare mana" É—an jim yayi idanunsa yana kaiwa ga wacce take tsaye a waje tana danna waya ya hadiye wani yawu yace “Alrigh Nima can nayi dama" godiya Huda tayi ta kalli Siyama Tace “Sai Kizo mu tafi yar wahala kin zubar wa da mutane kuÉ—in transport kuma kin tsaya miskilanci Ni da na saba zubar da abin na zubar" Takowa tayi cikin takunta na Æ™asaita tana kara wayar a kunnenta tace “Sweet zansha Baby" tsaki Huda tayi tace “Yar babyn bura uba ai wallahi sai na faÉ—awa Mama ke kullum bakida aiki sai kula Æ™ananun yara" Kallonta tayi tayi Murmushi ta shige gaban motar tana ci gaba da amsa Wayarta ta wani lafe a jikin kujera tana magana Æ™asa Æ™asa shidai yaja motar suka tafi Huda  nata tsaki ita kam Siyama hankalinta na kan Wayarta har Saida ta gama sannan ta kalli gefenta ta kalli me driving É—in tace masa “Sannu fah" jinjina kai yayi yana Kallonta ta kawar da kai taci gaba da danna Wayarta sunyi tafiya me É—an tsayi sannan Ya buÉ—e baki yace “Ina zakuyi?"  Siyama yayiwa magana amma tayi banza dashi kamar bata san da ita yake ba sai huda ce taci gaba da yi masa kwatance suka isa har Æ™ofar gidan yana parking siyama ta buÉ—e ta fice
Bin bayanta yayi da kallo cike da mamakin ita wacce iri ce? Muryar Huda yaji tace “Mun gode Allah ya saka da Khairan" jinjina kai yayi ta tafi ya jima tsaye yana kallon ƙofar gidan tabbas su ɗin ba wasu masu alamar kuɗi bane da dukkan alamu ma suna cikin talakawan unguwar amma kuma wayewarsu ta burge shi basu da duhun kai saidai kuma da alamun girman kai a tare da wadda ta zauna a kusa dashi, ya jima tsaye Baisan me yake yi ba kafin ya samu ya ja motar ya nufi inda ya fito zashi yana tafe zuciyarsa na baya da haka ya isa gidan yayan nasa yayi parking ya fito yaran gidan suka rugo da gudu suna ihu suna cewa “Uncle Farooq Oyoyo Uncle Farooq Oyoyo" Murmushi yayi ya ɗauki karamin yaron yayi kissing nasa ya kama hannun babban yace “Oyoyo my Kids ina daddy?" Kallon saman sukayi Yaron yace “Daddy Bayason surutu ya hau sama ysƙi saukowa" shiga parlourn sukayi da sallama Aunty Zeey dake zaune ta amsa tare da cewa “Aa Farooq dama kana duniya?" shafa kansa yayi yace “Wlh inanan Matar yaya ayyuka ne suka min yawa Daddy ya kulleni ya hanani sakat yanzu ma ƙararsa na kawo wajen big bro"
Murmushi tayi tace “Shikam Daddy yaga ta kansa bini bini a kawo Æ™ararsa to yana sama bayajin daÉ—in jikin ne ma tun jiya" haurawa yayi saman ya buÉ—e kofar parlourn ya shiga da sallama Yaya Habibu dake zaune saman soffer da jarida a hannunsa ya dago ya kalleshi tare da amsa sallamar ya nemi guri ya zauna suka gaisa Ya zuba masa ido kafin yace “Da magana ne Farooq?" shafa kansa yayi yace “YaÆ™i ya Barni na huta dashi da Mommy kullum sai sunyimin maganar aure na faÉ—a musu idan lokaci yayi zanyi  amma sun kasa ganewa daga Æ™arshe dai Mommy tace zata nemamin mata tunda Ni tsoron yammatan nakeyi kuma na fahimci da gaske take yi don tun jiya tace wai naje gidan Æ™awarta naga Æ´aÆ´anta yammata guda uku cikinsu na zaÉ“i É—aya"


*Paid book regular 400 VIP 700 via *** fauziyya Tasiu Umar Opay evidance of payment ****


*Oum Hairan*