3-4
by @oumhairan1
*💧💧GADON ZINA💧💧....*
_*(romance & destiny)*_
*Oum Hairan*
*3-4*
Dariya abin ya bawa Habibu yace "To banda abinka Farooq ina ganin ai sauƙi aka nema maka maimakon ka tafi neman macen da zaku daidaita kaga saidai kawai a kawo maka daga buhu sai tukunya" Miƙewa yayi cikin damuwa yace “Nifa Yaya don Allah a ƙyaleni zan kawo matata da kaina wlh ban samu irin matar da nakeson aura ba har yanzu but akwai alamun komai ya kusa zuwa karshe" Murmushi Habibu yayi yace “Maida wuƙar Bro babu wanda Zaiyi maka dole kawai abinda ake buƙata kayi gaggawar nemowa saboda su mom sun gaji da ganinka a haka gsky Nima kusan kullum magana sukemin akan zaman nan naka babu aure" ajiyar zuciya yayi ya koma ya zauna yace “Ni bance ba Zanyi aure ba amma a bani dama tukunna" Miƙewa Habibu yayi yace “An baka yanzu kai muke jira amm ya maganar tafiyar mu kuwa?" Kwantar da kansa yayi jikin kujera kafin ya dago yace “France ko?" da takaici Ya Habib ya dubeshi yace “Inda ka sani" shafa gemunsa yayi yace “Ok zakuyi gaba zan biyo ku a baya" banza Habib yayi masa domin yasan halinsa shi komai baya daukarsa da muhimmaci.
***** ***** *****
Koda Siyama da Huda suka shiga gidan kamar yanda suka tsammata basu ishe mahaifiyarsu a gida ba hakan ya tabbatar musu ta fita yawonta Siyama tayi ƙwafa ta aje littafai da Wayarta ta cire kayanta ya rage daga ita sai under sikelt ta nufi bayi ta watsa ruwa ta fito daure da towel tans goge ruwan dake cikin sumarta ta shiga daki ta buɗe akwatin kayanta ta ɗauki wata riga mara nauyi me kama jiki ta saka ta fito kitchen ta nufa ta buɗe kular da aka zuba abincin shinkafa ce da wake ta buɗe miyar tasha kayan haɗi kifi nama duka a ciki flat ta dauka ta zuba a ranta tana cewa “Ita dai mama ba dai son jin daɗi ba" guri ta samu ta zauna bayan ta ɗauki lemon ta me sanyi taci abincin ta ƙoshi tayi gyatsa ta koma ta kwanta daidai lokacin ta tuna da abinda take burin yi idan ta dawo gida ta zabura ta miƙe ta dauki ƙaton Hijjab ta ɗora saman lalatacciyar rigar jikinta ta dauki Wayarta ta fita Huda na kiranta tana cewa tana zuwa, kai tsaye wani babban chamist dake kallon layin nasu ta nufa a cike wajen yake da mutane amma Siyama bata saurari kowa ba ta shige ciki ta tsaya gaban wani babban mutum dake zaune saman kujera yana latsa waya tace “Mal Sallameni" ɗagowa yayi ya sauke mata wani mugun kallo tayi dariya tace “Wlh Tallahi kodai ka Sallameni cikin rufin asiri ko kuma ka Sallameni bayan ka wulaƙanta nifa Habibu abin kunya gaba na bashi ba baya ba" Tsawa Ya daka mata ta kuwa kama ƙugu ta ɗauki waya ta fara danna wa tana cewa “Bari kaga kalar nawa ɗanyen kai Habibu Ni zaka cuta ka lallaɓani ka shanye min nono na dagani sai kai har kana cewa rabonka da nono me laushi da daɗin matsawa tun na wata shegiyar karuwarka data damfareka kuɗaɗe shine nima zaka damfareni to wlh baka isa ba yan sanda zan kaiwa ƙararka su dakar min kuɗina.........
*Paid book regular 400 VIP 700 via *** fauziyya Tasiu Umar Opay evidance of payment ****
*Oum Hairan*