KADDARAR ZUCIYA

PEACE AFTER THE STORM

by @jiddaahbarkum

KADDARAR ZUCIYA

CHAPTER FORTY-SIX: 46

PEACE AFTER THE STORM

JIDDAAH BARKUM

———-

Aliyu ya bi mutumin da ya wuce da kallo na ɗan lokaci, duk da bai ga fuskarsa sosai ba saboda duhun yamma da kuma yadda ya wuce cikin nutsuwa, ya ji kamar akwai wani abu game da shi da ya sa shi ɗan tsayawa da tunani, Yaya Umar… Ya furta sunan a cikin zuciyarsa, sai dai bai daɗe da ba wa lamarin muhimmanci ba, a hankali ya dawo da kallonsa kan Inteesar, ta riga ta janye daga jikinsa cikin kunya, kanta a sunkuye, hannayenta suna riƙe da gefen mayafinta, Aliyu ya yi murmushi kaɗan, “Babygirl,” ta ɗago idanunta a hankali, “Uhmm?” Ya kalleta sosai, kamar yana son haddace fuskarta, idanunta da suka yi jawur saboda kuka, laushin fuskarta, da yadda take kallonsa cike da so da kunya a lokaci guda, sai ya ce cikin muryarsa mai sanyi, “Ki shiga gida,” ta yi shiru tana kallonsa, ya ƙara cewa a hankali, “Akwai sanyi a waje,” wani irin daɗi ya ratsa zuciyarta, duk da yadda ya wahalar da ita a cikin waɗannan awoyin, har yanzu akwai wannan kulawar tasa da ke sa zuciyarta narkewa a gare shi, “Okay, Mi Amor,” ya gyada kai kaɗan, “Good girl,” Inteesar ta juya a hankali, tana tafiya zuwa cikin gidan, amma kafin ta kai ƙofar, sai ta waigo, Aliyu yana nan tsaye, har yanzu idanunsa suna kanta, da suka haɗa ido, sai ya yi mata wani ɗan murmushi na gefen baki, nan take ta yi saurin sunkuyar da kai cikin kunya, sai da ya tabbatar ta shiga cikin gidan lafiya sannan ya juya ya nufi motarsa, ya buɗe ƙofar, ya shiga, amma bai kunna motar nan take ba, ya jingina da kujerar, ya sauke numfashi a hankali, wani murmushi ya bayyana a fuskarsa, “Stubborn Babygirl…” Ya furta a hankali, sai ya lumshe idanunsa, yana tuna yadda ta fashe da kuka tana riƙe rigarsa, kar ka sake yi min haka… Muryarta ta dawo cikin kunnuwansa, wani irin tausayinta ya mamaye zuciyarsa, “I’m sorry, Babygirl,” ya furta a hankali, bayan wasu daƙiƙu, ya kunna motar sannan ya bar harabar gidan cikin nutsuwa.

A gefe guda kuma, da Inteesar ta shiga falon, sai ta tsaya, shiru, ba Nana, ba Umar, ba kowa, sai hasken TV da aka bari a kunne, ta sauke wani dogon numfashi na relief, “Alhamdulillah…” Ta furta a hankali, ba ta san dalilin da ya sa take jin kunyar a same ta cikin wannan halin ba, da sauri ta nufi matakalar gidan ta hau sama, tana isa ɗakinta, ta rufe ƙofar a hankali, sannan ta jingina da ita, wani murmushi ya bayyana a fuskarta, ba tare da ta shirya ba, sai ta rungume kanta tana murmushi ita kaɗai, “Mi Amor…” Ta faɗa cikin sanyin murya, a hankali ta ƙarasa zuwa gadonta ta faɗa a kai, tana kwanciya rubda baya, idanunta suna kallon silin ɗin ɗakin, amma zuciyarta tana maimaita abubuwan da suka faru mintuna kaɗan da suka wuce, yadda ya kira ta, yadda ya ce, “Come outside,” yadda ya tsaya yana jiranta, yadda ya kalleta, yadda ya ce, “Na ji kamar na rasa ki,” da kuma… Yadda ya rungume ta, nan take wani irin murmushi mai cike da kunya ya bayyana a fuskarta, sai ta turo baki kaɗan, sannan ta ɗaga mayafin da ke jikinta ta kai shi kusa da fuskarta, nan take ƙamshin turarensa ya daki hancinta, wani irin sanyi mai daɗi ya ratsa zuciyarta, ta lumshe idanunta, tana sake jin kamar hannayensa suna kewaye da ita, kamar muryarsa tana raɗa mata a kunne, “Babygirl…” Wani murmushi mai cike da farin ciki ya sake bayyana a fuskarta, ta ƙara rungume mayafin a jikinta, “Allah…” Ta furta tana dariya kaɗan, sai ta sake tuna yadda ta fashe da kuka a ƙirjinsa, yadda ya shafa kumatunta, da yadda ya ce, “I’m sorry,” nan take ta turo baki, “Da farko ka kusa kashe ni da damuwa…” Ta yi magana kamar yana tsaye a gabanta yana sauraron ta, “…sannan kuma ka zo kana lallashi,” sai ta yi murmushi, bayan ɗan lokaci, ta miƙe daga kan gadon, ta cire mayafin daga jikinta sannan ta ɗauki towel, cikin wani irin annuri da ya ƙi barin fuskarta, ta nufi toilet domin yin wanka, bayan ta fito, ta sanya pink satin pajamas, ta shafa body cream, sannan ta yi addu’o’in barci, har ta shirya kwanciya, sai a lokacin ne ta ji yunwa, ta zauna a kan gadon tana tunanin ko ta sauka ƙasa ta ɗauko abin da za ta ci, sai kuma ta tuna da Yaya Umar, gabanta ya faɗi, “A’a,” ta girgiza kai, “Ba zan sauka ba,” bayan abin da ya gani ɗazu, ba ta jin tana son sauka ta haɗu da shi a yanzu, har yanzu ba ta san ko ya fahimci abin da ya faru ba, kuma tana jin kunyar tunanin cewa watakila ya ga yadda Aliyu ya rungume ta, sai ta miƙe ta nufi ƙaramin table ɗinta, ta ɗauko chocolate ta buɗe, ta fara ci a hankali, bayan haka ta dawo kan gado ta ɗauki wayarta, ta kunna data, nan take notifications suka fara shigowa, WhatsApp, Instagram, Messages, sai kuma… Mi Amor ❤️ Nan take murmushi ya bayyana a fuskarta, da sauri ta buɗe chat ɗin, saƙon farko da ta gani ya ce, Babygirl… Inteesar ta lumshe ido na ɗan lokaci kafin ta buɗe saƙon gaba ɗaya, wani saƙo ya biyo shi, I am really sorry, sai wani, na yi reacting before listening to you, Inteesar ta tsaya tana kallon screen ɗin, wani saƙon ya sake shigowa, and that was unfair to you, zuciyarta ta ɗan yi wani irin bugawa, Aliyu bai tsaya ba, wallahi ban ji daɗin yadda na bar ki kina kuka ba, tun daga lokacin da na tafi, abin yana damuna, Inteesar ta haɗiye yawu a hankali, sai wani saƙon ya sake shigowa, you didn’t deserve that, Babygirl, kin yi ƙoƙarin explaining, amma ban saurare ki ba, I’m sorry, a hankali ta ciji leɓenta, sai ta rubuta, it’s okay, ya yi reply kusan nan take, no, ba okay ba ne, idan wani ya yi miki haka, ni ma ba zan ji daɗi ba, Inteesar ta yi shiru tana kallon saƙon, wani ɓangare na zuciyarta yana jin daɗin yadda Aliyu ya amince da kuskurensa, amma har yanzu tana tuna yadda ta ji lokacin da ya ƙi sauraron ta, sai wayarta ta yi ringing, Mi Amor ❤️ Calling… Ta kalli screen ɗin na wasu seconds kafin ta ɗaga, “Hello…” Muryarta ta fito a hankali, a ɗayan ɓangaren, Aliyu ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya sauke numfashi, “Babygirl…” “Uhmm,” “Are you okay?” Ta ɗan yi shiru, “Eh,” Aliyu ya lumshe ido, ya gane daga muryarta cewa har yanzu ba ta dawo daidai ba, “You’re still upset with me,” Inteesar ta girgiza kai duk da bai gan ta ba, “A’a,” “You’re not telling the truth,” sai ta yi shiru, Aliyu ya yi wani ɗan murmushi mai ɗauke da nadama, “Kin san abu ɗaya da nake tsoro?” Ta yi shiru tana sauraron sa, “Na fi jin tsoron zama dalilin hawayenki,” Inteesar ta runtse idanunta, kalaman nasa suka taɓa zuciyarta, “Mi Amor…” Muryarta ta yi laushi, amma ya katse ta a hankali, “No, let me talk,” ya sauke numfashi, “Na ji kishi,” “Na ji zafi,” “Amma duk da haka, ya kamata na saurare ki,” sai ya yi shiru na wasu daƙiƙu, “Wallahi, da na ga idanunki yau…” Muryarsa ta yi ƙasa, “…na tsani kaina,” Inteesar ta lumshe idanunta, hannunta ya matse wayar, “Kar ka faɗi haka,” “To, me zan faɗa?” ya tambaya cikin sanyin murya, “Na sa Babygirl ɗina kuka har idanunta suka kumbura,” sai ta kasa hana kanta ɗan murmushi, Aliyu ya lura da canjin da ke cikin muryarta, “Finally…” Ya furta a hankali, “Murmushi kika yi, ko?” Inteesar ta turo baki, “A’a,” “Princess…” Muryarsa ta ɗan yi laushi, “I know your smile,” sai ta sauke kanta tana murmushi ita kaɗai, Aliyu ya sake sauke numfashi, “Now sleep, ki huta, kin ji? We will talk tomorrow,” a hankali ta amsa, “To, Mi Amor, sai da safe,” “Good night, Babygirl,” “Good night,” ta kashe wayar a hankali, zuciyarta cike da wani irin farin ciki da dumi mai daɗi, ta gyara kwanciyarta, ta ja bargo ta rufe jikinta, sannan ta lumshe idanunta tana yin addu’o’in barcin da ta saba yi, cikin ƙanƙanin lokaci, barci ya yi awon gaba da ita, tare da mafarkai masu daɗi.

Haka rayuwa ta ci gaba da juyawa, ranaku suna shuɗewa suna komawa makonni, yayin da makonni suke ƙoƙarin komawa watanni, kullum, Aliyu da Inteesar suna tashi da wata sabuwar dabarar nuna soyayya ga juna, soyayyarsu babu abin da take yi sai ƙara bunƙasa, tana cike da kulawa ta musamman da kuma wata irin ƙauna mai daɗin zama a rai, ba su sake samun wani saɓani mai girma ba tun bayan wannan ranar, Aliyu yana iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya faranta mata rai, yayin da Inteesar ma ba ta da wani buri da ya wuce ta ga annuri da natsuwa a tare da shi a kowane lokaci, a hankali, Inteesar ta fara fahimtar cewa soyayya ba wai kawai kalaman I love you ba ne, akwai sauraron juna, fahimtar juna, haƙuri da kuma iya amincewa da kuskure idan an yi shi, ita kuwa Aliyu, duk da ƙaunar da yake mata, ya fara ƙara fahimtar cewa ba zai iya kare soyayyarsu da kishi kawai ba, dole ne ya koyi yarda da ita, kamar yadda ita ma ta zaɓi yarda da shi, lokaci ya ci gaba da tafiya, a halin yanzu, lokaci ya ƙara matsowa sosai, domin saura watanni shida kacal kafin bikin aurensu, a gefe guda kuma, harkar karatun Inteesar ta yi nisa, saura watanni biyu kacal kafin ita da sauran ɗaliban Level 4 su fara jarabawar zangon karatu na ƙarshe, wato final second-semester examinations, hakan ya sa hankalinta ya fara rabuwa biyu tsakanin shirye-shiryen kammala karatun jami’a da kuma fargaba da ɗokin babban taron aurensu da ke tafe, wani sabon babi na rayuwarta yana gabatowa, kuma duk da farin cikin da take ji a zuciyarta, Inteesar ta san cewa watannin da ke gabanta za su kasance cike da aiki, shiri, da kuma yanke shawara da za su yi tasiri a rayuwarta ta gaba.