BEYOND THE GIFT
KADDARAR ZUCIYA
CHAPTER FORTY-SEVEN: 47
BEYOND THE GIFT
JIDDAAH BARKUM
————
Wata ranar Alhamis da yamma… Inteesar ta dawo daga makaranta cikin gajiya, ranar gaba ɗaya lectures sun wahalar da ita, sannan akwai wasu assignments da suka ɗauki lokaci mai tsawo tana yi tare da Amira, da ta fito daga mota a harabar gidan Nana, ta sauke numfashi a hankali, “Allah, na gode…” Ta furta tana gyara hijabinta, abin da take buri kawai a lokacin shi ne ta shiga gida, ta yi wanka, sannan ta kwanta na ɗan lokaci, a hankali ta tura ƙofar falon ta shiga, da sallama a bakinta, “Assalamu alaikum…” “Wa alaikumus salam!” Muryoyi biyu suka amsa lokaci guda, Inteesar ta ɗago kai, sai ta tsaya cak, idanunta suka zaro da mamaki, “Farry?!” Ta faɗa da ƙarfi, a gefen kujera kuwa, Farida na zaune cikin wani kyakkyawan jumpsuit mai launin cream, tana murmushi tana kallon yadda mamaki ya mamaye fuskar Inteesar, Nana kuma tana gefe tana ta dariya, “Wai da gaske ke ce?” Inteesar ta sake faɗa, Farida ta buɗe hannayenta, “Ko kuwa fatalwa kika gani?” Ba ta gama magana ba, Inteesar kamar wacce aka saka wa remote, ta ruga da gudu, nan take ta faɗa jikin Farida ta rungume ta sosai, “Farryyyyy!” Farida ta fashe da dariya, tana rungume ta ita ma, “Inteeeeee!” Duk falon ya cika da dariyarsu, Nana ma ta kasa riƙe dariyarta, “Ku dai ku karya min kujera kawai,” sai da suka yi dariya sosai kafin Inteesar ta sassauta rungumar, ta ja baya kaɗan tana kallon Farida kamar wacce ba ta yarda da abin da take gani ba, “Gaskiya wallahi ke ce kuwa!” Farida ta ɗaga gira, “A’a, clone ɗina ne,” Inteesar ta kai mata dukan wasa a kafaɗa, “Ban son rainin hankali,” Farida ta yi dariya, Inteesar kuwa har yanzu murmushi ya ƙi barin fuskarta, amma daga bisani sai ta turo baki, “Amma fa ba ki gaya min za ki zo ba,” Farida ta langwabe kai gefe, “Exactly,” “Haba, Farry,” Farida ta yi dariya, “I just wanted to surprise you,” sai ta nuna Inteesar da yatsa, “And clearly… it worked,” Nana ta fashe da dariya, Inteesar ta kalli Nana da zargi, “Yaya Nana!” Nana ta ɗaga gira, “Na’am?” “Ashe kin sani?” Nana ta gyada kai, “Eh,” Inteesar ta zaro ido, “Kuma kika ƙi gaya min?” Nana ta ɗaga hannayenta sama, “Toh ya zan yi? Ta ce kar na faɗa miki,” Farida ta gyada kai tana dariya, “I specifically said no spoilers,” Inteesar ta turo baki, “Ku duka kun haɗe min kai,” Nana ta yi dariya, “Ki ce mun yi nasara,” suka sake fashewa da dariya gaba ɗaya, Inteesar ta zauna kusa da Farida tana riƙe da hannunta, “Wallahi na yi missing ɗinki,” “Ni ma,” “Yaushe kika zo?” “Yau da safe,” “Yau da safe?!” “Eh,” “Kuma kika zauna kika yi shiru?” Farida ta yi dariya, “Na so in ga reaction ɗinki,” Inteesar ta girgiza kai, “You’re wicked,” “I know,” duk suka sake dariya, suna cikin hirarsu ne suka ji an buɗe ƙofar falon, duk suka waiga, Yaya Umar ne, ya shigo daga office, sanye yake cikin wani ash-coloured kaftan mai sauƙin kyau, agogon hannunsa na kyalli kaɗan, da alama ya gaji daga aikin ranar, amma da idanunsa suka sauka kan baƙuwar da ke zaune a falon, sai ya tsaya, fuskarsa ta faɗaɗa da murmushi, “Faridaa?” Ya faɗa da mamaki, sannan ya matsa gaba kaɗan, “Are you the one… ko idanuna ne suke yaudarata?” Farida ta fashe da dariya, ta miƙe tsaye, “Nice to see you, Uncle,” Umar ya girgiza kai yana murmushi, “Subhanallah,” Farida ta yi murmushi, “Ina yini, Uncle?” “Lafiya kalau,” ya amsa yana kallonta da kulawa, “Ya hanya?” “Alhamdulillah,” “Ya kika baro mutanen gida?” “Alhamdulillah suna lafiya,” ya gyada kai, “Madallah,” Inteesar da Nana kuwa suna kallonsu, Farida ta ci gaba da cewa, “Mommy ta ce in gaishe ku, da Daddy ma,” Umar ya yi murmushi, “Muna amsawa da kyau,” sai ya zauna a kujera kusa da su, yana kallon Farida, “Gaskiya kin girma,” Farida ta zaro ido, “Wai Uncle!” “Hmm?” “Wannan kalmar fa tana tsoratani,” Nana ta yi dariya, Farida ta girgiza kai, “Duk lokacin da kuka ce na girma, sai na fara tunanin ko ana shirin aurar da ni ne,” nan take Inteesar ta fashe da dariya, Nana ta rufe baki tana dariya, Umar kuma ya ɗan yi dariyar da ta bayyana fararen haƙoransa, “Toh ai idan lokaci ya yi…” “Uncle!” Farida ta katse shi da sauri, duk falon ya sake kaurewa da dariya, Farida ta yi dariya tana amsa tambayoyin Umar cikin ladabi, yayin da shi kuma yake sauraronta da kulawa, “Ya Lagos ɗin?” Farida ta ɗan turo baki gaba, “Lagos dai Lagos ne, Uncle, hayaniya ba ta ƙarewa,” Umar ya yi dariya, “Shi yasa nake cewa Abuja ta fi nutsuwa,” “Wallahi gaskiya ne,” duk suka yi dariya, Inteesar kuwa ta riga ta gaji da wannan hirar, tun da ta ga Farida, zuciyarta ta cika da wani irin farin ciki, ta daɗe rabonta da ita, kuma tana son su samu lokacin su kaɗai su yi hirar da ta dace, sai ta ja hannun Farida a hankali, “Zo mu je sama,” Farida ta kalleta tana dariya, “Kin fara ko?” “Eh mana,” Nana ta girgiza kai tana murmushi, “Ku je ku ci gaba da hirarku,” “Thank you, Yaya Nana,” Inteesar ta amsa cikin sauri, Farida ta miƙe daga kujerar, “Uncle, sai anjima,” Umar ya gyada kai, “Okay, ku huta,” ba tare da ɓata lokaci ba, Inteesar ta ja hannunta suka nufi stairs, tun kafin su kai saman bene, dariyarsu ta fara cika wajen, “Wallahi ban yarda da ke ba,” Farida ta faɗa tana dariya, “Me na yi kuma?” “Ki duba yadda kika janye ni ina hira da ubana,” Inteesar ta harare ta, “Toh me kike so in yi? Kin zo ba tare da kin faɗa min ba,” “Shi kenan, surprise,” “Da na sani da na zo airport ɗin,” Farida ta girgiza kai, “Wannan ne dalilin da yasa ban faɗa miki ba,” suka sake fashewa da dariya, da suka isa ɗakin Inteesar, ta buɗe ƙofar da sauri, “Welcome to my humble abode,” Farida ta yi dariya, “Please,” ta shiga tana kallon ɗakin, “Wow,” Inteesar ta juya, “Me?” “Room ɗinki ya canja,” “Really?” “Eh,” ta zauna a bakin gadon, “Very neat,” Inteesar ta ɗan yi ƙoƙarin yin kamar mai girman kai, “Of course, how do you see it? Like a real princess’s comfort zone,” ta faɗa tana kashe ido ɗaya, Farida ta ɗauki pillow ta jefe ta da shi, nan take suka sake fashewa da dariya, Inteesar ta zauna kusa da ita, a wannan karon kuwa ta kalleta sosai, “Wallahi kin yi kyau,” Farida ta ɗaga gira, “Ni?” “Eh,” “Kamar dai ke ba,” Inteesar ta yi dariya, “Ni fa kullum haka nake,” “Karya ne,” Farida ta ce tana kallonta da kyau, “Kin ƙara haske, kin ƙara kiba kaɗan, face ɗinki ma ya ƙara cika,” Inteesar ta turo baki, “Don Allah,” “Wallahi da gaske,” sai ta ɗan matsa kusa da ita, “Soyayya ce take aiki ko?” Nan take Inteesar ta buɗe ido, “Farida!” Farida ta fashe da dariya, “Me?” “Kar ki fara,” “Wallahi zan fara,” “Ban ma fara ba,” “Ai daga shigowa na gane,” Inteesar ta dafe goshinta, “Ya Salam,” Farida ta kwanta a kan gadon tana dariya, “Tell me everything,” Inteesar ta haɗe hannu, “A’a,” “A’a kuma?” “Ki fara ba ni labarin Lagos,” Farida ta nuna ta da yatsa, “Ni za ki wayancewa?” “Eh,” “Saboda na san abin da kike son ji,” “Exactly,” suka sake dariya.
Daga ƙasa kuwa… Nana ta bi bayan Umar zuwa corridor ɗin da yake kaiwa sashensa na gidan, Umar ya cire agogon hannunsa yana tafiya, sai Nana ta ce cikin murmushi, “Na ji daɗin zuwan Farida sosai,” Umar ya gyada kai, “Sosai, ta kyauta da ta zo ai, very respectful girl,” “Of course,” ya amsa a taƙaice, Nana ta kalle shi, “Daga office ka dawo kai tsaye?” “Eh, lokaci ma bai cika ba na taho,” “Ka ci abinci?” “A’a,” “Shi kenan, bari na kawo maka,” Umar ya ɗan yi murmushi, “Thank you,” sai Nana ta tsaya tana kallonsa, “Ka gaji,” ya sauke numfashi, “Very long day,” Nana ta gyada kai, “Toh je ka huta,” “Okay,” ya shiga sashensa, Nana kuma ta juya ta koma downstairs, a saman bene kuwa, har yanzu dariyar Inteesar da Farida ba ta tsaya ba, domin bayan watanni masu yawa na waya da video calls, a ƙarshe sun sake haɗuwa fuska da fuska, kuma cikin ɗan lokaci kaɗan, hayaniyar farin ciki ta mamaye gidan gaba ɗaya.
A can birnin Katsina kuwa… Yammacin ranar ya yi tsit cikin gidan Alhaji Kabeeru, iska mai sanyi tana kadawa a harabar gidan yayin da ma’aikata ke kai da komowa cikin nutsuwa, a cikin falonsa na musamman kuwa, Alhaji Kabeeru yana zaune shi kaɗai, wani brown envelope yana kan table a gabansa, idanunsa suna kansa, kamar wanda yake tunanin wani abu mai matuƙar muhimmanci, bayan wasu daƙiƙu, sai ya ɗauki wayarsa ya kira Aliyu, ba a daɗe ba aka amsa, “Assalamu Alaikum, Daddy,” “Wa Alaikumus Salam, Aliyu,” “Daddy, barka da yamma,” “Barka dai, Aliyu, ya kake?” “Alhamdulillah, Daddy,” Alhaji Kabeeru ya yi murmushi kaɗan, “Masha Allah,” sai ya ɗan yi shiru, “Ina son ganin ka,” Aliyu ya gyara zamansa, “Yanzu?” “Eh,” “Toh Daddy, in Sha Allah zan zo,” “Madallah,” bayan kusan awa ɗaya, Aliyu ya isa gidan, bayan ya gaisa da kowa a falo, sai aka ce masa Daddy yana jiransa a falonsa na sama, nan take zuciyarsa ta buga, ba don tsoro ba, sai don girmamawa, duk lokacin da Alhaji Kabeeru ya kira shi shi kaɗai, yakan ji wani irin nauyi da daraja a lokaci guda, a hankali ya isa ƙofar, ya buga, “Shigo,” muryar Daddy ta fito, Aliyu ya buɗe ƙofar ya shiga, sai ya ga Alhaji Kabeeru zaune a kujerarsa, nan take ya ƙarasa, ya durƙusa cikin girmamawa, “Assalamu Alaikum, Daddy,” “Wa Alaikumus Salam,” “Barka da hutawa, Daddy,” “Barka da ƙarasowa, Aliyu, ka zo,” Aliyu ya amsa yana sauke kansa ƙasa, sannan ya zauna, ɗakin ya yi shiru na wasu daƙiƙu, Alhaji Kabeeru yana kallonsa, Aliyu kuma yana zaune cikin ladabi, sai Daddy ya sauke numfashi, “Aliyu,” “Na’am, Daddy,” ya miƙa hannu, ya ɗauki brown envelope ɗin da ke gabansa, sannan ya miƙa masa, “This is for you,” Aliyu ya karɓa da mamaki, ya kalli envelope ɗin, sannan ya ɗago, “Daddy?” Alhaji Kabeeru ya jingina da kujera, muryarsa cike da nutsuwa, “Na ba ka gida,” Aliyu ya daskare, kamar bai ji da kyau ba, “Daddy?” Alhaji Kabeeru ya yi murmushi kaɗan, “Na ce na ba ka gida, kyauta, halal malak, inda nake so ka zauna da Inteesar bayan aure,” shiru, Aliyu ya kasa motsi, kawai yana kallon Daddy, sai Daddy ya ci gaba, “Kuma ban ce ita kaɗai za ka zauna da ita ba, idan kana so ka kai iyayenka, ko yayyanka, ko duk wanda kake so, za ka iya haɗa iyalinka gaba ɗaya, yadda ka tsara rayuwarka, haka za ka yi,” Aliyu ya ji zuciyarsa tana bugawa, amma Daddy bai gama ba, sai ya ɗan yi shiru, sannan ya ce, “Amma akwai abu guda ɗaya,” Aliyu ya gyara zamansa, “Ina sauraronka, Daddy,” Alhaji Kabeeru ya kalli idanunsa kai tsaye, “Ba na son Inteesar ta taɓa sanin wannan maganar, har abada, abin da ke cikin wannan ɗaki yanzu, tsakanina da kai ne, sai lawyer ɗina, sai Ubangijina, ko mahaifiyarta, ko yayyanta, ko ita kanta Inteesar, babu wanda zai sani,” daga nan ya nuna envelope ɗin, “Duk takardun gidan suna ciki, mukullansa ma suna ciki,” duk suka yi shiru, dogon shiru, Aliyu ya buɗe envelope ɗin da hannu mai rawa, sai ya ga takardu, original documents, ownership papers, location, details, sai idanunsa suka zaro, Abuja, mansion, babban gida, ba ƙaramin gida ba, ba irin gidan da ake saya a sauƙaƙe ba, Aliyu ya ji kamar maganar ma da yake so ya yi ta ƙi fitowa, kawai yana kallon takardun, sannan ya kalli Daddy, sai ya sake kallon takardun, a hankali ya sauke su, ya durƙusa sosai, idanunsa sun cika da hawaye, “Daddy…” Muryarsa ta yi rawa, “Nagode, Allah ya ƙara girma, Allah ya saka maka da alkhairi, Allah ya biya ka, Allah ya…” Sai muryarsa ta dashe, Daddy kuwa ya ɗaga masa hannu, “No,” Aliyu ya yi shiru, Daddy ya girgiza kai, “You don’t have to thank me,” kamar an danna wani maɓalli, Aliyu ya ɗago, Alhaji Kabeeru ya yi murmushi, “Ka gama min komai, tun ranar da na ga yadda kake kallon Fateema…” Aliyu ya lumshe ido, saboda ya san Daddy yana magana ne a kan Inteesar, “Tun ranar na san akwai wani abu daban a zuciyarka,” Daddy ya ɗan yi murmushi, “Sai kuma daga baya na ga yadda kake kula da ita, na ga yadda kake girmama ta, na ga yadda kake kare ta, ba wai da baki kawai ba, a aikace,” Aliyu ya ji wani abu ya tsaya masa a maƙoshi, sai Daddy ya ɗan matsa gaba, “Aliyu,” “Na’am, Daddy,” “Kowa na iya cewa yana son mace, kowa, amma ba kowa ne yake iya ɗaukar nauyinta ba, ba kowa ne yake iya kare mutuncinta ba, ba kowa ne yake iya zama amintaccen mafaka gare ta ba,” Daddy ya sauke numfashi, sannan ya ce a hankali, “Yarinyar nan… Ba ka san yadda nake sonta ba,” hawaye suka taru a idanunsa, “Ni da mahaifiyarta mun rasa barci saboda ita, yayyanta sun taso suna ɗaukarta kamar ita kaɗai ce mace a duniya, kowa a gidan nan yana kallonta a matsayin amanar Allah,” sai ya ɗan yi shiru, muryarsa ta yi ƙasa, “Amma daga ranar aurenta…” Kai tsaye ya nuna Aliyu, “Amanar nan za ta koma hannunka,” Aliyu ya runtse idanunsa, hawayensa suka zubo, Daddy ya ci gaba, “Idan ta yi kuskure, ka gyara ta cikin tausayi, kar ka wulaƙanta ta, kar ka karya mata zuciya, kar ka sa ta ji ita kaɗai ce,” sai ya haɗiye wani abu, “Saboda Inteesar, ko da ta nuna ƙarfi a wajen mutane, a zuciyarta tana da rauni sosai,” Aliyu ya goge hawayensa, wallahi ya kasa magana, Daddy ya ci gaba, “Idan wata rana kuka samu sabani, ka tuna cewa tana da gida, ka tuna cewa tana da uba, ka tuna cewa akwai wasu maza guda takwas da za su iya sadaukar da komai saboda ita,” sai ya yi murmushi kaɗan, “Amma kafin su isa gare ta, ina so kai ne za ka zama kariyarta,” Aliyu ya sunkuyar da kansa, hawayensa suna zubowa, a hankali ya ce, “Daddy… Wallahi…” Sai muryarsa ta karye, ya haɗiye wani abu, sannan ya sake cewa, “Wallahi zan kula da ita, da yardar Allah, zan kare ta, zan girmama ta, zan so ta, zan riƙe amanarka,” Alhaji Kabeeru ya kalli yadda hawayen ke sauka a fuskar Aliyu, sai zuciyarsa ta yi sanyi, saboda a karon farko, ya ji kamar yana kallon mutum ba suruki kaɗai ba, sai wanda zai iya zama mafakar Princess ɗinsa, sai ya miƙa hannu, ya dafa kafaɗar Aliyu, sannan ya ce cikin nutsuwa, “Na yarda da kai,” kalma uku kacal, amma kalmomin sun sauka a zuciyar Aliyu fiye da kowace kyauta da ya taɓa samu a rayuwarsa, domin amincewar Alhaji Kabeeru ta fi kowace dukiya nauyi, Aliyu ya zauna cak, envelope ɗin yana hannunsa, har yanzu bai gama yarda da abin da ya faru ba, mansion, a Abuja, kyauta, ba aro ba, ba rance ba, ba wani sharadi na duniya ba, sai kuma abu ɗaya… Kar Inteesar ta taɓa sani, hannunsa ya matse envelope ɗin a hankali, idanunsa suka sauka ƙasa, zuciyarsa ta cika da wani irin nauyi da ba zai iya fassara shi da kalmomi ba, ba nauyin gidan ba, ba nauyin arzikin ba, nauyin amanar da Alhaji Kabeeru yake ɗora masa ne, wani shiru ya sake mamaye ɗakin, sai Alhaji Kabeeru ya gyara zama, ya kalli Aliyu sosai, kallon uba, kallon wanda ya daɗe yana nazarin mutum kafin ya yanke hukunci a kansa, “Aliyu,” Aliyu ya ɗago kai a hankali, “Na’am, Daddy,” Alhaji Kabeeru ya sauke numfashi, “Ka san me yasa nake son ganinka kai kaɗai?” Aliyu ya girgiza kai, “A’a, Daddy,” Daddy ya yi ɗan murmushi, “Saboda akwai maganar da ba kowa zan iya yi wa ita ba,” Aliyu ya yi shiru, ya sake gyara zamansa, Alhaji Kabeeru ya jingina da kujerarsa, sannan ya ce cikin nutsuwa, “Mutane da yawa suna kallon Inteesar a matsayin yarinya mai gata,” Aliyu ya yi murmushi kaɗan, saboda hakan gaskiya ne, Daddy ya ci gaba, “Suna ganin dariyarta, suna ganin shagwaɓarta, suna ganin yadda kowa yake biye mata, amma akwai abubuwa da yawa da ba su sani ba,” Aliyu ya yi shiru yana sauraro, Alhaji Kabeeru ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci, lokacin da ya sake buɗe su, idanunsa sun nuna wata irin soyayyar uba mai zurfi, “Aliyu…” “Na’am, Daddy,” “Fateema ba yarinya ce mai ƙarfi kamar yadda mutane suke tunani ba,” Aliyu ya ji zuciyarsa ta buga, Daddy ya ci gaba, “Tana da zuciya mai laushi, mai tsananin laushi, idan tana farin ciki, tana farin ciki da gaske, idan kuma tana cikin damuwa…” Ya yi shiru, sannan ya ce a hankali, “…zuciyarta tana karyewa cikin sauƙi,” Aliyu ya runtse idanunsa, saboda ya san hakan, ya gani, ya gani lokacin da ya yi mata rashin fahimta, ya gani lokacin da ta yi kuka saboda shi, Daddy ya kalle shi, “Kada ka taɓa raina hawayenta,” Aliyu ya ji wani abu ya tsaya masa a maƙoshi, “Ba zan yi ba, Daddy,” Alhaji Kabeeru ya gyada kai, “Na sani, da ban yarda da kai ba, da ban ba ka aurenta ba,” wani irin sanyi ya ratsa jikin Aliyu, Daddy ya ci gaba, “Ina da maza takwas, kuma dukansu suna sonta fiye da yadda kake tunani,” Aliyu ya gyada kai, ya san hakan sosai, “Amma yau…” Daddy ya nuna shi da hannu, “Ni ne nake sake ba ka amanarta, ka kula da ita, ka kare ta, ka zama abokinta kafin ka zama mijinta, ka saurare ta idan tana magana, ka fahimce ta idan duniya ba ta fahimce ta ba,” sai ya ɗan yi shiru, muryarsa ta yi ƙasa, “Kuma idan wata rana kuka yi saɓani, kada ka taɓa barinta tana kuka ita kaɗai,” nan take Aliyu ya sunkuyar da kansa, idanunsa sun cika da ruwa, saboda kalaman sun shiga zuciyarsa kai tsaye, ya tuna ranar da ya ƙi ɗaga wayarta, ya tuna yadda ta yi kuka, ya tuna yadda ya same ta cikin wannan hali, wani irin nadama ya sake ratsashi, Daddy ya lura da yanayin fuskarsa, sai ya yi murmushi kaɗan, “Ba na cewa ba za ku iya samun matsala ba, ku mutane ne, amma ka tuna, ka fi kowa sanin yadda zuciyarta take,” Aliyu ya gyada kai, da ƙyar ya iya cewa, “In Sha Allah, Daddy, zan kula da ita, wallahi zan kula da ita,” muryarsa har tana rawa, Alhaji Kabeeru ya yi murmushi, murmushin uba mai nutsuwa, “Domin daga yau, ba ni kaɗai nake da alhakinta ba, mun zama biyu,” ya nuna kansa, “Ni mahaifinta,” sai kuma ya nuna Aliyu, “Da kuma kai, mijinta,” hawaye suka taru a idanun Aliyu, ya kalli Daddy, “Daddy…” Muryarsa ta yi rauni, “Ban san yadda zan gode maka ba,” Alhaji Kabeeru ya ɗaga masa hannu nan take, “Kada ka gode min, ka faranta mata rai kawai, shi ne godiyar da nake so,” shiru ya mamaye ɗakin na wasu daƙiƙu, sai Daddy ya yi murmushi, sannan ya nuna masa ƙofa da hannu, “Aliyu,” “Na’am, Daddy,” “Za ka iya tafiya, Allah ya yi muku albarka, Allah ya sanya alkhairi a rayuwarku, Allah ya sanya farin ciki a tsakaninku,” “Ameen, Daddy,” Aliyu ya amsa da sauri, muryarsa cike da girmamawa, a hankali ya risina, ya ɗan sunkuyar da kansa, kamar yadda ɗa zai yi wa uba, “Nagode, Daddy,” Alhaji Kabeeru ya yi murmushi kawai, Aliyu ya miƙe, envelope ɗin yana hannunsa, amma amanar da ke zuciyarsa ta fi gidan nauyi, ta fi kuɗi nauyi, ta fi komai nauyi, ya juya a hankali, ya nufi ƙofar, kafin ya fita, sai ya waigo, Daddy yana nan zaune, yana kallonsa da idanun da suka cika da yarda, yarda cikakkiya, yardar uba ga mutumin da zai ba amanar diyarsa, Aliyu ya ji zuciyarsa ta sake bugawa, sai ya gyada kai cikin girmamawa, sannan ya fita daga ɗakin, yana tafiya cikin corridor ɗin gidan, hannunsa ya matse envelope ɗin da ƙarfi, amma zuciyarsa tana maimaita kalma guda ɗaya, amanah, a yau, ya fahimci cewa ba Inteesar kawai aka ba shi ba, an ba shi amana ce da ta fi komai girma a zuciyar Alhaji Kabeeru.