21
by @asmybaliyu
OMRI HAYATII
by..
Asmy b Aliyu
21.....
tun daga sama har kasa noor din ke kallonta ganin ba kayan da ta fita dasu bane ajikinta,dan shewa ta saki
tana fadin.DANGEROUSE MALAAK......"wani murmushi ya subucewa malaak din Wanda bata shirya zuwansa ba.to ya akayi yazo Abuja?"Sai da uwar tasa ta basa umurnin
zuwa... murmushi malaak din ta Kara saki
a Karo na biyu jin tambayar da noor din
tayi mata zama tayi a gefen bed.ko a hakan mu'azzam ya biyata ya sakata farin cikin da bai taba sakata ba ya tako tun daga garin Lagos yazo abuja dan kawai
yaganta ya goge laifin da yayi mata.
"dama kin San gayen nan ya mutu akanki
shine kika tsaya kina wahalar da kanki.
a tafi ma a haka idan kika xama matar aurensa shikenan fa malaak ko uwarsa
batada iko dashi kamar yadda xakiyi
iko dashi.kuna zaune a falo keda uwar
tasa kina son ki shiga turaka da miji
dole fa ya tashi ya biki........Kuma bata isa tace uffan ba tunda baita Xata kwanta dashi ta sauke masa dukkan bukattunsa ba.wani irin girgiza legs malaak ta shigayi
tana jin kalaman noor din na Kara fasa mata Kai haka Suna mugun sakata farin ciki..........tana hango yadda Xata mayarda rayuwar miss Ayshaa marafa idan ta auri mu'azzam wannan takamar da isar da take nunawa akan mu'azzam duk sai ta sauke mata shi Sai ta tsiyaye ruwan kanta tas........ni ba uwarsa bace matsalata dan bata gabana.kin San Meye matsalar noory?"malaak ta fada muryarta na dan shaking har yanzu sunan Queen
yaki gogewa a idanunta da tagani acikin wayar mu'azzam din.babban fargabata
a duniya wannan ya'r aikin ta gidansu mu'azzam anan ta shiga bata labarin Ayusherh ta karasa da fadin "saboda tana da sunan miss Ayshaa marafa shine ake
kiranta da wata Queen.sunan nan bakaramin tafasa mun zuciya yake ba
koni mu'azzam bai taba kirana da Queen ba.ta karasa maganar sounding so very jealous a muryarta.a rikice noor ke
fadin."to ke wane matakin kika dauka?
baki nuna masa bakyaso ba,a fusace
malaak din ke fadin"sau nawa nake
nuna masa bana so Yana nuna mun bakomai bane wallahi tallahi na tsanin sunan nan na Ayshaa Kuma duka saboda shegiyar uwarsa ake cemata queen saboda a girmama sunan.ni tsorona
Kar tayi masa asiri ta fara xuba masa
abinci ya fara sonta.kin San Yan aiki
na hakanan.......shiru malaak din tayi
tana dan juya maganar noor din aranta
gefen zuciyarta har ta fara yadda ko asiri din Ayusherh din tayiwa mu'azzam yake kulata?"da sauri wata zuciyar ta kwabeta
tana fadin Karya ne dan ita bata cika
yadda da asiri ba kwata kwata musamman akan maleeka da mijinta.sai idan bai tashi rashin mutuncinsa ba har dukanta yake
idan abun ya motsa.malaak ta tashi
tana cire kayan jikin Kai tsaye bathroom ta nufa dan yin wani wanka....koda ta fito noor ta fitar mata da kayan bacci masu kyau da laushi sabbi dal.sakawa tayi
ta fesa turaren noor din ta koma kan bed....Sai lokacin ta samu natsuwar turawa maleeka text akan tana gidansu noor
Sai gobe Xata dawo.ta kira wayar
mu'azzam har sau biyu bai daga ba
da haka ta kunna chart ta fara chart
Sai wuraren 11 yayi mata magana.
kafin ya Kirata vidcall Suna hira
Yana famar rufe ido nan take fuskarsa
ta nuna gajiya da Kuma baccin da yakeji
dole malaak tace ya sauka yayi baccinsa....
#######
washegari Sai wuraren 12 suka tashi
wanka kawai sukayi aka kawo masu breakfast dinsu har karamin falon noor,anan sukayi breakfast zuwa 2 suka fice cikin motar noor din dan fara shirye shiryen birthday party din noor din
Sai da yamma suka dawo.ana gama magrib noor ta mayarda malaak din gidan maleeka da kanta.a Ranar Shima
mu'azzam ya koma Lagos ya cigaba da aikinsa kafin zuwa mami.tun daga ranar
ya zama busy itama malaak din busy
ta xama saboda shirye shiryen birthday party noor da sukeyi kullum cikin fita suke basa dawowa Sai yamma watarana ma malaak din gidansu noor take kwana.
daga ita har mu'azzam Sun zama busy
a rana bai wuce so daya suke yin
waya ba.akwai ranar da basa ma wayar.
Sai can tsakiyyar dare suyi chart.....
kwana biyu da komawarsa Lagos
Mami da Abba suka dira a garin Lagos
luxury mantion dinsu dake cikin
unguwar (Banana Island)suka sauka.
kwanan su mami biyu da sauka komai
ya gama Kammala suka shirya kayatacciyyar dinner acikin garin Lagos
dinner bude sabon estates din da aka
narka mahaukatan kudi idan bakada billions kudi baxaka iya mallakar gidajenba,Sun gayyaci manyyan manyyan
Yan siyasa masu kudi ,Yan kasuwa
Wanda sukaci suka tada Kai da naira.
nan Yan jaridu suka fara aikinsu
suna watsa pics da daukar gidajen,
Wanda sunan mu'azzam ke a rubuce
inda aka saka.(the young millionaires the young business tycoon (Ibrahim Ibrahim marafa)the marafas empire)haka manyyan
manyyan bloggers suka rika dorawa a kowane platform na social media
cikin awa ishirin da hudu labarin mahaukan estate din da marafa yayi cikin wannan shekara ya zagaye koina.....
#######
tunda ta fito wanka daga ita sai towel
ta koma kan bed ta kwanta sa'anan ta kira mum dinta data Kirata bata daga ba tana toilet,tana dagawa Cike da farin ciki
mum ke fadin "congratulations Mrs marafa.murmushi mai sauti malaak din
ta saki har mum din na jiyo haka ta cikin
wayar.ashe dai har yanxu Ibrahim marafa
arzikinsa dada habaka yake kinga babu labarin dake tashi a social media a yanxu
irin waya'nnan estate din.wlhi har na Kara jin kwadayin hada zuria dasu.ke ko bayan
Raina malaak idan baki auri mu'azzam marafa ba banyafe maki ba.wata daria
malaak din ta saki tana fadin"mum please please."zan mafa auresa Kuma insha
allahu kina a raye zaayi aurenmu."cike da alfahari mum din ta rika sakamata albarka
kafin ta katse wayar.tayi dialling number
mu'azzam a Kashe yau tun safe take Kiransa a Kashe ake fadamata.
suma yau ake birthday party din noor,
tun ajiya suka tare hotel din da zaayi
party.noor ce ta shigo dakin sanye ciki
wata arniyyar gown ta material Wanda
akayiwa wani irin dinki da yabi jikinta
ya kama Sai make up din da akayi mata
a kallon farko da zakayi mata zakayi
tunanin ko ba ya'r musulmi bace saboda
yanayin shigar a gaban rigar anyi wata tsaguya tun daga rabin cinyarta har kasa
Sai dogon gashinta da yasha gyara
aka kama mata shi da band.tayi wani irin sanyayen kyau.....malaak kina duba time kuwa,da sauri malaak ta sauka daga kan bed din.sorry my girl friend Ina mai make up din??"tana a falo please kice ta karaso
anan ciki tayi mun,bazai daukemu
lokaci ba I promise simple make up
zatayi mun.juyawa noor din tayi tabar dakin.kamar yadda malaak din tace
cikin kankanin lokaci akayi mata simple make up ta saka itama rigarta da ta kasance black shigen ta noor din
itama wani sanyayen kyau tayi,
Kai tsaye wurin da akayiwa wani irin decorations suka nufa babban falone
da babu kowace irin hayaniya acikinsa
Sai cool music da aka saki.duka duka
mata su 6 ne haka maxan da bazasu wuce Suma 6 ba duka ya'yan manyya ne
da naira ta gama jikasu da wani irin
class tattare da yanayinsu,a hankali
noor ta tsaya kusa ga Jeey shi din
saurayintane Wanda ya kasance dandan
ministern kudi maici a yanxu,
Jameel sarkii.sai sauran friends dinsa maza mutum 5 itama friends dinta
mata mutum 5 ga drinks nan an jera
Kala Kala hakama shishiiiiii.bayan malaak ta gama gaisawa da mutanen wurin
gefe ta koma ta zauna tana son Kara gwada Kiran mu'azzam har lokacin
a Kashe haka Kuma baya online,
duk Sai taji ranta ya Kara baci.
tana son yaga kwaliyyarta ko yayane
A hankali ta dauki shissha wacce aka gama hadawa,Cike da kwarewa ta fara ja
tana wani lumshe idonta.tamkar
a mafarki taji ance Hiiii!!!"tun kafin ta dago taga ko wanene tuni kamshin turarensa
yagama cikata dagowa tayi idonta
cikin nasa black beauty chaculate ne
dogone sosai Yana da wasu irin
idanu masu daukar hankali Sai dai ko kusa bai kamo mu'azzam dinta a komai da komai ba.Hii din ta mayar masa tana dauke kanta,ga mamakinta Sai taga yaja kujera ya zauna gafdaita Shima
daukar shishir yayi Yana ja Cike da wani
irin kwarewa......cikakken sunansa
ya fadamata sunan sa saleem Talba
atakaice ta amsa masa da malaak.
gyada Kai yayi Yana fadamata sunanta
yayi masa.dan juya ido tayi batareda
ta furta kalma ko daya ba juya idon
nan da tayi masa bakaramin tafiyar
dashi yayi ba.tayi masa ta kowane
bangare Yana son macce mai class,
Dan hira yake janta dashi haka
Yana fadamata idan babu damuwa
Zasu iya zama friends?"jin only friends
yasa xuciyar malaak din ta amince
dashi dan sanin mu'azzam marafa kawai ne a zuciyarta.bayan an yanka cake
aka saki cool music noor da Jeey aka baiwa fili ya rikata Yana rawa daita ajikinsa
kafin sauran friends din su shigo
a hankali saleem ya mikawa malaak hannu.dan Jim tayi tana kallonsa,
suna hada ido da noor ta wani marairace
mata.babu yadda malaak din ta iya dan ta saka noor din farin ciki ta basa right hannata ya kama ya jawota cikin
filin rawa ya rike dayan hannunta
dayan hannunn nasa ya zagaye kugunta
dashi suka fara wata irin rawa mai daukar
hankali tamkar daman can din su
masoyane,rabon malaak da irin wannan
rawar tun Suna America itama cikin
nishadi ta sake.har saleem din Yana mamakin kwarewarta wurin rawa,
wani irin juyata yake ajikinsa
Yana yimata wani irin kallon ..........tuni masu daukar hoto suka fara dauka
basu suka gama party ba Sai kusan 2
anci an sha anyi nishadi.a gajiye malaak
tabar wurin zuwa room dinsu kanta
har juyawa yake hannu ta dora aka handling ya dora hannunsa akan nata.
#ASMY B ALIYU
#Love/Fate
#Hotlove
#Noor
#malaak
#Jeey sarki
#Saleem Talba
#Party
#Omrihayatii
#***