BA NI DA MADOGARA

Chapter 24

by @narrnarhhbukar00

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*











*Ba ni da Madogara*
  (Sai Allah...)




 

024

     
Su dai ƴan ɗaki da ido suke kallon ikon Allah, kowa ya mastu yaga yadda wasan zai kaya. 

"Babu wani abu da Talatu ta saka a cikin shayin, matar da ta yi shekera da shekaru tana musu girki a ce ta saka wani abu a cikin shayin Arqam, meyasa a da can bata saka ba sai yanzun". Cewar Hajiyan Sama. 

Wani daɗi Hujayrah ta ji a ranta tana cewa *'Da kyau an zo wurin'* Barin wurin  Talatu Hujayrah ta yi ta wuce inda  Hajiyan sama take zaune ta miƙa mata Mug ɗin shayin tana cewa

"Tunda kin yarda da mai aikin Hajiya, mai zai hana Kisha shayin" tana maganar tana miƙa mata Mug ɗin shayin. Hannu  Hajiyan Sama tasa za ta kaɓe Mug ɗin shayin sai Hujayrah ta yi saurin matsar da Mug ɗin gefe. A fusace Hajiyan Sama ta miƙe 
za ta kwashe Hujayrah da mari sai Hujayrah ta yi saurin riƙe hannunta da ɗayan hannun da babu komai tana cewa

"A'a Hajiyan sama ban yi miki laifi ba kar ki ce za ki taɓa lafiyar jikina,hakan da kika yi ya nuna tabbas abin da nake zargi akwai a cikin shayin, Kema karan kanki kin kasa sha balle kuma ita wacce ta yi aikin, sannan kar ki ce za ki mareni akan gaskiyata, idan da laifi na yi miki za ki iya hukuntani yadda kika so amma kisani, ba a hukuntani a yayin da ban yi laifi ba" saukar mata hannu ta yi ta juya wurin Alhaji da yake kallon Ikon Allah ya kasa cewa komai, don ganin abun yake kamar a film, kusa dashi ta matso sannan ta ce

"Abbu ka yi haƙuri da abin da na yi yanzu, ba wai na rainata ba ne a'a  sai dai bana bari a hukuntani akan gaskiya shiyasa."

Mug ɗin shayin ta  nuna masa da cewa

"Abbu kaga wannan shayin wallahi ko rantsuwa na yi bazan yi kaffara ba akwai guba a cikinsa, sannan gubar da ke ciki mai haɗarin gaske ne, zuciyata da idanuna suka yi min nuni da hakan" 

Dummmmmmm! Ƙirjin Hajiyan Sama ya bada, jin Hujayrah na faɗa wa Alhaji guba ce, to ya aka yi tasan akwai guba a cikin shayin? Kodai taga lokacin da Talatu take zuba gubar ne? Babu mai bata amsar waɗannan tambayoyin.Sai dai  dole a yanzu ta rikita komai kar a gano ita ce ta aikata wannan ɗanyan aikin ta shiga uku, domin tasan idan aka matsi Talatu dole ta faɗi wanda ya turota. Sai da ta gyara tsayuwanta da kyau sannan ta ɗora hannunta a saman kanta ta kwarma uban ihu tana nuna Hujayrah da cewa

"Wayyooooooo ni Izzatu na yi gamo!!! Wayyooooooo ni Izzatu naga mugun halitta!!! Hujayrah ba mutum bace!!! Wallahi ba mutum bace!!!! Wallahi Aljana ce!!!  Alhaji ka yarda dani wallahi ba mutum bace!! Mayyar ce!!! " ihu take tana kururuwa, jikinta na rawa kamar ɗan mazari, lokaci guda ta sulale a bisa carpet ɗin sumamma. Mamaki ne ya cika kowanne a ɗakin har da ita kanta Hujayrah, a ranta tana cewa ' Makira, ki gama suki-burutsunki za ki farfaɗo ne, muguwa azzuluma'  Da sauri Alhaji ya miƙe yana faɗin Subhanallahi, Hajiya Nafisa ma da sauri ta zo  kanta tana salati. Arqam, Nazima da Halima babu wanda ya motsa a cikinsu amma kowannansu abin ya yi matuƙar bashi mamaki. Shi gogan namu wayarsa ya buɗe tare da  kunna data sai ya shiga App ɗinsa, kai tsaya ya kalli sashen kitchen inda Talatu ta dafa masa ruwan zafi, da yake akwai CCTV camera a kowani lungu da saƙo na gidan, babu wanda yasan da CCTV camera a gidan daga Arqam, Alhaji sai Mas'ud da Mahmoud. Ko Hajiya momma bata san akwai CCTV camera a gidan ba. Arqam ya yi amfani da micro CCTV camera wacce duk saka idonka ba zaka taɓa fahimtar akwai CCTV camera a gidan ba, don ƴar ƙarama ce sosai wanda mutane ba zasu fahimci wanzuwanta a gidan ba. Hujayrah  bata miƙe daga duƙyen da take ba tana kallon Hajiyan Sama da Hajiya Nafisa ke faman yayyafa mata ruwan sanyi  a duk ilahirin jikin hankalinta a tashe. Talatu na tsaye ƙiƙam  ta kasa sukuni sai waige-waige take tana neman hanyar da za ta sulale da tabar ɗakin, wanda daga nan za ta tattare ƴan komatsanta ta bar gidan don tasan yau dai sai Allah. Babban farin cikinta bai wuce maƙudan kuɗin da Hajiyan Sama ta danƙa mata don ta ji daɗin aikin sosai. Suna a wannan yanayin Arqam ya ɗago da sauri yana cewa

"Abba zo kaga Ikon Allah" 

Barin inda Hajiyan Sama take ya yi sai ya zo wurin Arqam. Ba tare da ɓata lokaci ba Arqam ya nuna masa abin da CCTV camera ta hasko a kitchen a lokacin da Talatu ke dafa masa ruwan zafi. Sosai gaban Alhaji ya buga ganin Talatu na zuba wani ruwa a cikin tukunyar da ruwan zafin ke ciki tana waige-waige kamar wata mara gaskiya. 

"Nafisa zo kiga abin mamaki, kai kowa ma ya zo ya gani" 

Da sauri Halima da Nazima suka je inda Arqam yake suna kallon abin da ce cikin wayan. Lokaci guda suka fara salati haɗi da sallalami, Hajiya Nafisa cike da tsantsan tashin hankali ta ce 

"Innalillahi Wa'innan ilaihi Raji'un!! Ni Nafisatu me zan gani haka" 

Ɗan buɗe ido Hajiyan Sama ta yi kaɗan gabanta na mugun bugawa, don tasan yau sai Allah. Karaf! Suka haɗa ido da Hujayrah daidai lokacin ta ɗago za ta kalli inda su Alhaji suke. Da sauri ta rufe idanunta gabanta na sake bugawa. Wani killing smile na gefan baki Hujayrah ta yi har dumple ɗinta ɗaya yana lotsawa.Ganin hankalin kowa na wurin Arqam sai Talatu  ta ruga a guje tana shirin barin ɗakin sai Hujayrah ta yi saurin kamota lokaci guda ta zube mata yatsunta guda biyar a fuska tana cewa

"Za ki gudu ne munafuka! a tunaninki Kinci ɓagas ko?" 

Jawota ta yi har tsakiyar ɗakin tare da wurgar da ita kamar kayan wanki. Hajiyan sama na jin duk dramar da ake a cikin ɗakin daman suman ƙarya ta yi don ƴan ɗakin su yarda da ita akan Hujayrah aljana ce ba mutum bace. Hankalin ƴan ɗakin sai ya koma kan Talatu wacce yanzu ta fashe da matsanancin kuka tana roƙon a yafe mata sharrin shaiɗan ne. sauke mata wasu zafafan maruka Hajiya Nafisa ta yi cike da ɓacin rai ta ce

"Ke har kina da bakin a yafe miki sharrin shaidan ne algunguma!? Wato duk wani kashi idan an tashi yayyaɓawa sai a yayyaɓawa shaiɗan saboda shi ne Ogan naku koh! A yau za ki bar mana gida shegiya muguwa! Baki yi tunanin halin da mahaifiyarsa take ciki ba kike son hallakar dashi ko " 

" Waya turoki? " cewar Arqam da kakkausar murya. Tuni Hajiyan Sama da sandare tana kakkafe idanu miyau na dalala daga bakinta. Kowa kanta ya yi hankali tashe. Hujayrah dai kallon ta take tana taɓe baki. Shi kuma Arqam ko kallon inda take bai yi ba, don yasan ita ce ta turo Talatu. Abin da Hajiyan Sama bata sani ba, ko'ina na part ɗinta Arqam ya saka an baza CCTV camera, duk abin da take ƙullawa yana sane. Kasancewar ya kwana biyu bai kalli abin da ke faruwa ba hankalinsa na akan lafiya Hajiya momma, shi yasa bai san da gubar  ba. Cicciɓarta Alhaji ya yi sai Nazima da Halima suka taimaka masa zuwa saman kujera. Kamar almara Hajiyan sama ta saki wata razatanniyar ƙara tana buɗe ido lokaci guda. Da sauri ta miƙe tana nuna Hujayrah tana cewa

"Ita ce! Wallahi Ita ce Aljanar! Ta zo ɗaukar fansa Alhaji"  sai wurqurga idanu take tana nuna Hujayrah. 

Rai ɓace Alhaji ya ce

"Waya faɗa miki Hujayrah aljana ce? Mutum ce kamar kowa sai dai Allah ya bata baiwa wacce ba kowa yake da irin ta ta baiwar ba, kar ki sake cewa Hujayrah aljana ce don baki ga kofato a ƙafarta ba. Yanzu ki koma part ɗinki ki kwanta, kina buƙatar hutu , muna nan sai Talatu da sanar mana da wanda ya aikota sakawa Arqam guba a cikin ruwa zafi don ya mutu "

" Alhaji zan zauna a nan ba sai na koma part ɗina ba, na ji sauƙi Alhaji" cewar Hajiyan Sama tana sharce zufar da ke kwaranyo mata a goshi. Girgiza mata kai Alhaji  ya yi yana cewa

"Hutu kike buƙata ba tashin hankali ba, bana son musu tashi ki koma part ɗinki" 


Kamar ta kwarma ihu haka Hajiyan sama take ji sai faman tmcije lips take da ƙarfi. Gwiwa a saɓule tabar falon zuwa part ɗinta, kai tsaye ta haura sama zuwa falonta na can ta zube a ƙasa tana kwarma uban ihu tana bubbuga kanta kamar wata motsattsa.Can kuma ta miƙe ta ɗauko wayarta daga saman centre table hannunta na rawa ta kira Hajiya Zinatu. Hajiya Zinatu da ke baccin safe hankalinta kwance ta ɗauki kiran tare da kara wayar a kunna, da sauri koma zaune ƙirjinta na bugawa jin Hajiyan sama na kuka ta ce 

"Aminiya meke faruwa?" 

Sai daHajiyan sama ta fyace majina sannan ta fara magana cikin muryar kuka ta ce

"Aminiya shikenan tawa ta ƙare, dubuna ta cika" 

Ras! Ƙirjin Hajiya Zinatu ya bada, hankali tashe ta ce

"Yi min bayani yadda zan fahimceki Aminiya, meya faru ne?" 

Miƙewa Hajiyan Sama ta yi zuwa bedroom ɗinta wayar na kunnanta tana shassheƙar kuka, sai da ta zauna a saman gado sannan ta fara ba wa Hajiya Zinatu labari tunda farko bata ɓoye mata komai. Sosai Hajiya Zinatu ta kiɗime tana dafe ƙirji tana cewa

" Wayyo ni Zinatu yanzu ya zamu yi Aminiya, kinga a wurina Nafisa taci abincin, don Prof na ba kular ya kai mata. To amma abin mamaki taya ita yarinyar tasan akwai guba a cikin abincin, ko dai taga lokacin da mai aikin ke zuba gubar ne?" 


"Taya zan sani Aminiya, komai ya jagulemin na gaza samun abin yi, wannan shaiɗaniyar yarinyar ta hanani cika burina. Wallahi yanzun tsoron yarinyar nake saboda shu'umancinta ya wuce na gaban kwatance, Gata bata da tsoro kai tsaye take maganarta son ranta" cewar Hajiyan Sama tana Share ƙwallar baƙin ciki da takaici. 

"Ni yanzu abin da ban gane ba Aminiya, yarinyar ta faɗi ke kika saka mai aikin ne?" 

"A'a amma dai nasan idan suka matsa wa mai aikin dole ta faɗi ni na sakata aikin" cewar Hajiyan sama. 

Sauke wata ɓiyayyar ajiyar zuciya Hajiya Zinatu ta yi sannan ta ce

"Ki kwantar da hankalinki Aminiya, ba za mu taɓa jin kunya ba, ba dai kin nuna musu cewa yarinyar aljana ce ba,ki tafi a hakan akan yarinyar aljana ce, zuwa gobe sai mu san abin yi kin ji" 


"Shikenan hakan zan yi komai za su ce sai dai su ce amma bazan taɓa canja maganata ba akan Hujayrah aljana ce, yanzu zuwa gobe za mu haɗu  a gidan Hajiya Badiyya wacce ta bamu gubar, nasan za ta bamu shawara mai kyau ta yadda za mu yi maganin yarinyar " cewar Hajiyan sama. 

"Sai mun haɗu goben, yanzu zuwa anjima da yamma sai ki leƙa part ɗin Hajiya momma ki dubata sannan ki cire tsoro a ranki, kar ki bari su ga wata alamar rashin gaskiya a tattare da ke. Zuwa goben sai mu haɗu" 

Daga haka suka ɗan taɓa hira har hankalin Hajiyan Sama ya fara kwanciya daga bisani suka yanke kiran. 

A can part ɗin Hajiya momma bayan fitar Hajiyan sama sai kowa hankalinsa ya dawo kan Talata wacce take ɗirzar kuka har da majina. Alhaji ya dubi Talatu a kausashe ya ce

"Waya turoki!" cewar Alhaji a wannan karon. 

Wani Sabon kuka Talatu ta saki hannunta bibbiyu tana roƙon Alhaji ya yafe mata. Cikin daka tsawa Hajiya Nafisa ta ce

"Ba da ke muke ba ne annamimiya! Waya turoki aka ce! Ko kurma ce ke tsinanniyaaa!" 


"Aunty just let her go I know who send her, zan ɗauki mummunan mataki akan wanda ya turota" cewar Arqam domin wani tunani ya yi, ba yanzu ya dace su san Hajiyan sama ce ta aiko ba, idan halinta ne yasan definitely za ta sake kawo wani harin, shi kuma a lokacin zai tuna mata maganar Hausawa da suke cewa *kifi na ganinka mai jar koma* fatansa Ammiensa ta samu sauƙi daga baya yasan matakin da ya dace ya ɗauka akanta. Alhaji ya so ƙin yarda, shi ma mai ya gani sai kawai ya ce tabar gidan yanzu-yanzu. Jiki na rawa Talatu ta miƙe daga zaunan da take ta yi hanyar waje. Cikin hanzari Hujayrah ta ce

"Ina kika birne asirin da aka aike ki?" 
Rantsuwa Talatu ta fara yi tana cewa 

"Wallahi tallahi ba a bani  asiri na birne ba, ki yarda dani na rantse miki da Allah da Annabi" 

"Dallah yi min shiru makira, za ki iya tafiya, munafukar banza munafukar yofi, a dai canja hali domin rayuwa ta inganta" cewar Hujayrah tana taɓe baki a ranta tana faɗin duk inda aka birne asirin sai ta tonoshi ta karya. 

"Yaya ni al'amarin Hajiyan sama tsoro yake bani, kodai ta yi gamo ne?" cewar Hajiya Nafisa. 

"Waya sanin mata Nafisa, abin da na lura akanta bata ƙaunar Hujayrah, from initial bata so Mubina ta riƙeta ba. Taso na koreta wai  bata yarda da ita ba" cewar Alhaji. 

"Gashi ta hanyarta Allah ya ƙaddara wasu abubuwa da dama da aka ƙulle sun kwance, ai Hujayrah alkhairi ce a gidan nan. Ta gama ƙaryan Aljanunta babu inda Hujayrah za ta je. Idan ma kunce ba za ku zauna da ita, ni zan ɗauketa ta koma gidana da zama" cewar Hajiya Nafisa tana murmushi. 

"A'a Aunty Nafisa baza ma a yi haka ba, we too want her existance here" cewar Arqam tsakaninsa da Allah. 

Sakin baki Hajiya Nafisa ta yi sai can kuma ta yi murmushi. 

"Mu duba Mubina  mu ga ya jikin nata,daga nan kowa ya kama gabansa don bata son hayaniya" cewar Alhaji. 

Miƙewa ƴan ɗakin suka yi zuwa bedroom ɗin Hajiya momma, sun sameta tana bacci, da alama baccin yana mata daɗi, juyowa suka yi. Hajiya Nafisa da yaranta suka nufi gidan Alhaji Sambo Dala. Arqam yakoma ɗakinsa sai Alhaji ya nufi kamfaninsa. Hujayrah aka bari a falo tana kallo kasancewar Razina ta tafi skul ... ✍️

            🌎🌎🌎🌎🌎🌎 

*New G.R.A. Bauchi state Nijeriya*

A ɓangaren Hajiya Ramla sai bayan magrib ta koma gida ita da Tahseen, bata sanar wa Tahseen abin da ke faruwa na rashin lafiyar Hajiya momma ba domin tasan halin kayanta, lokaci ɗaya za ta tashi balli. Bayan su ci abincin dare har da Senata, sai Tahseen ta wuce ɗakinta. Su kuma suka tafi nasu ɗakin. Kwance suke a makekyen gado su na alfarma, kowanne ya kasa bacci yana nashi Karatun zucin. Sun daɗe a haka sai can Hajiyan Ramla ta katse shirun da cewa

"Daddyn princess" ta yi maganar cikin taushin murya. 

Juyowa ya yi yana kallonta ba tare da ya ce komai, bata damu da shirunsa ba ta ci gaba da cewa 

"Wata muhimmiyar magana nake so mu yi" 

"OK ina sauraronki mummyn Tahseen" cewar Senata yana miƙewa daga kwancen. Ita ma tasowa ta yi daga kwancen fuskarta ɗauke da murmushi. Duk da dim light ne a ɗakin still suna iya kallon junansu. Gyara zama ta yi sannan ta ce

"Daddyn princess Ina wannan yarinyar nan da nace maka ta lalata mana aiki akan matar yayana Hajiya momma, to yanzu tana shirin lalata  auran Tahseen da Arqam " 

Da sauri ya ɗago yana kallonta tare da cewa

"Againnn!!! I thought sai bayan biki nace za a yi kidnapping ɗinta, Sai Princess ta Rama wulaƙancin da ta yi mata a public" 

"Hmmmm ai wasan ya canja salo Daddyn Tahseen,Hajiya Izzatu uwar gidan Yaya Imran nake tunanin ta yi wa Hajiya momma asirin ƙuraje wanda bansan wace manufa take da shi akanta ba. Kasan biki ya matso so a ranar da Sabrin za ta rasu na shirya na je gidan Yaya Imran mu tattauna da Hajiya momma na yadda bikin zai kasance. Muna zauna da ita har da Nafisa da yaranta, can ta ce za ta shiga bayi. Ko mintuna goma na a yi ba muka ji ihunta wanda hakan ya yi daidai da da shigowan Yaya Imran da dasu Arqam. I was shocked ganin Hajiya momma halittarta kamar an sauyata, every single part of her body akwai ƙurji baƙi, her body looks very scary babu kyawun gani. Yaya called a doctor Bayan ya yi gwaje-gwaje ya ce aikin yafi ƙarfinsa, Yaya was trying to reach his doctor Wanda Yake abroad Sai wannan shaiɗaniyar yarinyar ta shigo ita da autar Hajiya momma. That gurl was so courage and confidence, buɗar bakinta Wai asiri ne and asirin ma guda biyu ne kuma mutane biyu suka yi asirin sannan kowa da nasa nufin akan Hajiya momma. "

Waro ido Senata ya yi yana kallon matarsa, cike da tsantsan mamaki ya ce

"Who is this girl!!! I will like to see her naga how courage she is in front of me, dole mu yi kidnapping ɗinta before the marriage "

" Nima that's what I'm thinking, tsorona kar ta karya asirin da na yi wa Hajiya momma komai ya lalace" cewar Hajiya Ramla. 

"Dole mu jira matar yayanki ta samu lafiya because she is in charge of her treatment, Kinga Idan suka nemi yarinyar suka rasa There will be problem amma idan bayan matar yayanki ta samu sauƙi sai mu san yadda za mu yi kidnapping ɗinta cikin sauƙi" 

"Shikenan bari na haƙuri zuwa nan gaba, before na so mu aiwatar da ƙudirinmu a kanta amma tunda kace sai Hajiya momma ta samu lafiya fine" cewar Hajiya Ramla rai bai so ba. 

"Hakan shi yafi dacewa Ramla, we just have to be very conscious Saboda zargi" cewar Senata yana gyara kwanciyarsa. Ita ma kwanciyar ta yi amma bacci yaƙi zuwa. Kamar yadda suka kasa bacci a can ɓangaren Tahseen masha'arta take aikatawa ta hanyar kallon film ɗin batsa tana yin yadda ƴan cikin film ɗin suke.Tahseen ba ita ta samu natsuwa ba sai wurin ukun dare duk tana abu ɗaya. Babu tsarki tagyara kwanciyarta bayan ta kashe kallon ta kwanta bacci... ✍️

*TUNATARWA*

"Ƴan uwana iyaye mata mu saka ido a duk kai kawon da yaranmu suke yi, shin su waye abokansu, me suke yi da wayoyinsu, Ina suke zuwa. Idan mace ce wace kalar ƙawa yarinyarki take mu'amala da ita, shin yarinyar kirki ce ko kuwa bata da hali, dawa take magana a waya, su waye samarinta, Ina take samun kuɗi, su wa suke bata kuɗin. Duk waɗannan abubuwan dana lissafo dole uwar ƙwarai ta yawaita bincikensu domin yaro ka haife sa ne amma baka haifa halinsa ba, kina nan kina yi wa ƴarki tarbiyya wasu na can a waje suna lalata miki tarbiyyarta, dole mu saka idanu sosai akan yaranmu musamman mata saboda anfi saurin dulmuyar dasu akan yara maza. Allah kasa mu dace yasa a amfana da abin da aka karanta a ciki*



         🌎🌎🌎🌎🌎🌎

A ɓangaren Alhaji Sambo dala sabbin yara ya samo don su taimaka mishi wurin neman Hujayrah, domin yafi so kamar yadda shi ya nemota a farko haka yake so ya kasance shi zai sake nemanta a ƙarshe ya kaita ƙungiya. Duk da yana cikin jimamin rasuwar ɗiyarsa Sabrin amma haka ya nufi secret house ɗinsa wanda ya taɓa kai Hujayrah ta gudu. Kasancewar tun kafin ya je ya sanar wa yaransa yana hanya. Ƙwansu da ƙwarƙwatansu sun hallara suna jiran zuwansa. Ba a fi mintuna talatin ba ya shigo cikin gidan. Bayan ya yi parking sai ya fito zuwa inda yaran suke har da tsoffin yaransa, yawancinsu duk sun hallara har da Habib abokin Mas'ud. Yanzu abotar tasu ta yi ƙarfi sosai, duk da Habib bai san manufar Mas'ud ba haka yake kwance masa zare da abawa akan abin da Alhaji Sambo dala da mutanan ƙungiyarsu suke shirin aikatawa. 

Cike da girmamawa suke gaishesa, ɗaga musu hannu ya yi sannan ya tsaya a daidai inda kowa zai gansa. Yana sanye cikin ɗanyar shadda mai kalar sararin samaniya, ya saka baƙin tabarau saboda kar a gane yanayinsa. Gyara tsayuwa ya yi sannan ya fara da cewa 

"Na taraku ne a nan ba don komai ba sai don wani muhimmin aiki mai girman gaske, sannan idan kuka tsaya kai da fata kuka yi aiki tuƙuru to ina mai tabbatar muku za ku samu kuɗi kamar ɓar nan iska, aikin akwai sauƙi sannan akwai wuya. Wuyansa shi ne neman inda yarinyar take sai sauƙinsa kawota nan gidan. Duk wanda ya yi nasarar kawo yarinyar nan gidan, to ya saka a ransa shi da talauci sun yi hannun riga, domin zan jiƙasa da maƙudan kudi wanda har ya kammala rayuwarsa yana ci" 

Ihu da shewa yaran suka shiga yi, musamman sabbin yaran a tunaninsu aikin mai sauƙi ne. Tsofoffin yara irinsu Habib, Black scorpion squad Kasancewar yau Har da su a ciki, sun san aikin ba ƙaramin wahala garesa ba. Sai da ya ɗan nisa bayan kowa ya yi shiru sannan ya ci gaba da cewa 

"Yarinyar bata da wuyan kwatance domin suffarta a bayyane take, ɗaya ce tamkar dubu, ko ta tsaya cikin dubban mutane bazata yi wuyar ganewa ba. Yarinyar baƙa ce tana da koren idanu manya masu ɗaukar hankali, da wannan kaɗai ya isa bayani, Ina so ku shiga lungu da saƙo na garin nan da ma kewayansa, idan da hali za ku iya aiki da mata Fine, sai ku nema, ƙila tana cikin gidan mata sannan mata ne kawai za su iya shiga gidaje nemanta. Don haka na baku daga yau zuwa sati biyu ku jajirce wurin nemanta. Za ku iya tafiya" 

Yana gama maganar ya miƙawa Nasir briefcase Wanda ke ɗauke da kuɗi ya ce ya rabawa yaran. Motarsa ya tada  ya bar gidan...✍️

            🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Legacy Housing Estate, Bulunkutu, Maiduguri, Borno State. Nijeriya* 

Zaune yake tare da ƴan biyunsa  masu ƙusumbi yana musu wasa,sosai yake jin yaran a cikin ransa. Mahaifiyarsu na saman kujera tana latsa wayarta tana murmushi. Yana tsaka da yi musu wasa ya ji wayarsa na ringing. Sai da ta kusan tsinkewa sannan ya ɗauki kiran tare da karawa a kunne. Daga can aka ce


"Boss bamu samu yaron a gidan ba, mai gadin ya ce ya yi tafiya" 

Ɗan jimm ya yi kamar ba zai ce komai Still wayar na kunnansa,sai  can kuma ya ce

"Ku saka ido a Layin, Ina so duk mai yiwuwa ku kawosa wurina, kar ku ɗauki lokaci mai tsawo" cewar Sheikh Munnir. 

A can aka ce

"Angama Boss" 

Kit! Ya yanke kiran tare da duban matarsa wacce ita ma shi ɗin take kallo. Sauke ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce 

"Basu sai Abdul a gida ba" 

Taɓe baki ta yi sannan ta ce

"Waya sani ya je ɓoye Halima ne inda baza ka ganta ba" 

"Ashe ko da ya jawo wa kansa bala'i, Ina nan Ina jiran mahaifan nasa, duk abin da za su yi sai dai su yi don na riga da na bada auran Halima, don haka bazan canja maganata ba" cewar Sheikh Munnir yana miƙewa. 

"Suma dai akwai iyayin tsiya, uba da ƴarsa ina ruwansu da dolen-dole sai ta auri wanda take so,naga sauran yaran naka suma haka ka yi musu aure, suka haƙura suka zauna tare da majazensu, har Allah ya basu haihuwa" 

"Barta dukan da na yi mata ne bai isheta ba, za mu haɗu" cewar Sheikh Munnir yana lanƙwasa yatsun hannnayansa suna bada sautin ƙas! Ƙas! 

"Kun yi waya na Daddy kuwa Ya Sheikh?" cewar Mum. Kusa da ita ya dawo ya zauna sannan ya ce

"Eh, ɗazu da safe, ya ce min nan da kwana uku zai dawo Nijeriya baki ɗaya" 

Murmushi ta yi wanda yake ɓoye shekarunta a fili ta ce

"Haka Nima ya faɗa min, Allah ya dawo dashi lafiya" 

Bai amsa mata ba ya sake miƙewa ya haura sama, kai tsaye part ɗinsa ya nufa, yana shiga ya murza zobensa, lokaci guda ya ɓace ɓat!... ✍️

        🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Dajin ƙare kukanka*

A tsakiyar katafaran gidan da ke cikin dajin Sheikh Munnir ya bayyana kamar diran mikiya. Bayyanarsa da wasu mintuna su Baddoo da wasu sabbin yara suka fito daga cikin gidan kusan su talatin. Suna isowa wurinsa suka ƙame kamar sojoji, sun yi shigar suit baƙi da baƙin tabarau. Ɗaya bayan ɗaya yake kallansu daga bisani ya yi gyaran murya ya ce

"Dalilin da yasa na taraku a nan sai domin wani sabon aiki daya riskeni mai girman gaske, wanda nake so ku maida hankulanku sosai wurin ganin kun yi nasara a aikin" 

Jinjina masa kai su ka yi sannan ya ci gaba da cewa

"Akwai wata yarinya da ƙungiyarmu take nema ruwa ijallo, kwanakin baya Linkaku (Alhaji Sambo Dala) ya yi nasarar ɗaukota, sai dai ta gudu kafin ya yi yunƙurin kawota babbar ƙungiya. Yarinyar tafita daban da sauran mata, domin ko a cikin ɗaruruwan mutane take za ku iya ganeta. Abin da yasa ta bambanta da sauran mutane ba komai ba ne illa ƙwaryar idanunta, madadin kamar kowa a sameta da baƙin ƙwayar ido, sai nata ya kasance kore ne sharr! , don haka duk inda kuka da yarinya mai koren idanu to ku tabbata kun ɗaukota zuwa nan gidan ko kuma nan take ku nasar min. Duk wanda ya yi nasarar nemota to tabbas zan bashi kuɗi mai yawan gaske. Sannan kar wanda ya kuskura ya taɓata domin hakan ba ƙaramin matsala ba ne. Ina so a yau ɗin nan ku kama hanyar zuwa Bauchi State inda yarinyar da gudu. Mutane biyar kawai nake so su zauna a gidan nan. Baddo"

Cike da girmamawa Baddoo ya amsa da

"Yes mai girma Demon king" 

"Kai za ka yi jagorancin tafiyar nan sannan idan kun isa Bauchi ku rarrabu, ku saka idanunku sosai bana son a ɗauki lokaci mai tsawo, Ina so zuwa nan da sati ɗaya zuwa biyu ku nemota" cewar sheikh Munnir. 

"Angama Demon King, a yau za mu ɗauki hanya" cewar Baddoo yana sake ƙamewa. (Hmmmm sai ka ce a gidan soja wannan ƙamewa haka, ko commander Sai haka 🤭🤭🤭). 


Daga haka suka koma cikin gidan  shima ya  shiga ciki zuwa inda ake ajiyar yaran. Kamar kodayaushe wasu surkulle ya yi a tsakiyar ɗakin inda yaran suke suna baccinsu kasancewar an basu abinci wanda yake ɗauke da maganin bacci. Yana gama surkulle ya murza zobensa lokaci guda suka ɓace ɓat! Basu bayyana a ko'ina ba sai a babbar ƙungiya wacce take a saman ruwa...✍️

         🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Ƴan Majalisu, Unguwan Dosa, Kaduna state. Nijeriya*

A ɓangaren Abdul washe gari da safe ya yi sammakon zuwa gidansa shi da ƙanwarsa ɗaukar kayan da suke buƙata har da nashi kayan don zai kwana biyu bai dawo gidan ba, bayan haka yana so ya ga mai gadinsa don ya tuntubi lafiyarsa, kwana ya yi yana addu'ar Allah yasa basu taɓa mai gadinsa ba. Ɓadda kama ya yi ta hanyar saka nosemask da facing cap har da glass baƙi. Suna isa gate ɗin gidan ya yi parking motar a waje. Gabansa sai tsananta bugu yake yana fargaba tare da taraddurin abin da zai gani. Ƙanwarsa na biye dashi har suka isa inda gate ɗin yake. 

Ƙwanƙwasa ƙofar ya yi tare da jira, shiru ba a amsa ba, ya sake Ƙwanƙwasa ƙofar nan ma shiru, sosai ya karaya da tunanin ko sun kashe masa mai gadi ne. Ya kai hannu zai Ƙwanƙwasa ƙofar  ya ji mai gadi yana cewa

"Waye!" cikin sanyin murya ya yi maganar. 

Hamdala ya yi a ransa sannan ya ce

"Ni ne ɗan Asabe buɗe ƙofar" 

Da sauri mai gadi ya buɗa ƙofar tare da matsa musu suka shigo ciki, duk ya yi furu-furu dashi, kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da ba a cikin natsuwarsa yake ba. Suna shiga Abdul ya ce

"Ɗan Asabe fatan basu maka komai ba?" 

"Yallabai taya kasan an zo nemanka" 

Murmushi Abdul ya yi sannan ya ce

"A jiyan na dawo ɗaukar kayan haihuwa na muka manta sai na tarar da motoci kusan biyu a wajan gidana, mamaki ne ya cikani, wayata na ɗauko na duba CCTV camera a nan naga abin da ke faruwa. Juya kan motana na yi na bar Layin don ban san dame suka zo ba a tsakiyan daran " 

Sauke ajiyar zuciya Dan Asabe ya yi tare da cewa

" Ai yallabai Ubangiji ya so ka da rahama ba ɗan kaɗan ba, domin da waɗannan mutanan sun sameka a gidan nan bansan me zai faru ba"

"Sun faɗa maka wanda ya turo su ne" 

"Aa basu faɗamin komai ba" 

Ɗan shiru Abdul ya yi can kuma ya dubi ɗan Asabe ya ce

"Ɗan Asabe abin da za a yi yanzu shi ne, zan turama dubu dari ka koma garinku idan komai ya lafa zan kiraka ka dawo domin nima a yau zan ɗauki wasu muhimman kayana ni da na matana mu bar gidan. Kaga bai dace mu barka ba ƙila mutanan su sake dawowa" 

"Hakane yallabai godiya nake sosai da sosai, Allah ya saka da mafificin alkhairi ya Raya abin da aka haifa" cewar Ɗan Asabe fuskarsa shimfiɗe da farin ciki marar misaltuwa. 

Shiga cikin gidan su ka yi bayan Abdul ya yi wa ɗan Asabe transfer ɗin kuɗi, shima ya shiga ɗakinsa ya fara kwasar kayansa yana saka su cikin jaka. Sun daɗe suna kwasar kaya wanda suke buƙata kasancewar Hassana ta faɗa masa abubuwan da take buƙata ya ɗauko mata. Bayan sun kammala kwasar komai ɗan Asabe ya tayasu jidar kayan zuwa cikin booth. Sai Abdul ya kulle gidan ya koma cikin motar, ɗan Asabe ya zauna a gaban motar, sai ƙanwarsa a mazaunin baya suka bar Layin. Ko awa ɗaya cikakke basu yi ba wasu daga cikin yaran Sheikh Munnir suka sake zuwa gidan. Sun Ƙwanƙwasa ƙofar har sun gaji shiru babu amsa, haka nan suka koma cikin motar suka bar Layin. 


Sai da Abdul ya kai Ɗan Asabe har tasha sannan ya wuce gidan mahaifinshi ya sauke kayan, sai suka sake komawa asibitin lokacin har wasu daga cikin ƴan uwan Hassana da nasu ƴan uwan sun iso. Babu jimawa aka sallamesu ganin mai jegon bata jin ciwon komai. Kai tsaye suka dugunzuma zuwa gidan mahaifansa. Gidan babba ne sosai sannan akwai extra part wanda akwai kaya a ciki ba a amfani da part ɗin sai kawai suka sauka a can. Gobe suke saka ran dawowan Alhaji, momin Abdul ta kawo shawarar ya bari zuwa gobe idan mahaifinshi ya dawo sai asan abun yi da kuma maganar auran Halima. Daman saboda Alhaji baya Nijeriya shiyasa Prof bai zo maganar ba. Amma yana dawowa za su tunkaro Sheikh Munnir game da batun auran Halima... ✍️

         🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Kwanar Faru ƙwai, Kaduna state Nijeriya*

A ɓangaren Alhaji Zakari sosai ya yi farin ciki da shawarar da aminsa mai unguwa ya bashi, daga nan ya koma gida don faɗawa kakulle Hujayrah da mijinta sun yi tafiya, yana tafiya yake yana jin kansa a sama, ganin komai ya zo masa cikin ruwan sanyi ba tare da an ɗauki lokaci mai tsawo ba. Yana shiga gidan ya yi kaciɓis! Da Zaliha ta fito ita da yaranta za su fita. Kallo ɗaya ta yi masa ta kauda kanta tana jan siririn tsaki. Bai damu da tsakin da ta yi ba ya matso kusa da ita a lokacin tana niyyar fita daga ƙofar. Cikin sanyi murya ya ce

"Zalihatuwa sai inaaaa, ko ɗan tambaya ki yi baki yi ba, alhalin kinsan ba hanaki fita zan yi ba eh Zalihatuwata" 

Bata so amsa mishi tambayarsa ba, can kuma mai ta gani sai ta gyara tsayuwanta tana masa kallon ƙasa da sama cike da izza ta fara magana da cewa

"Sai na faɗa maka idan zan fita! Nifa na faɗa maka ka sakeni kawai shi ne zaman lafiyarka! Auran dole ne! Nace maka auran dole ne!!! Haba Don Allah ka rabu dani mana! Nace bana yi bana yi a'a dole ne auran, ka dawo ma uwar yaranka mana Mtssss!" 

Bata jira cewarsa ba ta ja hannun yaranta suka bar gidan. Kamar wanda aka dasa haka ya tsaya yana bin inda Zaliha ta wuce da kallo. Ya daɗe a haka sai can ya saki murmushi tare da shafa tumbinsa ya nufa cikin gidan. Duk maganganun da Zaliha ta yi babu wanda ya ɓata masa rai, hasalima wata wutar ƙaunarta ce take sake ruruwa a cikin zuciyarsa. Da sallama a bisa labɓansa ya shiga cikin ɗakin kakulle, lokacin har little Zakari ya yi bacci. Zaune ya sameta tana cin goro. Ɗagowa ta yi fuskarta ɗauke da mamaki ganinsa a wannan lokacin bayan ko awa biyu ba a yi ba ya bar ɗakinta. Zama ya yi a hankula kamar mai tsoran ƙwai ya fashe masa. Sun ɗan ɗauki wasu sakanni a haka babu wanda keda niyyar cewa komai. Ganin shirun ya yi yawa Alhaji Zakari ya buɗi baki ya ce


"Innayi daman na dawo na sanar miki akan batun Hujayrah ne" 

Ras! Gaban Kakulle ya bada, kallonsa take ba tare da ta ce komai ba ya ci gaba da cewa 

"Ɗazu dana na bar wurinki na kira shi mijin Hujayrah, ashe shekaran jiya suka bar ƙasar, sun tafi aikin Umra Saudiyya. Ya ce sai nan da wata ɗaya za su dawo. Da yake na sanar mishi akan kuna so ku zo ku ganta, ya ce karku samu damuwa shi da kansa zai turo driver ya ɗaukeku zuwa gidanta"

Ƙarashe maganar ya yi yana addu'a a ransa Allah yasa Kakulle ta yarda don idan taƙi yarda akwai matsala don shi bai san yadda zai yi ba. Kallonsa kakulle  take tana nazarinsa, can ta ce

"Allah ya nuna mana nan da wata ɗayan, ai rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, ba dai sai nan da wata ɗaya za su dawo Nijeriya ba, shikenan bama buƙatar wata motarsa, mu da kanmu za mu je" 

Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya Alhaji Zakari ya saki, yasan nan da wata ɗaya zai san abin da ya dace ya yi kar kowa ya sake tado da zancen Hujayrah har da iyayenta. Katse mishi tunani Kakulle ta yi da cewa

"Ɗazu bayan ka fita wani tunani ya zo min, me zai hana ka dawo da Uwar yaranka ɗan yaya?" 

"Innayi Naje can giwa a satin nan wurinta, na yi na yi da ita akan da dawo amma taƙi, ƴan uwanta ma haka sun so ta dawo amma taƙi, Ni yanzu bansan ya zan yi da ita ba" 

Taɓe baki kakulle ta yi sannan ta ce

"Ai duk kai ne da laifi tun farko, kai ga mai amarya ko sati ɗaya bata yi ma ka saki uwar yaranka kamar wanda aka yi wa asiri. Ai ga irinta nan ita wacce kake so kamar gwal ta ƙi ɗaukar yaronka sai ka ce ita ba yaran wani kake ciyarwa ba,Ni da kaina zanje giwa bikon Hannatu"


"Allah ya baki iko innayi" cewar Alhaji Zakari. 

"Ai ko baka roƙa ba Allah zai bani iko" tana maganar tana ɓallan goranta. Yasan haushinsa take ji, cikin sanyi murya ya ce

"Allah ya huci zuciyarka Inna" 

"Da ban huce ba za ka ganni a haka ne" 


Sum-sum ya miƙe ya yi mata sallama ya bar ɗakin. Kai tsaye ya wuce kasuwa abinsa hankalinsa kwance... ✍️

          🌎🌎🌎🌎🌎🌎

A ɓangaren Zaliha daman ta fito ne za ta wuce Ƙwarin ɗan dodo kai yaranta daga can ta ƙarasa ƙarshen gari wurin Malam Tani mai Allon ƙarfe don ya warware asirin  ya yi mata na mallakar Alhaji Zakari. Ganin Murja ba za ta taimaketa ba, gwara ta nemar wa kanta mafita tun kan wata matsalar ta sake ɓullowa. Mashin ta hau ita da yaran, kai tsaye ya wuce dasu Ƙwarin ɗan dodo daga can kuma ko tsayawa bata yi ba ta ƙarasa ƙarshen gari , ko mahaifiyarta bata faɗawa abin take shirin yi ba tsoron karta hanata ko kuma ta yi mata Allah ya ƙara. 

Kamar kodayaushe gidan maƙil yake da mata har ma yafi na sauran lokacin yawa don yanzu babu laifi Malam Tani mai allon ƙarfe ya ƙara shahara domin aikinsa yana yi sosai, sai dai idan mutum ya kuskure zai gane kuransa. Tsayawa kan layi ta yi har ya zo kanta. Shiga ta yi ta zauna inda masu neman taimako suke zama. Wannan karon Malam Tani mai allon ƙarfe ya juyawa ƙofa baya, sun daɗe a haka har tana tunanin ko ta yi masa magana ne sai can taga ya miƙe zumbur kamar wanda aka tsikara, juyowa ya yi yana kallonta fuskarsa babu yabo babu fallasa. Kallon ƙasa da sama yake mata kamar idanunsa za su faɗo. Can kuma ya sake zaunawa yana kallonta. 

"Muna sauraronki!!!" 

Tsinkar muryarsa ta ji a cikin kunnanta, firgigit ta dawo hankalinta, zama ta gyara sannan ta fara magana cike da sanyi murya mai nuni da karaya

"Malam Tani mai allon ƙarfe na zo gareka ne don ka warware asirin da ka yi wanda kasa na mallake mijina Zakari, Ina so kasa ya tsaneni, ya ji baya sona sannan ka saka ya sakeni" 

Tsura mata idanu ya yi ta wasu mintuna baya ko ƙyafta ido, can kuma ya bushe da wata iriyar mahaukaciyar dariya, babu daɗin ji balle sauraro, Zaliha dai idanunta a ƙasa gabanta na tsananta buguwa, gashi dariyar da yake bai da niyyar tsagaitawa, tsoro da firgici suka ɗarsu a zuciyarta lokaci guda har ta fara tunanin ko dai ya haukace ne ta gudu kar ya illata ta. Lokaci guda ya tsagaita da dariyar kamar ɗaukewar ruwan sama. Cikin wata iriyar murya mai matuƙar firgitarwa ya fara magana da cewa... ✍️





*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***