EP_________ 6️⃣
by @swrites22
🕊️ DESTINED MARRIAGE 🕊️
*HAUSA EDITION*
🕊️ QADDARARREN AURE🕊️
SWRITES
A-K-A
YOUNG WRITER✍🏻
Ina son sake jaddada cewa wannan labari ƙagagge ne, kuma ban rubuta shi da nufin cin zarafin wani ko wata ba. Idan kuma ya yi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata, to a sani arashi ne.
EP_________ 6️⃣
Sai da ta ajiye wayar, sannan Walida ta kalleta ta ce, "Faryal ni wallahi wani lokacin mamaki kike ba ni".
"Da na yi me?".
"Yadda kike mannewa mutumin da bai damu da ke kamar yadda kika damu da shi ba mana, ba kya ganin cewa kin fi karfin haka? Ke kyakkyawa ce, mai ilimi, kuma ƴar gidan mutunci. Babu wani abu da kika rasa, me zai sa ki tsaya da mutumin da bai san darajarki ba? Ki kalle mu, da me muka fiki, amma kiga yadda samari suke layi a kan mu, sai wanda muka zaɓa".
Faryal ta ɗan yi murmushi kafin ta ce, "Walida, Hamdan yana so na, kawai matsalarsa har yanzu kuruciya na dawainiya dashi, shi ya sa ku ka kasa fahimtar sa".
"Faryal zan faɗa miki gaskiya, mutumin da kike magana kan cewa yana fama da matsalar kuruciya, shi kike tunanin zai iya auren ki har ya kula da ke? Haba Faryal, ki yi tunani fa, ni shawara kawai nake ba ki".
Faryal ta ɗan sauke numfashi, ba tare da tace komai ba, Walida kuma ta cigaba. "Na san kina da masoya da yawa, sai dai kawai dan kin maƙalewa Hamdan ɗin ne shi ya sa ba kya basu dama. Yanzu kin ce Hamdan yana son ki ko?". Ta ɗan tsaya ta yi murmushi, sannan ta cigaba, "Ina so ki bawa wani dama. Idan har ba ki samu soyayya daga wurinsa fiye da ta Hamdan ba, to zan yarda da ke cewa yana son ki. Na san ki tun lokacin da kuka fara dating, amma har yanzu ban ga wani ci gaba a kan soyayyar taku ba, kullum jiya iyau kamar cin gorubar kuturu".
Zuciyar Faryal ce ta fara bugawa da ƙarfi a yayin da ta fara fahimtar gaskiyar maganganun Walida, saidai ta riga da ta shaqu da Hamdan. "Ni fa mace ce, zan iya canza shi, in mai da shi yadda nake so idan muka yi aure". Maganar zucin da take ta fito fili ba tare da ta sani ba.
"Faryal duk mutumin da baki iya canzawa ba kafin aure, to kuwa ba za ki taɓa iya canza shi ba bayan aure. Kun shafe shekaru biyar tare, da a ce za ki iya canza shi, to da yanzu ya canza".
Faryal ta ɗan yi shiru tana nazarin kalaman Walida.
Katse mata tunanin Walida tayi da faɗin, "Tun da kinzo, muje ki raka ni kasuwa, dama ina tunanin zuwa in yi yan tsince tsincen abubuwan da suka ƙare min". Faryal wadda maganganun Walida suka taɓa zuciyarta, ta miƙe a sanyaye tana faɗin, "Ni ma kuwa Maama ta bani aiken siyo mata wasu spices, amma muje na fara gaishe da Umma idan tana nan sai mu wuce".
"Eh, tana ɗakinta". Walida ta amsa tana ɗaukar mayafinta suka fice daga ɗakin zuwa ɗakin Umman su Walidar. Faryal ta gaisheta kafin Walida ta shaida mata zasu je kasuwa da Faryal, ta musu a dawo lpy, sannan suka fito.
Ko da suka hau hanya ma, labarin Abuja kawai Walida ke yi wa Faryal. Sun kwashe sama da awa ɗaya a kasuwar kafin su gama siyayyar ta su. Faryal ta maida Walidan gida sannan ta wuce nasu gidan.
Da yake lokacin har 4pm ta kawo kai, sallah kawai tayi ta ɗan huta zuwa lokacin girkin dare. Kamar yadda suka saba idan dukansu suna available, ita da Hadiyyah ne suka girka dinner ɗin. Bayan sun gama, Faryal ta yi wa Hamdan funnel cake ɗin da yace.
Bayan ta gama shirya komai, ɗakin Nasar ta nufa inda inda ta same shi yana buga game a ƙaramin Tv ɗin dake ɗakin nasa.
"Nasar!".
"Na'am". Nasar ya amsa yayin da dukkan hankalinsa yake kan Tv.
"Dan Allah je ka kakkabe min falon bakin can".
Ɗan kallonta yayi kafin ya ce, "Surukin namu ne zai zo kenan?".
Ɗan murmushi tayi kana ta ce, "Eh".
Ajiye remote ɗin yayi ya miƙe yana murmushi ya ce, "Ahh, dole na je na shirya muku falon nan yanzu yanzu kuwa".
"Yau dai baza ka zauna ka dame mu ba, kar ka ce ma ban gaya maka ba". Faryal ta faɗa dan ta san halin Nasar ɗin da Hamdan, saboda Hamdan ɗin ɗaukan Nasar yake kamar wani abokinsa, kasancewar dukansu suna da surutu yasa tasu ta zo ɗaya.
Tare suka fito daga ɗakin Nasar yana gaba tana biye da shi. Beta ce ta iso wurinsu tana tambayar, "Bhana fita zakuyi ne?".
"Ba in da zamu sarkin yawon. Zan je in shirya musu falon baƙi ne Hamdan ne zai zo". Nasar ya bata amsa.
"Yeyyyyy". Beta ta sa ihu tare da rugawa cikin gidan da gudu tana shelar ga Hamdan nan zai zo.
Faryal ta dafe goshinta tana faɗin, "Kai wannan yarinyar, bakinta baya shuru". Ta faɗa tana bin Beta ɗin zuwa ciki, yayin da Nasar kuma ya nufi compound ɗin gidan inda falon baƙin yake.
Ɗakin su ta wuce kai tsaye, ta yi wanka a gurguje sannan ta gabatar da sallar Magariba, ta shirya cikin wata simple doguwar rigar atampa marar hayaniya ta ɗan yi kwalliyarta sama sama. Ɗagowa tayi ta kalli Hadiyyah dake chatting a waya sai dariya take ita kaɗai, "Wannan wayar sai ta saki hauka idan kika yi wasa".
Hadiyyah ta ɗan kai tafin hannunta kan bakinta still tana dariyar ta ce, "Yi haƙuri, ba laifina ba ne, Abubakar ne".
Faryal ta dan girgiza kai tana murmushi ta ce, "Ina gaisuwa". Ta faɗa tana tashi ta nufi ƙofa ta fita.
A dinning ta hangi Daadee da Beta dan haka tayi joining ɗin su tana tambayar Maama fa? Beta ta shaida mata tana ɗakinta tace bata jin yunwa ne yanzun.
Haka dai suka gama cin abincin nasu tare sannan suka koma falo suka zauna suna yar hira har lokacin sallar Isha'i ya yi.
Ɗakin Daadee suka nufa gabaɗaya, suka gabatar da sallar acan tare da ita. Bayan sun idar, suka zauna a ɗakin suna ci gaba da hira, tare da tsokanar juna irin na wasan jika da kaka. Agogo na Buga 9pm daidai, Nasar ya leqo ɗakin yana faɗin, "Faryal, Hamdan kuwa zai zo? Naga har ƙarfe tara ta yi".
Faryal ta ɗan kalli wayarta dan sake duba lokaci, yayin da Daadee ta ce, "Ya kamata ki kira shi kiji ai". Ba musu kuwa ta shiga contacts ta lalubo number sa ta danna masa kira, saidai har ta katse bai ɗaga ba. Ajiye wayar tayi jiki a sanyaye, ta ce, "Bai ɗaga ba, maybe yana kan hanya ne".
"Alryt?". Nasar ya faɗa yana barin ƙofar ɗakin.
Faryal ta ɗan yi shiru ta shiga tunani, yayin da Daadee da Beta kuma suke wasa da teddy bears ɗin Betan a kan gadon na su, dan tare suke bacci abinsu ita da Daadee. Lokacin da Faryal ta ga 9:36pm, hankalinta ya tashi, ta sake kiran Hamdan amma still bai ɗaga ba. Tashi tayi tare da faɗawa Daadee tana zuwa, zuciyarta na mata wani irin babu daɗi, tana fatan Hamdan ba kunya zai sake ba ta ba kamar yadda ya saba. Maama, Nasar da Hadiyyah ta tarar a falo suna kallon TV, kafin ma su mata wata maganar tayi saurin tarar su da faɗin fitsari zata je yi tana dawowa, ta samu ta wuce ɗakin su.
Ko da ta shiga ɗakin ta kasa zama, kai komo kawai ta shiga yi daga wannan gefe zuwa wancan, tana kallon wayarta lokaci zuwa lokaci. Ko da agogo ya nuna 10pm, ta gama yarda yau ma Hamdan ya sake yin abin da ya saba. Canza kayanta kawai tayi zuwa na bacci kafin ta haye gado ta kwanta, zuciyarta cike da damuwa, dan ta kasa fita ma ta je ta yi wa su Maama sai da safe. "Wai sai yaushe Hamdan zai ɗauke ta da muhimmanci ne? Yaushe zai zama cikakken mutum kamar sauran maza?". Tambayoyin da ta riƙa yi wa kanta kenan wanda bata da me ba ta amsarsu, tana a wannan yanayin ne bacci yayi awun gaba da ita ba tare data sani ba.
Washegari, bayan sun gama duk abin da ya kamata, ta ɗauki wayarta, tunanin abinda Hamdan ya yi mata a daren jiya ya dawo mata wanda ya sata jin ba daɗi. Data ta kunna ta shiga social media tana ɗan kalle kalle, sai kuwa tayi karo da story ɗin Hamdan ɗin wanda ya ɗaura 16h ago. Sake kallon storyn ta yi, sai ta fahimci cewa jiya da ƙarfe tara na dare ya ɗaura shi. Ma'ana dai yana ganin kiran da ta yi masa. Cikin takaici da bacin rai tayi cilli da wayar kan gado.
Hadiyyah wadda ta fito daga bathroom ɗaure da towel da alama wanka tayi, ta kalli Faryal ɗin sai dai kafin ta ce wani abu aka turo ƙofar ɗakin nasu Manira ta shigo, rungume juna sukayi da Hadiyyah, kafin ta juya zuwa ga Faryal wadda take zaune tana kallonsu kawai, fuskarta ɗauke da damuwa. "Kar ki ce min har yanzu ko wanka ba ki yi ba, alhali kin san mun yi wa Shenal alƙawarin wuni tare yau?".
"I'm not in the Mood Manira, dan Allah ki ƙyale ni".
Manira ta kalli Hadiyyah wadda take gaban mirror tana shafa mai kafin ta ce, "Me ya ɓata mata rai ne Hadiyyah?".
"Hmm, wa zai ɓata mata rai in ba Hamdan ba?".
"Me kuma ya faru a tsakaninsu?".
"Kamar yadda ya saba mata wasa da hankali ne, ya fada mata zai zo, ta shirya, har da su snacks amma yaqi zuwa".
"Kai, wannan mutumin, wannan mutumin, ni ban san me ta gani a tare da shi ba har ta makale masa haka, haba ko shi ne autan maza ai sai haka, ba fa kwantai ki ka yi ba, Ballatana ace neman kai ake da ke". Manira ta faɗa cike da takaicin Faryal ɗin, daga nan kuma suka koma Maganar ita da Hadiyyah yayin da Faryal take jin su, amma ba ta da bakin da zata kare Hamdan ɗin a wurin su. Yana ta gwada haƙurinta dai amma bakomai, tashi tayi ta nufi bathroom tana jin Manira na faɗin, "Wallahi ki yi wa kanki faɗa dai Faryal, time doesn't wait".
Ko da ta shiga bathroom ɗin, jingina tayi da ƙofar ta dage kanta sama, how she wish kowa zai fahimci irin soyayyar da take yi wa Hamdan. "Shin wannan ne dalilin da ya sa Hamdan yake hurting ɗin ta har haka?". Goge hawayen da bata san lokacin da ya zubo ba ta yi tare da furta, "Wallahi a wannan karon zan tabbatar da ka san darajata, na daɗe ina haƙuri, ba zan iya ci gaba da tafiya a haka ba, kowa laifi na yake gani sannan kai ɗin da nake faɗa akan ka, ba ka ma ɗauke ni a matsayin wani abu mai muhimmanci ba, ni to ina zan sa kaina in ji daɗi?".
Haka dai ta yi wankan ta fito ta samu dakin ba kowa. Shiryawa tayi cikin wata Turkish abaya yellow. Ta kalli kanta a mirror take maganganun Walida suka shiga dawo mata, "Ke kyakkyawa ce, mai ilimi, kuma ƴar gidan mutunci. To me na rasa ne?". Ta yiwa kanta tambayar, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tare da furta, "I deserve the best life has to offer, me zai sa in damu da wanda bai san darajata ba? Yake wulakanta ni". Ta yi wani ɗan murmushi mai ɗauke da takaici yayin da take shafa maroon lip gloss a kan matsakaitan lips ɗin ta, sannan ta sanya medicated glasses ɗin ta. Ta ɗan daidaita nutsuwarta, ta ɗauki handbag ɗin ta grey colour ta fice daga ɗakin.
A falo ta same su, ta yi ƙoƙarin nuna kamar komai lpy, kafin ta ce, "Manira kun gama?".
Hadiyyah ta amsa, "Eh, dama ke muke jira. Tun da kin gama muje".
"Okay". Ta faɗa, daga nan suka yiwa Maama sallama suka yi waje.
Ranar wuni sukayi tare da Shenal, wanda yasa Faryal mantawa da kaso 70 na damuwar ta. Lokacin da suka dawo gida, Magarib har ta yi, dan haka suka matsawa Manira sai ta kwana, daga ƙarshe dai ta amince. Haka suka shafe rabin daren suna hira da tsokanar juna har dare ya raba, sannan suka kwanta bacci.
Washegari ta kama Monday. Haka Faryal, Manira da Hadiyyah suka kasa aikin gidan a tsakanin su. Manira da Hadiyyah za su yi shara da mopping, ita kuma Faryal za ta girka breakfast. A gurguje tayi girkin saboda yadda ta kusan makara.
Bayan ta shirya dinning din, ta nufi falo tana kiran Manira, maganarta ce ta katse a yayin da idanunta suka sauka akan yadda gabaɗaya falon ya hargitse maimakon gyara. Duk an watsa komai, juyawa tayi inda ta hango tsintsiya, parker da kayan mopping ɗin. Kwafa taja ta wuce ta ɗauki parkers ɗin guda biyu sannan ta nufe su da sanɗa.
Suna zaune a ƙasa kan tiles sun baje suna karanta chat ɗin Maniran da Amin. A kawunan su ta buga musu parkers ɗin, wanda yasa suka dago a firgice.
"Ƴan iska kawai, wannan ne aikin da aka ce ku yi? Ai dama na san tunda kuka ce in bar muku ba wani abun kirki za ku yi ba, duk kun sake hargitsa gidan ma". Ta Ƙarashe tana kallon Beta data fito daga ɗaki sanye da uniform ɗin makaranta.
"Beta, ki je ki yi sauri ki karya. Lunchbox ɗin ki yana kitchen. Shi kuma wannan yaron yana ina?". Ta tambaya a yayin da ta jefawa Hadiyyah da Manira parkers ɗin, waɗanda suka tashi suka hau gyaran falon. Ita kuma ga nufi ɗakin Nasar, a daidai lokacin da yake fitowa shi ma.
"Kai Nasar, me kake yi ne haka, zaku yi late fa".
"To laifin waye? Ku ne ba kwa girka breakfast da wuri ai". Ya faɗa yana nufar dinning.
Ɗakin su Faryal ta wuce, ta ƙirgo wasu yan canji sannan ta sake fitowa. Dinning ɗin ta nufa ta rabawa Beta da Nasar kuɗin break, yayinda Nasar ya shiga complaint kan cewa tana rage musu kuɗin da ake ba su, shi gsky sai ya faɗawa Appah.
Barin dinning ɗin tayi ba tare da ta bi ta kan mitar ta sa ba, ta komawarta ɗaki. Wanka tayi ta fito ta shirya, tana cikin tarkata abubuwan da take buƙata dan zuwa office, sai ga wallet ɗin nan. Zama ta yi, ta buɗe tana duba abubuwan dake ciki, ATM cards ne guda biyu tare da IDs biyu. Ɗaya daga cikin ID ɗin na wani Company ne mai suna A.M SARAKEE MOTORS. Maimaita sunan tayi tana juya ID ɗin, a ƙoƙarinta na son tuna inda ta taɓa jin sunan a baya, ganin bata iya tunawa ba yasa ta ɗage kafaɗu. Ta karanta Address ɗin da ke jikin ID ɗin sannan ta mayar da shi cikin wallet ɗin, ta sanya wallet ɗin a cikin jakarta. Ta tashi ta saka takalmanta sannan ta fita. Sai da ta gaishe da Maama da Daadee, kafin ta wuce dinning ta yi breakfast.
Bayan ta gama, ta nufi ɗakin Daadee, dan ta san Manira da Hadiyyah baza su wuce can ɗin ba. Hakanne kuwa dan a can ɗin ta same su, sun gama gyaran ɗakin. Hadiyyah tana tsaye a bakin ƙofar bathroom ɗin yayin da Manira ke tsaye jikin gadon. Hadiyyah na bawa Manira wani labari, sunyi nisa cikin hirar tasu har ba su san da shigowar Faryal ɗin ba, sai da ta ce. "Ehen two parrots, anan nan ana yi ko? To ni zan fita".
Manira who was visibly disturbed by Faryal's presence, saboda yadda ta sa Hadiyyah yin shuru ya sata faɗin, "Dan Allah jeki, a sauka lpy".
Faryal da take shirin rufe ƙofar ɗakin ne ta tsaya, tare da shigowa ɗakin, ta isa wurin Manira ta ɗaka mata duka a baya tana faɗin, "Marar kunyar banza kawai".
Manira ta dafe wurin da Faryal ta dake ta kafin ta ce, "Babu damuwa, za mu gauraya anjima, amma yanzu dai bani da lokacin ki, dan Allah ki tafi".
Faryal ta yi yar dariya tare da faɗin, "Ba ki da lecture ne yau Hadiyyah?".
"Sai da yamma". Hadiyyah ta amsa.
Gyaɗa mata kai Faryal tayi kafin ta rufo musu ƙofar. Zuwa ta yi ta yiwa Maama da Daadee sallama, tana daurawa da faɗin, "Daadee idan ba ki fitar da waɗancan yaran daga ɗakinki ba, sai sun ɓata miki komai". Ta ƙare maganar tana dariya, ta nufi waje, tana jin yadda tuni Daadee ta fara kwala kiran Hadiyyah da Manira.
Ko da ta isa Company, ta tarar da aiki sosai, amma ta yi ƙoƙarin kammala komai kafin 3pm. Dan a lokacin da agogo ya buga ƙarfe uku, tuni ta gama komai, dan haka ta tattara ya nata ya nata ta bar Company, ta nufi address ɗin da ta gani a jikin ID nan.
Ba tare da ta sha wata wahala ba, ta gano A.M SARAKEE MOTORS, dan sanannen Company ne. Ta danna horn, sai ga ɗaya daga cikin securities ɗin ya fito dan duba wanda yake cikin motar. Rage glass ɗin motar tayi tare da faɗin, "Good afternoon".
Security da ya fi kama da Christian, ya amsa da, "Good afternoon Madam. How may I help you?".
"Umm....". Sai kuma ta ɗan dakata tana ƙoƙarin tuna sunan da ke jikin ID ɗin kafin ta ce, "Nazo ganin Mr Aryan ne".
"I'm Sorry Madam, this company is for men only".
"Men's only?". Faryal ta maimaita tana masa kallon rashin fahimta. "Ban gane ba? shin dama ba Company da ake kasuwanci ba ne? Ko kuwa akwai zaɓi a waɗanda ake business dasu? I think both mace ko namiji zai iya zuwa siyan abu a wuri".
"Sorry Madam, wannan shi ne abin da na rantse akai a lokacin da za'a ɗauke ni aiki a wannan Company, dan ba a yarda mace ta shiga ba".
Faryal ta riqe baki cikin mamaki, dan ba ta taɓa cin karo da irin wannan abun ba a duk tsawon rayuwarta. Sai kuma ta yi dariya saboda maganar ma dariyar ta baga. Tana shirn sake magana, sai ta ga an fara buɗe gate din alamar mota zata fito daga ciki. Cikin rawar jiki security ya shiga faɗin, "Madam, please kada ka janyo a kore ni daga aikina, please ka tafi, CEO ne zai fita idan ya ganka za'a samu masala". Ya shiga faɗa a rikice cikin gurbatacciyar hausar sa.
Faryal wadda ta ƙuduri aniyar sai ta ga abinda ya turewa buzu naɗi, dan whl baza ta koma ba. Reverse ta sakeyi ta yi blocking hanyar da motar zata wuce, sannan ta ɗauki wallet ɗin ta buɗe ƙofar motar ta fita ba tare data kashe motar ba, ta wuce security dake roqonta kan ta koma mota.
Mansur ne ya yi saurin buɗe ƙofar motar ya fito tun kafin ma Faryal ɗin ta ƙaraso kusa da motar. Ya tare ta da ɗan murmushi akan fuskarsa, dan har ya hasaso abin da zai iya faruwa idan Faryal ɗin ta ƙarasa wurin motar tasu bayan Aryan na ciki. "Barkan ki". Mansur ɗin ya faɗa.