Chapter 41
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
Chapter 41.
Na yi iyakar yina wajen ganin ban haɗiyi maganin ba amma ina ƙarfina dana Hafsa ba ɗaya, gashi ta riga ta danne ni, ta kuma toshe mashaƙar iskana har sai da ya riga da ya wuce cikin cikina.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, Hafsa mi kika aikata haka, bakida tunani ne???."
Saminaka daya shigo gidan yanzu ta ƙofar bayan daga ɗakina ake fita waje ta cikinta ya faɗi yana sakin ledojin hannun shi ya ƙarasa wajen da nike da sassarfa.
Zafaffan maruka lafiyayyu guda biyu ya soma saukewa Hafsa yana faɗi a tsawace.
"Ina hankali da tunaninki ya tafi ne, mi kike shirin aikata mata haka, anya kinada hankali kuwa?."
Sai kuma yayi kaina ya soma jijjigani a birkice yana kiran sunana.
Bansan abin da ke faruwa da ni ba, kamar yanda bana iya gane komi, amma bakina bai gushe ba wajen furta kalmar.
"Cikina, Yah Allahu ya rahaman banaso, ina jin ciwo, ku taimaka min dan Allah kar in rasa babynah."
Haka nike faɗa ina maimaitawa bayan na riƙe hannun Saminaka katamau ina hana idanuwana kullewa.
A daidai wannan lokacin da nike tsananin buƙatar taimako a wannan lokacin ne kuma al'amurra suka soma sauyawa.
Gani a kwance ina buƙatar ɗaukin mijina, yayinda shi kuma wani shafin ƙaddara me cakuɗe da son zuciya ya buɗe masa.
"Abubakar Muhammad Samina, ni matarka Hafsa Bishir ban yarda ban amince ka ƙara taɓa koda hannun wannan matar ba."
Ta taɗa da wani irin murmushi akan fuskarta, lokaci ɗaya kuma tana murza wani abu a cikin tafin hannunta.
Wani irin dummmm kan Saminaka a sara, gani dai yana kallo cikin halin ciwo me tsanani, dan kuwa zuwa lokaci har jini ya ɓalle min, amma kuma ya gagara sake motsawa kamar wanda aka ɗaure.
Kukan azaba da raɗaɗin ciwo kawai nike ina miƙa ma shi hannu, amma ya gagara mitsi yadai kafe ni da ido yana kallona shima wani abu baibaye da fuskar shi amma bai iya cewa komi ba.
Haka Hafsa taja hannun shi suka fice daga ɗakin suka tafi suka barni ni kaɗai cikin halin ciwo da azaba."
Zuwa lokacin kuka sosai Rimsha ta fashe da shi wanda ke nuni da tsantsar baƙin ciki da damuwar da take ciki.
Matsawa Maryam ta yi kusa da ita, tare da saka hannayenta duka biyun ta tallabi haɓar Rimsha, fuskarta da damuwa ta ce da ita.
"Kiyi haƙuri ina son inji labarinki duka."
Rimtse hannun Maryam ta yi a cikin nata, zuciyarta na suya muryarta na rawar kuka taci gaba da faɗin.
"Daga wannan ranar na samu matsala matsalar data cigaba da tafiya da rayuwa har zuwa yau da nike a raye.
Hafsa maganin zubar da ciki ta bani, maganin da ya yi min illa sosai har takaiga mahaifata ta lalace, hatta da cikin da nike da shi sai da ya taɓu sauƙin ɗaya bai zube ba amma ya raunata sosai, babban abin da ya ƙara kawo matsalar rashin kaini asibiti akan lokaci har sai da na fita a hayyacina.
Na raini cikina ni ɗaya na sha wahalar ciwo da laulayi ni kaɗai, ganin mijina ya gagare ni, baya zuwa inda nike baya kulawa da ni, cikin sati ɗaya kacal na rame na fita a hayyacina, ko abincin kirki bana iya ci, ga damuwa da ta yi min yawa, ga kuma kula da Muhammad da baya zuwa ko nan da can yana manne da ni, ga shi Ma'u ta gudu tun da suka saikata min wannan aika-aikar.
Hafsa ina zaune take zuwa har inda nike ta yaɓa min mugayen maganganu tare da yi min kashedi tana tsoratar da ni game da zaman gidan.
Nan da nan matsanacin tsoronta tare da fargaba suka dirar mi, musamman yanda naga shi kanshi me gidan juya shi take yanda taga dama.
Idan na ji sauƙin jikina ina zuwa kusa da ƙofar fita sashena intsaya jiran ganin shige da ficen shi ina jin kewarshi na lulluɓe shi.
Ina so insamu kusanci da mutane musamman wanda zasu dinga ɓebe min kewa amma kuma na rasa ta inda zan fara, nidai ban wani saba da mutanen dake shigowa gidan jifa-jifa ba, gashi kuma bani da wadatacciyar hausa hasalima iya gaisuwa kawai na iya da yare sai kuma godiya, wanda na koya tun ina Dubai wajen kasuwanci da muke haɗuwa da baƙaƙen fata ƴan amurika.
Gashi banida kyakkyawar alaƙa da ƴan uwana bare kuma in neme su, banida kowa sai Allah dan haka sai kawai na dage na duƙufa wajen yin addu'a, cikin ikon Allah na soma samhn sauƙin nauyi da raɗaɗin da zuciyata ke yi, naci gaba da rainon cikina me rauni ina kuma zuwa asibiti akai akai.
Har cikina ya cika watanni bakwai babu wani cigaba tsakanina da Saminaka, sautari muna haɗuwa da shi amma ya ɗauke kai kamar bai gane ni ba, ko doguwar magama bata haɗani da shi.
Sannan Muhammad ya yi yawo danko ya cika shekara harda watanni, a kuma lokacin ne nayi applying aiki a campanys ɗin da nayi aiki da su a dubai, a lokacin babu hanyoyin sadarwa sosai, amma dayake mun rigada mun yi sabo sai na samu sauƙi wajen abubuwa da yawa.
Suna turo min kaya ta jirage ina amsa inraba a hannun masu sari da shaguna, cikin ikon Allah sai kasuwancina ya soma haɓaka danma dai ba wadatacciyar lafiya gare ni ba nakan kwanta sau uku a sati asibiti ina jinya tare da rainon cikina.
Na tsayar da kasuwancina ne a sanda watan haihuwata ya tsaya, domin kuwa har an fidda ranar da zanje ayi min CS kasancewar bana iya haihuwa da kaina mahaifata ta raunata matuƙa, kuma anbani bed rest bana komi hatta da kasuwancina na tsayar nacigaba da rainon cikina tare da tsananta addu'a a kaina da kuma lafiyar babyn da zan haifa sai kuma akan mijina da zuwa yanzu na gama gane sam bana gabanshi.
Kwatsam a daren ranar wata alhamis ranar da bazan iya mantawa da ita ba a tarihin rayuwata, Allah ya haska min wani abu game da Hafsa matar Saminaka.
A ranar na fita ina motsa jiki cikin dare, saboda ciwon da nike ji yana taso min sama-sama, ba tare dana ankara ba na fice daga sashena sai cintar kaina na yi a sashen Hafsa, tsakar dare ne a lokacin wajajen ƙarfe biyu na tare idanuwana suna hasko min mutum sanye da baƙaƙen tufafi, ba'a iya ganin komi nata ta rufe ruf.
A ƙasa kuma Saminaka ne kwance ta cire kayan jikin shi tana zuba ma shi wasu ruwa tana sambatu da faɗar wasu maganganu masu tada tsigar jiki.
A gabanta kuma kwarya ce kala uku ko wace ɗauke da wani ruwa.
Ta jima tana zagaye shi tana yayyafa ma shi wannan ruwan tana sambatu.
Ni kuma na toshe bakina dan kada sautin na ya fito, na dafe ɗan cikina dake barazanar fitowa a lokaci, wata iriyae kyarma jikina yahau yi har fitsarin tsoro sai da ya kubce min lokacinda ta yaye lulluɓin fuskarta, ta zaro wata iriyar wuƙa me kyalli ta ɗagata sama tana jujjuyawa, kafin naga ta nufi wajen shi ta ɗuka ta ɗaga wuƙar da iyakar ƙarfinta tana shirin ɗaba ma shi.
Bansan lokacin dana suri wani katako dake wajen ba ya nufi wajenta na maka mata shi a gadon bayanta da ƙarfi, har ƙosar jikin katakon na hudata.
Saboda tsabar taurin rai na matar nan sam bata razana ba saima juyawa da tayi da idanuwanta da suka koma jajaye tayo kaina da wuƙar tana buɗe bakinta cike da ban tsoro.
Wani juyin azaba ɗan cikina ya kuma yi da ƙarfi, lamarin daya tilasta min duƙewa ƙasa ba shiri na saki azababbiyar ƙasa, ina jin yanda jini ya kunce min yana zuba kamar fanfo.
Da iyakar ƙarfinta ta ɗaga wuƙar zata soka min a ciki, na saka hannuna na rirriƙe duda na soma fita daga hayyacina amma bansaki hannunta ba duda ƙafarta datasaka ta dinga harbina a ciki cike da mugunta.
Lokaci ɗaya ƙarfina ya soma ƙarewa na soma gazawa ta dinga mamayata tana kusantoni da wuƙar har takaiga tsinin wuƙar ya taɓa fatar cikina, hannuwana suka yi sanyi na gagara riƙeta, kaina ya sara gangar jikina ta soma amsar azabar naƙuda, azababben ciwo da rauni suka rufe rayuwa, nan take na sadaƙar.....✍🏻
MARYAM STAR AMANAR BILYN-ABDUL