TASWIRAR KADDARA

Page 19

by @oumamani

*TASWIRAR KADDARA*



 DijahAM(Oum Amani)



Page 19



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM





    Hade rai nai nace "wuce mu tafi"



Juyawa Mimi tai ta kalli Azlan da ya nade hannun sa yana kallon su kamar ya samu TV sai kuma ta juyo ta kalle ni kamar zatai kuka tace "Maa bamu gama magana da Daddy bafa"



Zaro idona nai bansan lokacin dana ce kuttt***** cikin bacin rai nace "ta ina ya zama daddyn naki"



Da sauri Mimi ta koma jikin sa ta rungume sa sbd yadda nayi zagin da kuma yadda nai mata magana ba karamin tsoro ya bata ba.



Hade rai Azlan yai yana kankance idonsa yace "kar ki sake yiwa yarinya ta ihu haka bare ki kai ga zagi"



Kallon sa nai sai na juya na kalli Asma'u kawai na fashe da kuka cikin kuka nace "Asma'u kina ji wai yarinyar sa banda kalan dangi ina Shi ina Mimi wallahi ba abinda suka hada dashi."



Kallon ta kawai yake yana kokarin controling kansa kar yai dariya lallai yarinyar nan, sbd kawai yace wa Mimi yarinyar sa shine take kuka wani Murmushin mugunta ya saki ya janyo Mimi sosai jikinsa yace "yarinyar Daddy kar kiyi kuka kinji zo mu tafi"



Daga masa kai tai tana satar kallo na sai boye fuskar ta take a jikinsa sbd kar mu hada ido, binsu da kallo nai har suka fita daga cafeteria din suna rike da hannun juna.



Zama nai akan kujerar da Mimi ta tashi na dora kaina a jikin table din ina sake fashewa da kukan bakin ciki, yau nice Mimi take kallo ina kuka amma ko ta tsaya Mimin da In taga raina ya baci hankalin ya yake tashi ko Umma ce tai min fada Mimi bata sake yiwa Umma magana ta dinga fushi da ita knn sai gashi tana kallo ina kuka da hawaye amma tabi wani Wanda bata San sa ba sai yau dole nai kuka ai.



Dafa ni Asma'u tai tace "kiyi hakuri mana Batul sai kace wata yarinya kin zauna kina kuka kinga duk mutane kallon ki suke".



Girgiza kaina na shiga yi ina fadin "baxa ki gane halin da nake ciki ba Asma'u, yau ni Mimi zata tozarta don ubanta"



Zaro ido Asma'u tai tace "ynxu ita Mimin kike zaga"



A fusace na mike nace "na zage tan kuma wallahi har dukan ta zanyi in mun koma gida don ubanta."



Kama haba Asma'u tai tana jinjina lamarin lallai abin yai tsamari tunda batul ta bude baki ta zagi Mimi, mikewa nai na share fuskata muka fito daga cafeterian.



Kallona Asma'u tai tace "ina muka nufa ynxu"



Cikin fushin da har ynxu yaki sauka nace "office din Mr Wicked zamu, don ni ban yadda dashi ba gaba daya kina gani fa ko ke Mimi bata sake dake ba har ynxu amma daga haduwa da wannan mugun lecturen har tana ce masa dadi," hawaye na share ina gyada kaina kawai.



Ita kam Asma'u ynxu abin dariya ma yake bata, Shiru tai kawai don ta kula a yadda Batul take in ta matsa ita kan ta sai ta zage ta.



Jamim hijab akai da karfi Wanda har saida Hijab din ya sauka daga kaina ya dawo kafada saukin tama ina da hula akai amma itama hular sai da tayi baya sosai gaban gashina ya bayyana.



A hankali na juyo ina hadiyar zuciya sbd wani turiri dana ji kirjina yana min, Zuby CE tsaye ita da kawayen ta wani mugun kallo na zuba mata nace "sakar min Hijab"



Sakin Hijab din tai tana wani yatsina fuska tace "zuwa nai na Miki gargadi wannan ya zama na farko kuma na karshe da zaki dinga shiga harkar Mr Azlan, don na kula kin cika rashin kamun Kai sai tusa kanki kike garesa sbd yace yana sonki toh kwalelen ki yafi karfin ki."



Kallon ta kawai nake ina tauna lips dina, ganin nai mata banza yasa Nana fadin "bada ke ake magana ba yar rainin hankali kawai sbd kin raina mutane suna maki magana kina musu banxa"



Zuby ce ta cafe da fadin "bar yar iska ashe ma matar aure ce shine sbd rashin kamun Kai take makale wa wani daban, har da makala masa shegiar yarr...... " bata karasa ba sbd wani zazzafan mari dana shinfida mata a fuska.



Zaro ido Asma'u tai tana kallona don bata san lokacin dana yi tsalle na koma gaban Zuby ba kawai karar marin taji.



Nana da Hafsa ma bude baki sukai suna kallona ku kalle ni su kalli Zuby data dafe kunci tana kallona.



Cikin bacin rai ta bude baki tace "ni kika mara"



Takowa nai har gabanta nace "an mare ki ko zaki rama ne ehe karamar yar iska, kar kiga ina miki shiru ki dauka ko ina Jin tsoron kine kawai ina yin shiru ne don baki kai matsayin da zan tsaya ina sa'in sa dake ba ni nasan darajar kaina."



Numfashi na sauke na dan juya na kalli yadda aka samu a tsakiya ana kallon mu, dan tabe baki nai nace "ki kiyaye zagar min yarinya zaki iya min komai na kyale ki amma banda zagar min ya, sannan Shi malamin da kike magana akan sa ke ya dama ni baya gabana don ba wannan nazo yi makaranta ba.."



Juyawa nai na kalli Nana nace "amma dai kinyi asara sbd kwadayi kullum kina tare da wannan kafa da kafa sbd abin duniya Allah ya kyauta, sannan kar ki kara sani a shirmen ki don ni ba sa'ar ki bace"



Janyo hannun Asma'u nai muka juya don na fasa ma zuwa office din nasa tunda akan sa ake min wannan wulakancin aikin banxa kawai na fada a fili ina Zama a kan kujera.



Ban Kara waiwayar su Mimi ba sai da muka gama lecturen mu 4 bayan munyi sallah sannan muka nufi office din sa nida Asma'u ina mitar ynxu in naje karbar yarinya ta ya hanani mana in ya isa..



Knocking nai ba tare dana tsaya jiran aban izinin shiga ba na tura kaina kawai, suna zaune akan doguwar kujera sun dukufa suna kallon wayar sa da dukkan alamu game suke sai dariya suke su biyu sam basu ji shigowar mu ba.



Nida Asma'u kasa karasowa cikin office din mukai muka zuba musu ido, gabana ba abinda yake sai faduwa har yanayin dariyar su iri daya da yanayin dimple dinsu na gefen kumatun dama, lumshe ido na nai ina ambaton sunan Allah.



Dagowa yai ya kalle mu sai ya hade rai, muna hada ido da shi na falla masa katuwar harara na murguda masa baki ina kauda kaina gefe.



Lasar lip dinsa kawai yai ya kalli Mimi da ta kara kwanciya a jikinsa tana kallona, sbd ita kanta hararar na ke Mata.



Cikin kausasa murya nace "tashi kizo mu wuce tun kafin ki gama kaini bango"



Mikewa tai tana kallon sa rungume sa tai tace "bye Daddy" 



Kallon ta kawai yai ya kasa magana ji yake kamar ya hanata tafiya amma yasan bashi da wannan damar, lumshe ido kawai yai yana taunar lips dinsa.



Ina janyo hannun Mimin sai da na saki wata ajiyar zuciya sannan na dube sa nasan zai jini hakan yasa ni fadin "kuma wallahi a dinga sa tsoron Allah a cikin lamuran rayuwa a daina kwacewa iyaye yaran su."



Banxa yai mata don bashi da lokacin tanka mata, shidai abinda ya sani kawai baya Jin zai iya kwanaki ba tare da ya kuma haduwa da Mimi ba, haka kurin Allah ya dora masa kaunar ta a cikin zuciyar sa.



Fitowa mukai daga office din ko magana ban yiwa Mimi ba don itama sunkuyar da kanta tai taki yadda ta dago mu hada ido, sallama nai wa Asma'u muka hau adaidaitar dana tsayar.



Ban ce mata uffan ba Saida muka isa gida, nan na zauna na zayya nawa Umma komai, abinda na boye mata kawai kamar da suke da juna.



Tagumi Umma tai ta kalli Mimi tace "mai yasa kikai haka uhm Mimi"



Hawayen ta take sharewa tace "baxan sake ba Umma Allah ki bawa Maa hakuri"



Tsaki nai na galla mata harara na mike daga gurn na shige daki, tana ganin na bar gurin Umma ta rungumo ta jikin ta tace "ban labari mai dame Daddyn naki ya baki"



Washe baki tai ta shiga bawa Umma labarin yadda Daddyn ta ya dinga lallaba ta yana bata chocolate.



Dariya tai tace "Umma har kaza ya siyo min katuwa, kuma yace zai je school dinmu yace shine daddy na"



Murmushi Umma tai hankalin ta yana kwanciya daga bayanin da Mimi take Mata ta gane ko waye wannan Daddyn nata yana sonta sosai, amma kuma meye dalilin dayasa Batul bata sonsa.



Tashi tai kawai ta shiga kitchen ta bar Mimi agun tana wasa.



Sam kin sakar mata fuska nai har muka zo kwanciya, duk da hakan yana damuna amma na maze don so nake ko gaba in suka kara haduwa taki yadda dashi duk da bana fatan su sake haduwar ma.



Mirginowa Mimi tai ta rungume ni tace "Maa kiyi hakuri baxan sake ba Maa, dama sbd yace Shi Daddy nane shiyasa nake ta murna Nima na sami Daddy kuma yace zai je school dinmu yace shine daddy na sbd yan class dinmu su daina cewa banda Daddy"



Rintse idona nai sai kuma tausayin ta ya kamani, a hankali na rungume ta nima ina shafa kanta nace "shiknn Daughter amma kar ki sake yadda kije gunsa kinji"



Daga min kai tai ta rufe idon ta, ni kuwa tunani na shiga yi kawai sai da tayi bacci na mike a hankali na kunna fitilar dakin dana kashe, juyawa nai na kalli Aisha ganin bacci take na dan sauke ajiyar zuciya.



Wardrobe na bude na dauko wata jakata da ta dade sosai a hankali na bude jakar hannu na zura cikin karamin zip din na zaro wani kyakkyawan bracelet na Maza mai kyau, walwalin da yake ne zai nuna ma na zallar azurfa ne.



Warwarwe Shi nai na kura masa ido shine kadai abinda nake da shi mallakin baban Mimi, sai dai bansan ta yadda abin zai kaini gare sa ba Kura masa ido nai sosai ganin rubuta karami mai kyau a jiki, cikin rawar jiki na kara Kura masa ido gabana yana faduwa zaro ido nai ganin ansa *AJ* Shiru nai ina tunanin Mai hakan yake nufi ganin ba mai bani amsa yasa na mike kawai na maida jakar Inda na dauko ta Shi kuma bracelet din na wulla cikin jakata ta makaranta.



Kwanciya nai Nima ina addu'ar bacci, ban dade da kwanciya ba bacci ya dauke ni......











***