TASWIRAR KADDARA

Page 20

by @oumamani

*TASWIRAR KADDARA*



 DijahAM(Oum Amani)



Page 20



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM





  Washe gari ina kallon yadda Mimi take kallona ina shirin tafiya makaranta nai mata banxa don na gane mai take nufi wato na tafi da ita, da yake kuma tasan tai min ba dai dai ba bata fito kuri ta fada min manufar zagayen da take ba.



Sallama nai wa Umma na fita ina jaddada wa Aisha kar ta sake ta cimin kudin ciniki nada ake yi in na tafi makaranta.



Ban sha wahalar samun abin hawa ba, ko dan na fito da wuri ne ban sani ba.



Ina zuwa makaranta hall din da muke da lecture kawai na nufa don ban duba littafina ba jiya sbd takaicin da Mr Wicked ya kunsa min Shi da Mimi.



Ina zaune Asma'u ta shigo itama zama tai a gefena tana fadin "wash Allah na"



Dan Kallon ta nai nace "badai kin gaji ba wai"



Lumshe idonta tai tace "wallahi baki ji kafafuna ba kamar an min duka, ni da cewa nai ma baxan xo ba sai da Hubby ya lallabani"



Kallon ta nai nace "Anya kuwa Asma'u ke kadai ce kodai kodai" na karashe ina fashe wa da dariya



Harara ta tai tace "kodai me ban gane mai kike nufi ba"



Juyawa nai ina dariya nace "wa ya sani ko an kusa yiwa Mimi kani ko kanwa"



Dundu Asma'u ta min muka shiga dariya anan take fada min ciki ne da ita wata biyu knn, sosai nai mata murna don ni kaina sai na shiga lallabata ina tambayar ta mai take so na flour nai Mata na kawo mata gobe.





Cikin lokaci kan kani karatu ya dau zafi don sati mai zuwa zamu fara exam din first semester shiyasa gaba daya mun xama busy, karatu kawai muke sosai.



Mr Wicked kuwa bama haduwa da shi sai dai ko a class shima bana yadda mu hada ido da shi.











***********



Dan bude idonsa yai Jin maganar Baffa, a hankali ya mike daga kwancen da yake ya kalli Baffa daya zuba masa ido yana jiran ansar sa.



Ganin ya ki magana yasa Baffa Kara fadin" Mai ke damun kane Zaki? Ina lura da kai gaba daya ynxu Ka chanja kamar wani Abu na damun Ka."



Ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe idonsa gaba daya baya Jin dadin rayuwar ne, ko mai yake tunanin Mimi yake tun ranar daya ganta Allah ya dora masa kaunar yarinyar ji yake tabbas suna da wata alaka Mai karfi tsakanin sa da ita, amma ya rasa tame har mafarkin ta yake tana Kiran sa da Daddy yazo suyi wasa.



A hankali ya bude idonsa ya zuba wa Baffa yace "tunanin wata yarinya ne yake damuna"



Zaro ido Baffa yai yace "wata yarinya ce haka tai nasarar damkar zuciyar ka da karfi haka har tunanin ta yake damun Ka"



Dan yamutsa fuska yai yana murza idonsa da bai Sawa kwalli ba yau yace "Kaga tsoho bana son Vawulence, karamar yarinya ce fa shekarar ta hudu."



Kallon sa Baffa yai yana gyara zama yace "yar shekara hudu kuma kake so zaki mun shiga uku"

 

Hade rai yai sosai yace "Yarinya tace fah kake cewa ina son ta Baffa, ina sonta mana amma ba irin Wanda kake tunanin ba"



Cikin rashin fahimta Baffa yace "ban gane yarinyar Kaba yimin bayani."



Lasar lip dinsa yai yana shafa gemun sa yace "kana ji tsoho a cewar student dina wai yar tace ita ta haife ta ni kuma gaskia ban yadda ba don basa ma kama?"



Kallon sa Baffa yai ganin yai shiru yace "ina jin Ka mana"



Wani shegen murmushi yai yana shafa gemun sa yace "Yarinya dani take kama kamar nayi kaki baka ganta ba har dimple dinta irin nawa ne, har shape din kafar mu."



Mikewa Baffa yai ya nufi gurin da Azlan yake hannun sa yasa a wuyan Azlan ya taba sai ya kalle sa yace "kuma gashi jikin Ka ba zafi bare nace zafin zazzabi ne yake damunka."



Dan hade rai Azlan yai ya zaro wayar sa photos ya shiga ya nemo pics din daya musu shida Mimi, mikawa Baffa yai yace "kalla toh"



Karbar wayar Baffa yai ya zubawa Hoton ido salati ya saki sai ya kalli hoton ya juya ya kalli Azlan, wuce wa yai ya zuba ma wani wanda Azlan yai mata ita kadai ta ware ido ta tsuke baki, gabansa ne ya fadi sbd yadda tai kamar Azlan da yana yaro tabbas Yarinyar kamar Azlan yai kaki.



Duk da kamar Azlan da Junaid daya amma suna da banbanci Shi Junaid fari ne Azlan kuma Ja ne sannan Shi Junaid Dimple duka kumatun sa yake da sabanin Azlan da yake da na gefen kumatun dama kadai, sannan shape din idon Suma ya banbanta na Junaid manyan ido ne dashi Azlan kuma sexy eyes ne dashi shiyasa bai cika bude suba kusan kullum in zai kalli mutum sai ya kankance ido, yarinyar ya sake kalla kamar ta daya sak da Azlan ba inda ta baro sa komai irin nasa ne har yanayin murmushin su.



Ajiyar zuciya Baffa ya sauke ya Kalli Azlan yace “ikon Allah kamar ta baci fah zaki”



Shima ajiyar zuciya ya sauke yace "wallahi tsoho so daya na ganta amma tunda na ganta na rasa nutsuwa ta nidai yarinyar nan ina ji a jikina jini nace amma bansan ta ina ba kuma nidai ina tattalin budurwarcina bare nace ko na danne wata ne"



Dan tsaki Baffa yai yace "meye kuma haka ana zancen Arziki Ka kawo zancen budurci"



Kankance ido yai yace "ai dole nayi haka tsoho baka ga kamannina da yarinyar bane, ni fa badan badan ba da sai na fara xargin budurcina anya baxan je asibiti a duba min lafiyar sa ba kuwa"



Salati Baffa ya saki hakan yasa Azlan fashewa da dariya yana kashe wa Baffa ido daya.



Shiru sukai kafin Azlan yace "kuma tace min bata da Daddy mamanta tace Mata daddyn ta ya mutu amma kuma bata san sunan dadyn nata ba, shiysa kawai nasa ma Yarinyar question mark"



Baffa ne yace "A'a Zaki badai kasan maman yarinyar ba kawai inaga kamanni ne zuka zo daya"



Shiru kawai Azlan yai kansa Yana masa ciwo, amma shifa gaskia bai yadda beauty dinsa yar wannan mara kunyar bacee.....











**********



Cikin nutsuwa Samira take takowa tasha kayan baccin ta masu daukar hankali sai zuba kamshi take, a hankali take tafiya har ta iso bayan kujerar da Junaid yake zaune baisan ta iso ba sbd yadda gaba daya hankalin sa yake kan wayar sa.



Zuro fuskar ta tai ta leka wayar tasa ganin pic din babies kawai yake kalla, idonta ne ya soma Tara kwalla da sauri tasa hannu ya goge su, zagayo wa tai ta gaban sa ta dauke wayar hannun sa da sauri ya dago ya kalle ta yana sakin ajiyar zuciya.



Dan hade rai tai tace "haba Noor ban hanaka sawa kanka damuwa ba ynxu in wani ciwon ya kamaka fa, Ka kwantar da hankalin ka insha Allah komai zai warware lokaci ne kawai."



Kallon ta yake cikin tausayin ta dake kwance a idonsa ya janyo ta jikin sa ya rungume yana lumshe idonsa yace "Noor ina son ganin gudan jini na dake nima, yau naji ana cemin Baba amma sai naji kamar baxan taba samun wannan damar BA"



Da sauri Samira ta sa hannu ta rufe masa baki tace "don Allah kayi shiru Noor kar na sake jin wannan maganar daka bakin Ka bana so komai mai wuce wane kuma lokaci ne ka Kwantar da hankalin ka."



Daga mata kai yai yana sake rungume ta sosai, yana son Samira don mace ce ta gari, yar kanwar Mamin suce tun tana karama yake sonta shiyasa itama ta girma da sonsa bai bata damar Kula ko wanne saurayi ba bayan shi, kuma tunda iyayen su dama sunsan da son junan da suke shiyasa Koda ya nunawa Abie yana so a masa aure yana da shekara 28 Abba bai wani damu ba tunda lokacin ya fara aiki kuma ya kai minzalin aure, Azlan ne dai ba yadda baiyi da shiba shima ya samo Mata a musu aure lokaci daya amma sai ya ce masa budurcin sa bai nuna ba tukun...









***********



Alhamdulillah cikin Amincin Allah mun fara exam gaba daya banda lokacin kaina don karatu kawai nake yi, ko a gida bana wani biyewa Aisha ko Mimi kullum ina daki da paper ina karatu, har tsokana ta Umma take wai na sassauta wa kaina.



Cikin sati biyu muka gama exam dinmu sai dai fatan Allah yasa result yai kyau.



Kamar yadda class rep dinmu yace washe garin ranar da aka gama exam muje mu karbi test din Mr Wicked, badon Asma'u baza taje ba sbd bata Jin dadi da ba abinda zai sani zuwa amma dole naje na karbo mana ni da ita.



Shiryawa nai cikin doguwar rigar atampa na dora hijab iya gwiwa light pink ban shafa komai ba amma nayi kyau, bama yadda hancina ya kara tsayi sbd ramar da nayi.



Mimi dake kallona tace "Maa plz zan raka ki kinji"



Kallon ta nai kamar zanyi magana kawai kuma sai na ce zo mu tafi don nasan ba lallai mu hadu da Mr Wicked ba kuma ko mun hadu ai na dade wa zanba.



Jaka ta na dauka na chanja wa Mimi Kaya zuwa wata riga da wando na English wear sai hula dana samata tayi kyau sosai kamar ka sace ta, dafa kanta nai na Mata addu'a, juyawa nai nace "Umma mun tafi baxa mu dade ba Insha Allah"



Aisha ce ta fito daga daki itama sanye da Hijab tace "don Allah Ya Batul Nima zan raka ku yau dai naga ya university take."



Na bude baki zanyi magana Umma tace "ku tafi tare mana Batul"



Daga kai nai ina maka ma Aisha harara, dariya tai tana riko hannun Mimi sallama mukai wa Umma muka fito.



A bakin titi muka samu adaidaita, muna zuwa makarantar hall din da class rep dn yace azo a karbi test din muka nufa sai suruta Aisha take min tana fadin "Nima na matsu nayi na gama secondary dinnan Ya batul wallahi"



Tabe baki nai nace "meye na sauri ki nutsu ma ina fada Miki, ni baki ga yadda na rame ba"



Dariya tai tace"duk da haka wallahi Allah ma ya taimake ni Abba ya yadda nai jamb a SS 2"



Dariya nai nace "yarinya zaki gane kuren ki ne"



Muna hira har muka isa hall din, bamu dade ba na karbo mana nida Asma'u jakata na bude nasa, tsautsayi garin zuge zip din ya balle tsaki nai ina gyara zaman kayan ciki yadda baxa zu zube ba.



Mun iso daidai gurin da ake parking motoci idon Mimi ya sauka akan Azlan da yake sauri ya shiga ya tafi kasancewar family meeting suke kuma sai da Abie yai masa magana akan in ya kuskura yaki zuwa zasu hadu ne shiyasa yake sauri ya tafi dama Abu ya shigo dauka.



Cire hannun ta daga na Aisha tai ta kwasa da gudu ta nufi gurin sa tana fadin "Daddy oyoyo"



Wani irin faduwa gabana yai daidai lokacin daya juyo yana ganin Mimi ya bude Mata hannu da sauri, fadawa jikin sa tai a tare suka sauke ajiyar zuciya.



Dago da fuskar ta yai yace "Beauty na nayi missing dinki sosai"



Itama shagwaba fuska tai tace "Nima nayi missing dinka Daddy kullum sai na fadawa yan school dinmu nayi sabon daddy amma sai suce karya nake yi"



Shafa kanta yai yace "kyale su zanje har school din naku ai kina lafia"



Murmushi tai tace "eh Daddy kullum In nayi wa Maa maganar ka sai tace na daina mata maganar ka in ba haka ba saita Zane ni"



Zaro idonsa yai yace "ta zane min ke"



Dariya tai har hakworan ta na bayyana tace "ai ba duka na zatai ba Daddy, Maa bata duka na"



Shima murmushin yai mata yana jan kumatun ta.



Aisha data yi mutuwar tsaye cikin rawar baki tace "Ya Batul Mai nake gani waye wancen mai kama da Mimin mu"



Banxa nai Mata na nufi gurin su raina yana baci bansan wata masifa ke damun Mimi ba da inhar taga Mutumin nan take manta wa dani.



Azlan da yana ganin tahowar batul ya bude motar ya sa batul a gaba ya zagaya shima ya shiga driver sit hadi da kunna motar.



Cikin tashin hankali na shiga ihu ina fadin a taimaka min zai gudar min da yarinya ganin ba mutane a gurin gashi reverse yake hakan yasa ni janyo hannun Aisha na bude back sit na tura ta ciki nima na shiga.



Ihu nake masa a motar ina fadin ya bude mu mu fita amma yamin banxa kamar bana Jin sa, Mimi kuwa tuni ta sunkuya a kasa don kar na dake ta kuka kawai nake ina fadin "wallahi Ka bude mu in ba haka ba sai na kaika Kara police station"



Bai tsaya ko ina ba sai a compound din gidan baffa yana tsayawa ya zagayo ya bude ma Mimi kofa ya dauke ta cak ya nufi palourn baffa, da gudu na mara masa baya ina fadin "baxa ka tsaya ba"



Da kafar sa ya tura kofar ya shiga duk juyowa mutanen palourn sukai suka zuba masa ido sauke Mimi yai yana sauke numfashi.



Da sauri Baffa, Abie, Uncle Mustapha, Mami, Mummy, Mama, Aunty Sarah sai Junaid suka mike tsaye cikin rudewa ganin Mimi tsaye tana kallon su itama sai kuma ta rungume Azlan tana fadin "Daddy tsoro nake ji"



Da sauri nace "a gidan ubanki ya zama Daddyn naki Mimi"



A fusace Azlan ya juyo ya kalle ni yace "ban hanaki zagar min yarinya ba"



Fashewa na sake yi da kuka nace wallahi ba yarinyar Ka bace kuma Baxa ta taba Zama ba har abada.........















***