Yar mai gadi

Yar Mai gadi Chap 2

by @lariryatouaziz

CI GABAN LABARI…..
Daga inda inna take zawna tana hango duk me tahowa inda gurin bangaranta zai taho… dan tana zawne ne a filin tsarar gidan idan wata babar bishiya take kuma da akoy wasu shukokin a gurin irin su zogale, tunfafiya, da dai sawran su … 
Asiya ce tafe cikin wanan tafiyar tata kamar batayi… sai kace ba tafiya take bah koh tana tsoran taka kasar ne !!!
kyakyawar yarinya bafulltana usul…
fara fatt kamar ka taba jini ya tsarto idanuwan ta kamar na mage dan haka halittar ta take…
da akoy dimple a kasan gemun ta wanda koh batayi murmushi zakaga kullin ya dan lotsa…
    Tana karaowa cikin filin gidan rai a dan bace sai ta nifi dakin dake gefen in ka shigo cikin bangaren … saida ta kusa kaiwa sanan taji muryar wata dattijuwar matar tana ce :

 ¨ kaii Asiya lafiya kika shigomin bah koh Sallama sanan kin kama hanya zaki shigemin daki kamar naki ?? tsofuwar ta fada cikin daga muryar dan ba lalle yarinyar ta jiyota bah daga inda take …. HAJIA BAKURA kenan mamar usman da habib shekaru sun ja lokaci yayi tsayi !!!!!
  Asiya tadan jiyo tace Bakomai….
ta huce dakin bah tare da ta kara cewa komai bah .. … 
INNA tace toh yau kuma waya tabo ta kuma…
ta mike ta shiga dakin ta tarar da Asiya kwance kan daya daga cikin kujerun alfarman dake dakin . kaman bah dakin tsohuwa bah dan komai ah gare kuma cikin tsafta… bah wata hayaniya … 
kaii waii uban me aka miki kike kunbura baki kamar fulawa…. koh mamar kice ??? 
Asiya tace toh INNA  bah mama bace !!!!
INNA meye tayi miki…
kiji fah Ummy ce taban kaza da tamin alkawari shineh na tafi da kazar sashin mu ina zuwa mama ta karbe waii bazanci tunda na zama maya banda aiki sai na cin kaza … 
ta karasa maganar tana zubar da kwalla …😭😭 
INNNA tace Innalilahi Nashiga uku ni bakura waii Zahra’u me take son zaman ne ina ita ina hanaki cin abinda ranki yake so !!! koh ita ta siya miki ne ??? nace bah Ummy batace ta baki ?   
INNA ta fada cikin bacin rai da Rikici irin na tsufa… 
bari naje na karbo miki abarki tunda bah itace ta saya miki bah in kuma da kudin a ciki ta fada inji… yanzun nan nasa jikina a turomin na biya ta ….
INNA  ta sabi mayafinta ta huce ta fita cikin sawri kamar zata kifa … 
tana zuwa bangaran su Asiya koh sallama batayi bah tace … 
Zahra’u yaushe kika zama haka ehh … 
kaway yarinya nason abun sai ki hanata ci … 
Toh kodai Ummy da kudinki ta saya kaza??? 
tih tun muna shedar juna tafi dawkumin kazar nan ki bani !!!!
Mama. wace taji magar INNA kamar daga sama … kuma sai a sanan ta dago da kanta ta kwalli INNA tace   Tohh 
Dama plat din kazar na gefenta !! Ta mika hanun ta dawku sanan ta mikawa INNA  cike da ladabi 
dan tana girmana tsofuwar kamar ita ta haifeta… 
ah ranta kuwa tana saka irin fadan da zata yiwa Asiya idan ta shigo !!!!
kamar INNA  tasan me mama take sakawa ah ranta tace …
Kuma kar inji kar in gani kin mata wani abu waii shi fada !!!
Ta huce ta koma bangaranta …. 
 ah hanyar komawar ta ta hadu da baba Ali wato baban Asiya kuma mijin Zahra’u Rike yake da wasu file a hanunshi yazo fita da bangaren Ummy wato matar gidan…  
INNA  tace yawa Aliyu haidar dan Allah ka dinga yiwa matar kah fada ta daina takura Asiya …. 
kaga yan Ummy ce fah ta bata kaza kaway ta karbe waii ta cika mayta… 
Baba Ali yace Toh insha’Allah INNA yanzu sawri nake zai kaiwa Alhj sako bari na dawoo… 

Inna  Tace  toh !!!! 
tahuce ta shige bangarenta .. Tana zuwa ta mika Asiya plat din kazar tace 
 kuma wallahi karki batamin falo !!! 
kina gama cii ki kai plat din kichten sanan ki wanke..
 tahuce dakinta dan wanka zatayi… 
Asiya ta baje ta kama cin kazar nan kama bata taba cinta bah bayan bata  kwana biyu koh uku bata ci bah in Abban ta bai saya mata bah toh Ummy zata saya mata  kuma wani abun Ikon Allah bata cin wanda akai dafawa ah gidan sosai 
tafi ganewa ta sayar wa irin mai zafin nan…
Tanan gamawa ta shiga cikin kichten din ta wanke plat din ta koma falon ta kwanta sai barci …