FADIANA

Chapter 7: The stranger she already disliked

by @hauwajaywrites

Da misalin ƙarfe biyar na yamma, Rayyan ya fito daga office ɗinsa bayan ya gama wasu daga cikin ayyukan da suka dame shi tun safe. Ya gaji, amma duk da haka bai yi niyyar komawa gida kai tsaye ba


Ya shiga motarsa, ya kira Safiyya a waya tana ɗagawa ya ce “Where are you?”


“Home, zuwan zaka yi?”


“I’m coming over”


Safiyya ta yi murmushi tana kallon wayarta “Really, Habibi?”


“Unless you don’t want me to come”


“Who said that? Kazo kafin na canza ra’ayina”


Rayyan ya yi murmushi kafin ya katse wayar, bai ɗauki dogon lokaci ba kafin ya isa gidansu Safiyya, tana jin ƙarar motarsa, sai ta fito cikin farin ciki, sanye da doguwar riga mai kyau, fuskarta cike da murmushi


“Habibi!” ta kira shi tana tunkararsa


Rayyan ya buɗe hannayensa, ta ƙarasa wajensa. Ya rungume ta a hankali, yana sauke numfashi kamar kasancewarta kaɗai ta isa ta rage masa gajiyar ranar “You look beautiful” ya faɗa yana kallon fuskarta


Safiyya ta ɗan ɗaga gira “Just beautiful? Shikenan abun da zaka ce kawai?”


“Very beautiful” ya fad’i yana murmushi


“Better”


Ta ja hannunsa zuwa cikin gidan, tana masa dariya, suka zauna a main parlour, sannan ta kawo masa abinci can Ammah ta fito suka gaisa sannan ta wuce ciki, Rayyan ya ba ta labarin yadda wani ma’aikaci ya kusan ɓata masa wani important document a office


Safiyya tana dariya har ta riƙe cikinta “You need to relax Habibi, ba komai ba ne sai ka ɗauka da serious”


Rayyan ya kalle ta “Shi ya sa nazo nan ai, at least someone knows how to make me smile”


Murmushi Safiyya take yi, ta matsa kusa da shi, ta ɗora kanta a kafaɗarsa “ Kuma ina fatan ka san cewa a ko da yaushe za ka iya zuwa gare ni idan kana buƙatar wani abu”


Rayyan ya ɗauki hannunta, ya sumbace shi a hankali “I know, baby”


Sosai suka sha hira, can Rayyan ya kalli agogonsa “Ya kamata na koma, It’s getting late”


Safiyya ta ɗan yamutsa fuska “Already?”


“I’ll see you soon”


“Promise?”


“Promise, sweetheart”


Ta raka shi har ƙofar gida. Kafin ya shiga motarsa, ya ja ta kusa da shi, ya sumbaci goshinta “Take care of yourself”


“You too, nd don’t let work steal you from me”


Rayyan ya yi dariya “Zan kokarta”


Ta tsaya tana kallonsa har motarsa ta fice daga harabar gidan, ta koma ciki da murmushi a fuskarta, tana jin daɗin lokacin da suka yi tare


A gidansu Rahama, ana cikin shirye-shiryen tarbar baƙi ne


Dawowar Hajiya ƙasar ya zama babban abin farin ciki a both gidajen, Saboda kasancewar both familyn abokan juna ne na tsawon shekaru masu yawa kuma suna gudanar da kasuwanci tare, sai kuma ta ce a gidan Mammy zata sauka


Da suka iso, Mammy ta fito cikin farin ciki ta tarbe su, ta rungume Hajiya, suna musayar gaisuwa da tambayar juna halin da ake ciki


“Alhamdulillah Hajiya, Allah ya dawo da ke lafiya” Mammy ta faɗa cikin farin ciki


“Alhamdulilah kam ynx sai stress” Hajiya ta amsa


Sosai aka yi girki na musamman hakan yasa aka kawo different dishes, gashi d’an Hajiya da matarsa Mommy sun iso suma


Mammy ta kalli wajen ƙofar parlour kamar tana tsammanin ganin wani “Rayyan fa? Rameez fa? Ya bangansu tare da ku ba?”


Daddy ya girgiza kai “A’a, ba sa nan ai, Rayyan yana da aiki sosai a kwanakin nan, Rameez ma yana da nasa abubuwan”


Mammy ta yi murmushi mai ɗan nuna kewarsu

“Wlh rabona da ganin Rayyan ya fi shekaru biyu, har na manta sanda yake yanzu”


Daddy ya yi dariya “Zai zo ya gaishe ku ai, aiki ne kawai ya yi masa yawa, In Sha Allah zai samu lokaci ya zo”


“To, Allah ya yi musu albarka ya kare min su, ka gaishe min da su duka” Mammy ta faɗa


“Ameeen, za suji”


A lokacin suka fara jin sounds na saukan Rahama daga saman bene “Hey! Ina baƙinmu na musamman?”


Muryarta ta riga ta isa parlour kafin ita kanta ta bayyana, ta sauko tana gyara vintage ɗinta, amma da ta ga yadda kowa ya kalle ta, sai ta tsaya a stairs na ƙarshe tana murmushi


“Me ya faru? Kamar an ga wanda ya zo da report card ɗin da babu ko A a ciki”


Baba ya girgiza kai “Rahama ba zaki taɓa girma ba, yanzu kuma zaki fara ko?”


“Baba I haven’t even started”


Ta ƙarasa cikin parlour, ta gaishe da kowa cikin girmamawa, da ta zo gaban Hajiya, sai ta durƙusa ta rungume ta “Hajiya ta! Kin dawo amma ba ki kira ni ba, da na san kina zuwa, da na shirya special welcome party, wlh da kin ga yadda zan yi”


Hajiya ta shafa bayanta “Ke kuma, wace irin party za ki shirya?”


Rahama ta ɗago da fuskar nan tata mai ɗimbin fara’a “First of all, zan saka a yi girki iri-iri. Then a kawo cake, sai a sa ni a tsakiyar hotuna, because I’m the most important person in the house”


“Ke ce most important person?” Daddy ya tambaya yana dariya


Rahama ta juya gare shi da sauri “Of course Uncle, who else? Kai ne?”


Kowa ya fashe da dariya


Hajiya ma ta kasa ɓoye murmushinta, sai ta ja Rahama kusa da ita “Zo ki zauna nan, bari in ga ko za ki iya zama shiru na minti biyar”


Rahama ta zauna kusa da ita, ta ɗora kanta a kafaɗarta “Five minutes? Hajiya that’s too much to ask, even my silence has a time limit”


“Allah ya kyauta!” Hajiya ta faɗa tana girgiza kai


Rahama ta yi dariya, sannan ta miƙe don ta ɗauko abu, kafin ta tafi ta sake juyowa “Hajiya kina son tea ko juice? Ko kuma in kawo miki komai ki zaɓa?”


“Smoothie kawai”


Rahama ta ce “To as you wish, my queen” Ta yi salo kamar wata ma’aikaciyar gidan sarauta kafin ta fice, abin da ya sake jawo dariyarsu Daddy


Hajiya ta bi ta da kallo, murmushi a fuskarta ta san Rahama tun tana ƙarama, kuma ta saba da irin shirmen nan nata, amma duk da haka, wani abu game da ita ya sa tunaninta ya tsaya na ɗan lokaci


Yadda take karkatar da kanta idan tana son ta rinjayi mutum. Yadda murmushinta ke bayyana dimples dinta both su fito, har da wani irin salo da take yi da hannunta idan tana magana


Wani tsohon tunani ya gifta a zuciyar Hajiya, ta yi saurin kawar da shi, ta mayar da hankalinta ga hirar da ake yi


Bayan an ɗan daɗe, Rahama ta koma kusa da Hajiya da plate ɗin kayan ciye-ciye a hannunta


“Hajiya ki ɗan ci. Kina buƙatar energy saboda zan dami kowa yau”


Hajiya ta kalle ta “Kin riga kin fara damun mu tun kafin ki kawo abincin ai”


Rahama ta yi dariya, ta zauna a ƙasa kusa da kujerarta “That’s love Hajiya, idan ban dame ki ba, taya ya zaki san Ina sonki?”


“Toh ki tashi ki zauna a kujerar can kafin in sa a kore ki daga nan”


Rahama ta ɗaga hannayenta sama “Kash! Babu buƙatar ki yi mini barazana a gaban baƙi na”


“Guests ɗinki kuma?” Baba ya tambaya


“Baba plsss let me enjoy my moment”


Hajiya ta kama hannunta kafin ta sake yin wani shirme “Okay zauna ki ci fruits, ba sai kin yi wa kowa magana ba”


Rahama ta yi shiru na ɗan lokaci, ta fara cin kayan ciye-ciyen. Amma bai wuce minti biyu ba ta karkata ta rada wa Hajiya wani abu da ya sa ta girgiza kai tana dariya


Duk wanda ya san Rahama ya san ba ta iya zama cikin natsuwa na dogon lokaci. Duk da haka, ba ta rasa girmamawa ga manya ba. Ta san inda za ta yi wasa da inda ya kamata ta nutsu


Hajiya ta kalle ta a ɓoye, tana jin wani irin kusanci a zuciyarta wanda ta kasa bayyana dalilinsa, ta san yarinyar, amma wani lokacin wasu halayenta suna tayar mata da tsoffin tunane-tunane


Sai dai ba ta son ta yi saurin yanke hukunci


Ta ci gaba da hirarta da Mammy tana ɓoye abin da ke zuciyarta


Bayan an gama cin abinci, wasu daga cikin matasan familyn suka zo ma Hajiya sannu da zuwa kafin ta koma gidan d’anta, suka taru a wani other parlour, Rahama tana neman wayarta ne lokacin da ta ji ana maganar wani mutum mai suna Rayyan


“Haka yake fah, ai Rayyan ba ya son a yi masa gardama” wani daga cikin samarin ya faɗa “Idan ya yanke shawara, sai an bi yadda ya ce”


Wani ya yi dariya “Shi fa yana ganin komai sai an yi shi his way. Kuma idan ya yi fushi, sai ka ji kamar kai ka jawo masa matsalar duniya sbd yadda zai sauke maka su”


Rahama ta tsaya da wayarta a hannu, tana sauraron maganar ba tare da sun san tana kusa ba


“Seriously?” wata yarinya ta tambaya “Ashe haka yake?”


“Ki tambayi duk wanda ya san shi. Mutum ne mai son komai ya tafi yadda yake so”


Rahama ta ɗan ɗaga gira Oh, really? Another one of those men who think the world revolves around them


Ta koma kujerarta, ta ɗauki wayarta tana tunanin abin da ta ji


Ba ta taɓa zama da Rayyan ba, balle ta san halinsa da gaske, amma maganar da ta ji ta riga ta zana wani irin hoto a zuciyarta


“Allah ya kiyaye ni da irin waɗannan mutanen” ta faɗa a hankali “A haka shine Mammy ke damuwa baya zuwa gaisheta?”


Cousin dinsu da ke kusa da ita ta juyo “Wane irin mutane?”


Rahama ta gyara zamanta “Mutanen dake tunanin ko da yaushe sune suke kan gaskiya, you can’t even breathe around them without asking for permission”


Cousin ta yi dariya “Ba ki ma san shi ba fa”


“Exactly! Kuma na riga da naji ba zan so sa ba”


Ta ɗauki abin shanta, ta sha kaɗan

“Idan mutum yana son komai ya tafi yadda ya ce, ai sai ya zauna shi kaɗai. Ni ba zan zama punching bag na wani ba”


Cousin ta sake dariya, amma Rahama ta ɗaga kafaɗunta kawai


A zuciyarta, ta riga ta yanke shawara cewa ba za ta taɓa jituwa da irin wannan mutumin ba


Da daddare, baƙi suka fara shirin tafiya, bayan an yi sallama, gidan ya yi shiru ba hayaniyar mutane, Rahama ta koma ɗakinta, ta cire hijab ɗinta, ta zauna a gefen gado tana duba saƙonnin wayarta


Wayarta ta yi ƙara, da ta ga sunan Baba a screen, ta ɗauka


“Hello, Baba”


“Rahama, kina ɗakinki?”


“E Baba what’s up?”


“Na kira ne in sanar da ke cewa tafiyarki Lagos za ta kasance next tomorrow, In Sha Allah. Ki fara shirya kayanki tun yanzu, kar ki bari sai gobe da dare ki ce zaki yi”


Rahama ta gyara zamanta “Next tomorrow? As early as that?”


“Eh workshop ɗin na kwana biyu ne ba wani kaya zaki dauka ba, ki tabbatar kin shirya komai da wuri kuma”


“To Baba, zan shirya”


Baba ya yi ɗan shiru kafin ya ci gaba “Sannan akwai wani abu da nake tunani. Ina son in haɗa ki da wani, ke kadai ba zai zo miki da sauki ba, amma zan yi miki bayani dalla-dalla idan muka samu lokaci”


Rahama ta daure fuska “Wani mutum kuma Baba? Who is he?”


“Ki yi haƙuri, zan yi miki bayani ba wani abu ne da za ki damu da shi yanzu ba”


Ta yi shiru na ɗan lokaci, tana ƙoƙarin fahimtar abin da yake nufi “Okay Baba, whatever you say”


“Allah ya yi miki albarka, ki kwanta da wuri”


“Aminnn! Good night Baba”

“Good night, my daughter”


Bayan ya katse wayar, Rahama ta kalli screen ɗin na ɗan lokaci, wani mutum? Hada ni da shi don me?


Ta kwanta a kan gadonta, ta ɗora wayarta a ƙirjinta “Bari dai in je Lagos tukuna, Maybe it’s nothing serious”


Sai ta tuna da wani abu, ta zauna da sauri

“Wait! Zan je Lagos, kuma har yanzu ban shirya snacks ɗin tafiyata ba?”


Ta miƙe ta buɗe wardrobe, tana ta magana ita kaɗai game da kayan da za ta tafi da su da abubuwan da za ta saya kafin tafiya


Mammy data zo wuce wa ta corridor ta ji muryarta tana magana ita kaɗai, sai ta yi murmushi “Allah ya shirye ki, Rahama”


Hajiya ta kwanta tana tunanin abubuwan da suka faru a ranar


Tana son Rahama sosai tayi shiru ta nutse cikin tunanin daya addabeta, sosai ta manta inda take har sai da wani abu game da ita ya sake tayar mata da wani tsohon tunani


Everything about her sosai yake bata mamaki, gashi dai tun lokacin data san Baban Rahama har sanda suka haife ta bata ji wata magana ba, hakan yasa as babba bata son fara wani magan


Hajiya ta lumshe idanu, me ya sa nake tunanin wannan yarinyar yake damunta ne?


Ta juya a kan gadonta, tana ƙoƙarin kawar da tunanin


Ba ta da wata hujja da za ta sa ta danganta abubuwan biyu. Kuma ba ta son ta bari zato ya rinjayi hankalinta


Sai dai duk da ƙoƙarinta, tunanin ya ƙi fita daga zuciyarta


A ƙarshe, ta buɗe idanunta ta kalli rufin ɗakin


“Ya Allah, ka yaye min wannan tunanin daga zuciyata” Ta lumshe idanunta a hankali