Chapter 35
by @umsar
WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
YOUNG TELENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA)
@umsarArewapen
Wattpad: Umma Mustapha
PAGE 35
Nihla tana gama waya dashi, toilet ta shiga ta yi brush. Tana fitowa, Hafiz ya shigo ɗakin.
"Ya dai, yar Yar Jami'a kin tashi?"
Nihla ta yi murmushi, ta kai masa ɗan duka, amma ya yi saurin kaucewa.
"Ke! kin rainani fa saboda kin ga ina miki wasa ko?"
Dariya ta yi, gami da harararsa, sannan suka juya gaba ɗaya zuwa falon.
Baba Jummai ta gani tana ɗan aikace-aikacenta. Ta risina ta gaida ita, sannan ta gaida sauran mutanen gidan da ta tarar a falon. Wasu daga cikinsu ma sun riga sun fara karin kumallo.
Sai dai ba ta ga Hajiya Mama ba.
Kallonta ta mayar kan Hafiz.
"Ina Hajiya?"
"Hajiya ba ta fito ba. Ciwon ƙafarta ne ya tashi, tun jiya da ta yi zaman mota. Kar ki tasheta, ta sha magungunanta ta samu bacci."
Nihla da ke ƙoƙarin zuwa wajen Hajiya, sai ta dakata.
Dawowa ta yi ta zauna. Ta ɗauki kofi ta zuba kunu da kosai. Yana daga cikin abubuwan da take so, don haka ta ci sosai har sai da ta ji ta ƙoshi.
Bayan ta gama, ta koma ɗakinta. Ta shiga wanka, ta fito ta shirya cikin riga da siket na atamfa. Tana zaune a gefen gadonta tana saka safa a ƙafarta. Da ta gama, ta koma falon.
Zuwa lokacin Hajiya Mama ta fito. Tana zaune tana kallon Sunnah TV. Kusa da ita Nihla ta zauna tare da yi mata ya jiki.
Tare suka ci gaba da kallon talabijin suna ɗan taba hira. Nihla tana ɗan matsa mata ƙafafunta, tare da ba ta labarin makaranta da abubuwan da suka faru tun bayan tafiyarta.
Hajiya kuwa tana saurare cikin kulawa, tana yi mata tambayoyi a tsakanin zancen.
Nihla ta ji wani irin daɗi da ta sake samun kanta a cikin yanayin gida. Zaman da tayi da Hajiya ya ɗan kawar mata da tunanin da ya addabe ta tun daren jiya.
Suna cikin wannan hirar ne lokacin sallar Azahar ya yi.
Nihla ta nufi ɗakinta domin yin alwala da sallah.
Tana Shirin shiga dakin, ta hango Jafar ya fito daga nasa ɗakin, kamar mai shirin zuwa masallaci.
"Ya Jafar, dama kana gidan nan? Na yi tunanin ka tafi kasuwa."
Jafar ya yi murmushi kaɗan.
"Yau ba inda na je. Ba na jin daɗi ne. Maganin mura na sha, ya kashe min jiki."
"Ayyah sannu. Allah Ya sawwaƙe."
"Amin."
Daga nan Jafar ya fita, Nihla kuma ta shiga ɗakinta. Hajiya Mama ma ta riga ta tashi daga falon.
Nihla ta yi alwala, ta yi sallar Azahar. Bayan ta idar, ta ɗauki wayarta.
Da ta kunna screen ɗin, sai idonta ya sauka kan missed calls uku daga Irfan.
Zuciyarta ta ɗan buga.
"har 3 miss calls?"
Nan take ta ji wani irin sha'awar kiransa ta taso. Ta buɗe lambar, yatsarta ta kusa danna maɓallin kira, amma sai ta dakata.
"Wataƙila yana masallaci yanzu. Bari sai an jima na kira."
Ta ajiye wayar, ta ɗan zauna tana kallon screen ɗin kamar tana Neman Wani Abu a jikin wayar.
A ƙarshe ta miƙe ta fita falo.
Ta tarar da Jafar yana zaune a kan kujera. Ta wuce kai tsaye zuwa kitchen, ta ɗauko musu abinci-tuwon semo da miyar kubewa.
Ta kawo ta ajiye a gaban Jafar, sannan ta samu wuri ta zauna.
Jafar ya ɗauki cokali ya fara cin abincin. Ita ma hannu ta saka a cikin abincin, ta fara ci, A hankali tunanin Irfan ya fara fizgarta, wayar da ta danyi dashi dazu da safe ta fara dawo mata.
"Tunanin me kike yi haka?"
Jafar ya katseta.
"Ba komai, Ya Jafar."
"Ke dai faɗi gaskiya. Ko dai kinyi saurayi ne, ba mu sani ba?"
Sai da gabanta ya faɗi. Da sauri ta girgiza kai, har tana kwarewa da abincin da take ci.
"Ah-ah, Yaya Jafar, ba..."
Ba ta samu damar ƙarasa maganar ba, tari ya sarketa.
"sannu" Jafar yay saurin fada, gami da Mika mata ruwa
"Karɓi ruwan ki sha."
Ta karɓi ruwan ta sha, amma idanunta sun riga sun yi ja saboda tari.
Da mamaki Jafar yake kallonta. Yadda maganar saurayi kawai ta jefa ta cikin wannan yanayin. Har ma abin ya ɗan ba shi dariya ganin yadda gaba ɗaya ta firgita.
Haka dai suka kammala cin abinci. Nihla ta gyara wurin da suka ci abincin, sannan ta shige cikin ɗaki tana sauke numfashi.
A zuciyarta, kalmar Jafar na ta dawowa:
"Ko dai kinyi saurayi ne, ba mu sani ba?".
Umsar ✍️