HABIBULLAH

Shafi na daya

by @queenmeemi

Reposting

🌻 *HABIBULLAH* 🌻  
[4:59pm, 19/04/2016]  

☁️ *HABIBULLAH* ☁️  
*By*  
Queen meemi bashir  
NWA  

◆ 1 ◆  

Sauri ya ke yana kulle d'an A kurkin d'akinsa, wanda ya ke tamkar shago, ba komai ne aciki ba, in ban da kayansa da wata jemammiyar katifa, gefe kuma ga wata Akwati duk ta fita hayyacin ta, hannunsa ne ke ta rawa saboda tsabar yunwar da ya ke ji, da k'yar ya samo muk'ullin k'ofar d'akin ya janyo d'akin yana k'ok'arin rufewa.  

"Habib! habib!! habib!!! ya ji ana ta k'wala mai kira,juya wa yai ya tsaya yana kallon mai kiran ,ya san dama za'a rina, nan da nan jikinsa ya kama rawa, dama ga yunwa nacinsa hakan ya sa ya dad'a rikicewa don yasan kwanan zencen. 

Da zuwansa ya ce:  
"Habib nai maka ta marmari nai maka ta arziki, amma kak'i ka ban kud'in hayar ko? to yau zan maka ta tsiya, ba ni kud'ina, ko ka tattara ko matsanka kai gaba ina sauraronka."  

Tsugunnawa Habib yai yana rok'on Malam Habu akan ya k'yaleshi, amma fafur ya bud'awa idonsa toka ya ce sayya bashi kud'in sa,habib ya rasa me ke masa dadi sai dawurwura yake yana caje aljihunsa, wata yagaggiyar Naira d'ari biyar ya zaro a aljihun wandonsa ya mik'a mlm habu, shi kuwa ya Juyar dakai fuskar nan a tamke, cikin in ina habib ya ce:  

"Malam Habu dan girman ALLAH da Annabi ka karb'a zan ciko maka dubu d'aya da d'ari biyar d'in, shago zan tafi ko Allah yasa a dace. 

Tausayinsa ne ya kamashi, ta yanda yaga hannunsa na rawa, ga idanuwansa sun fada sunyi zuru -zuru sai layi yake tamkar zai fadi. 

malam habu ya Karb'a ya danna a Aljihunsa ya ce:  
"Allah ya soka yan tausayin sun bijiromun  amma Zan kuma biyowa."

A sanyaye ya kalli gabas da arewa, siririn hannun sa na rawa, tamkar wanda baya ganin gabansa saboda yunwar dake cinsa, hanya kawai ya mik'a yana tafiya,kana ganinsa kaga yunwa na cinsa, dama naira d'ari biyar d'in ya ke saran ya sai abinci da ita na dari biyu sauran canjin ya sai littafin makaranta. 
Amma ga abinda ya faru,siririn tsaki ya saki ya na tafe yana tunani.

Wucewa yai ta shagon Sauk'i kansa a sunkuye, k'wala mai kira Ado sauk'i yayi ya ce:

"Malam HABIB ina zuwa haka?."
Cikin halin rashin son yin magana ya ce:

 "Wallahi za ni kasuwa ne ko dako na d'auka" 

Dariya Ado sauk'i yai "haba dai! ai kafin ka kai bakin titi ka fad'i,bari kaga,nan ya juya ya d'auko mai wani ragowar d'umame na jallof rice da pure water d'aya.
ya bashi
  Da sauri ya karb'a, siririn hannunsa kamar ba zai iya rik'e ruwan ba.
Cikin mintuna k'alilan ya tashi da Abincin, godiya yayi ta masa cike da jin dad'i.

Da k'arfinsa ya tashi ya doshi bakin titi, tafiya yake da cikin tunanin mai zai samu a kasuwar sauri kawai yake zubawa,haka yayi ta
tafiya har yaje kasuwa inda yayi buga- bugarsa, dakon ma da k'yar
ya samu d'ari biyu, haka ya kuma biyo hanya da k'afa ya koma a kurkin dakinsa.

Zamansa keda wuya kan shafaffiyar katifarsa,sai ga shigowar wani
Saurayi mai suna Aleb'una ya zauna gefen katifar ya ce:

"Kai HABIB baka da d'an Abinci?."

"Da zan samu ma a gunka ai da na ji dad'i," ya fad'a yana mai kallonsa.

Gari fa yaci wuta, ban da ko sisi fa cewar aleb'una yana doka hamma.

Murmushi Habib yayi ya ce:

"Kaima kenan ballantana ni." Yana fad'a ya tashi ya d'auko buta ya fita waje  Ya tsugunna fara Alwala.

Ganin hakan ya sanya Aleb'una ya ce "to ni bari na k'ara gaba, dan 
nasan inka fara sallah har se nai bacci baka gama ba".

 HABIB yace" kaima kazo kayi."

"Kai k'yaleni, ta isha'i ma banyi ba."

Habib yace" kai Aleb'una adinga tuna LAHIRA fa,Sallah haske ce kuma babbar Ibada,domin SALLAH wajibi ce, itace farkon aikin da ake fara tambayar bawa ranar gobe k'iyama."

Aleb'una ya sosa k'eya. "kai dad'ina da kai da Mutum ya zo sai ka
hau Yimai wa'azi, ai kawai ka share ba Akwai ISTIGFARI ba."

"Haba Aleb'una, Bawa yana mantawa ne amma bai san Ranar mutuwarsa ba, ayanzu anjima, ALLAH ne masani, to idan bakai sallar ba Ayanzu Allah ya d'au ranka mai zakacewa Mahaliccinka?."

  Jikinsa ne yai Sanyi, "to godiya nake, bara na zaga gida na rama Sallolin."

Habib ya ce; 

"Allah yasa ya kuma shirye ka."

       
Alebuna ya daga masa hannu yana dariya.

***