GADON ZINA

7-8

by @oumhairan1

Juyi kawai Simah take yi saman katifar abin duniya yayi mata zafi inda hudah ke danna Wayarta hankali kwance ba tare da wata damuwa ba tuni ta cire damuwar halin gidansu da rayuwar mahaifiyarsu a rai tun suna ƙananu suka taso ana musu gorin yayan karuwa  da suka fara girma kuma kalmar ta canza daga yayan karuwa zuwa karuwai a unguwar tasu gidan mata ake kiran gidansu domin kuwa tunda suka taso basu ga wani namiji daya jiɓanci lamarin rayuwarsu ba daga su sai mahaifiyarsu Da akewa laƙabi da Hadiza karuwa suke rayuwa, Numfasawa tayi tare da yin kasaƙe kamar tayi bacci daidai lokacin da ta ji motsin tafiyar mahaifiyarsu ta sake lafewa a katifar mama ta leƙo tace “Huda wai Simah bata dawo ba har yanzu?" kallon inda Siyamah ke kwance tayi tace “Gatanan ta dawo tana ƙuncin rai kamar wacce akayiwa saƙon mutuwar ki" takawa tayi ta isa kusa da Simah ta zauna a gefenta Simah taja baya da sauri abinda yasa suka kalleta gabaɗaya ta tashi kamar wadda aka tsikara ta nufi hanyar da zata bar da ita ɗakin kiran sunanta Mama tayi ta ja ta tsaya cik ta taso ta iso gabanta ta kamo hannunta ta janye Hajiya Hadiza ta saƙale hannunta a ƙirjinta tace “Kullum ƙara fito min da kalarki kikeyi Siyamah Bana son mu shata layi dake kamar yanda muka shata da ubanki da dangin ubanki Wlh Tallahi akan ra'ayina idan kikace zaki yi jayayya Dani zan iya tsine Miki......" 
Da sauri ta dago ta kalli mahaifiyar tasu ta durƙushe ta rushe da kuka tace “Wlh mama na kasa sabawa da abinda kikeso nayi duk da cewa Nasan abinda yafi dacewa Dani kenan domin gadonsa nayi amma kuma inada zaɓi akan rayuwata bawai komai ne don ya zama gado na zai zama zaɓina ba Mama ina bada kaina a guraren daya zame min dole don neman mafita ko don gujewa wulaƙanci amma na kasa saba bada kaina don neman kuɗi a duk lokacin da wani namiji ya huta da wani sashi na jikina ya samu Nutsuwa nakan fice ba tare da na tsaya na karɓi tukuicin aikina ba kuma bana yi don jin daɗi, Please kar ki ƙarsa lalatani da bakinki na rantse da Allah Indai zama karuwa shine abinda zai faranta Miki to daga yau nayi Miki alƙawarin na karɓi lasisin saidai kuma shiga ta cikin harkar da gaske zai iya zamowa nadama a gareki a lokacin da Tuba yayi mana nisa, sannan ina roƙonki ki sanar Dani dalilin da yasa kika zaɓi muyi GADON ZINA maimakon gadon iliminki kika zaɓi dole sai mun lalace mun amsa sunan da muka taso mukaji ana kiranki dashi na Hadiza karuwa?"
Wani hawaye da kullum sukayiwa uwar tasu tambaya makamanciyar wannan take sharewa yau ma su ta share ta juya ta nufi kofar barin ɗakin tace “Ki shirya akwai wanda yayi order ki yau ya Turo da rabin kuɗin da na yanka masa 300k saura 300k idan bakiyi masa halin baki Bama zai iya cikasa Miki ya zama 1M  Bayason ɓata lokaci na faɗa masa 8:30pm yazo kin zama ready" Tana faɗin haka ta fice itama Simah ta tashi cike da kasala ta shiga bathroom ta sake sakarwa kanta ruwa tayi wanka da manyan Sabulan da mama take siya musu ta fito ta zauna ta ɓata lokaci wajen shafe shafen mayuka turaruka ta dauko wasu matsiyatan riga da wando masu kyau ta saka abinka da dirarriyar mace suka zauna das a jikinta ta haɗe gashinta me tsayi yawa da ƙyalli ta ɗaure da ribbon guda ɗaya ta kama tayi donut dashi ta fesheshi da turare ta dauki wata hula hana sallah ta saka daidai lokacin Mama ta shigo da wani cup a hannunta ta miƙa mata sarai basu da ikon musu da umarnin da wannan ta karɓa ta shanye tsumin maganin ta miƙa mata cup ɗin tayi mata Murmushi tace “Yana jiranki a ƙofar gida"