BA NI DA MADOGARA

Chapter 25

by @narrnarhhbukar00

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*













*Ba ni da Madogara*
  (Sai Allah...)




 025

Lokaci guda ya tsagaita da dariyar kamar ɗaukewar ruwan sama. Cikin wata iriyar murya mai matuƙar firgitarwa ya fara magana da cewa

"Inaaaa!!!  Idan mu ka yi aiki bama warwarewa! Tun farko sai da muka gargaɗeki akan kar ki mallakesa akwai tashin hankali da bala'i a cikin auran amma kika ce kin ji kin gani kin yarda za ki aurasa! To me zamu yi miki yanzu!!! Kar ki ɓata mana rai, maza ki bar wurin nan tun kafin fushinmu ya sauka akanki!!! "

Cikin rawar jiki Zaliha ta miƙe tabar gidan,tafiya take tana zubda ƙwalla, akai-akai take share wa wanda hakan bai hana wani sabon hawayen fita daga gurbin idanunta. Tare mai mashin ta yi ta hau,cikin ƙwarin ɗan dodo ta umurcesa ya kai ta, babu  ɓata lokaci ya wuce da ita gidansu. Bayan ta sallami mai mashin ta shiga ciki. 

Zaune  innar Zaliha da Baraka  suna tsintar shinkafa cikin matankaɗi kusa da  bishiyar mangoro, sauran yaran suna kusa dasu suna wasa. Sallamar Zaliha suka ji cin sayin murya wanda hakan  yasa Innar Zaliha saurin ɗagowa tana bin ta da kallo, da gudu yaran suka je yi mata oyoyo, ɗaukar ɗaya bayan ɗaya ta yi sannan ta wuce ɗakin inna, tsam inna ta miƙe zuwa cikin ɗakin don a yadda Zaliha ta shigo gidan fuskarta shimfiɗe take da damuwa. Koda ta shiga sai ta samu Zaliha ta zuba uban tagumi hawaye na mata zirya a ido. 

"Zaliha wai meke damunki ne kwanan nan, tun lokacin da Ɗahiru ya rasu kika sukurkucewa, kika kowa wata iriya da ke, Kin bi kin lalace kin rame"  faɗin inna tana ƙarasowa cikin ɗakin tare da zama kusa da ita. 

"Inna na gaji da auran nan,wallahi na gaji, bana sonsa inna, a dalilin auransa ne fa  Ɗahiru ya rasu, Ni wallahi na gaji" cewar Zaliha tana yakice gyalen da ta yafa. 

"Faɗin Hausawa da suke cewa abin da babba ya hango ko yaro ya hau sama ba zai hango ba. Tun farko ni, Murja da kawunku Isa har da Mallam Tani mun guje miki auran Zakari amma kika ƙi, ba auran ba matsalar da ke cikin auran shi ne abin dubawar. Boka ya ce akwai bala'i a tattare da auran, amma kika ce Eh za ki auresa a haka har kina neman maganin mallaka. To ai ga irinta nan tun ba a je ko'ina ba kin fara shiga damuwa haɗi da tashin hankali" cewar Inna wacce ita ma fuskarta akwai damuwa domin tun lokacin da Malam Tani mai allon ƙarfe ya faɗa akwai matsala a auran ta karaya. Ta so Zaliha kar ta auri Alhaji Zakari amma Zaliha taƙi, ita a tafau babu wanda take so sai shi. Wasu zafafan hawaye Zaliha ta share sannan ta ce

"Inna don girman Allah ki saka baki mutumin nan ya sakeni, wallahi na tsanesa kamar yadda na tsani ranar mutuwata" 

Sauke ajiyar zuciya inna ta yi sannan ta ce

"Zaliha banda abin taimaka  miki a yanzu, don tun farko sai da na guje miki auran Zakari amma kika ƙi, to ya kike so na yi, yanzu ai hukunci baya hannuna, wurin mijinki za ki koma ki yi yadda zai rubuta miki takardar saki" 

Waro idanu Zaliha ta yi waje tana faɗin

"Inna mutumin da ya zauce akan so da ƙaunata zai rubuta min saki, asirin fa ya yi matuƙar tasiri a jikinsa, kinga ai ba zai ma fara amincewa ya rabu dani ba, Ni dai ko baba ne ki mishi magana ya umurci Zakari ya sakeni wallahi na tsanesa" 

Wani dogon tsaki Innar Zaliha ta ja tana cewa

"Wallahi Sai yau na tabbatar da baki da hankali Zaliha, wato Babanki ne kike tunanin zai saka Zakari ya sakeki saboda kin maida shi mutumin banza ko?  Aka ce miki shi Zakarin bai san me yake yi ba ne, to wai baza ki koma gun Malam Tani daya miki aiki akan Zakari ya karya ba"cewar Inna. 

Wata nauyayyar ajiyar zuciya Zaliha ta sauke tare da cire tagumin da ta yi tana duban Innarta da cewa

"Hmmmm dawowana ke nan daga wurinsa inna, ban so kika san naje ba" 

"Ya karya asirin ne yanzu?" cewar Inna 

"Ina fa Inna! Hayayyaƙo min ya yi kamar zai dukeni" cewar Zaliha

"Duka kuma!" Inna ta yi maganar cike da mamaki. 

"Yooo duka mana, wai su idan su ka yi aiki basa warwarewa, ai tun farko sun gargaɗe ni naƙi, don haka na tashi na bar musu wuri tun kafin fushinsu ya sauka a kaina" 

Waro idanu Inna ta yi waje tare da riƙe haɓa. Sai jinjina kai take tana faɗin

"Eh lalle kam! To ai ni ban ga laifinsu ba tun da tun farko sun gargaɗe ki amma kika ƙi sauraronsu" 

Turo baki Zaliha ta yi gami da ƙunƙuni tana cewa

"To to shi idan ya kasa warwarewa, zan sake zuwa wurin wani malamin nasan zai iya warwarewa" 

"A'a Zaliha zuwa wurin bokan ya isa haka, ke baki ga ishara a gun ƴar uwarki Murja ba ne, ce nike duk boka ɗaya ya yi muku aikin, kuma ya ce bai zai warware ba, haka ta yi ta yawo gidan malamai da bokaye akan a warware asirin Jabiru ya samu lafiya amma kowa ya kasa. Ni dai shawarata ki yi haƙuri ki rungumi mijinki ki zauna da ƴan gidanku lafiya, don aikin gama ya gama, karki ɓata kuɗinki gun malamai a banza, don na fahimci duk shirme ne, nima sai yanzu nake yin da na sanin zuwa wurin bokaye a lokacin mu. ki koma ga Allah Zaliha, tunda kin riga da kin bar gini tun ranar zane, sai ki yi haƙuri " cewar Inna. 

Wani malolon baƙin ciki Zaliha ta haɗiye a ranta tana faɗin 'Haka kurum na zauna a kashemin yarana ban ji ban gani ba, zuwa wurin boka yanzu na fara inna, naga lokacinku kin sha zuwa wurin boka kar baba ya ƙaro miki kishiya, sannan yanzu da kika tsufa kika tuba, to nima haka zan yi idan na tsufa zan tuba amma yanzu na fara zuwa wurin boka wallahi'  katse mata tunani inna ta yi da cewa

" Baki ji magana ta ba ko Zaliha, Kin yi shiru alamu baki yi na'am da abin da na ce miki ba ko Zaliha?" 

"Na ji inna, zan yi yadda kika ce" faɗin Zaliha amma a cikin ranta ba haka  ba ne. Miƙewa Inna ta yi tana faɗin

"Ki tashi ku wuce gida kar dare ya muku a hanya" tana faɗin haka ta fito tsakar gida inda ta baro Baraka tana gyaran shinkafa. Ta yi kusan mintuna goma tana saƙa da warwara daga bisani ta miƙe tare da yafa gyalanta ta fito, ce ma Baraka ta je ta ɗauko hijabinta da takalman ƙannanta a ɗaki, da gudu Baraka ta ɗauko ta fito, tsaf! suka shirya tare da yi wa Inna sallama suka bar gidan. Sun Ko ci sa a mai mashin ya zo gittawa suka tare shi sannan suka hau. Babu ɓata lokaci suka doshi kwanar faru ƙwai. Basu suka iso gida ba sai wurin magrib,kai tsaye Zaliha ta wuce da yaran ta sashenta. 

A daren ranar Alhaji Zakari sai da ya zo amsar hakƙinsa amma Zaliha taƙi yarda haka ya haƙura ya koma sashen Hannatu. Bacci ya ƙi ziyartarta sai juye-juye take a saman gadon, tana neman ma kanta mafita amma ta gaza samu, bayan haka ta ɗaukar wa kanta alƙawarin ko Murja ba za ta san sirrinta ba tun ita ma son kanta take. Haka ta yi ta tunane-tunane daga bisani bacci ya yi awon gaba ita ba tare da ta ankara ba... ✍️

          🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Washe gari*
*ƙarfe 8:12am na safe*

A daidai wannan lokacin Kakulle ta shirya ita da fatsima zuwa bikon Hannatu Giwa. Bada mammin Hujayrah za a ba saboda lalurar mijinta dole ta zauna tare dashi. Har bakin ƙofa mammin Hujayrah ta rakosu sannan ta koma ciki, har ta kusa isa ƙofar sashenta ta ji Murja na kiran sunanta. Tsayawa ta yi tare da juyowa tana jiran ta iso wurin. Tafiya mai cike da taƙama haɗi da izza Murja ta shiga yi har ta ƙaraso inda mammin Hujayrah take. Babu gaisuwa Murja ta dubi mammin Hujayrah ƙasa da sama sannan ta ce

"Jiya sai na ji Innayi na faɗin za ta je bikon Hannatu ita da Fatsima?" 

"Eh Innar Balki, sai kuma aka yi me" ta yi maganar tana tsare da manyan idanunta, tabbas Hujayrah mahaifiyrarta ta gado wurin manyan idanu sai dai ita mammi nata ƙwayar idon baƙar ce kamar ba kowa ba kamar na Hujayrah wacce ta kasance  kore ba. Taɓe baki Murja ta yi sannan ta ce

"Sai kuma aka yi komai Zaytuna, Hmmmmm kifi na ganinka mai jar homa, Ina sane da abin da kuke yi Zaytuna, wato kun haɗe kai da Hannatu kun dawo kuna bina da sharri ko"  

Mamaki ne ya cika mammin Hujayrah, cikin ranta tana faɗin 'Jahilci bai yi ba wallahi' sai kuma can ta ce

"To me kike so mu yi uwarmu? Ina ruwanki da sasancin da muka yi, sannan mu bama bin ki da sharrin, Ni ban da lokacin wannan jahilcin, idan ke baki da ra'ayin mu zauna lafiya ai sai ki ƙyale wacce take muradin haka, Ni kina ɓata min lokaci na bar mijina shi kaɗai a ɗaki" 

Tana gama maganar ta juya zuwa ƙofar sashenta. 

"To ku shirya yaƙi da Murja domin bana yafiya! karan batta dani babu daɗi! kamar yadda kuka yi sanadin ɗana ya koma mahaukaci to na rantse da izufi dubu saina rama, saina illata yaran ku! " 

Har mammin Hujayrah ta buɗe ƙofa za ta shiga ciki sai ta tsaya cak! Tare da juyowa cike da mamaki don ita bata san Jabiru ya haukace ba. 

"Allah sarki ai ban san Jabiru ya haukace ba, to Allah ya bashi lafiya da sauran marasa lafiya.Ni Zaytuna bama nufin ɗan kowa da sharri, a duk sallah idan na kai goshina ƙasa ina nema wa yaran kowa shiriya. sannan abu na ƙarshe da zan faɗa miki, shawara ce Innar Balki idan kin ɗauka ta yi miki amfani, idan kuma baki ɗauka ba ni dai ƴar kallo ce. Ki sani Innar Balki idan mutum zai gina ramin mugunta to ya ginashi gajere domin idan bai yi wasa ba watan wata rana shi zai faɗa, sannan ki sani shi sharri da kike ganinsa ɗan aike ne, komin daran daɗewa zai dawo wa mai shi. Duniya makaranta ce mai ɗauke da aji-aji mabambanta, Innar Balki ina guje miki duniya, kibi ta a sannu, kullum tsufa muke ya kamata ki san da haka amma fa idan Kunne ya ji gangan jiki ta tsira" Tana gama faɗin haka ta shige ciki tare da barin Murja a daskare a wajen.

Sosai ranta ya yi ƙololuwan ɓaci duk da tasan wace ce Zaytuna a wurin iya gasa wa mutum magana hankali kwance, lallai yanzu aka fara wasan don kamar yadda ta ɗaukarwa kanta alƙawarin illata yaran su Zaytuna to babu gudu babu ja da baya, koda kuwa za ta tafi tsirara sai ta cika burinta. Da wannan tunanin Murja ta bar wurin zuwa sashenta. 

A can Giwa da ƙyar Kakulle da mahaifiyar Hannatu suka shawo kan Hannatu har ta ce za ta dawo zuwa gobe ko jibi, sosai suka yi farin ciki da hakan daga bisani suka dawo ƙauyensu bayan ƙanin Hannatu ya cikasu da sha tara ta arziƙi. Haka suka dawo gida da farin ciki... ✍️

           🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Gida-dubu Gubi Housing Estate,Bauchi State. Nijeriya*

A ɓangaren Hajiya momma sauƙi ya fara samuwa domin tun lokacin da Hujayrah ta fara  bata ruwan addu'a tare da shafa mata ruwan a duk ilahirin jikin sai ƙurajen suka fara ƙamewa daga baya ma sai suka ɓabɓace. Cikin kwana biyu sauƙi ya fara samu, farin ciki da annashuwa a fuskokin su Alhaji baya misaltuwa, Hujayrah  tasha godiya ba adadi. Abin da ya yi matuƙar ɗaurewa Hujayrah kai shi ne rashin maganar Hajiya momma sai dai tabi kowa da ido, sosai hakan ya damu Hujayrah har take tunanin anya ba sai ta nemo inda aka birne asirin ta karya ba. Wannan ce ƙarshen mafitarta in har tana so Hajiya momma ta fara magana. Da wannan tunanin ta nufi part ɗinsu ɗauko kayan da za ta canja. 

Razina da Arqam sun  tafi airport ɗauko ƙanwar kakarsu wacce ta riƙe mahaifiyarsu,ta zo daga Niger gaida Hajiya momma daman tana gab da zuwa ita da sirikarta bikin Arqam. Sai kuma suka ji rashin lafiyar Hajiya momma dalilin haka yasa ta taho daga baya sirikarta ta biyo bayanta. Bayan tafiyarsu ne Hujayrah ta koma ɗakinsu ɗauko kayan da za ta canja sannan ta dawo part ɗin Hajiya momma. Wanka ta yi ta shafa mai sai ta dawo falo ta zauna, bata jima da zama ba sai ta ji sallamar Nazima da Halima, cike da fara'a ta amsa musu tare da gaishesu, zama suka yi a two sitter suna amsa mata. Nazima ne ta dubi Hujayrah ta ce

"Hujayrah su Ya Arqam da Razina har su tafi airport hala?" 

"Eh Aunty Nazima nasan ƙila ma sun isa iya fort ɗin" cewar Hujayrah tana kwaikwayon kalmar airport da Nazima ta faɗa. 

"Har na ƙosa mami ta zo nasha dariya" cewar Nazima tana tuno da darun mami musamman idan aka zo maganar gayu da tsafta. 

"Aaaa lalle ki ce nima zan sha dariyar Nazima" cewar Halima tana murmushi. Kowanne murmushi ya yi a cikinsu. 

"Muje mu duba jikin Ammie" faɗin Nazima tana miƙewa, ita ma Halima ta miƙewa ta yi suka nufi bedroom ɗin Hajiya momma Hujayrah ta biye dasu. Sun sameta tana baccinta hankali kwance, duk babu ƙurajen sai tabonsu kaɗan-kaɗan. Haka suka tsaya na ɗan wani lokaci daga bisani suka koma falon. 

"Amm Hujayrah kun yi wa mami girki kuwa"  cewar Nazima tana zama. 

"Eh Aunty Nazima mun yi ni da Razina har da baaba Uwale ta tayamu" cewar Hujayrah tana ɗaukar magenta. 

TV suka kunna, shiru ɗakin ya yi hankali kowa na kan abin da ake yi a Tv. Sun daɗe a haka sai can suka ji  sallamar Alhaji, ya shigo duba Hajiya momma. Cike ga girmamawa suka gaishesa sannan ya wuce ciki duba Hajiya momma. Bayan ya fito ya dubi Nazima ya ce

"Mominki fa?" 

"Tana gida sai anjima za ta zo nan gaida Ammie daga bisani da wuce gidan Uncle Ayyub" cewar Nazima. 

"OK, Mami ma ta sauka yanzu haka su Arqam na hanyar dawowa" cewar Alhaji. 

"Abba na ƙosa ta iso mu fara cin dariya" cewar Nazima. 

"Eh fa wato ku fara tsokanarta ko, Hujayrah ya masu jiki!" 

"Jiki Alhamdulillah, ƙurajen su fara ɓacewa amma har yanzu Abbu bata fara magana ba" cewar Hujayrah. 

"Alhamdulillah Hujayrah tunda ƙurajen sun fara ɓacewa, da sannu za ta fara magana in shaa Allah, mu dai ba za mu gaji wurin gode miki Hujayrah" 

Murmushi Hujayrah ta yi sannan ta ce

"Babu komai Abbu, Nike da Godiya" 

Murmushi ya yi sannan ya bar part ɗin. Bai daɗe da tafiya ba su Arqam suka shigo part ɗin. Razina ce a gaba sai wata farar dattijuwa tasha shadda da gyalenta irin na tsofoffi amma mai tsada. Ta shafa farar powder da farin kwalli har da ɗan jan baki a bakinta. Arqam kuma na biye dasu shi da wani bodyguard ya riƙo ma Mami jakarta. Miƙewa su Nazima suka yi har da Hujayrah suna mata oyoyo. Yamutsa fuska Mami ta yi tana zama a kujerar mutum ɗaya har da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Yadda ta zauna ya bawa kowa dariya har da Arqam sai dai shi gintsewa ya yi don yasan Mami da faɗa kamar za ta ari baki. Hakan nan ba a mata komai ba za ta fara masifa ina ga an taɓata. Da sauri Nazima ta nufi kitchen ta ɗauko wa Mami bottle water da kofi. A gabanta ta ajiye ruwan tana faɗin

"Mamina ga ruwa Kisha ki jiƙa moƙoshinki" 

Taɓe baki mami ta yi da cewa

"Mts! Shiyasa bana son zuwa Nijeriya saboda zafi, wani jiƙa maƙoshi a nan, Ni wanka ma nake so na yi yanzu"  tana maganar tare da zuba ruwa a kofi tana sipping irin na ƴan gayu. Mami kenan mai budurwar zuciya, ta tsufa sosai amma komanta na ƴan mata ne, a rana sai ta yi wanka kusan sau biyar ko fin haka. Ƙafarta bata rabo da ƙunshi, gashin kanta duka furfura  ne amma tana shafa mishi jan lallai da kayan ƙamshi, sai gashin ya koma jajja. Fara ce sosai Mami ga hanci da idanu, duk da fuskarta a yamutse take saboda tsufanta amma kullum cikin gyara take. Shiyasa idan ta zo Nijeriya ake daru da ita musamman idan ta ga abun yayi ta nuna tana so aka hanata, to a nan za ta kwana ta yini tana kumfar baki . Sai an siyan mata kafin hankalin kowa zai kwanta. Yanzu haka tana shan ruwan ta miƙe tare da cewa

"Kafin na yi wanka ku kaini wurin ɗiyata na duba jikin nata" tana maganar tana duban Nazima, juyowan da za ta yi karaf! Suka haɗa ido da Hujayrah sai dai Hujayrah bata ji ƙirjinta ya mugun bugawa ba. Wani sanyi taji a ranta kenan Mami ba muguwa bace. Murmushi Hujayrah ta sakar mata, abin mamaki Mami ma  murmushi  ta yi mata tare da faɗin

" Oh ni Asiyatu ina muka samu kyakkyawa yarinya haka Maa shaa Allah Tabarakallah wankan tarwatsa" 

"Ƴan uwansu baaba Uwale ce Mami, tare muke zaune da ita, Ammie ce ta ɗauke" cewar Razina. 

Murmushi mai ƙayatarwa Mami ta yi, tana faɗin

"Ya sunanki ƴan mata?" 

"Sunana Hujayrah ɗiyar Audu jikar Kamalu Angon Hindatu mai tsoran mutuwa" 

"kai Maa shaa Allahu wannan suna haka da tsayin gaske sai ka ce dogon yaro, yanzu dai wanne sunan a ciki zan ɗauka?" 

"Hujayrah ne Sunana" 

"Toh Hujurya ko" 

"A'a Kakulle ba Hujurya ake faɗa ba Hujayrah za ki ce" cewar Hujayrah tana ɓata fuska don a rayuwarta ta tsani a ɓata mata suna. Taɓe baki Mami ta yi tare da cewa

"Ni dai sunanki akwai wahalar faɗa gaskiya, Hujurya zan dinga kiranki. Haka ƴaƴan Mubina suke, Sunansu wahalar faɗa yake, gwara matan akan namijin, Aramqam ne ko mi suke cewa oho, har yanzu ban iya faɗin sunashi ba, ya yi fushin har ya gaji ya ƙyaleni" 

Murmushi kawai Hujayrah ta yi tana jinjina lamarin Mami lalle akwaita da Daru ba kaɗan ba. Sai da Mami ta shiga inda Hajiya momma take ta duba ta sannan ta nufi bayi ta watsa ruwa. Wani Sabon wankan  ta yi kamar mai shirin fita ta ci abinci sannan aka kaita masaukinta ta kwanta don huce gajiya. Arqam tun lokacin daya Suka shigo tare da Mami ya duba Ammiensa sannan ya koma part ɗinsa don sun yi waya da Mas'ud ya ce yau zai dawo saboda gobe shi da prof za su wuce Kaduna wurin mahaifin Abdul akan maganar Halima. Bayan haka akwai aiki da ke gabansa wanda yake kusan raya dare yana yi a laptop ɗinsa. Koda yake a gida amma babu abin da bai sani ba a harkar business ɗinsa na cikin gida na da waje, sannan komai yana tafiya a bisa tsarinsa ne. Baya ɗaukar kuskuran ma'aikaci, da ka yi kuskure to hukuncinka sallama ne, shiyasa ma'aikatansa suke taka-tsantsan a ayyukansu, basa fatan su yi kuskure don sun san halin mai gidansu. Bayan haka suna jin daɗin aiki dashi don yana biyan ma'aikatansa albashi mai tsoka ga allowances masu yawa. Ko abin ci ma Nazima ta kai mishi part ɗinsa . Wannan kenan...✍️

          🌎🌎🌎🌎🌎🌎

A ɓangaren Hajiyan Sama kamar yadda aminiyarta ta ce ta je part ɗin Hajiya momma da yamma ta dubata, haka ta je sannan bata nuna alamun tsoro ko rashin gaskiya ba, haka ta fito ta dawo part ɗinta. Washe gari da safe wurin ƙarfe 11:30 am ta shirya zuwa gidan Hajiya Badiyya daman tun jiya ta sanar mata za ta zo ita da Hajiya Zinatu wurinta. Fauziyya da Zahriyya yau za su dawo daga wurin iyayensu, basu san wace waina ake toyawa a gidan ba, har ta da ƙin amincewar Alhaji akan haɗi da Hajiyan Sama ta so a yi da Fauziyya basu sani ba. A can garin Fauziyya sai shelar takusa aure take ta yi, za ta auri yaron Alhaji. Daɗi sosai iyayenta suka yi don sun san akwai maiƙo, za su dangwali arziƙi. Duk da suma babu laifi suna da kuɗi daidai gwargwado. 


Hajiyan Sama ta iske Hajiya Zinatu a gidan kasancewar gidan Hajiya Zinatu yafi kusa da gidan Hajiya Badiyya. Bedroom ɗin Hajiya Badiyya suke zauna, bayan mai aikinta ta kawo musu abin sha sun sha sannan Hajiya Badiyya ta yi gyaran murya tana duba su ta ce

"Hajiya wai meke faruwa ne, jiya kika kirani hankalinki a tashe" 

Sauke ajiyar zuciya Hajiyan Sama ta yi sannan ta ce

"Hmmmm ai komai ma ya faru Hajiya, ƙaramar yarinya ɗiyar cikina tana niyyar haukani, duk plans ɗina ta wargazasu, tun lokacin da Alhaji ya auro Mubina nake tsara yadda zan ci dukiyarta, ya zamana ni nake juya komai, amma a dare ɗaya! Lokaci ɗaya! Yarinya ɗaya! Ta lalata komai! Ai dole hankalina ya tashi"

"Wace ce yarinyar nan kuwa da har take baki ciwon kai, Haba ƴar cikinki za ta baki ciwon kai Hajiya, a gaskiya kin bani mamaki, Ni na zaci wani abun ne daban" 

Sakin baki Hajiya Sama ta yi ba tare da ta ce da ita komai ba. Hajiya Zinatu ne ta caɓe da cewa

"Hmmmm Hajiya Badiyya yarinyar nan kamar aljanna take, kina ganin duk tsafin boka mai Zaki koran kare ya yi mana saboda its, wai aljanun kanta sunfi ƙarfinsu, wai su bayinsu ne, mene ne da mene ne, ke haka muka taso gwiwa a saɓule. Ga yarinyar bata da kunya  ƙadan daga cikin aikinta ne faɗa wa babban mutum baƙar magana hankalinta kwance" 

Jinjina take Hajiya Badiyya ta shiga yi tana faɗin 

"Eh lallai yarinyar shaiɗaniya ce, kenan ita ta faɗi akwai guba a cikin shayin?" 

"Hmmmm ai ni abin nata akwai ɗaurewan kai, na rasa wasu kalan aljanu suke tare da ita. Yanzu haka har Mubina ta fara samun sauƙi kuma yarinyar take mata magani , duk wannan ƙurajen da suka feso mata babu su sai dai tabonsu. Magana kaɗai ne bata iya yi. Saboda Yarinyar bata san inda na birne asirin ba, Ni da kaina na birne. Na ji daɗi  ko babu komai, Mubina za ta dawwamar kamar matatta, Ni dai yanzu matsala yarinyar ce, Hajiya Badiyya idan akwai wata hanya da kika san za mu iya bi mu hallakar da Hujayrah ki taimaka mana dashi domin asiri bai cin yarinya" Hajiyan Sama ta ce taan gyaran zamanta. 

Gyara zama Hajiya Badiyya ta yi sannan ta ce

"Akwai hanya ɗaya ƙwallin-ƙwal da na san tabbas  za ku iya gamawa da Yarinyar har abada" 

Murmushin nasara Hajiyan Sama da Hajiya Zinatu suka yi. Sai Hajiyan Sama ta ce

"Aminiyar ƙwarai bamu musha ko hankalinmu zai kwanta musamman ma ni" 

Ɗaukar glass cup  ta yi takai bakinta ta ɗan yi sipping sannan ta ajiye gefe tana sake gyara zamanta. Fara koro musu bayani ta yi da cewa 

"Hanyar ba wata bace illa ku saceta, ma'ana ku saka wasu su yi kidnapping ɗinta, daga can mutanan su kasheta, shiƙenan ƙurun-kus kan ƙusu,kun gama da babinta " 

Wata iriya kuɗa Hajiyan sama ta yi tare da tafawa da Hajiya Zinatu, cike da ɗumbin farin ciki Hajiyan Samam da jinjina wa Hajiya Badiyya babban yatsan da cewa

" Jinjinar ban girma a gareki aminiyar ƙwarai irin albarka, ke kaɗai ce babu ƙari, uwar gida kuma amarya, a gaskiya mun ji daɗin wannan shawarar, Ni ban taɓa yin wannan tunanin ba, ai da tuni na gama da babinta" 

"Hakane kuwa Aminiya, a gaskiya mun yi farin ciki da wannan shawarar taki sosai da sosai, Ni kinga ana kirana ma" cewar Hajiya Zinatu tana ciro wayata daga jaka. Ganin mijinta ne yasa  da sauri da ɗaga kiran tare da kara  wayar a kunnanta. Kafin ta ce wani abu daga can Prof ya ce

"Duk inda kike ina son yanzu-yanzun nan ki dawo gida ina jiranki " 

Ras! Gaban Hajiya Zinatu ya bada, duk da bata san meke faruwa ba amma haka nan tasan akwai matsala don daga jin muryarsa kasan yana cikin ɓacin rai. Bai bari ta ce wani abu ba ya katse kiran. Nan da nan fuskarta ta sauya daga farin ciki zuwa tsantsan damuwa. 

"Aminiya lafiya naga fuskarki shimfiɗe da damuwa?" cewar Hajiyan Sama. 

"Ina lafiya Aminiya, yanzu Prof Yake sanar min da in gaggauta dawowa gida yanzu-yanzu, Ni kuma ban san meke faruwa ba" Hajiya Zinatu ta ce tana maida Wayar a cikin jakarta. Taɓe baki Hajiya Badiyya ta yi sannan ta ce

"Barshi Hajiya bari ku gama da yarinyar sai ki mallake sa, muga bakin maganar" 

"Hakane kuwa, bari mu tashi nima su Fauziyya na hanyar dawowa, ban ajiye musu komai ba. Anjima zamu yi waya daga nan sai ki sanar mana yadda aikin zai kasance"  faɗin Hajiyan Sama tana miƙewa tare da gyara zaman jakarta. Miƙewa sauran suka yi sai Hajiya Badiyya ta rakosu zuwa parking space, kowanne ya hau motar sannan suka bar gidan. 

         🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Gidan Professor Abdulrahman Saminu Kwankiyal*

Safa da marwa Prof yake yi a tsakiyar falo Hajiya Zinatu, ya goya hannunsa a baya, lokaci bayan lokaci yana jan tsaki, sosai ransa ya yi matuƙar ɓaci, jira kawai yake Hajiya Zinatu ta dawo ya sauke mata kwando rashin mutunci. Yana tsaka da kai kawonsa ya jiyo sallamarta cikin sanyin murya kamar mutuniyar ƙwarai. Cak! Ya tsaya daga kai kawon da yake ya juya yana kallonta. Sosai gaban Hajiya Zinatu ya faɗi don bata saba ganinsa a irin yanayin nan ba, domin a baya ta mallakesa sai abin da ta ce ya yi shi zai yi,shekeru kusan ashirin asirin na jikinsa, sai yanxu da Hujayrah ta bankaɗo da komai ta karya. Sannan ya koma cikin hayyacinsa har ma yake abubuwa irin na mutane. Cikin tsawa Prof ya dubi Hajiya Zinatu ya ce

"Ashe ƙwaƙwalwar kifi kike dashi Zinatu ban sani ba?" 


Dummmmm! Ƙirjin Hajiya Zinatu ya bada, yaushe suka fara haka da Prof? Mutumin da mari ta yi masa a baya bai iya ce mata komai, sai ma ta umurcesa ya gode mata amma yau shi yake buɗar baki yake kiranta da mai ƙwaƙwalwar kifi, a ranta take cewa ' kutumar dumadu! Yau ake yi ta a gidan nan, Ashe kuwa zai san ya taɓo tsuliyar dodo' katse Mata zancen zuci ya yi da cewa

"Ko ƙwaƙwalwar tunkiya gareki ban sani ba?" 

"Proffff!!!! Ya isheka haka! Nace ya isheka!!! Ni yarinyarka ce da za ka zaunar kake kirana da mai ƙwaƙwalwar kifi. Tunda nake da kai kusan shekara talatin baka taɓa zagina ba balle ka aibatani " 

Murmushin takaici Prof  ya yi sannan  ya ce

"Ki fito fili Kice a lokacin da kike juyani kamar waina a tanda ba, yanzu kuwa nafi ƙarfin ki juyani wallahi. Kin bani mamaki Zinatu a ce Rayyan na gadon asibiti amma kika kasa sanar min, sai dai abokina  da yaje asibitin duba wani mahaukacin da suka kai yake sanar min, ashe shaye-shaye ne ya zautar da ƙwaƙwalwarsa. Ban yi dacen mata ta gari ba, Kin haifar min da guba, bayan haka Nadiya ciki ne a jikin na tsawan wata uku, ta je zubarwa a karo na uku likitan ya ce It's impossible domin mahaifarta za ta samu matsala amma da yake goyon mai ƙwaƙwalwar tunkiya ce ta yarda, Allah yasa yaron abokina was a doctor there, Shi ya hana a zubar da cikin sannan ya faɗa wa mahaifinsa shi kuma ya sanar min a yau. Kina ina hakan ta faru! Kina ina Nadiya ta ɗauki ciki har ta iya tunanin zubar wa baki sani ba, Wallahi kin cuceni Zinatu, Kin cutar da rayuwata, Laila na dawowa daga makaranta zan maida ta hannun Nafisa don ina da yaƙinin za ta samu cikakkiyar tarbiyya ba kamar ki ba. Kalli yanda Mas'ud yake aikinsa gwanin burgewa ba kamar Rayyan ba, ga Nazima natsattsiya kuma kamila mai sanin ya kamata.kin yi Asara Zinatu! "

Duk maganar da Prof yake Hajiya Zinatu bata damu ba, sai da ta ji ya ambaci Nadiya na da ciki har na tsawan wata uku sannan taje a zubar a karo na uku sai hankalinta ya tashi, lokaci ɗaya kanta ya sara mata, yaushe Nadiya ta yi cikin, anya kuwa ba mai ƙwaƙwalwar kifi ko tunkiya bace ita kamar yadda prof ya faɗa. Ina hankalinta ya tafi har Nadiya ta yi ciki ta zubar har sau biyu bata sani ba, sannan yanzu haka tana da wani cikin har ba tsawon wata uku. ' wayyo ni Zinatu naga ta kaina, na shiga uku na lalace, wace irin uwa ce ni mara kula' cikin ranta take maganar amma bata ma san a waje take yinsa ba. Wani mugun kallo Prof ya watsa mata zuciyarsa na yi masa suya. Murmushin takaici ya saki sannan ya dubeta ya ce

"Baki shiga uku ba Zinatu yanzu dai ne za ki shiga ukun, bari Nadiyar ta dawo gida saina mata dukan kawo wuƙa, sannan sai ta faɗa min wani shegen ne ya yi mata cikin har sau uku. Bayan haka da zarar na dawo daga lafiya zan ɗauki Rayyan na kai shi India a duba ƙwaƙwalwarsa, idan ma sun ce baza su iya ba to dawo dashi zan yi ki yi jinyarsa, Allah ya gani kuma shi ne shaidata, na yi iya bakin ƙoƙarina akan yarana amma ban samu abokiyar rayuwa ta gari ba wacce za ta tayani tarbiyyarsu"

Kuka mai tsuma rai Hajiya Zinatu ta saki tare da duƙawa ƙasa, sosai take kukan don zancen cikin Nadiya ya yi matuƙar gigita ƙwaƙwalwarta. Ita da take shirin haɗata da yaron aminiyarta Hajiya kilishi, mijinta na da kuɗin gaske sannan yaron bai yi rayuwarsa a Nijeriya ba, kusan a Saudiyya ya yi rayuwa. Yanzu ya za ta yi kenan plans ɗinta ya rushe, babban abin kunya ne a gareta a ce ƴarta ta yi cikin shege bayan haka ta zubar da ciki yafi sau ɗaya, shikenan ta gama kunyar duniya. Suna cikin haka Nadiya ta shigo falon da sallamarta, turus ta tsaya ganin mahaifiyata na ruzgar kuka. Cike da tashin hankali ta ƙaraso ciki bata ma lura da Prof da ke kallonta ba, tana gab da isa wurin mahaifiyarta ta ji an kwashe Ƙafarta, ji kake Timmmm! Ta faɗi ƙasa bai jira komai ba, ya fara dukanta ta ko'ina, ihu take tana neman mai kawo mata ɗauki amma babu mai taimakonta, don Hajiya Zinatu ko kallon inda take bata yi ba. Ita ma tana takanta ne, tun tana iya ihun har ta kasa. Ƙyaleta ya yi tare da cewa 

"Nnniiii! Nadiya kike so ki tozarta Eh, to kaɗan na yi miki, da na dawo daga tafiya ki shirya faɗa min shegen da ya ɗirka miki ciki har so uku, munafukar banza munafukar yofi,baki ga Nazima ba yadda take da natsuwa da kamun kai, ba ruwan ta da samari tunda aka faɗa mata bata da miji sai Mas'ud ta rungumi ƙaddararta sai ke, ko ɗan gidan uban waye ya yi miki cikin shi za ki aura. Koda yake har da laifin uwarki mai ƙwaƙwalwar tunkiya babu abin da ta sani ta kishi, bata koya miki tarbiyya ba sai bin maza, ai gashi nan, Mtsssssss! " yana gama jan dogon tsakin ya bar musu falon yana huci kamar wani kumurcin maciji. 

Hajiya Zinatu bata bi takan Nadiya ba ta wuce bedroom ɗinta tana kuka, sosai take kuka tana baƙin cikin abin da Nadiya ta janyo mata. Da wani ido za ta kalli ƙawayenta idan suka ji labarin. A can falo da ƙyar Nadiya ta miƙe zuwa ɗakinta tana kuka. 

Bayan Prof ya bar part ɗin Hajiya Zinatu sai ya wuce part ɗin Hajiya Nafisa, bai nuna mata akwai damuwa a tattare dashi ba, amma ita ta ga alama sai dai bata ce dashi komai ba tunda bai sanar mata ba. A ranar Mas'ud ya dawo cikin dare, washe gari ya shirya shiga Prof zuwa Kaduna. Wanda tafiyar da sassafe suka yi sammako, ba tare da Halima suka taho ba da ya ke a jiya sun yi waya da yayansa mahaifin Abdul ya sanar masa ya bar Halima a wurinsa, idan tun daidaita da Sheikh Munnir sai a kai masa ita. 

        🌎🌎🌎🌎🌎🌎

Basu suka iso Kaduna ba sai wurin 1:45pmna rana. Bayan sun yi salla sannan a suka ci abinci suka huta. Cikin gida suka shiga tare da gaggaisawa da mutanen gidan har ƴan uwansu waɗanda suka zo barka suka gaisa dasu, sai suka koma masaukinsu. Cikin dare mahaifin Abdul ya dawo daga wurin aiki ya nufi masaukinsu Mas'ud ya gaisa da ƙaninsa tare da tsara yadda tafiyar za ta kasance da abin da ya dace su sanarwa Sheikh Munnir. A daran suka tsara komai sannan ya nufi cikin gidan. 

*Washe gari*
*ƙarfe 5:57am na safe*

A daidai wannan lokacin motarsu Mas'ud da nisa a saman kwalta. Su huɗu ne a cikin motar, Abdul ne a mazaunin driver, Mas'ud a mazaunin kusa da driver, sai Mahaifin Abdul da Prof a kujerar baya. Sun sha tafiya sosai har sun gashi don Mas'ud sai da ya amshi tuƙin suka ci gaba da tafiya. Basu suka iso Maiduguri ba sai cikin dare kai tsaye gidan ƴan uwansu na Maiduguri suka nufa. Washe gari da safe wurin 9:12am suka nufi gidan sheikh Munnir ,domin a yau suke son komawa Kaduna komin don Prof yana da meeting da zai halarta gobe a jami'an Ahmadu Bello sannan meeting ɗin mai matuƙar muhimmanci ne. Bayan sun iso mai gadi ya wangame musu gate sun shigo ciki sai suka yi parking. Masaukin baƙi wani daga cikin masu aiki ya kaisu. Bayan sun zauna da kusan mintuna goma sheikh Munnir ya shigo ɗakin ta ɗayan ƙofar. Fuskarsa ɗauke da murmushi ya miƙa musu hannu suka yi musabiha. Wuri ya samu ya zauna yana jiran ya ji meke yafe dasu duk da yasan batun Halima ne sannan ya yi mamakin rashin zuwansu da ita. Shiru ɗakin ya yi baka jin motsin komai sai ƙarar A.C. Can prof ya katse shirun da cewa

"Sheikh Munnir ba komai ya kawomu Wurinka ba sai batun auran Halima. Kwanakin baya Abdul da mahaifiyarsa sun zo akan ka yi haƙuri Halima ta auri wanda take so amma kaƙi, har daga baya ka saka ranar auranta da wanda bata so. Ita Halima marainiya ce bata da uwa, sannan hakƙin auranta ba a kanka kaɗai ya rataya ba har da mu yayyin mahaifanta. Hakƙin mahaifi akan ɗiyarsa shi ne ya zaɓa mata abokin rayuwa na gari, ganin kai malami ne kuma kasan ya kamata shiyasa tun farko bamu ɗauki Halima daga hannunka ba. Yanzu kuma da Allah ya ƙaddara ta girma har ta samu wanda take so sannan shi wanda take son mutumin ƙwarai ne mai zai hana ka bari ta auresa. Idan da a ce wanda ka zaɓa mata mutumin kirki ne wannan da sauƙi"

Ƙafa ɗaya kan ɗaya sheikh Munnir ya dora yana Sakin wani munafikin murmushi, a ransa sai ayyana mugunta yake kala-kala, a yau haƙarshi za ta cimma ruwa. Gyaran murya ya yi sannan ya ce

"Abdulrahman ka gama karanta tatsuniyar taka in wuce ko da saura?" 

Sakin baki kowanne a cikin ya yi, babu wanda ya yi zaton Sheikh Munnir zai iya faɗin irin wannan maganar. Cike da ɓacin rai mahaifin Abdul ya ce

"Wani Irin rainin hankali ne wannan sheikh Munnir! Mu Yara ne da za ka faɗawa irin wannan maganar, me kake nufi da tatsuniya?" 

Ƙaran Sakin wani munafikin murmushi Sheikh Munnir ya yi sannan ya ce

"Tabbas abin da Abdulrahman ya faɗa daidai take da tatsuniya domin abin da kuke so na yi bazan taɓa yinsa ba, aure ne Halima bazata auri wanda take so ba sai wanda na zaɓa mata ko taƙi ko ta so, ku kuma baku isa ku hanani abin da naso da ɗiyata ba don baku kuka haifamin ita ba. Daidai nake daku ko kotu za ku Kaini bazan janye maganata ba.Ku yi ta riƙon Halima amma kusani sai dai ku ga mijinta ya zo ɗaukarta don sati mai zuwa zan ɗaura auranta da wanda na yi niyyar aura mata, babu fashiiii!!! "

Yana gama maganar ya miƙe tare da barin ɗakin ya koma cikin gidan. Sosai ran kowa ya ɓaci da rainin hankalin da Sheikh Munnir ya yi musu. Gwiwa a saɓule suka baro ɗakin, motarsu suka hau sannan suka bar Estate ɗin, titi suka hau suna lafiya ran kowa a jagule sai da suka tsaya wani gidan mai suka cika tankinsu sannan suka ci gaba da tafiya. Mahaifin Abdul ne ya dubi Mas'ud ya ce

"Mas'ud ka ce wanda Halima take so abokin ka ne ko?" 

"Ek Kawu, wurin aikinmu ɗaya dashi" 

"OK, idan Allah ya kaimu lafiya m za ka kiramin shi, domin ina so kafin Sheikh Munnir ya aura wa Halima wani mu mun aura mata wanda take so, sai muga ta tsiya, idan shi-shi ne to mu ma muɗin ne. Sai mu ga wanda zai yi nasara" cewar mahaifin Abdul. 

Prof Ne ya caɓe da cewa

"Wannan shi ne daidai, Ni wallahi mamaki Sheikh Munnir yake bani kamar ba malami ba, gaskiya ina kokwanto akan maluntarsa akwai tankarɗa wallahi, kaga yanzu idan muka yi saurin aura mata abokin Mas'ud kaga bai da halin jayayya masu, mu ne da nasara sannan Halima na wurin "

" Hakane kuwa, wannan shi ne.... "

Bai ƙarasa abin da ya yi niyyar faɗa ba motarsu ta fara Layi a saman titi, Abdul yayi-yayi ya tsayar da motar amma taƙi tsayuwa. Kowa a motan salati yake yana ambaton sunan Allah, babban tashin hankalin shi ne ga wata trailer tana tahowa  a ɗayan gefen da gudun gaske. Da matuƙar ƙarfi Abdul ya riƙe kan motan don tana niyyar ƙwace masa. Wani sauti motar ta bada ji kake Ƙiiiiiiiiiiiii!!!  Ƙiris ya rage motar da haɗu da trailer. Daji motar ta dosa sai kuma ta haɗu da wata bishiya, tana haɗuwa da bishiya sai ta kama da wuta... ✍️







*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***