INUWAR KADDARA 🖤

TSORO DA TAUSAYI😚

by @meelahbazata978

INUWAR ƘADDARA 🖤

Book 1

Page 12 ✍️

"Sayyid"

Ammah ta kira sunansa, tsayawa ya yi cak tare da dawowa baya. Nuna masa inda ya tashi ta yi, hakan ya sa ya koma ya zauna a hankali, fuskarsa a daure. Ji yake kamar ya haɗiye zuciyarsa don baƙin ciki.

Ita kuwa baiwar Allah, ba ta daina wannan ihu da sambatu da take yi ba, sai da Ammah ta kira sunanta sannan ta yi shiru.

"Leenah, ki yi shiru, kin ji? Tashi ki zo nan. Ki daina tsorata idan kika gan shi, yayan ki ne, babu abin da zai yi miki."

Rooman da ta tsayar da dariyarta saboda ganin yadda Leenah ta kwanta a ƙasa, abin ya ba ta dariya sosai. Hakan ya sa ta sake yin magana cikin dariya.

"Ammah, ki ƙyale ta. Ni ma na gaya mata babu abin da zai yi mata, amma ta ƙi yarda. Ji yadda take ihu, don Allah! Kamar ta ga aljani."

Wata harara Leenah ta jefa mata tana goge hawayenta, tare da zubar da wasu sabbi tana cewa:

"Ai yanzu na sake yarda da abin da ake faɗa a duniya, babu tabbas! Yanzu na ga zahiri. A gaban Rooman ake neman kashe ni, amma ba za ta iya kawo wa rayuwata ɗauki ba. Hmmm, ai shikenan!"

Tana maganar tana hawaye, kuma tsakaninta da Allah take wannan kukan. Ita kuwa Rooman, maganar dariya ta ba ta sosai.

Sai da Ammah ta sake magana sannan Leenah ta miƙe ta nufi gurin da take zaune, kuma har zuwa lokacin jikinta bai daina rawa ba.

Ba ta yarda ta sake kallon inda yake ba, kawai ta tunkari gurin da Ammah take zaune.

Tana zuwa, ta shige jikinta ta kwanta, har da sauke ajiyar zuciya. Shi kuwa Sayyid kamar zai cinye ta don harara. Mamakin yadda ta shige jikin Ammah yake yi, kamar ta samu jikin uwarta.

Shafa kanta Ammah take a hankali, cikin sigar rarrashi ganin yadda hankalin yarinyar ya tashi sosai. A hankali ta fara cewa:

"Me ya sa kika tsorata haka? Yanzu ga shi kin zubar da maganin, kuma shi nake ta jira. Na so ma na aika Sayyid ya amso min kawai..."

Ai da sauri ta ɗago kanta. Ta ma manta da wanda take kusa da shi, har wani zaro idanuwanta masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali ta yi, ba tare da ta san ma ta zaro idanun ba.

"Ammah, wai shi Yaya Madugu ɗin za ki aika gidanmu? Da mun shiga uku wallahi! Allah ya taimake mu. Ai duk sanda ya..."

Wata tsawa ya daka mata, wanda hakan ya sa maganar da take yi ta maƙale a maƙogwaronta.

"A gidan uban wa na zama yayanki? Iyeeh? Na ce, a gidan uban wa na zama yayan naki? Neman suna kike ko me? Tashi a jikinta, aljanar banza mai kama da mayu! Kin zo kin wani kwanta kamar kin samu jikin uwarki. Kuma idan ba ki tashi kin je kin gyara gurin da kika ɓata ba, yau babu abin da zai hana Rocky cinye waɗannan ƙafafun naki, tashi!!!"

Girgiza kai kawai Ammah ta yi. Ba ta san mene ne haɗin Sayyid da Leenah ba. Ita tana matuƙar tsoronsa, shi kuma ya yi matuƙar tsanarta, kuma tun tana ƙarama abin ya samo asali.

Yarinyar ta taso ne da wani irin surutu da kuma tsiwa. Ana kawo mara Leenah a lokacin kuma tana da cikin Rooman, shi kuma Madugu haushi da kishin yadda Ammah take goya Leenah tana lelen ta ya sa gaba ɗaya ya tsani yarinyar.

A duk unguwar nan, babu gidan da Ammah take shiga sai idan ya zama dole. Mahaifiyar Leenah ce suke zumunci sosai da Ammah, tun bayan haihuwar Leenah.

Da yake kuma Ammah ba mai yawan shiga mutane ba ce, babu inda take yawan zuwa. Ita kuma Ammah tana son Leenah, hakan ya sa idan aka yi mata wanka sai a kawo wa Ammah ita.

Shi kuwa Madugu ba ya so, saboda ya tsani ganin yadda Ammah take ɗaukar Leenah ta goya ta. Tun daga lokacin shi ma ya tsane ta. Ita kuma tun farko ba ta zuwa ko kusa da inda yake saboda tsoron da yake ba ta.

Katse tunanin nata ta yi saboda jin muryar Rooman tana cewa:

"Kin ga ki tashi, na taimaka miki mu gyara gurin kafin lokacin makaranta ya yi. Tunda Yaya ya ce sai kin gyara, na san dole za ki gyara gurin nan. Ga lokaci ya kusa ƙurewa."

Wani kallo ya yi wa Rooman mai kama da gargadi, yana harararta kamar idanunsa za su faɗo. Cikin takaicin irin iyayin na Rooman, ya ce:

"Bari na ga ƙafarki a gurin nan, ki ga yadda zan dake ki!"

Aikuwa cak ta tsaya. Hakan ya sa Ammah ta ɗago Leenah da ke jikinta cikin sigar rarrashi ta ce:

"Tashi ki ɗauko mop ki goge gurin, kin ji, yar albarka? Ki daina tsoron shi, babu abin da zai yi miki. Kuma zan yi maganinsa, kin ji ko?"

Ammah ba ta san yadda haushin da yake ji yake ƙara ƙule zuciyarsa ba.

Ita kuma sarkin tsoro, da ƙyar ta iya miƙewa. Gani take kamar idan ta bar kusa da Ammah, zai iya binta ya kashe ta.

Hanyar ɗakin Rooman ta nufa ba tare da ta lura da inda take bi ba.

Muryarsa ta dawo da ita hayyacinta, tare da sake jefa ta cikin wani irin tsoro.

"Ke!!!"

Muryarsa ta dawo da ita hayyacinta. Ya waiga ya kalli Ammah kamar zai fashe da kuka don takaici.

"Haba Ammah, don Allah ki duba abin da yarinyar nan take yi fa! Kuma a haka kike bari tana shigowa nan? Wata rana idan ba kowa fa, ta zo ta rufe ki da duka? Ji abin da take yi! Kina gani, kin san tana da lalurar hauka, amma kina ƙyale ta!"

Ammah ta ɗan yi shiru, tana kallonsa cike da mamaki. Ta san halin Sayyid sarai, in ta ci gaba da mai faɗa ba zai fahimta ba, hakan ya sa ta ce:

"Sayyid, ka daina faɗin haka. Leenah ba mahaukaciya ba ce. Yarinyar nan kana shiga haƙƙinta da yawa, Sayyid. Me ya sa kake haka ne, don Allah? Yadda Rooman take ƙanwarka, ita ma haka ne."

Ya ɗan juya kansa gefe yana fitar da iska daga bakinsa, ƙara daura fuska ya yi.

"Ni kanwa ɗaya gare ni a duniya, kuma ita ce Rooman. Ki daina faɗin haka, Ammah."

Yana maganar yana sake hararar Leenah. Ita kuwa cikin sauri ta ɗauko mop ɗin ta fara goge gurin, tana yi tana kuma kuka. Sosai take kuka, in ta goge ta goge sai ta tsaya ta share hawayenta.

Ga tsoron ɗaga kanta kar ma ta gan shi, saboda duk da haka ji take a jikinta, domin girmansa take gani sosai.

"Idan na ƙara jin kukan ki a nan, to ki sani sai na sa wuƙa na sake yanka wannan bakin naki kamar gidan tsutsa."

Yadda ta tsinkayi muryarsa ya sa ta yi tsit daga kukan da take yi, sai faman jan ajiyar zuciya.

Sai da ta gama gyara gurin tas, sannan ta tsugunna tare da rufe idanunta ta ce:

"Yaya Madugu, na gama gogewa, ban bar ko digo ɗaya ba."

Ko lallonta bai yi ba, ya ce:

"Saita ma kanki hanya."

Aikuwa da gudu ta bar falon. Ba ta tsaya ba ma balle ta yi wa Ammah sallama. Sai Rooman ce da ta miƙe ta shiga ɗakinta ta ɗauko hijab ɗinta da jakar makarantar ta fito ta ce wa Ammah da Madugu ta tafi makaranta.

Haka ta fita ta bar Ammah tana yi wa Madugu faɗa a kan ya sauya halinsa. Amma jinta kawai yake yi. Ƙarshe ma tashi ya yi ya fita daga ɗakin, ya bar gidan gaba ɗaya. A zuciyarsa yake ji yau duk wanda ya taɓa shi akwai ƙura.

Ita kuwa Rooman tana fita, gidan su Leenah ta shiga. Ta tarar da ita tana can bakin bishiya tana wanke fuskarta, kuma ba ta daina kukan ba. Ga Mama sai faɗa take mata a kan ta yi maza ta shirya, kuma ta yi mata shiru kafin ta zo ta tarar da ita a gurin. Sai faman ajiyar zuciya take yi.

Gaishe da Mama Rooman ta yi sannan ta ƙarasa gurin Leenah tana faɗin:

"Haba kawata me capacity, duk tsoron ne har yanzu? Mama, wai fa Yaya ta gani a falon, shi ne ta sake maganin ya faɗi ya fashe a ƙasa, shi ne Yaya ya ce sai ta goge inda ta ɓata."

Rooman ta yi maganar tana kallon Mama. Ita kuwa Mama takaici ne ya sake kamata domin ba ta san cewa ta zubar da maganin da ta aike ta ba. Cikin takaici take kallon Leenah.

"Ai ban ji daɗi da bai haɗa mata da bulala ba. Ai zan ga Sayyid ɗin, duk ranar da ta sake ganinsa ta gudu, to ya sa bulala ya zane jikinta. Yanzu ga shi babu damar sake amso wani maganin a yau, dole sai gobe. Gaskiya ban ji daɗi ba wallahi."

Tana maganar tana takaicin yadda Leenah ta zubar da maganin. Tsaki Mairo da take can bakin maƙwarara tana wanke-wanke ta yi tana cewa:

"A yi dai mu gani in ta so za ta hura wuta. Ba dai ke kin dage sai kin yi alaƙa da waɗannan annoba ba? a kaf unguwar  ya addabi kowa,yar taki ɗaya jal, ita ma da kika haifo mana bala'i, to shi ne zai yi ajalinta. Muna nan muna kallo. In ba munafurci ba, har meye na alaƙa da matar da ɗanta ya addabi gari gaba ɗaya? A nan a gaban idanunki ya shigo har gidan nan ya yi wa yaron nan mugun duka, amma da yake ba ɗanki aka yi wa ba ai ba ki damu ba. Kuma kada ki ƙara gayyato mana shi nan atohh."

Haka dai Mairo ta ci gaba da sababin ta tana jin baƙin cikin dukan da Madugu ya yi wa yaron nata, da irin yadda karen sa ya yi kaca-kaca da shi. Shi ya sa a duniya ta tsane shi kamar mutuwarta.

Ita dai Mama ba ta ce komai ba har Mairo ta gama masifar ta. Ɗaki ma ta shige bayan Leenah ta taso daga bakin bishiyar suka shiga gaba ɗaya.

Sai da ta shirya sannan Mama ta yi musu addu'a suka tafi makaranta.


Yau kwana uku kenan da faruwar hakan. Da misalin ƙarfe goma da rabi na safe, ita Leenah tana ɗaki tana bacci, da yake yau ba makaranta.

"Aishatu! Aishatu!!"

Kiran Baba ne ya tashe ta daga baccin da take yi, domin kuwa akwai ƙauna mai girma tsakanin ta da bacci. Tashi ta yi tana goge idanunta tare da sanya takalminta ta fito.

A tsakiyar gidan ta tarar da Baba, ga yayarta Karima tana tsaye kusa da Baba. Zuwa ta yi ta tsugunna ta gaishe shi. Kallonta ya yi cikin kulawa da son da yake yi wa yarinyar, domin ita ce autarsa, kuma ita kaɗai Mama ta haifa, sauran duk yaran Mairo ne.

"Aishatu, sarkin bacci, ga shi kuma na katse miki baccin naki. Ga yar uwarki nan, ku shirya yanzu ku je gidan gwaggon ku, ba ta jin daɗi. Ku gaishe ta sannan ku yi mata wasu ayyukan. Idan an yi la'asar sai ku dawo. Kada ku bari magriba ta yi, kun san ba na son unguwar yamma."

Yana maganar yana miƙawa Karima kuɗin da ya ciro daga aljihunsa. Amsa ta yi suka haɗa baki gurin amsa masa da toh.

Addu'ar dawowa lafiya Mama ta yi masa, yayin da Mairo take ta faman cika tana batsewa. Babu wanda ya bi ta kanta. Baba ya sa kai ya fita daga gidan.

Yana fita, Karima ita ma ta koma ɗakinsu domin shiryawa. Ita kuwa Leenah ba ta tashi a gurin ba har sai da Mama ta yi mata magana sannan ta tashi. Har zuciyarta ba ta ji daɗin haɗa ta da Karima da aka yi ba, domin ba sa shiri ko kaɗan. Karima ta girme ta domin ta ba ta shekara kusan biyu, kuma Karima ita ce autar Mairo.

Ba sa shiri ko kaɗan da Leenah. Sanin haka ya sa Mama ta yi mata magana a kan ta tashi ta je ta yi wanka ta shirya, domin kuwa in ta tsaya ba ta lokaci ba, jiran ta za ta yi ba. Ita kuma ba ta iya zuwa gurin mai nisa ba ita kaɗai.

Haka ta tashi ba don ranta ya so ba, ta shiga ta shirya. A gaggauce ta yi wanka ta fito, wata doguwar riga ta ɗauko mai sawai-sawai, da yake ba ta shiri da kaya masu nauyi. Sai da ta sa kayan sannan Mama ta ce mata:

"Da kin koma kin canza wannan riga, Leenah. Kin ga ba ta da kauri, ki saka atamfa mana. Ni ban san mene ne haɗinki da kaya ba, ga su jibge, sai dai na gaji na yi kyauta da su."

Cikin maganar ta ta shagwaɓa ta ce wa Mama:

"Ni fa Mama, ba na son atamfa, damun na take a jiki, duk in yi ta faman zufa, ga ƙaiƙayi."

"Allah ya shirye ki to. Ga abinci ki ci da sauri kafin ku wuce..."

Mama ba ta gama maganar ba suka ji maganar Karima tana faɗin:

"In yarinya ta tsaya ,wucewa zan yi na barta a to, don ba baiwarta ba ce da zan zauna jiran sai ta gama iyayi."

Ko abincin ba ta tsaya ci ba, ta ce wa Mama idan sun je can za ta ci, sannan ta bi bayan Karima da gudu, har ta fita daga gidan ma.

Ko da ta fita, har ta yi nisa, ita domin ta san Leenah ba ta iya sauri ba. Ita kuma tana bakin cikin jerawa da Leenah ɗin, duk da take fara sol, ga shi kuma tana ƙarawa da mai, kuma tana ganin ta girme wa Leenah. Amma duk inda za su shiga tare sai an yaba da halittar Leenah ɗin. Haka ake faɗa, duk gidan babu mai kyawunta, duk da kasancewarta ba fara ba.

Har ta kai bakin titi, Leenah ba ta ƙaraso ba. Sai da ta ga tana niyyar tafiya ta bar ta, hakan ya sa ta ƙara da gudu ta cimma ta, ita ma ta shiga.

Ranar dai a gidan gwaggonsu suka wuni, wanda sam wunin bai yi wa Leenah daɗi ba saboda yadda Karima take yawan yi mata shagube da zagi. Don ma ita ma wani lokacin idan abin ya kai ta bango tana ramawa, ga shi gwaggonsu bayan Karima take bi saboda ba sa shiri da Mama.

Har biyar saura sannan Karima ta tashi ta ce za su wuce, bayan Leenah na ta magana a kan Baba ya ce su dawo da wuri.

Ko da suka tafi, Karima cewa ta yi ba za su tafi a mota ba, wai wani saurayinta ne zai zo ya ɗauke su. Hakan ya sa ta kashe kuɗin motar da Baba ya ba su.

Babu yadda Leenah ta iya domin akwai nisa, ba za ta iya tafiyar ƙafa ba, kuma ita tsoro take ji. Hakan ya sa sai da ta bi Karima har inda saurayinta yake aiki. A nan ma suka ɓata lokaci, sannan bai zo kawosu ba sai kuɗin mota ya ba su, ya ce su hau su tafi gida, yana da uzuri.

A bakin kan layinsu aka sauke su, a lokacin Leenah ta kai wuya da haushin abin da Karima ta yi. Ga shi yanzu kusan biyar da rabi, kuma Baba cewa ya yi su dawo da an yi la'asar.

Ko sauraron Karima da ke mata magana ba ta yi ba saboda ta yi fushi. Hakan ya sa ta bi bayanta tare da jan hijab ɗin ta ta baya, wanda tana jan shi ya yage tare da biyo hannunta. Dama irin mai V ɗin nan ne fashion, wanda ake yi da doguwar riga.

Take kanta, wanda babu ko ɗankwali, haɗi da gashinta wanda yake kitse, ya bayyana. Jikinta, wanda ko bra babu, kana ganin shatin yan madaidaitan ƙirjinta suka bayyana.

Ita kuwa bayan jan hijab ɗin take ta jefa shi cikin kwatar da take kusa da su. Aikuwa me Leenah za ta yi in ba kuka ba? Ga shi ko ɗankwali babu a kanta. Rasa yadda za ta yi kawai ya sa ta tsugunna ta fara kuka.

Ita kuwa Karima zagi take mata na rashin mutunci tare da aibata ta. Tsaki ta yi ta juya za ta bar gurin, sai ta ji muryarsa.

Duk abin da suke yi yana kallonsu, domin shigowarsa unguwar kenan. Hakan ya sa ganin yarinyar nan, wacce yake cewa mahaukaciya kamar yadda yake fata, kawai sai ya yi niyyar wucewa. Amma kuma sai zuciyarsa ta darsa masa tausayinta, domin rauninsa shi ne ganin hawayen mace. Yana ganin inda Rooman ce zai iya wucewa kuwa. Kuma yadda take kukan har cikin zuciyarta abin yake taɓa wa.

"Ke kuma aikinki da kika zo yi duniya kenan, kuka? Aikuwa kin yi asara!"

Abin da ya fito daga bakinsa kenan. Duk da irin tsoron da muryarsa ta dasar a zuciyarta, amma ba ta iya daina kukan ba, domin ta muzanta sosai, ganinta a bakin titi babu ko ɗankwali bare kuma hijab.

Ita kuwa Karima tun jin muryarsa hanjin cikinta yake juyawa. Yau kuma wace ƙaddara ce ta haɗa ta hanya da Madugu? Sosai jikinta yake rawa.

"Cire hijab ɗin jikinki sannan ki cire kallabin da ke kanki hatta da takalman kafarki ki ciresu!"

Shi ne abin da ya fito daga bakinsa cikin sautinsa mai ban tsoro. Har ita da ba da ita yake ba sai da ta firgita, amma Karima da ta yi suman wucin gadi ba ta cire hijab ɗin ba.

Marin da ya sauƙa wa fuskarta shi ne ya yi sanadin dawo da ita hayyacinta. Aikuwa babu shiri ta yi abin da ya umarce ta cikin gigicewa da azabar marin da ta sha.

"Madugu baya maimaita magana."

Shi ne abin da ya faɗa ba tare da ya kalli inda take ba.

Ita kuwa a garin saurin cire ɗankwalin, acuci mazan da ta yi da ɗan kamfai ya faɗo ƙasa, ga kan kamar hammatar 'yan iska. Hakan sai ya ba Leenah dariya, duk da halin da take ciki. Ba ta san sanda ta ƙyalƙyale da wata irin dariya mai matuƙar ƙarfi ba.

Da mamaki Madugu ya waiga ya kalleta, domin yanzu dai ya tabbatar da maganarsa a kan ciwon hauka ke damun yarinyar.

Sai dai kuma shi ma ganin abin da take yi wa dariya da kuma yadda take dariyar, bai san wani ɗan ƙaramin murmushi yana niyyar bayyana a fuskarsa ba.

Da sauri ya daure fuskarsa damau, amma a zuciyarsa abin ya ba shi dariya. Hijab ɗin ya ɗauka ya miƙa wa Leenah, wacce har lokacin dariyar ba ta tsaya ba.

"Ke!"

Ya daka mata tsawa. Aikuwa take ta haɗiye dariyar, jikinta kuma sai ya sake ɗaukar rawa. Miƙa mata ya yi, ta sa hannu ta amsa ta saka a jikinta.

Ita kuwa Karima kallonta ya yi ya ja wani dogon tsaki.

"Shegiya mai kama da maza,mummunan,Wai Kuma Nan mace kike? sannan ki fara tsallen kwado tun daga nan har zuwa gidanku."

Abin da ya umarce ta ta fara yi, domin har lokacin ba ta dawo daga azabar marin nasa ba.

Kamar mahaukaciya haka take tsallen kwadon, zuciyarta kamar za ta fito. Ita babban tsoronta ma shi ne ta kai gida ta daina ganin sa.

"Ke kuma mahaukaciya, wuce ki tafi, wawiya kawai."

Suf-suf ta fara tafiya. A zuciyarta tana faɗin, wai dama yana da kirki? Tunda ga shi ya taimake ta.

Tana tafiya shi ma ya biyo bayanta. Jin takunsa sai kuma zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi, tsoronta ya dawo farko.

Har suka kai ƙofar gidan nasu, Karima tana tsallen kwadon, ga mutane masu wucewa, da masu son su yi magana. Amma suna hango Madugu sun san aikinsa ne, kowa sai ya ja bakinsa ya yi shiru.

Ita ma Leenah Allah-Allah take ta kai gida, domin har yanzu ba ta cire tsammanin zai iya janyo ta ita ma ya yanka ta ba.

Ko da ya kai ƙofar gidansu, kamar ma bai san abin da ya faru ba ya shiga gida. Ita ma Leenah hakan ce a gare ta, domin gida ta shiga. Karima kuwa dama ta riga su isa gida.


Last free page 🙏✍️

Yanzu za mu tsunduma cikin wannan ƙasaitaccen labarin. Kada ku bari a yi ba ku, domin labari ne na musamman.


🖤🔥 INUWAR ƘADDARA 🔥🖤


Shin me zai faru idan mutumin da ya fi kowa ƙin ganin mutum, shi ne ya zama wanda zai fara taimaka masa a lokacin da duniya ta juya masa baya?


Madugu! Mutumin da sunansa kaɗai yake sa Leenah rawar jiki. Wanda tun tana ƙarama bai taɓa ɓoye ƙiyayyarsa gare ta ba.

Amma fa wannan karon, ƙaddara ta haɗa su a wani yanayi da ba ta taɓa zato ba. 😭


Wani hijab da aka yaga...

Hawaye da suka cika idanun Leenah...

Da kuma hukuncin da Madugu ya yanke wa Karima! wannan shine sanadiyar kulluwar wani al'amari na musamman.


Amma tambayar ita ce: Shin wannan tausayi da ya fara ji a kanta zai iya sauya ƙiyayyar da ya daɗe yana mata?


Ko kuwa wannan ma wata hanya ce ta ƙara shiga cikin INUWAR ƘADDARA?


shin Wai wanene sayyid ma gaba daya???

🔥 Kada ku bari a ba ku labarin, ku karanta da kanku!


💬 Bayan karantawa, ku zo  🖤🔥 INUWAR ƘADDARA 🔥🖤

🔥 Kada ku bari a ba ku labarin, ku karanta da kanku!


✍️ Marubuciyar INUWAR ƘADDARA 🖤


meelah bazata na alfahari daku✍️🥰ku shirya ku sake  gyara zama,zaki nishadantu sosai✍️✍️