BOOK ONE CHAPTER 25
*ALIYA*
Tunda suka kamo hanya babu wanda yace da ɗan uwansa ci kanka. kuwwa da abinda yake saƙawa azuciyarsa.
Yayi packing ta sauko. tasa key ta buɗe falon tai shigewanta ɗakinta kai tsaye.
Tana shiga bedroom ɗin ta ta murza key aƙofar. Ta silale ajikin kofar tai zaman dirshan aƙasa hawaye na sauko mata. Ba abinda take gani acikin idanunta sai kalan kallon da Ustaz yakema Jamila.
"Kenan har yanzu Jamila ce acikin zuciyarsa, ita kadai ce take haukarta."
Kuka mai sauti ya kwace mata. sosai take kokawa da dukkan zuciyarta wani irin zafi na ratsa ƙahon zuciyarta.
Ita kuma tata kalan ƙaddaran kenan rayuwa da miji amma zuciyarsa na wurin wata daban.
Abin da ciwo matuƙa gayan. Hakan yasan yata yin kuka sosai harse da taji kanta na sara mata sannan ta miƙe daƙyar ta cire hijjab ɗinta ta ninke. Ta sauya kaya zuwa na bacci ta hau kan gado hawaye na saukar mata.
Tanajin lokacin da Ustaz yazo yana buga mata kofa tai mai banza don batada zuciyar da zata kara kallonsa ayanzu.
Kafin akai matakin daze bude baki ya gaya mata baya sonta yana rayuwa da itane amatsayin bayada zaɓi gwara tai nesa dashi.
Ko bata sami soyayya ba zata tsira da lafiyarta saboda yanzu haka jin zuciyarta takeyi kamar ana kunna mata wuta.
Awannan daren baccin da Aliya tayi sedai ɓarawo.
Athuba nayi ta mike taje tai sallah. bugun kofarsa baisa ta buɗe ba sai da yayi yagaji yayi tafiyarsa masallaci. Daya dawo ma seda ya kuma buga mata kofa.
Seda ta tabbatar ya shiga ɗakinsa sannan ta fito daniyyar ɗora musu abin karyawa.
Cikin hanzari take komai don batason yazo ya isketa a falon amma se akai rashin sa'a, ta gama jera abinci a dining ta shiga kicin dauko faranti sai gashi ya shigo.
Batare da ta kalli inda yake ba ta gaidasa acukule, murya can ƙasan maƙoshi kamar wacce aka tilasta mawa yin gaisuwan.
"Ina kwana."
"Jiya kin rufe min ƙofa. nai knocking kinƙi buɗewa bayan nasan kina jina. mai yasa Liya?!"
"Ba komai."
Ta amsa tana ƙoƙarin raɓashi ta wuce. Hannu yasa ya riƙo damtsen hannunta yana kallon fuskanta data runtse idanunta alaman shine batason gani.
Ya silale akan guiwoyinsa har lokacin yana riƙeda hannunta. Ya soma magana da muryansa dake rawa.
"Idan laifi nai miki na roƙeki da ki yahakuri ki yafe min bazan iya jure wannan hukuncin naki ba agareni don Allah ki yafe min."
Kanta ta juya gefe zuciyarta na karyewa, hawaye na saukar mata tace "kadaina roƙona....bakaimin laifin komai ba....kawai ina ƙoƙarin cire kaina ainda banada wani matsayi ne."
"A'inane bakyada matsayin Liya?!."
Aliya taja numfashin kukan da take yi. Ta rigada takai ƙarke babu buƙatar cigaba da ɓoye mai.
"Azuciyarka ce banada matsayi....!"
Wani gunjin kuka ne ya taso mata ta dannesa hawayenta na ƙara ƙarfi wajen fita. Cikin rishin kuka mai ciwo tacigaba.
"Tun farko nasan bani bace acikin zuciyar ka. Banda qualities ɗin da zaka soni...Ni bazan taɓa zama Aunty Jamila ba agareka....don Allah ka sake Ni...!!!"
Taƙarke maganar wani irin gunjin kuka na taho mata. Ƙafafuwanta dake rawa suka gaza ɗaukarta sai kawai ta silale tai zaman dirshan awurin.
*ZAINAB*
Ta ƙarika gabansa asanda yake jefa mata tambayar data daskaradda ita atsaye.
"Daga gidan wani kwarton kika dawo."
Tambayar ta zauna mata ita kadai atare da ita batareda ta bama komai damar zuwa inda take ba.
Ahmed yayi wani dariya da bayada alaƙa da nishadi. Ya kalleta cikin idanu yana fesa mata kalaman da suka sanya zuciyarta tarwatsewa afilin ƙirjinta.
"Mazina ciya....Fasiƙa....Na tsaneki! Duk bayan hakurin kallon fuskarki da nake yi da abinda zaki sakamamin kenan! Allah ya'isa ban yafe mikiba. Kije na sakeki...saki..uku!"
Kalaman Ahmed suka faɗo mata kamar tsawa a cikin zuciya. Ta zuba masa ido, amma idonta ya ƙi yarda da abin da kunnuwanta suka ji.
Bayan duk shekarun da ta sadaukar masa, duk haƙurin da ta yi, duk lokacin da ta haɗiye hawayenta domin kada gidansu ya rushe… yau shi ne ya zo ya rushe ta da kalma ɗaya.
Rinannun idanunta na kafe akansa ta buɗe bakinta da wata ƴar ƙaramar murya mai cikeda rauni na ciwo tai magana daƙyar
“Ahmed! bayan duk abin da na yi maka… da gaske wannan shi ne ƙarshen labarinmu?”
"Ba iya labarin muba ayau komai ya kare. Ki tafiyarki."
Yana gama faɗin haka yasa hannu yaja Ramlat da Anis dake kuka suna turjewa.
Zainab ta bisu da idanu har suka shige gidan. Ahmed ya maida ƙofa ya rufe.
Ta ɗaga ƙwayannin idanunta da nauyi mai girma ta kalli kayanta dake yashe kalolinsu na cika mata kai.
Hannu ta kai kan kayar ta soma tsincesu tana cusasu acikin trolly din ta. Akaran kanta take jin kanta sama-sama. Kamar ana hasko mata rayuwarta awani fefen majigi da batada masaniyar lokacin da aka ɗauka.
Ba tasan ko ta kammala kwashe kayanba zuciyarta ta isar matada ta tashi ta tafi.
*JAMILA*
Cikin rashin fahimta yace"I couldn't understand what you are saying."
"Oh sir get the point your wife have pregnant for one month."
"Pregnant?!."
Samir ya tambaya arazane kamar aranar ya soma jin kalaman. Doctor Emanuel yai turuss ganin yanda Samir ya kiɗime.
"Is that any problem?"
"No thank you so much."
Ya amsa mai yana ƙoƙarin yin murmushin dako leɓunansa basu sanda wanzuwan shiba.
Kai doctor yajin jina ya fita. Samir yayi zaune yana kallon Jamila dake kwance tana bacci. Wasu abubuwane marasa kyau suke mai yawo. Ji yake yi kamar ya shaƙeta. Kamar yasa pillow ya danneta ta mutu ko kuma ya fizgota daga kan gadon yayi ta dukanta. da sauransu da sauransu.
Gudun aikata abinda zai kaishi ga danasani yasan yashi fita yaje office ɗin Doctor Emanuel sukai magana akan idan ta farka ya sallame ta zebar driver ya kaita gida.
*
Bayan tafiyarsa da awanni biyu da mintina talatin da biyar Jamila ta buɗe idanunta. Nurse din dake zaune tai mata sannu tare da zuwa ta kira likita yazo.
Ya ƙara dubata ya tambayeta abinda take ji tace ba komai. Akaro na biyu yayi mata congratulations.
Kamar wanda mutuwar ɓarin sashin tinani ya kama haka Jamila ta zama. Ta ƙame tana jin wani abu da bata taɓa jin irin saba na saukar mata atsakiyar filin zuciyarta. Idan ta ɗora abinda takeji akalmar tashin hankali kadai ta rabasa da ma'anarsa gabadaya. Wannan wani abune da ita kadai zata fahimta sai ko macen da ta tsinci kanta a irin yanayin.
"Muje na rakaki ki hau mota."
Nurse ta fadi ganin Jamila batada niyyar motsawa ta sauko daga gadon.
Tasan ko ta buɗe baki muryanta ba zata fito ba. Natsuwa ke bama ƙwaƙwalwa daman sanin abinda ya dace da jiki. Ƙwaƙwalwan Jamila ta rasa wannan natsuwar shiyasa take taka ƙafarta lafiya ƙalau batareda ta gane babu takalmi aƙafar taba.
Baicin Drivern yana tsaye ne ajikin motar shi ya tarbesu da yaga fitowansu da ba makawa sai Jamila ta bama watannan nurse din wahala kafin su gano motar.
Suka shiga motan suna tafiya asannu yayinda Jamila ke jin gine abayan kalaman da likita ya gaya mata.
"Madam...Madam .....Madam .....mun iso."
Driver yake fadi akaro na bila'adadin yana buga seat.
Jamila ta ɗago ta kallesa. Ta sanya duk ƙarfinta ta ɓalle murfin motan ta fito.
Kai tsaye bedroom dinta ta shiga. Tana zama taji anbude ƙofan an shigo. Tun kafin ta ɗago kanta take jin kaifin idanunsa akanta.
"Explain it"
Kalmar farko ta maganar Samir tai mata amsakuwwa da ƙararrawar tashin hankali acikin kanta.
A wasu shekaru can baya kalmar 'explain' wato bayani kalmace da take matuƙar ƙauna. Idan malami yace tai mai bayanin ma'anar abu gamsashshiyar cikakkiyar bayani kuwa takeyi. A lokuta da dama takan juya fuskar tambayan ga masoyanta da suka zo cikin wankakkun sutura, suna ƙamshin tiraren daya kasa gusar da warin talaucin dake jikkunan su.
"Ta ina zata soma ma Samir bayani?!"
Tambayar ta dira afilin zuciyar ta. Ƴan hanjinta suka yamutsa suna bada sautin dake bayyanar da tsaka mai wuyar da take ciki.
LAIFIN DAƊI ƘAREWA
Jama'a anan muka kawo karshen book one na littafin kyaure kariyar gida.
Baku buƙatar na fada muku wannan shimfida kawai mukayi a labarin batareda munyi sharan fage ba balle mu tsunduma acikin kogin rayuwar su.
Tarin zaƙwaƙuran tambayoyin da suke sargafeda zukatanku a ƙarƙashin alƙalamina sunada tarin yawa kadan daga cikinsu akwai
......wani madafa Zainab zata kama bayan bangon data jingina dashi ta kirasa abokin rayuwarta ya watsar da ita atsakiyar titi batareda yabar mata linzamin kamawa ba.
......shin har yanzu tanada ƙarfin cigaba da zama ƙyauren gidanta ko ko ƙyauren ya gaza ya kaima rushewa ta hanyar da komai zai iya samun iyalinta da take karewa da dukkan rayuwarta?!...
...... shigowar Zaliha cikin cikin gidan Zainab laifin waye? Kuskuren Zainab ne?!...laifin Ahmed ne?!!...
...... ayanzu Zainab zata iya komawa ga ahalinta ko zata cigaba da zama ƙyaure kariyar gidanta ta wata fuskar?...
......shin wacece Zainab? Meye asalinta? Wani irin kuskure tayi abaya da sadaukarwa ga Ahmed arayuwa?!....
KOWANI ZAƁI YANADA SAKAMAKO
...... Jamila tayi zaɓi arayuwarta. Shin har yanzu tanada damar kuma yin wani zabi arayuwar ta?...
......waye zai ɗauki nauyin cikin jikin Jamila? Samir ko Raihan? Ko kaddara da zabi?!....
......soyayya itace jigon rayuwa. Tanada dadi idan aka lashi zuma. Tanada ɗaci idan ka tadda maɗaci. Akwai bayyananniyar gamsashshiyar gagarumar soyayya mai ƙarfi atsakanin Ustaz Rayyan da Jamila.
.......meya faru a rayuwar aurensu?...
......meye ainihin musabbabin rabuwan aurensu?!....
......wata kaddara ce ke jiransu agaba?!...
ZUCIYA KAN ZAƁI ABOKIN RAYUWARTA BATAREDA TA TSAYA JIRAN AMINCEWAR MUTUM BA.
......ga Ustaz Rayyan ga Aliya....ga soyayya...ga rikici...ga zabi.
......shin Ustaz Rayyan ze iya kare kansa ga Aliya?...
......ze bayyana mata abinda yake cikin zuciyarsa ko zai cigaba da ɓoyewa?...
......kun hango min wata sabuwar kaddara mai zafi arayuwan wadannan ma'auratan?...
#Rikicin soyayya
#Rikicin zumunci
#Rikicin kaddara da rayuwa.
Kyaure Kariyar Gida book two na jiran ku akan farashi 1k kacal.
Zaku biya kudinku ta wannan details din:
***
Hindatu Auwal.
Opay.
Ki screen shot na shaidar biya ki turomin ta wannan numbern ***
#sakonku ta dabance yan kyaure kariyar gida comments section. Soyayyar ku daban. Ƙaunarku daban. Matsayin ku daban. Ina matuƙar jinku acan ƙasan zuciyata fiyeda yanda kuke jina anaku zukatan.
Se mun hade a book two.
TAKU HINDATU AUWAL
AMANAR SADI-SAKHNA 😘