NI DA YA NABIL

007

by @swrites22


_ NI DA YAYA NABEEL _


  _YOUNG WRITER✍️



* 007 *



Yana fitowa ya samu Jumayma ta takure jikin bangon gado sai zare Ido take, dariya taso bashi amma ya share, mamaki kawai yake ashe akwai abinda zai tsorata jumayma har haka, lalle asum ta ciri tuta. Bai ce da ita komai ba ya karasa ya shirya sannan ya juya zai fice, da gudu ta sauko ta tare shi haɗi da riqo rigar sa. Ƙara hade fuska yayi dan bayasan ta kara sa masa ciwon kai a wannan lokacin, "Sakeni". Ya fada muryarsa ba alamun wasa. 

Sakin nasa tayi tare da fadin, "Ni dai whl baza Ka barni da mahaukaciyar matar nan taka ba, saidai duk Inda zakaje muje tare".

"Ba inda zani dake, ki koma ki zauna kuma ki kama kanki in ba haka ba duk abinda ta miki ni ba ruwana".

"Ni dai whl ba zan zauna ba". Ta sake faɗa tana turo baki. A tsawace ya ce, "Zaki bace min da gani ko yaya?". Da sauri ta bashi hanya ta koma in da ta taso.

Garden ɗin gidan ya nufa ya zauna tare da fadawa duniyar tunani, ya daɗe a wurin har sai da dare ya raba kafin ya tashi ya koma ciki. Bai nufi ɗakin sa ba saboda yasan Jumayma na ciki kuma yasan damuwa zata ƙara masa kawai, sai ya wuce ɗayan ɗakin, har ya kwanta sai kuma ya miqe ya nufi ɗakin Asum. Tana zaune gaban mirror daga ita sai wani dan fingilgilin towel, mai take shafawa amma hankalin ta yayi wani wurin, ta kasan ido yake kallon ta har ya karasa bakin gadon ya zauna ba tare data lura da shi ba. Tashi tayi ta nufi gaban wardrobe ta fito da kayan da zata sanya, a hankali ya janye idanunsa ganin tana kokarin sakin towel ɗin. Ita kuwa ko a jikinta bata ma san yana yi ba ta saki towel ɗin ta shirya cikin silk pajamas pink me touch din milk, sun mata kyau sosai, sun bi kyakkyawar surar jikinta su kwanta, saidai kana kallon fuskar ta zaka fahimci tana cikin tsananin damuwa.

 Juyowar da zatayi kawai idanunta suka shige cikin nasa, saurin dafe kirjin ta tayi tare da runtse idanunta jikinta ya ɗau rawa dan ba ƙaramin tsorata tayi ba ta yi tunanin ma gamo tayi. A hankali kuma ta bude idanun ta sake kallonsa kafin ta sauke ajiyar zuciya ta nufi hanyar fita, kamar walkiya haka ta ganshi a gabanta, keɓewa tayi zata wuce shi, amma sai ya matsa ya yi locking ƙofar haɗi da jefa key a aljihun sa, kamar Wanda akawa dole yace, "Koma ki zauna muyi magana".

 Ba musu ta koma Kan sofar dake dakin ta zauna, shi ma zama yayi yana facing din ta, ganin ya sata a gaba yayi shuru yasa ranta kara ɓaci, a kufule tace, "Me ya kawoka ɗaki na? ko zuwa ka yi nima Ka shirga min karyar daka saba ne, tunda nan kafi karfi". Shuru yayi yana kallonta da mamaki, ita kuma ta cigaba, "Ni dai baka isa ka yaudare ni da kalaman bogi ba. An kuma ji kunya whl tunda gulma da dauke dauken magana ya fara tashi daga kan dankwali ya koma kan hul....". Tsawar da ya daka mata ya sata yin shuru ba shiri, ta takure jikinta. 

"Sa'an wasanki ne ni? wai ko dan kinga ina lallabaki, baki sanni ba ko?". Sai kuma yayi shuru yaja kwafa.

A yadda take ba tare data motsa ba cikin tsiwa ta sake fadin, "Ahhh lalle Ya Nabeel, To whl sai na kira Baffah naji dama an aura min wanda ba Sa'a na bane dan yazo ya dinga zalinta ta". Tarar numfashinta yayi da faɗin, "Kinga, ki dinga tausa harshen ki yayin magana dani. Ni zuwa nayi muyi magana ta fahimta ba wai ife² da hayaniya ba". Ya faɗa calmly.

"Inaji". Ta amsa tana hararar sa kasa ². Sai da ya nisa kafin yace, "So nake ki bani dama na gyara kuskurena na baya, sannan ki sani duk abinda kikaji Jumayma ta fada tayi hakan ne kawai dan ta fusata ki, kuma gashi nan tayi nasara tunda gashi ta birkita ki tasa kina gayamin maganganun da basu dace ba, har kina kirana da sunaye masu muni wanda ban cancance su ba. Tunda mukazo ƙasar nan kin taba ganin na shiga fadanku, in dai ba naga kuna ƙoƙarin illata kanku bane. Karki manta kema fa matata ce, taya kike tunanin zanje in fadawa Jumayma wani abu marar kyau game da ke bayan nasan auran mu auran zobe ne, in dai ba wata qaddarar Allah ba ai babu batun rabuwa. Ki sani ba zanso tashin hankali a gidana ba, wanda kuma in dai na kasance mai Kai maganar wanna wajen wanna to dole fitina ta samu matsugunni cikin gidana, kiyi tunani sosai ni ba mahaukaci bane da zan dinga hada matana fada, sannan ki sani Jumayma kishiyar kice ba kowace magana zata fada ki hau kai ki zauna akan lalle haka take ba ki dinga tace abun da yake gsky da kuma qagagge, saboda akwai kishi a tsakaninku". Yana gama fadin haka ya tashi ya nufi kofa ya buɗe ya fice.

Shuru Asum tayi tana tunani, kwarai zafin zuciya ya rudeta bata tsaya zurfafa tunani ba. To me ma ya shiga kanta da har ta tafka irin wannan wawancin? Take taji wata kunya ta lullube ta, kalaman data dinga jifan sa dasu ɗazu ne suka shiga dawo mata, ji tayi kamar zatayi kuka, in kuwa hakane dole ta koyawa Jumayma hankali wato so take ta hadasu. Kwafa taja ta tashi ta haye gado ta kwanta, da wannan tunane² bacci yayi awun gaba da ita.

Washe gari tunda sassafe ta fice scul bata dawo ba sai la'asar lis, a gurguje tayi wanka ta fesa kwalliya kamar wata sabuwar amarya, fita tayi dan ta hango Nabeel ta window ɗakinta yana zaune a garden yana aiki. Tsayawa tayi a dinning taci abinci sannan ta shige kitchen, a gurguje ta dauki ragowar tamarind ɗin data siyo rannan a kasuwar yan hausa dake a nan Russia din, ta gyara ta haɗa tamarind juice me musulmin daɗi, ta zuba kankara a ciki sannan ta juye a wani ƙaramin jug mai kyau, ta ɗaura kan ƙaramin tray ɗin jug ɗin ta sanya tumbler sannan ta ɗauka ta fice, ta nufi garden ɗin.

Da sallama ta ƙarasa cikin hut ɗin da yake zaune, ta ɗaura tray akan ƙaramin table ɗin dake wurin sannan ta zauna tana faɗin, "Sannu da aiki". Ta faɗa a ɗan ɗarare. Sai a lokacin ya ɗago, kallo ɗaya ya mata ya maida kansa ga aikin da yakeyi ba tare da ya amsa mata ba. 

Gabanta ne ya shiga faduwa, a ranta kuwa faɗi take mutumin nan sai kace mai aljanu kamar bashi bane jiya yake ta sunkui da Kai yana roqon kar na fadawa su Baffah abinda ke faruwa. Hmmm ta sauke numfashi kafin ta karya harshe tace, "Eyyerh yayana ka yi haƙuri ka yafe min, nasan nayi ma laifi amma na gane kuskure na whl, bana so Kana fushi dani kaga bani da kowa anan kai ne mamana Kai ne babana Kai ne kowa nawa dan Allah karkayi fushi dani, whl gidan ba zai min daɗi ba Ka yafemin na tuba na amsa laifina, na bi Allah na bika bazan Kara ba".

"It's Okay". Ya fada ba tare da ya dago ba. "To ga tamarind juice, da kai na na hada maka". Shuru ya mata, har ta fidda ran zai yi Magana sai kuma ta ga ya kai hannu ya ɗauki tumbler ɗin ya miqa mata. Ai bata san lokacin da bakinta ya furta, "Thank you". Ba. Shi kuma ya dago ya zuba mata ido yana kallon yadda take rawar jikin zuba masa juice ɗin. 

Karba yayi bayan ta gama zubawar, ya kai baki ya kurba yana binta da kallon wutsiyar ido da ya sata yin ƙasa da kanta tana murza yatsun hannunta, kusan 5 minutes suka ɗauka a haka, kafin ya ɗaura tumbler a kan table ɗin ya maida hankalinsa ga aikinsa. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗago tace, "In ƙara ma ne?". Jinjina mata kai yayi kawai alamar eh. Da sauri kuwa ta sake zuba masa. Shuru ne ya sake ratsawa shi yana aikinsa, ita kuma tana kallon tsuntsaye da ruwan pool ɗin dake wurin, time to time tana kallon aikin da yake yi wanda ta kasa fahimtar komai a ciki.

Kamar daga sama ta tsinkayo muryarsa na fadin, "Kin shirya zaman auren ne?".

"Ehh?". Ta faɗa a ɗan rikice kamar wata marar gsky, tsayawa yayi da abinda yake ya sake dagowa ya zuba mata ido. Kame² ta shiga yi kafin tace, "Dama dama ni ai zaman aure ne ya kawoni ƙasar nan, in ba haka ba ai ba zan bar iyayena da dangina ba na taho wata uwa duniya". Girgiza Kai yayi ya dan kalli takardun dake gabansa kafin yace, "Zuwan da kikayi da niyyar ki kashe auren ki bawa sister ɗinki dama shi kike Kira zaman aure?". A wani irin sukwane ta kai kallonta gare shi. Girgiza kai ta shiga yi, murya na rawa ta shiga faɗin, "Ah aa ah ba ba haka bane".

"Karya zan miki Kenan?". Da sauri tace, "Ahh ahhh whl ni ce dai nayi karyan".

"Hmmm, baki san duk wani abun da kikeyi kallon ki nake kawai naga iya gudun ruwanki ba? Karki dauka ban sani ba nasan komai. Kuma nasan yanzu haka zancen auren su yazo miki Shiyasa nake son sanin ke yanzu kin shirya zaman naki gidan auran ko har yanzu da saura, dan ni mai binki ne a duk yadda kike so". Ya faɗa ba alamun damuwa a tattare dashi.

Jikinta ne ya hau rawa ta zame daga kan kujerar da take zaune, ta yi kneel down a gabansa, "Dan Allah Ya Nabil ka yi haƙuri kar maganar nan taje kunnen su Abbah, ni...". Daga mata hannu yayi tare da faɗin, "Ba abinda na tambaye ki ba Kenan, shin kin shirya zama cikakkiyar matar aure kamar ko wace mace? Kin shirya farfaɗo da rayuwar auren ki?". Kasa tayi da kanta tana harhaɗa Maganganun kafin ta yi ƙarfin halin faɗin, "Kayi hakuri Hamma, ba rayuwar auren bace ban shiryawa ba, rayuwa da mijin auren da bana gabansa ce nake tsoro, Ka sha faɗi ni zabin su baffah ce Jumayma itace zabin Ka, ina tsoron Ka kasa adalci tsakanin mu Allah ya tambayeka akan hakan, tunda ita kake so, ita ce zabinka". Ta kawar da batun Naseem cikin dabara. Kurbar tamarind juice ɗin ya sakeyi kafin ya miqe ya tattare kayansa ya nufi hanyar barin wurin yana faɗin, "Bayan sallar isha ki sameni a falo na". Yana faɗin haka ya ƙarasa barin wurin.

Da sauri ta miqe tana share zufar da bata san lokacin da tayi ta ba har wani murdawa cikin ta yake, "Wash Allah na, Allah ka taimakeni ni dai, ni anya mutumin nan baya aiki da jinnu kuwa? To ya akayi ma yasan wannan zancen? Kai na shiga uku ni Assumi, Allah yasa ba saki na zaiyi ba. Ta samu kanta da yin wannan addu'ar dan ta san whl Abbah zai iya tsine mata idan har Nabil ya saketa kuma yaji dalilin sakin, kai ko Umma ta san sai tayi farfesun ta a gidan nan. Oh ni ina zan sa kaina, ah ah hakuri zan cigaba da bashi whl. Gabaɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye sai zagaye wurin take tana sambatu ita kaɗai, karshe dai ta koma ciki ta wuce dakin ta da gudu, kan gado ta faɗa tana haki kamar wadda aka biyo.

Kamar yadda ya faɗa da daddare bayan tayi sallar isha wanka tayi ta fito ta zauna ta mulke jikinta da mayuka masu kamshi sannan ta bisu da haɗaddun turarukanta, kafin ta tashi a sanyaye ta nufi wardrobe ɗinta ɗan samo kayan da zata sa cox har lokacin gabanta faduwa yake. English wears ta ɗauko zata sa amma sai wani tunani yazo kanta, ita a iya ganinta da Jumayma ai ko a nigeria bata taba ganinta da shigar hausa ba kullum cikin yan bingilallun kayan nan take. Murmushi tayi tare da ciro wani sequins ombre lace red and black dinkin fitted gown, ta shirya cikinsa duk da kuwa daƙyar rigar ta shige ta saboda kibar data kara amma kuma yabi jikinta sosai ga colour ya haskata. Simple make up din ta tayi ta dauki karamin gyale baki ta yafa akanta ta ɗauki orbit chewing gum ta wurga a bakin ta sannan ta sake wankan turare ta saka takalminta me tsini ta fita, saidai duk takun da zatayi daidai yake da bugawar zuciyar ta dan bata san me zataje ta tarar ba .

 A falon nasa ta samesu, suna zaune kujera daya manne da juna kamar yadda suka saba, kamar yadda dai tayi tunani Jumayma sanye take da mini skirt da wata top da ko cibiyar ta bata rufe ba .

Takun takalmin ta yasa su dagowa dan in dai ta iso waje kafin tayi magana suke shaida isowar ta bare kuma yanzu data daura dammarar shawo kan mijin nata shiyasa takun yau ma na dabanne. Sallama tayi cikin wata irin sassanyar murya da ita kanta bata san tana da irin ta ba, bude baki Nabeel yayi zai amsa sallamar tari ya sarqe shi. Sosai yake tarin, tashi Jumayma tayi a rikice ta nufi water dispenser dan samo masa ruwa.

 Dukda yadda take a cikin fargaba haka ta ɗaure ta ƙarasa ta zauna kusa dashi inda Jumaymah ta tashi, hannunta dake rawa ta kai kan bayansa ta shiga bubbugawa a hankali tana hura masa iskar bakinta tare da masa sannu. Suman zaune Nabeel yayi lokaci guda tarin ya faɗa, sai kawai ya zuba mata Ido kamar yau ya fara ganin ta, ganin irin kallon da yake binta dashi yasa a kunyace ta janye hannunta tana kokarin tashi, kamar daga sama sukaji an wanke su da ruwa. Jumayma ce tsaye gaban su sai huci take riqe da tumbler din ruwan data tsiyayo wa Nabeel din, dakyar ya iya bude bakin sa yace, "Wai meysa baki da hankali ne Jumaymah, haba da Allah kullum a dinga abu ɗaya".

 A fusace tace, "Bani da hankalin Nabeel, kaji? nace bani da hankalin ka sammin naka. Kai ko kunya bakaji ba dubi kanka fa ka dubeta, kai amma girma ya fadi whl. Ke kuma na dawo kanki shegiya tsohuwar alakwankwan". Ta fada tana kamo wuyan rigar Asum ta fisgota da karfi. Daga in da yake bai motsa ba yace, "Na rantse da girman Allah Jumayma in baki saketa ba yau zan mugun saba miki". 

Kallon sa tayi kafin ta hankada Asum din. Tagal² tayi zata fadi saboda takalmin kafarta da kuma santsin tiles da ya ɗibeta, cikin zafin nama ya tarota ta fado kan kirjinsa, wani kukan kissa ta saki dan ta ƙular da Jumaymah. Sai kuwa ya kara rungume ta, cikin fada yace, "Whl whl whl kunji na rantse ko, duk wadda ta sake kawo min tashin hankali a gidana sai nayi maganin iskancin ta, dan ku sani ba fin karfi na kukayi ba tunda duk a karkashina kuke. Ki kuma koma ki zauna magana zanyi daku". A sanyaye Jumayma ta nemi wuri ta zauna tana mamakin yadda Nabeel din ya juye lokaci guda .

Zaunar da Asum yayi sannan shi ma ya zauna tare da faɗin, "Dan Allah kimin shuru kema". Tsitt Asum tayi kamar anyi ruwa an dauke dan dama ba kukan tsakani da Allah bane. Tsaki ya ja kafin ya fara magana, "Ke jumayma kin sani Asum matata ce kuma ita ma na fara aura kafin ke, dan haka a yanzu zan fara raba muku kwanakin ku dukda kuwa hakan ya kamata ayi tun farko to amma saboda wasu yan dalilai na jinkirta hakan, in a nutshell dai kawai kar muje da nisa da farko zan mata sati gudan ta sannan kuma zan ringa muku kwana uku uku, sannan ba wadda zan dinga bi daki kowacce ke da kwana zata zo bangare na ne ta sameni. Akwai mai magana?". Rasa mai cewa wani abu akayi dan Jumayma ta shiga tsakanin shock, mamaki take shin anya Nabeel ɗin ta ne kuwa, bata Kara tsinkewa ba saida taji ya sake fadin, "Gobe zanyi tafiya germany wani aiki tunda tafiyar ta fada a kwanan Asum zan tafi tare da ita".

Ya juya wajen Asum ɗin, "Ki shirya gobe around 10am". Yana gama fadin haka ya miqe. Da sauri tace, "Ya nabeel to scul din fa?". Wata harara ya wurga mata ba shiri ta kame bakin ta. Sai da ta ga ya shige kafin ta sauke ajiyar zuciya ta tashi ta bar falon. Ita kuwa Jumayma sai a lokacin taji wani kuka yazo mata, cilli ta ringa yi da duk abinda ta gani sai da ta gama hayagagar ta ita kadai sannan ta tashi da gudu tana kuka .

Daki ta bishi tana kuka da surutai marassa kan gado, shi dai girgiza kai kawai yayi ya ƙarasa shirin da yake ya dauki wasu takardu ya fice daga gidan ma gabadaya a ransa yana fadin jin dadi ne ya muku yawa, Ku dai mata in anaso aga ruwan bala'i kankarar masifa to a hada ku da kishiya ko ayi zancen ta, baku da wata damuwa data wuce haukan kishi.