MATAR SALMAN

Chapter One

by @hauly3030

*đź’«MATAR SALMANđź’«*

Daga Alkalamin: Hauwa Salihu


➡Part One

P1

🌹 _TSOKACI_ 🌹
 ***Kasancewar jiya ban samu nayi bacci ba gabadaya, shiyasa ina idar da sallar Asuba ban san sanda bacci barawo ya saceni ba, daga zaunen nake bacci na sosai.
Buga kaina da nayi a jiki drawer shi ya tashen na dafe kaina da yake mun ciwo dama ga damuwa ga rashin bacci .
Kama kan nayi da karfi ina karanto addua.....
Bansaki kan ba naji kamar horn din motarshi.

Ban San sanda na saki kaina na mike da sauri na tafi window, kasancewar window din bedroom dina tana facing harabar gidan.

Ina daga labule Rass! Zuciyata ta tsinke, lokaci guda mamaki ta lullubeni.
Naji wani irin bacin rai da bakin ciki kamar na hadiye zuciyata.

Da sauri na fita daga dakin na nufi harabar gida ko ganin gabana banayi da kyau tsabar bacin rai.
Can na hangoshi ya fito gabadaya sojojin gidan sun zo suna kwasan gaisuwa.

Da sauri na nufi can wurinshi a lokacin da ya juyo shi kuma bayan sun gama gaisheshi sun tafi. ya bude gaban motarshi.

Bansan sanda na tsaya na saki baki ina musu kallon mamaki ba.

Itama ni take kallo daga fitowarta fuskarta daukeda tsoro da fargaba .

Ganin yadda muke kallon kallo yasa shi riko hannunta a hankali suka nufo inda nake ka min su karaso tuni na daga musu hannu ina kara tamke fuskata. Na kalleshi cikin tsantsar mamaki da ɓacin rai nace" me zan gani kuma?Nafisa a gidana?

Fuskarsa ba yabo ba fallasa yace min "Haka ne, Nafisa ta dawone.”

Na zaro ido hade da fadin ”what! ....Wlh bazai yiwu ba, wannan karon bazan dauki iskanci da rainin hankali da aka mini a baya ba bari kaji ni bazan zauna da Nafisa a gidan nan ba.”

Na nunata da yatsa hawaye na zubo min na kalleshi nace ”Ko ka mance ne in tuna maka? ....Wata daya da suka wuce aka kawota gidan nan a matsayin amaryarka, kawai daga shigarta daki ta yanki jiki ta fadi ta suma, 'yan uwanka suka sakoni a gaba da zagi ciki harda mahaifiyata da bataji ba bata gani ba, sukace mu mukayi tsafi don mu wargaza aurenka da Nafisa.”

Hawayene masu zafi suka gangaro bisa kumatuna na ce "jiya jiyan nan aka kai maka ita a gidan ka na Abuja ta tare, mukayi sallama da kai ka tafi, sannan yau ka daukota kuyi sammako kuzo min gida kace ta dawo?”

Ko kallo ban ishe shi ba ya kalleta yace ”ke shiga ciki ina zuwa.

Ta wuce sum sum jikinta a sanyaye na bita da kallo har ta shige cikin gidan.

Sannan na dawo da kallona gareshi ina share hawayena nace ”shikenan tunda haka ka zaba ni zan bar maka gidan ka yanzu ba sai anjima ba, kaje ka zauna da matarda mahaifiyarka da 'yanuwanka suka zaba maka.”

Wucewa yayi ba tare da yace min komi ba.

Kamar zan fashe don bakin ciki nayi ciki a zuciye ba ɓata lokaci dauki jakata da wayata da key din motata. Juyawan da zan yi sai ganin mutum nayi tsaye ya zuban ido fuska daure.

Ban kulashi ba na saka takalmina na karaso bakin kofan ba tare da na kalleshi ba nace ”Zan wuce.”

"Ina zakije? Ya fada can kasan makoshinsa.


Banza na masa. Juyawa yayi zai fita yace min ”Salim yazo da Farida suna palona.”

Daga nan ya fice


Zuciyata ce ta buga nace Farida da sassafen nan kuma Ya Ilahi me ta ballo kuma?” Wayyo Allah da wanne zanji ni RUMAISA?

Na ajiye jakata na tafi side dinshi a Palo na samesu suna zaune shiru Farida na zaune a kasa kanta a sunkuye.”

 Na karaso na zauna jikina a mace na kalli Salim nace "Ya Salim ina kwana?

Cike da kulawa ya amsa min ”Lafiya RUMAISA ya karfin jiki?”

Nace ”Alhamdulillah

Shiru ya biyo baya daga bisani ya Salim ya gyara zamansa yace ”To kun ganta nan duk yadda naso ta zama mutum abin ya faskara, RUMAISA ke kam kinsan komi gameda halin ta dama Salman Kaine muke boyewa saboda gudun zuciyarka amma yau an wayi gari Fareeda da kanta tace min in dawo da ita gaban iyayenta wadanda suka haifeta, don bazata iya ci gaba da zama a gaban mu ba. Ba wai na dawoda ita saboda maganarta bane.... A'a kawai na kawota ne domin duk musan halinda take ciki sannan mu samo mafita a tare, zan kuma barta anan saboda hankalinta ya kwanta kafin ta koma Abuja.”

Zaro ido nayi na kalli Farida da mamaki nace "Fareeda dama rashin hankalin naki har ya kai haka bansani ba?.....Wai shin Yaya suwaye suke hure mata kunne ne haka?”

Salim yaci gaba da fadin ”hmm kamar dai yadda kika sani kawaye ne da samari, sai Farouq da yafi kowa hura mata kunne, Rumaisa maganar da nake miki jiya har karfe dayan dare na ganota a wurin club suna tare bayan duk tsaro da na sa akanta sai da tasan yadda tayi tayiwa momynsu wayo ta fice. jiya gaba daya bamu yi bacci ba dan tashin hankali. na tambayi Fareeda me takeso a rayuwa in mata don ta rabu da Farouq......

Sai a lokacin yayi magana ta hanyar katse ya Salim da faɗin ”Waye ne Farouq din?”

Yayi tambayar ne yayinda ya dauki Kofin ruwa dake gabansa yana sha.
Salim ya danyi shiru cikeda bakin ciki sannan yace ”Humm Farouq ɗane ga Alhaji Ahmad umar ministern Ab.....”

Tuni ya kware ya kama tari babu kakkautawa

Nikam na kara zaro ido a tsorace gabana na faduwa don koni ban taba sanin Farouq ɗan Ahmad Umar ba ne sai yau.”

Kamar da wasa tarin sai tsananta yakeyi ya Salim ya mike da sauri ya isa wurinshi
"Sannu don Allah karka daga hankalinka kan wannan maganar.”

Hannu ya daga masa sannan yace ”ba komi.”

A hankali fareeda tace ”Sannu daddy.

Ya dago jajayen a fusace idanunsa ya watsa mata su sannan yace ”zo nan!”

Ta mike ba tare da fargaba ko dar ba don tasan yana matukar ji da ita baya son ɓacin ranta duk zafin sa.

Ta karaso ta zauna kusa da kafarsa.

Ya fara magana cikin sanyin murya amma akwai fushi "Fareeda haka kika zama? Me yake damunki? Menene kikeso a miki?”

A shagwabe ta fara magana tace ”Daddy ni bana son inje makaranta, bana son ci gaba da karatu, ni zan yi aure ne....

Nikam na bushe a zaune dan tsabar mamaki da tsoran Farida da ya shigeni lokaci guda.

Yace ” Hmm waye ne wanda kike so kuma kuka shirya maganar aure a samarin naki?”

Kai tsaye tace ”Daddy Farouq ɗin ne.......

Ya mike tsaye a fusace idon nan ya kara yin jazir yace ”Fareeda ni bazan yarda ɗan wajen Ahmad ya aureki ba koda kuwa babu maganar aure tsakaninki da Munir, bare kuma kin gama amincewa Munir kike so har mun tsaida magana akan in ya dawo daga kasar waje za'ayi bikinku.don haka bazanyi magana biyu ba, don ni ba mutumin banza bane. Farida ko kiso ko ki ki Munir shine mijinki...Sannan kinga wannan?

Ya nuna ya Salim yace ”Ɗan uwana banda kamarsa duk duniya, duk abinda kika masa tamkar ni kikayiwa, idan kin masa biyaiya kamar ni kikayiwa haka nan idan kika saɓa masa kamar ni kika saɓawa, naji kince don ba shi ya haifeki ba to bari kiji duk duniya bakida Ubanda ya wuce Salim! Ina so ki sani akan Salim zan iya rabuwa dake. Don haka se kije ki nemi wani uban bani ba tunda kince Salim ba mahaifinki bane, baida iko akanki.”

Tunda ya fara maganar kuka takeyi, bata taɓa tunanin abubuwa zasu juye haka ba, tabbas ta tafka kuskure, son Farouq ya rufe mata ido.

Ta durkusa gabanshi tana ”Daddy don Allah kayi hakuri ka yafe min na tuba, wallahi na gane kuskurena.....

A fusace ya bugeta da kafa ya fice ciki.

Ta na kuka ta mike ta iso gabana ta durkusa tace ”Mama don Allah kuyi hakuri wlh ......

Tsaki nayi nace ”Dallah tashi gabana mara hankali me zakice min kuma? To bari kiji ina bayan mahaifinki dari bisa dari.”

Tana kuka ta juya gun ya Salim tace ”Dada don Allah kayi hakuri ka yafe min.”

Dagota yayi yace ”Na yafe miki fareeda Allah ya shiryeki.”

Sannan ya mike yace ”Ni na tafi.”

Nima na Mike nabi bayansa  

A bakin kofa mukayi kicibis da Nafisa bata ce mana komai ba ta wuce ciki na bita da kallo sai naga ta wuce direct dakinsa.
Wani irin kishi naji to waye nuna mata turaka bayan dazu tazo?

Tabe baki nayi.

 Bayan ya Salim ya tafi na dawo dakina na rasa me yake min dadi a rayuwata ta duniya ni RUMAISA, ya zama dole ne kawai inje in sameshi domin mu tattauna maganar fareeda musan yadda zamu É“ullo ma lamarin.

Na tashi na fita, A babban Palo na tarar da khalilullah yana kallon ball.
Yana ganina yayi murmushi yace ”Mama ina kwana?”

Nace ”Lafiya Babana ina ka shiga tun da safe ban ganka ba?

Yace ”Na tafi gidansu Innah ne a can nayi breakfast ma.”

Na gyada kai nace ”Yayi kyau Babana, jeka duba min Daddyn ka yana Palonsa ne?

Yace ”to”
Sannan ya mike ya tafi ba'a jima ba ya shigo yace ”Mama yana nan.”

Nace "Nafisa fa?”

Yace ”Aunty Nafisa dazu ta wuce kitchen.”

Nace ”to ina Fareeda?”

Yace ”Na dai ganta ta fita dana tambayeta tace zata kai karar Daddy gun Innah, Mama me ya sami sister ne naga tana kuka?”

Na danyi shiru sannan nace ”Maganace mai tsawo kar ka damu ina zuwa.”

Na wuce palonsa. A zaune na sameshi yana waya da abokan kasuwancinsa na sami guri na zauna har ya gama.

Ya zuban ido yana jiran jin mezan ce.

Na sauke ajiyar zuciya nace ”Nazo ne mu tattauna yadda zamu bullo ma lamarin Fareeda kamin yafi karfinmu.”

Ya danyi shiru kamar bazai tankani ba sai kuma yace ”Ina jinki.

Na gyara zama nace ”Ni a ganina gara a bar ta tayi auran ta auri Farouq din tunda akansa ne take wannn......

A fusace ya katseni da fadin ”Lallai ba yarda bakida hankali. kina tunanin cewa ni SALMAN zan dauki 'yata ta cikina in bawa Dan Ahmad aurenta?......To bari kiji ni na yanke hukunci koda zatayi aure yanzu to Munir ne zata aura bare ma kuma makaranta zata tafi, ko tana so ko bata so har sai m
Munir ya dawo.”

Nace "Yaran nan fa na zamanin yanzu daban suke da na da, tunda kaji ta bude baki bataji kunya ba tace maka aure takeso a mata kuma ga wanda take so, to ka barta kawai karkace zaka tursasa mata domin watarana zata bijire mana.”

Kallona yake rai ɓace sannan yace ”zata bijire min mana, in dai mugun halinki ta dauka da banzar dabiarki........

Raina bace na mike nace ”Ya kake gaya min bakar magana hakane don kaga ina lallabaka?...... Ok to bari kaji ni ƴata aure zatayi kuma wanda takeso zata aura Farouq din dai tunda aure bai haramta a tsakaninsu ba, kuma ni a matsayina na uwa na gama yanke nawa hukuncin.”

Har na juya zan tafi yace ”tsaya!

Ya mike ya karaso gabana ya zuba min manyan idanunsa da sukayi jazir dan bala'i yace ”Sai yanzu na fahimce ki Rumaisa wato saboda Ahmad tsohon saurayinki ne yasa ka kike son ɗansa ya auri 'yarki ko?”

Takaicine ya cikani kawai nace ”Eh hakane sai me Salman? Tunda Mahaifiyar Farouq din ma Salima tsohuwar budurwar kace kaima don haka menene a ciki?”

Na juya zan tafi ya fincikoni da iya kacin karfinsa wani irin kyakkyawan riko ya min. Sai faman kokarin kwatar kaina nakeyi na kasa hawaye suka ciko idona na runtse idon saboda azabar matsar da ya min.

Murmushin mugunta yayi yace ” Ina fatan yanzun kin fahimci banbanci dake tsakanina dake Rumaisa?”

Ya sassauta min rikon yana kallona yace ”Ni ne nakeda ikon aurad da Fareeda ga duk wanda naso bake ba. Don ke kanki a karkashin ikona kike don haka bakida ikon zartar da komi a gidan nan, dole ne duk yadda na dama kowa yasha!”

Hawayene ya kara cikowa idona fal har ya fara saukowa don takaici.
Yana kallona yace ”Kina da wani abu da zakice kuma?”

Na girgiza mishi kai kawai.
 
Ya sakeni hade da fadin ”good girl haka nake so.”

Fita nayi na tafi daki kuka na kama yi kamar raina zai fita, na rasa meke min daÉ—i a duniya Ni RUMAISA.

Karar wayata ce na jiyo a kan bedside drawer ban kula ba har ya tsinke.

A Jere aka kira sau uku ana hudun na lalubo wayar ban lura da kowaye ba nayi answering.

Muryana a sarke nace ”Salamu alaikum.”

Muryar Inna na jiyo tana " To uwar makirai annamimiya ba sallamarki na ke bukata ba ki fada min me yasa kika ce Salman ya dawo da Nafisa Kano alhalin jiya jiya aka kai ta Abuja ?”

Cikin muryar kuka nace ”Inna bani ce nace ya dawo da ita ba nima jiya mukayi sallama akan sai bayan sati daya zaizo kano kawai sai gasu sun yo sammako.....

Ta katse ni da fadin ”dallah rufe min baki da zancen wofi, wai kawai ganinsu kika yi makaryaciyar banza to bari kiji na gaya miki idan kika kuskura ko ciwon kai Nafisa tayi sai kin gane kurenki wallahi, don haka ki kiyaye don hakane na kira ki. Sannan abu na biyu ga 'yarku nan tazo ta fada min komi wato bazaku mata aure ba sai ta yi karatun boko ko? .....To me karatun zai tsinana mata? Ke kanki lokacin da uwarki ta nace sai kinyi jami'a ina karshenta a karuwanci da shaye shaye kika kare ko an gaya miki na manta ne, to wallahi bari kiji ahir dinki daga ke har Salman Ku kiyayi fushina.”

Ka min nayi magana tuni ta kashe wayar.

Tirkashi!



 *RUMAISA SALMAN BY MAMAN KAUTHAR*